Showing 81001 words to 84000 words out of 104658 words

Chapter 28 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

213

salo alƙur'an”.
     Murmushi nai mata ina taɓe baki kaɗan, “Nikam minayi Amina? Kune dai kuke ganin nazo da sabon salon kawai, amma ina nan a Bilkisu na”.
      “Tab, inji wa? Wlhy kin canja sosai, kamarfa ba makaranta kikajeba yasin”.
      Murmushi kawai nai musu ban sake cewa komaiba.

       A ranar dai nasha labari wajen Amina, har rikicin da akasha tsakanin Aunty Shahudah da mijinta, da kuma barin ƙasar da tayi, nasha mamaki, naga kuma wautar su Dad a nan gaskiya, dan ni dai a ganina kamata yay su ɗauki hanyar gyara ɗabi'un yaransu musamman ma Shahudah da nake ganin tafi kowa nuna tsagwaron wayewar, amma gashi son zuciya ya sakasu sake dulmiyar da ita kuma,
     “ALLAH ya ƙyauta” kawai na iya faɗa naja bakina na tsuke.
    Da yamma Dad yace na shirya muje shopping, ban musaba kuwa nai shirina, ni da shi da Aamilah muka tafi.
     Koda muka isa sai ta katsatstsare itace zata zaɓamin komai, da farko na bata dama, amma danaga duk abinda ta ɗauka baiyi dai-dai da tsatinaba saina dakatar da ita ina zaɓa, dan ko kayan kwalliya saita dinga ɗaukar mayukan da zasu sakani fari, niko batasan ba farin nake buƙataba, wannan baƙin da basaso ni shine abin sona, fatar dai ta goge tayi laushi kawai ya wadatar, banyi zariba na ɗiba komai dai-dai misali, ko kayama da yace na ɗauka nace masa atanfa nakeso to, dan naga duk kayana na gida yanzu babu suturun malam bahaushe, niko ina zan iya rayuwa babu kayan gado.
     Bai hananiba yace na ɗauka, suma na ɗauki dai-dai musali mukaje Aamilah ta biya bayan ya ɗaukar mini waya shima muka fito.
     Naji daɗin wayarnan sosai, dan na tsinci kaina amatuƙar farin ciki bana wasaba.
     Na kumayitama Dad godiya da nuna masa farin cikina akan ɗauwainiyar da yakeyi dani, aduk sanda nake masa godiya idan ya saya min abu hakan na sakashi jin wani iri daban, yakanji daɗi kuma sosai a ransa, dan baisaba ganiba daga ƴaƴansa, basusan yay musu abuba suce sun gode, basu da laifi, dan tun farko ba'a nuna musu su godema wanda ya ƙyautata musuba koda a ƙanƙanin abune.

          Kwanana huɗu da dawo gidan nacema Dad zanje gidan Inna Zainaba, baiko hanaba yace mu shirya ni da Aamilah driver ya kaimu.
     Aiko wannan abu ya mata ciwo, dan masifa taitamin da muka tafi, saima tace mu sauketa a wani anguwa idan mun dawo mu biyo mu ɗauketa dan batai niyyar zuwa ko inaba, bazata wannan ƙazamar anguwar tasu Yaya Shu'aibu ba ta dawo ta kasa shan ko ruwa.
       Tausayima ta bani nikam, dan kuwa arziƙin da take tunƙaho dashi wanda ya bata bai manta dasu talakawanba da take kallo ba komaiba.
         Mun isa har ƙofar gidan, na shiga ciki da ɗokina ina kiran Inna.
       A tsakar gida na isketa tana ɓarar gyaɗa, tunda na shigo ta ɗora idonta a kaina sai fuskarta ta canja, dan kuwa na kula bataso ganina hakaba fes, ban damuba naje na rungumeta ina hawayen farin cikin ganinta, Lawisa dake ɗaki ta bankaɗa labule ta fito, daka ganta kasan barci takeyi, “Waye haka yake mana ihu a cikin gid....”
    Bata iya ƙarasawaba saboda tozali datai dani, ta wani taɓe baki tana jan tsaki ta koma cikin ɗakin.
       Murmushi nayi ina muƙewa daga jikin inna, na durƙusa har ƙasa na gaisheta, sannan naja kujera na zauna ina tayata ɓarar gyaɗar.
     Duk da bata sakarmin fuskaba mun ɗanyi hira, ananma ne nakejin ashe Yah Shu'aibu ya wuce ƙasar ghana karatu, na tayasa murna sosai, duk da naso muhaɗu shima yaga cigaban dana samu, amma dai inna ta bani Number sa dan Dad ya saya mata waya saboda suna waya da Yah Shu'aibun.
     Banbi takan Lawisa ba har na baro gidan, bakuma ta sake fitowaba itama har na taho.
     Biyawa mukai muka ɗauki Aamilah muka wuce gida, bankuma faɗama kowa ba tare mukaje ba.

       Amina na tambaya ko akwai islamiyya a anguwar? Tako tabbatarmin akwaita, bazan iya zama hakaba, nako samu Dad da maganar inason shiga islamiyya tunda ta yamma sukeyi, shima bai hananiba, yace tom na binciko yaya abun yake?.
     Tare da Amina mukaje, ta haɗani da yayanta da shima anan yake koyarwa, komai yay mana bayani na tsarin islamiyyar, nima nazo na sanarma Dad.
   Sai cewa yay to itama Aamilah taje mu shiga tare mana da zaman banzan da takeyi.
     Ai tunma Dad bai kai ƙarshen zancenba tai tsalle ta dire akan bataso, ita da zata bar ƙasar ta koma karatu miye na wahal da kanta shiga cikin kucakan yaran nan wai wani karatu kuma, ai dai ta iya na salla (Ita a nata tunaninma na salar kawai ake buƙata ta iya🤦🏻‍♀, ALLAH ka ganar damu gaskiya😢🙏🏻).
        Nayi zaton Dad da Mummy zasu mata faɗa, a kuma tursasata dole ta shiga, amma sai naji babu wandama yace mata uffan, sai ƴar dariya kawai da Mummy tayi.
        Nima ban tankaba, naje nai duk abinda ya dace na fara zuwa abuna ba tare dana sake bi takan Aamilah ba.
      Da safe zuwa rana nakan nutsu wajen koyan girki a wajen kuku, da yamma na wuce makaranta.
     Satina kusan biyu da dawo gidan saiga Nazifa, Ummie, Zuhrah, Rebecca sun kawomin ziyara, nayi matuƙar murnar wannan ziyara, dan kuwa kowama agidan ya fahimci hakan.
     Ranar mun yini muna shaftarmu, sai dare suka wuce, ko islamiyya tare dasu mukajeta.
     Tun daga sannan muka koma ziyarar juna akai-akai, nima Dad yasa duk aka kaini gidajensu, zuminci mai ƙarfi ya sake ƙulluwa tsakanina dasu da ahalinsu, harma yayan Zuhrah ya maƙalemin wai sona yake, ranar harda kuka nayi, dan nikam ba'a taɓa cewa ana sonaba sai ranar.
    Ban dai bashi fuskaba, amma muna gaisawa ta waya lokaci-lokaci.

★★★★★★

       Ba a wani ja dogon lokaci ba jarabawarmu ta fito, dukanmu mun sami sakamako mai ƙyau, ranar dai murna ai ba'a magana, dan kowa na gidan sai da ya fahimci ina tare da farin ciki kuwa.
    Babu wani ɓata lokaci Dad ya fara nema min skull, da yake bakinmu ɗaya da su Zuhrah, yana tambayata zaɓin makarantar da nakeso na sanar masa wadda muka shirya.
       To ashema Daddyn Ummie ne zai nema mana skull ɗin.


A gurguje Please😹🥴⛹‍♀

            Makaranta dai ta samu, inda cikin amincin UBANGIJI duk muka dace da cikar burinmu, dan kuwa mun sake tsintar kammu a muhalli ɗaya ni, Zuhrah, Ummie, Nazifa, Rebecca.
         Komai dai an gama mana tsaf, hakama shirin tafiya nima an mani na ƴan gata, na bar gida cike da kewarsu musamman Dad da Amina dasu kuku.
       
Ƙaramin gida aka kama mana kusa da makarantar mu duka biyar ɗin, ɗaki biyune sai falo sai kicin kawai a gidan, duk kuma abinda zamu iya buƙata su Dad sun haɗa hannu wajen saka mana, an kuma haɗamu zama da wata dattijuwa yayar Dadyn Ummie, itace zata zauna damu saboda kula da duk wani motsinmu, kusan yaran yanzu sai ana saka mana idanu, duk ƙoƙarin tsare mutuncinka idan babu mai ƙwaɓa maka a kusa tuni kake kaucewa ko wata ƙawa ko sauriyi su sakaka a hanyar banza, hakanne yasa aka ajiye mana Gwaggo Hari danta zauna damu.
       Ni da Ummie ne muka fara isa, sai ga Zuhrah, bayan magriba kuma sai ga su Rebecca, Zuhrah kam sai washe gari ta iso.
     Yau kuma ga inda ƙaddara ta kawo bilynku, sai ku tayamu da addu'ar tsare mutunci da maida hankali akan abinda ya jehomu nanɗin😊...........✍🏻
Barkanku da juma'a, a sakani a addu'ar wannan rana mai albarka Please😑😥

Page 30

.............Salon rayuwa ya kuma canjawa, ga Bilkisu a matakin da zuciya bata taɓa hasasowa ba, balle sakashi a jerin burin mallaka, mun tsunduma a cikin karatu gadan-gadan babu kama hannun yaro. Sannan kamewar kai babu kula samari ko ƙawayen banza kamar yanda mukaima kammu alƙawari, inhar jerin ɗalibai masu ƙwazone, dolene ka samu sunan group ɗinmu a sahun farko, cikin lokaci ƙanƙani sunanmu yay kuwwar fita sararin subahana a makarantar.
      Bawai a rashin kunyaba, ko nuna rashin tarbiyya, a'a tamu zarran mu a karatu take da kamun kai.
       Ɓangaren samari akwai masu bibiyarmu akoda yaushe, sai dai sam basa samun fuska daga garemu, burinmu kawai cika alƙawarin da muka ɗaukama kawunanmu inhar muna cikin masu tsawon rai.
       A haka kwanaki sukaita ja babu ko gargada a ciki, wataran a mori yini da kwana da farin ciki, wataran a riskeshi da saɓanin haka.
     Kafin wani dogon nazari watanni biyar suka shuɗe mana, mukazo gida hutun sati buyu.
         Bazance hutun baimun daɗi ba, sai dai babu wani farin ciki daya bani, dan na iske Mummy tayi tafiya itada Aamilah zuwa wajen aunty Shahudah, hakama Dad baya ƙasar, sai Salman da Qaseem kawai.
      Tun saukata gidan na fahimci bazai zaunu a gareniba, dan kuwa ni kaɗaice mace a cikinsa, Amina ma bata zuwa kamar yanda Mummy ta bata umarni, wannan damar data samu ne ya sakata nufar ƙauyen babanta taɗan huta itama.
          Ƙananun ƴan akuyancin da Salman ya fara nuna mini ne ya sakani tattara inawa-inawa tunkan abun yay nisa na fece gidan Inna zainabu kamar yanda na nema izini wajen Dad, nakuma taki sa'a babu musu ya bani dama ba tare daya bincikeni dalilina ba.
         Ban wani samu gamsashahiyar tarbaba daga wajen Inna, sai dai hakan bai dameniba, dan hakan ya fimin zama cikin ƙattai.
        Lawisa kam yanda ta shareni nima hakan na shareta, tadai san bata isa sakani wani aikiba a yanzu, dan wannan ba Bilkisun da bace data raina.
        Nai amfani da damata kuwa, wajen ziyartar gidajen dangin mahaifina harma da sauran na mahaifiyata, duk da kuwa a baya sun nuna basa buƙatata.
        Wasu a cikinsu sunji kunya sosai ganina a ƙyaƙyƙyawan yanayi, saɓanin abinda sukai mini fata, ni dai ban maida kaiba, koba komai dai na samu ladan zuminci, kuma duk duniya bani da kamarsu.
      
       A haka na cinye nawa hutun, Dad ya turo mini kuɗin sayayyar komawata ta hannun Qaseem.
        Dan haka dole na shirya na koma gida ana saura kwana biyu komawarmu, naji daɗin rashin iske Salman, sai dai shima Yaa Qaseem ɗin yawan kallo da yake bina dashi ya fara takurani, abin mamaki da zanje sayayyama shine ya kaini, sai kuma wani takalata yake da hira, ni abunma sai ya ɗaure kaina matuƙa.
          Ban dai nuna masa komaiba ko a fuska, na samu muka kammala ya maidoni, tunda na samu na sheƙa ɗakina saina kulle kaina bai sake ganinaba ban sake ganinsa ba.
         Sai dai bayan isha'i naji ana ƙwanƙwasa min ƙofa, koda na buɗe sai na ganshi, mamaki ya kamani, amma kafin nace wani abu sai cewa yay nazo na dafa masa shayi.
            Ban masa musuba nabi umarninsa, duk da a zuciyata ƙunƙuni naketayi akan hakan, ga kuku amma ni zaizo ya saka aiki.
        Abin al'ajab sai ya biyoni kitchen ɗin, yaja kujera ya zauna, ni dai inata neman tsarin ALLAH daga sharrinsa inma dashi yazo, ina gamawa kuma zan wuce ya tsaidani.
           “Zauna mana, kina ganin gidan shiru babu wani abokin hira shine zaki barni ni kaɗai”.
       Idanu kawai na ɗaga na kallesa, ganin ya kafeni da nasa idanun sai na sauke numfashi kaɗan, nace, “Yah Qaseem kasan ina shirine fa, gashi sammako zanyi idan ALLAH ya kaimu”.
     Kamar bazai tanka minba sai kuma ya sake kallona, baice komaiba ya miƙe yana faɗin, “Muje to kina shirya kayan kina tayani hira”.
       Tamkar zan fasa ihu haka naji, haka ya tasani gaba har ɗakina, ya zauna a kujerar gaban mirror ni kuma ina daga wajen gado saman kafet ɗin wajen ina kimtsa kaya, gaba ɗaya jina nake a takure, gashi ba wani hirar mukeba, ya zubamin idone kawai yana shan shayi, niko ina aiki.
      Sauri-sauri na kammala nai gefe dasu, cikin kwantar da murya yanda zaiji tausayina nace masa barci nakeji.
     Murmushi kawai yayi, ya miƙe ba tare da yace min uffanba ya fita.
    Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi a fili ina faɗin, “Wannan takura har i...n...a...”
        Na ƙare maganar da ɗai-ɗai saboda tozali danai dashi ya dawo baya, munafukin ashe ba tafiya yayba.
     Kaina na sunkuyar ƙasa jikina na tsuma saboda tsoro.
      Sai da ya gama ƙaremin kallo sama da ƙasa sannan ya juya ya fice abunsa.
       Ai yanzu ko motsi banyiba sai da naja lokaci mai tsaho sannan, cikin sanɗa naje na rufe ƙofar tare da murza key.

          Washe gari da safe, koda na idar da sallar asuba ban kwantaba, nai dukkan shirye-shiryen daya dace na fidda kayana waje, ɗaki na dawo nai wanka sannan na shirya tsaf na fito.
     Nasan dai driver zai kaini, dan haka na nufi wajen motar dana kai kayana.
      Cikin girmamawa yace, “Ai kayan suna can” yay maganar da nuna motar Qaseem.
     Da mamaki nace masa, “Can kuma? Mikuma ya maidasu can ɗin Nura?”.
         “Yallaɓai Qaseem ne yace a maida”.
     Kafin na bashi amsa takun takalman Qaseem suka katseni, ba tare daya kalleni ba yace, “Malama ki zagaya mota sauri nake inada wajen zuwa”.
     Tamkar na zauna naita ƙwaɗa ihu haka naji, dole nabi umarninsa naje na shiga inda ya buɗemin da kansa bayan ya shiga.
       Haka muka tafi tamkar kurame, sai lokaci-lokaci yakan jani da hira, wata na amsa da baki, wata nace, “eh ko A'a”.
Da haka muka iso.
             Da kansa ya fito ya taimaka min muka shiga da kayan, ba tare daya zaunaba yace zai wuce.
      Sake rakosa nayi wajen mota nai masa godiya.
      Harya tada motar sai yace na bashi wayata.
    Bashi nayi ina ƙunƙuni a zuciyata, duk da bansan miyayi da itaba naji a jikina number ta ya ɗauka, ya haɗo wayar da kuɗi ya miƙomin.
     Zan zare wayar ya harareni, dole na haɗa da kudin na amsa nai masa godiya.

★★:★★:★★

       
          Tun daga wannan lokacin abubuwa suka fara sauyawa tsakanina da Yah Qaseem, tun yana kirana lokaci-lokaci harya fara komawa kullum.
       Banaƙin ɗauka, dan koba komai matsayin yaya yake a gareni, sannan banjin zan iya tozarta zuri'ar Dad, Yah Qaseem kuma namijin da kowace mace zata iya sone, dan akwai ƙyawu, yana aikinsa, tunda nake dashi ban taɓa kamashi da wani abu mara ƙyauba, sai dai idan a ɓoye yake kayansa, wannan kuma ya rage nasa ai, matsalar sa dai rashin ilimin addini, wanda gaba ɗaya ɗiyan dad ya zama babban tawaya wa rayuwarsu, tsagwaron wayewarce kawai da duniya suka sani.
          Munja kusan shekara ɗaya da rabi a haka, shi baice yan sonaba, sai dai alamomi, dan duk randa ya bushi iska zaizo busting ɗina da kaya niƙi-niƙi, zanma ce yafi kowa ziyarata a gidan, idan kuma naje hutu yata bani kulawa kenan harna taho, ko wani abu Aamilah ko Salman sukaimin sai yayi magana a yanzu.
       Kulawar da Yah Qaseem ke bani a yanzu na kula tana ɓata ran Mummy, duk da dai bata magana ni nakan hasaso ɓacin rai a fuskarta.
        Ni kaina take-takensa suna tsoratani, dan ni dai nasan yafi ƙarfina ta kowanne fanni, duk da canjin dana samu a rayuwa bansama raina zan samu koda wanda bai kaisaba matsayin miji, ni dai kullum addu'ata ALLAH ya bani nagari da zai zamarmin mijin marainiya.

         Muna shekara ta uku a makaranta Yah Qaseem ya fiddo manufarsa fili a kaina a kaina, dan kuwa ya tabbatar min shifa sona yake.
      Na shiga tsantsar ruɗani da wannan furuci, duk da na daɗe ina hasashen haka, dama a lokacin munje gida weekend ne, ALLAH ma ya soni ana gobe zan komane, aiko washe gari baisan na gudu ba.
       Koda na sanarma su Ummie sai sukaita zugani akan na karɓa masa, dan Yah Qaseem ya cancanta, idan kuma bana sonshine to, amma sun daɗe su dama suna hasashen akwai wani abu a ransa game dani, sudai suna bani shawara nai amfani da damata gaskiya.
         Ni dai kasa cewa komai nayi, dan idan nacema banson Yah Qaseem nayi ƙarya, ya fini komai a rayuwa, sannan ya cancanta a soshi, amma idan harna amsa to na ɗeboma kaina gagarumar rigima daga ahalinsa, musamman Mummy da tunkan ya furtama take ƙyamatar abun, inaga yanzun yace yana so.
           Bai sake bi takaina akan sonjin amsar na aminceba koni ina sonsa, ya dai ƙara ninka kulawarsa kaina fiye da ta baya.
        Yana cigaba da sakani sakin jiki dashi ba tare dana saniba nima.
        Shi dai Dad koda ya fahimta baice komaiba, amma Mummy ƙiri-ƙiri ta nuna bazata saɓuba, hakama Aamilah da Salman.
       Wannan soyayya ta Qaseem ce ta kuma ƙirƙirarmin samubawar tsangwama da tsana a gidan, a wajen Dad da yah Qaseem kawai nake samun sassauci, gashi Dad ba mazauni bane.
  
       Cikin wannan yanayin tsangwama muka shiga shekarar ƙarshe a makaranta nida ƴan uwana guda huɗu.

        
______________________
           JAWAAD   
______________________

        A ɓangaren Jay kuwa komai yana tafiya dai-dai, sai dai yau da gobe ba'a kiranta da nasara ko farin ciki ɗari bisa ɗari, dolene wataran tazo da daɗi, wataran saɓanin hakan.
         Yana shekara ta biyu da rabuwa da Shahudah wani cigaba na musamman ya zomasa shida tawagarsa, dan kuwa wani horaswa ta musamman aka turasu zuwa ƙasar amuruka.
      Duk masoyinsu dolene ya tayasu murna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login