Showing 12001 words to 15000 words out of 104658 words

Chapter 5 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

187

bai da girman kai, bai da wulaƙanci, sanan sam ba miskili bane ba. Abu ɗayane yake yawo a jinin Jawaad da ke saka jama'a dangantashi da waɗancan ɗabi'un na sama, shine rashin sabo, sam baisan sabo ba, kana takashi zai shata maka dogon layi, tsautsayi ko rawar kai ya saka ka ƙetara to lallai kun ƙulla kenan, kuma ka ɗaura kanka a danja mai haɗarin gaske. Babu ruwansa da kai wanene? Ko kuma ina ka fito? Miye matsayinka a garesa duk ba'abin kallonsa bane.
     Jarumi ne ta fannin aiki da rayuwa, sannan gagararrene a duniyar tsagerun mutane, idan ya ɓalle sam bai san bari ba, duk abinda ya saka a gabansa sai ya cimma manufarsa yake yankan filin hutu.
      Waɗannan ɗabi'un nasane suka jawo masa abokan tsama ta fannoni daban-daban, a cikin hukumarsu da wajenta, harma da tsagerun gari. 

★★★★

              Shahuda ɗiya ce ga yayar marigayi Alhaji Abdull, wato Hajiya Humaira, tuni suna ƙasar Holland ita da mijinta, yaransu biyar suma, mata uku maza biyu, asalin sunan Shahuda *Sabeerah*, dan sunan mahaifiyar Abbansu aka saka mata, amma sai suke mata alkunya da suna Shahuda, ita ce ƴa ta huɗu a gidansu, ƴan gatane na haƙiƙa, waɗanda suka tashi da ɗabi'un turawa a cikin jininsu, sam basu san bari ba, dan bama a faɗa musu.
          Hajiya Humaira tana son Jawaad, shiyyasa lokuta da dama take matsa masa zuwa ƙasar Holland wajensu ya ɗan huta. To annan fa Shahuda ta ga Jawaad ta mutu a kansa, tun yana basarwa dai har shima ya zurma, dan Shahuda ƙyaƙyƙyawace ta haƙiƙa, saboda mahaifinsu bafilatanine ɗan asali mai asalin madarar ƙyawu, duk cikin yaran kuma Shahuda tafi biyosa, ga jin daɗi da suke ciki, saboda inda suka taso, wannan ya haɗu ya maida Shahudah son kowa ƙin wanda ya rasa.
      Jawaad yana son Shahudah, sai dai halayenta na bashi tsoro, dan kuwa dai irin yarannane da babu kwaɓa babu harara, idonsu ya buɗe da ƙazamar wayewa mai wahalar canja ra'ayi cikin sauƙi. Dan haka sai bai wani cika sake mata fuska ba, dama can yaran Family ɗin shakkarsa suke, dan bayan gaisuwa baya basu wata fuskar shiga huruminsa, sai dai fa yana ƙyautata musu akan bukatunsu, idan abu suke buƙata kafin su tambayi sauran yayyensu sun nema da ga wajensa, kuma inhar yana da halin yimusu yakan musu gwargwado.
 
         Aikin da ya kai mahaifin su Shahudah ƙasar Holland ya ƙare, dan haka ya tattarosu suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, tunda suka dawo Shahuda ta dawo nan Tafida Family house ɗin su Jawaad ta tare duk dan shi. Ba zamuce baya kulata ba, sake mata ne kawai bayayi, wannan kuma badan hulaƙanci yake mata haka ba, rashin sakin jiki da jama'a halinsa ne kowa ya san haka, ita kanta sanin hakanne ya sata bata damun kanta da lamarin nasa, burinta kawai ta mallakesa matsayin miji, dan badan Jawaad ba bazata taɓa dawowa zaman ƙasarba sam, duk abinda ya shafi afirika ɓata mata rai yakeyi, a haukarta bayan aurenta da Jawaad saita ja ra'ayinsa sunbar yankin afirika gaba ɗayanta sun koma turai da zama. (😂🤣Babbar magana shahudah).

           *★★★★★★★★*

    Hankalin Hajiya Humairah ya tashi ganin tunda suka dawo ƙasar Jawaad yaƙi yay maganar aurensa da Shahudah kusan shekara uku, hasalima yafi maida hankalinsa ga aikinsa fiye da komai, ga Shahudah kullum cikin damunsu take akan batun Jawaad.
      Shiryawa hajiya humaira tayi ta nufi *Tafida family house* domin tattaunawa da ƴan uwanta akan batun auren, dama gashi lokacin meeting ɗinsu na family ya kusa. Koda takai kukanta akan zancen sai kowa ya bada goyon baya, aka kuma tuntuɓi Jawaad akan maganar.
        Haushi abun ya bama Jawaad matuƙa, dan sam bai shirin wannan auren nan kusa ba, so yay sai ya maida Shahudah cikin hankalinta da aƙidar yankinta da addininta, amma sam an wani zo an masa titsiye. Cikin ƙuluwar haushi akan zancen yace suyi duk yanda ya dace kawai.
          Wasunsu sun fahimci bai soba, amma sai suka watsar da fushin nasa aka hau shirin biki na ƴaƴan gata, dan dama babban burinsu suga yayi aure kamar sauran yaran gidan kodan su gujema zaginsu da jama'a keyi akan sunƙi sakashi yay aure.
           Sam ƙin bama bikin muhimmanci Jawaad yayi, hasalima hankalinsa na kan aikinsa, komai sai iyayensa keyi, sai da Shahudah ta sakashi gaba da kuka sannan ne yaɗan maido hankalinsa shima ba duka ba.
     Haka dai dangi sukaita lallaɓata akan ta manta da lamarinsa tunda kowa yasan halinsa ayi auren kawai, idan ta shiga zai bata kulawa insha ALLAH.
      Son da take masane ya sata yarda da shawarwarinsu akai biki lafiya aka tashi, sai dai a hidimar bikinma ta mugun shaƙar baƙin ciki, dan ƙin zuwa yay taro ko guda ɗaya har dinner ɗin da suka shirya bayan ɗaurin aure ta garari ta nunawa a gidajen tv saboda tsabar haɗuwarta, sam baijeba, a ranarma tsabar iskancin Jawaad a wajen aiki ya kwana, a washe gari kuma yaƙi yarda ya hadu da kowa a gidan saboda tsiyar da ya tsula musu.
        Shahuda kuma tace bazata tareba sai yazo ya bata haƙuri.
     Nanma sharewa yay kamar baisan sunayiba, sai da Hajiya Ummah ƙanwar mama bilkisu mahaifiyarsa ta kirasa tai masa faɗa sannan yaje, mai makon ya bata haƙurin sai ma ya sake gaggasa mata magana, ya kuma ce inma bata tareba baida matsala da hakan.
       Da yake su kaɗaine a ɗakin sai Shahudah ta ci kukanta ta share hawaye da burin sai ta rama amma a gidansa, ga sauran ƴan uwa kuwa sai ta nuna musu ai ya lallasheta ne itako tanata masa shagwaɓa (😂😝).
       Kowa ya yarda da batubta, dan an tabbatar Jawaad nason Shahudah, halinsa na nuna ko in kula da abu ne yake sakashi ɓoyewa, amma yanda ma yake ɗan kulata fiye da sauran yaran gidan zai tabbatar maka da yana sonta.
       Daga ƙarshe dai sai amarya ta tare a nan gidan sashin Alhaji Abdull mahaifin Jawaad, dama tun bayan tashinsu babu wanda ya shiga sashen, yanzu kam sai Jawaad yay masa gyara mai burgewa aka saka masa amaryarsa anan.
      A farkon amarci abin nasu ɗoɗa-ɗoɗa, amma son jiki da shegen ɗaukar dala babu gammo na ɗabi'un Shahudah ne ya zamarma auren nasu matsalolin da baibayi da sukai ma zaman nasu ƙullin goro. Tunda gashi har Jawaad na complain a kan auren watanni bakwai kacal🤦🏻‍♀️..........✍🏻

Page 6

..........A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗinkace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce, kowacce ka zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta, saɓanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurɓatacciya.
       A yau dai ga ni a matsayin marainiya, wadda babu ɗumin duka mahaifa guda biyu, sannan babu bangon jingina daga tsatson zuminci ko guda ɗaya. Rayuwata ta cigaba da tafiya a hannun mutanen kirki ahalin fiddausi, sun zamemin uwa da uba bayan ƙasa ta rufe idanun nawa, yanzu sune ci na sune shana da dukkan buƙatun rayuwa da aljihunsu sai iya ɗauka.
     Zuciyata na kewar iyayena, amma jarumtata na ɓoye hakan a koda yaushe, haƙuri kuma ya zamemin sandar jagora yayin tafiya ba tare da na lalubi hanya ba saboda makantar zuci.
    Tabbas rayuwar gidanmu ta canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da iyayena na raye akanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna ƙyamata ko hantara ta ma kai tsaye, idanun maman firdausi ne kawai kan hana wasu cin zarafina koda da harara ne, amma da zaran babu ita a tsakar gidan to kare ma ya fini daraja.
        Matsala ta farko dana fara cin karo da ita a gidan mai ƙona zuciya da barin tabon da ba'a mantawa shine zuwan mai gidan Alhaji lado naira, koda iyayena suka rasu bana tunanin Alhaji lado yazo gidan gaisuwa sam, amma rana tsaka sai gashi danƙyas-danƙyas yazo koramin bayanin na kwashe kayana daga ɗakinmu zai zuba ƴan haya.
          Cikin ƙarfin hali da dogaro da kuɗin hayarmu na shekarar basuyi ko rabi ba na shiga kora masa bayani akan ai da sauran lokacin tashinmu.
      Alhaji Lado ya bankamin harara tare da watsamin yatsun hannunsa biyar cif alamar zagi (daƙuwa) “Kinci uwarki, kujimin lalatacciyar yarinya, yo ko yau kuka biya tunda wanda yay biyan ya tafi barzahu ai kuɗinku sunyi isfaya (expire) kuma, to dan shelen uwarki ma😱, gidan tsohonki ko nawa da har zaki zauna jamin sharaɗi. Maza tashi kiyo waje da komai tafe nake da mai fenti, ki zauna wannan bacar har kuɗin su kare, dan itama zaki fara biyan kuɗin hayane tunda yanzu ƙofar ɗakin wasune”.
     Kasare nai ina kallonsa tamkar wata wawuya ko sokuwa, wasu da ga jama'ar gidan ko dariya suketa tuntsurawa, ƙalilanne basu ji daɗin lamarin ba, amma babu wanda yace ma Alhaji lado baiyi dai-dai ba, dan sunajin tsoron ya shuka musu shika-shikan rashin arziƙinsa suma, kaɗanma da ga aikinsa yace kaima ka tashi ka bashi ɗakinsa. Baka da yanda zakai dashi kuma dolenka ka tashi, inba hakaba ya saka yaransa subi tsakkiyar rana ko duhun dare su naɗa maka na jaki🤦🏻‍♀️.......
      Tsawar da ya dakamin ce ta sakani zabura na miƙe tsaye, ya nunamin ƙofar ɗakinmu yana haɗe fuska tamkar kashin ƙato na farar safiya.
    Jikina na ɓari na nufin ɗakin, dan fuskar Alhaji lado tafi baƙin kashin shanu barazana idan ya murkite ta, ina shiga itama firdausi na shigowa, itace ta taimaka min wajen haɗe kayan muka ƙuƙƙulle ina sharar ƙwalla, sauƙina ɗaya ma kayan bawani uban yawane da suba, marasa amfanin ciki kuma sunfi masu amfanin yawa.
      Bayan mun gama haɗesu ta taimaka min muka fiddosu zuwa cikin bacar da muke kwana, wadda kayan suka mamaye kusan rabinta, dan dama bawani girman azo agani bane da ita.
     Alhaji Lado bai kuma bi takaina ba sai ma yaransa da suka shiga suka fara fente ɗakin da fenti mai ƙyau da ya bama kowa mamaki, dan duk ɗakunan gidan da farar ƙasa aka shafesu  maimakon fenti🤦🏻‍♀.

            Da daddare munacin abinci a ɗakin su Firdausi innarsu ke bani haƙurin abinda ya faru da rana, dan ɗazun bata da sukunin nuna tausayina suma ta shafesu, shiyyasa sukai gum da ga ita har baba.
     Murmushi nai mai ciwo ina faɗin, “Babu komai inna, ALLAHN da ya bashi muma bai manta da muba ai”.
    “Hakane Bilkisu” inna ta faɗa tana murmushi, ta dafa kafaɗa ta tana ƙara nuna min muhimmancin haƙuri da amfaninsa.
    Naji daɗin bayaninta, dan naƙara samun ƙwarin gwiwar ɗaura ɗammarar zama jaruma akan kaina.

★★★★★★

       Faruwar hakan da kwanaki biyu kacal waɗanda zasu zauna a ɗakin suka tare.
      Abinda ya tada hankalin dukkan jama'ar gidan, shine wanda zai tare a ɗakin da muka zauna.
     Kusan sha biyun rana saiga ƙattai suna shigowa da kaya cikin gidan, waɗanda kallo ɗaya zakai musu ka fahimci addu'a kawai rayuwarsu take buƙata. Sune suka saka komai a ɗakin suka gyarashi tsaf, duk da bamu shigaba munsan dolene ya haɗu, dan kayan da akaita shiga dasu babu ma mai kwatankwacinsu a cikin gidanmu.
     Mun daɗe bamu da wutar nefa a gidanmu, amma sai gashi anzo a ranar an gyara, washe gari kuma sai ga masu gyaran fanfo tunda farar safiya.
     Irinmu da bamusan wanene zai tare a ɗakinba dai mamaki ya matuƙar kamamu, burinmu muga wanene zai zauna a ɗakin kawai.

       Da yamma gan da magriba mun dawo islamiyya mukaci karo da baƙon lamarin da sam ada babu kwatankwacinsa a gidanmu. Kana kusanto gidan kunnenka zai fara jiyo maka sautin kiɗa da ke tashi da ƙarar Janareto (Genretor).
     Kallon juna mukai ni da firdausi, dan munsan dai babu wani shagali da akeyi a gidan, koma anayi ba'a taɓa kalar wannanba.
      Badai muce komaiba muka shigo da sallama a bakunanmu. Fetal tsakar gidan yake tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, gidanmu da idan ka shigo da yamma zaka ɗauka biki muke sai gashi tsitt, idanunmu suka sauka akan matasan samari da adadinsu zai kai goma sha uku acan jikin ɗakinmu da muka tashi, wanda bacar da muke kwana ni da firdausi take kallonsa, Mutum ɗaya ne zaune a kujera kawai yana zuƙar sigari, sauran kuma duk suna saman tabarna babba da aka shinfiɗa, wasu karta sukeyi, wasu kuwa zaune suke suna kallon masu kartar, sai ɗaya dake matsama na zaune saman kujerar ƙafa tamkar wani sarki.
        Kallon juna muka sake yi ni da firdausi, yayinda suma matasan samarin suka zubo mana idanu su duka.
      Gyaran murya da na kan kujerar yayne ya saka dukkan samarin saurin nutsuwa kowa yana sunkuyar da kai.
       Baice uffanba shikam, sai zuba mana idanu da yay yana ƙare mana kallo da ga sama har ƙasa duk da sanye muke cikin hijjabai har kusan ƙasa.
     Firdausi ce tai ƙarfin halin kama hannuna muka cigaba da takawa dogon tsakar gidan muna dosar inda samarin suke, dan ɗakin su firdausi shine jikin nami dama can, sannan bacarmu a tsakanin ƙofar su firdausi da ɗakinmu na da inda samarn suke yanzu take, hakan yasa samarin suke zaune har ƙofar bacarmu da gaban ɗakin iyayen firdausi.
        Duk da munga a yanayin da suke da bana mutanen kirkiba, ga kuma kiɗan dake tashi da bamu da tabbacin zasujimu, hakan bai hanamu gaishesu ba. A mamakinmu sai mukaji suna amsawa kuwa, wanda ke kan kujerarne kawai bai amsaba, kuma har yanzu idanunsa na kanmu.
      Wanda ke zaune saman ƙofar su firdausi ne ya matsa mana fahimtar da yay kamar nan zamu shiga, cikin sassarfa muka faɗa ɗakin kuwa da hanzarinmu ko sallama babu.
      Maman firdausi dake zaune ta miƙe zumbur tana nufomu, hannunmu ta kama zuwa tabarma jikinta har rawa yake.
    Mamaki ya sake kamamu, mun buɗe baki zamuyi magana tai azamar mana nuni da muyi shiru. Shirun kuwa mukayi muna cigaba da binta da kallo.

         Haka mukai kwannan yau babu wani sikuni ga jama'ar gidan, kowa ya maƙure a ɗakinsa yana tsoron fitowa, mu kanmu yau a ɗaki ɗaya muka kwana da iyayen firdausi, baba ya hanamu zuwa bacarmu.

MAFARIN MATSALA

         Baƙon dai da ya tare a ɗakin da na taso tun ƙuruciya na ganni a ciki matsayin namu, ɗan Alhaji Lado Naira mai suna Jazuli (Jazuuuga) ne ya tare.
      Jazuli ko nace Jazuuuga ɗane na huɗu ga Alhaji lado, shine namiji da aka fara haifa masa a gidansa, yana matuƙar ƙaunar yaron tun yana ƙaraminsa, hakanne yasa ya tashi a sangarce, sam Jazuuuga bayaji tun bai kai girma ba, tun yana secondary sukul ya haɗa dabarsa, yana da yara masu take masa baya da haɗarinsu ya sa ake matuƙar tsoronsa, duk yanda kuke tunanin takadaranci irinna Jazuli abin ya wuce gaban nan, bayan ya kammala sakandire dinne kuma baban nasa ya ƙarama sheɗancin nasa armashi ta hanyar fiddashi karatu can kudancin ƙasar, acewarsa zaifi samun ilimi acan.
       Karku tunanin ilimin Jazuli ya nema koda yaje can ɗin, sam yama manta karatune ya kaishi, ya shige cikin manyan marasa jin magana yay kane-kane yana ɗaukar nasa karatun acan, tsawon shekara biyar iya abinda ya ƙaro ilimi a kansa kenan, idonsa ya matuƙar sake bushewa, ya zama jan wuya na sosai.
      Abinda ya maido Jazuuuga gida kuwa kashe oga kwata-kwata na ƙungiyarsu da yay ne, hakanne ya sakashi gudowa ya dawo gida dan yasan dai idan yazo nan ya tsira.
     Duk da hankalin Alhaji Lado ya tashi akan halin da ɗansa ya sake ƙwarewa a kai hakan baisa ya daina masa gata ba, saima ya ninka, a cewarsa ai hakanne zaisa ya shiryu.
    Ɓarin kuɗin da Alhaji Lado kema Jazuli ne ya bashi damar jan ra'ayin yara takadarai irinsa, wasuma abun nasu ƙaramine, amma saiya horar dasu matsayin sojojinsa, ya haɗa ƙungiya mai matuƙar haɗari da barazana.
      Akwai dalilin da yasa Jazuuga ya dawo gidan hayar na mahaifimsa, dukda gidansu kuwa yaci uban wannan sau fiye da goma, ga kayan alatu da morewar rayuwa a cikinsa, amma saboda son samun cikar burinsa shine ya cema mahaifinsa nan yakeson zama, babu ɓata lokaci kuma Alhaji Lado ya zo ya tada Bilkisu da ga ɗakinsa aka gyarama Jazuuuga............✍

Page 7

JAWAAD

............Cikin ƙunar zuciya da ɗacin da ya keji akan halayyar Shahudah yay shirin fita a gaggauce domin komawa Office. Bai bawani ɓata lokaci ba ya fito cikin shigar ƙananun kaya sai zabga ƙamshi yakeyi.

        Shahudah na a falon kwance cikin kujera, ga kiɗa mai taushi ya na tashi ta cikin sifikun da aka ƙawata falon dasu, sanye take cikin wando da riga masu azabar ƙyau kalar ruwan hoda, kasancewar kayan robane sunyi mugun bin jikinta tamkar da fatarta aka haliccesu, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigar da bata rufe mata ko cibiya ba, dan ƙyau tayi ƙyau sosai, dolene ka kalleta ka sake kallo.
     Gaban ɗayan imaninta nakan waya ɗinta da take cheating, gefe ɗaya tana sauraren waƙa.
        Har Jawaad ya gama sakkowa bata sani ba, sai da mayen ƙamshin turarensa ya bugi hancinta ne ta ɗan lumshe ido tana zuƙarsa kafin ta buɗe ta yunƙura ta tashi zaune, ƙyawawan fararen idanunta a kansa.
         Shima idanun nasa na kanta, dan kwalliyar tata ta masa ƙyau, sai ya ji kaso mafi yawa na haushinta ya ragu a zuciyarsa, sauran cake ɗin da taci ta rage da kofin da ta sha tea ya kalla ya kauda kansa, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana sake haɗe fuska.
         Murmushi Shahudah da ke kallonsa tayi, dan sam ita bata da riƙo, dama ko faɗa sukai zai ta shareta, itako mintuna kaɗan ta manta sai kuma an sake wani.
    Yanzu ma dai hakan ita harta huce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login