Showing 63001 words to 66000 words out of 104658 words

Chapter 22 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

216

ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ya kaɗa mata yatsun hannunsa biyu yana kuma fiddo idanu waje sosai yace, “Wasa ƙwaƙwalwa. Dan haka ki faɗa min minene gaskiyar zance akan cikina?”.
            Babu shiri Shahudah ta saki kofin shayinta a ƙasa, ya zube kofin ya tarwatse, jikinta sai ɓari yake, murya na rawa tace, “Bb wace irin magana ce wannan? Kana zargina nina zubar kenan?”.
          Wani murmushi ya sakar mata yana bin kofin dake tarwatse a ƙasa ga shayin ya jiƙe musu ƙafafu da kallo, ya wani wulƙita idanu luuu yana maido dubansa gareta har lokacin fuskarsa da murmushi wanda ita tasan ma'anarsa sam bana farin ciki bane, ya janye ƙafarsa daga laimar ruwan yana miƙewa tsaye.
         Key ɗin hannunsa ya shiga kaɗawa yay taku ɗaya biyu kamar zai nufi hanyar fita sai kuma ya juyo gareta yana nunata da key ɗin.
        “Hudah nai miki farin sanin da inaga ko iyayenki basu gama nutsuwa sun mikiba, tun muna mu biyu a ɗakin nan ki faɗamin da haɗin kan wa kika aikata?”.
       Cikin son kare kanta ta aro jarumtar dole ta fara masa bayanin abinda likitansu ya faɗa.
      Uffan baice da itaba ya zaro handkherchief a aljihunsa yana rissinawa ya ɗauki wani abu a ƙasa, takowa yay ya dawo gabanta, ƙafarsa ya maida a saman gadon ya nuna mata syringe ɗin daya ɗaukko.
        “Ki bani amsa da gaggawa kafin nakai maƙura, Wane likitane ya bada?”.
          Karon farko a rayuwar Shahudah da taso karanto wata addu'a a harshenta saboda tsagwaron tashin hankali da ruɗani, sai dai batama san miya kamata ta karantan ba tunda ba addu'oin ta saniba.
       Kanta ta shiga girgiza masa tana hawaye da matsawa baya, “Bb ni bansan komaiba wlhy, wannan abun bansan wanene ya kawosaba, sai dai idan likitocin nan suka yardashi by mistake, ka yarda dani dan ALLAH”.
       Cikin halin ko in kula yace,  “Ba dolema na yarda dakeba ƴammata” yay maganar yana ɗaukar leda a saman mirror ɗinta ya saka sirinjin, ko kallonta bai sake yiba ya juya ya fice daga ɗakin cike da izzar da ɓacin rai ya haddasa masa.
  
      Da ƙarfi Shahudah tai yunƙurin miƙewa tsaye danta bisa, sai dai rashin ƙwarin jiki yasa jiri ya kwasheta ta koma saman gadon yaraf ta kwanta hawaye na gudu saman fuskarta, ita kanta a yanzu jitai tana buƙatar cikinma, kodan tashin hankali da tsagwaron bala'in data hango cikin idanun Jawaad.
         Mummy da Aamilah na falon, sai dai Aamilah ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kaikawo take tsakanin kujeru, gaba ɗaya yanayin Jawaad ya kuma tsoratata.
    Duk da ac dake aiki a falon ita zuface ke tsatstsafoma goshinta.
     Sarai Mummy ta lura da halin da Aamilah ke a ciki, amma ta kasa tambayarta mike damunta, dan tunda aka shaida musu cikin nan ya faɗi komai ya sukukuce mata, ko mama Atika ta kasa kira ta sanarmawa balle sauran ƴan uwanta......
     Sakkowar Jawaad a fusace daga sama ya katse mata tunani, daga ita har Aamilah suka zuba masa idanu kamar yau suka fara ganinsa.
         Baiko kallesu ba yay ficewarsa saboda shiyasan shika-shikan rashin mutuncin daya shiryama kowa a gidan akan cikinsa.
      Sosai abinda Jawaad yayi ya kuma birkita zuciyar Mummy, hakama Aamilah da tasan dokar.

      A bakin ƙofa Jawaad da Qaseem sukaci karo, kallon kallo sukaima juna Jay ya ɗauke idanunsa ya raɓa Qaseem ɗin ya cigaba da tafiya tamkar baisanshi ba.
     Shiko Qaseem ya bisa da kallo har sai da Jawaad ya shiga mota yabar gidan sannan ya taɓe bakinsa, cikin falon ya ƙarasa shiga inda ya samu su Mummy yanda Jawaad ya barsu.
       “Mummy miya kawo wancan shashashan gidannan kuma a daren nan?”.
        Mummy data maido kallonta ga Qaseem tace, “Kamin wannan tambayar bayan kasan matarsa tana a gidan”.
      Zama yay yana jan tsaki, “To ba gidansu tazoba, halan zuwa yay yace su tafi taƙi dan naga yana faman haɗiyar baƙar zuciyarsa da wataran zata zama ajalin sa”.
      Kai kawai Mummy ta iya girgizawa tana haɗiye yawu da ƙyar, bayanin dukkan abinda ya faru da Shahudah ta bashi.
    Qaseem ya miƙe zumbur yana faɗin, “Mummy anya yarinyarnan ba ɓarar da cikin nan taiba kuwa da gangan?”.
       “Wace irin magana kake haka Qaseem? Yanzufa na gama maka bayani akan abinda Doctor ya faɗa mana dangane da mahaifarta ce bata da ƙwari......”
        Saurin katse Mummy yay da faɗin, “Kai Mummy impossible, a wannan fushin na Jawaad akwai magana, inkuwa har da gaskene abinda Doctor ya faɗa to lallai shi bai yarda ba, kuma zaiyi bincike”.
        “Bincike kuma Broth...?”. ‘Aamilah ta faɗa tsigil cikin sarƙewar harshe’.
      Kallonta Mummy da Qaseem sukayi, Mummy dai kuma rikitar da ita sukai, shiko Qaseem ya kafe Aamilah da idanu dan yanayinta ya tabbatar masa bata da gaskiya.
     Kafin ya samu damar yin wata magana Salman da Jack suka shigo falon.
        Wucewa Qaseem yay sama wajen Shahudah, hakan yasa suma su Mummy take masa baya su duka suka bisa.
       A yanda duk suka tarar da Shahudah ne ya tabbatar musu akwai matsala, kusan duk a tare suka shiga jera mata tambayoyi, bata amsa na kowaba a cikinsu sai hawaye da take zirararwa.
       Mummy ta zauna tare da jawo kan Shahudah ta ɗaura saman cinyarta, kanta ta shiga shafawa a hankali alamar lallashi.
       Hakan ya saka Shahudah fara sambatu da roƙon Mummy akan Jawaad, jinfa zata ɓallo musu ruwa Aamilah ta zauna tana riƙe hannun Shahudah da faɗin, “Haba sister kiyi shiru mana, ki kwantar da hankalinki bakida lafiya fa, insha ALLAHU komai zai zama normal indai Brother Jawaad ne zai huce shima, yanzu yana cikin ruɗanin rashin cikinne da halin da take ciki, amma ki bashi kwana biyu zai sakko ya fahimta kamar yanda kowa ya fahimta”.
        Ita dai Shahudah kawai tana sauraren ƙanwar tatane, amma ita tasan wanene Jawaad da abinda zai iya, ballema tun farko tariga da ta saka masa shakku akan cikin tun fil azal, tasan yanzu kam sai abinda ALLAH yayi kawai, amma tabbas akwai ƙura bata wasaba.

★★★★★

              Jawaad kam koda yabar gidan gida ya koma, amma tunda yay fakin sai ya gaza fitowa daga cikin motar, kifa kansa yay saman sitiyari yay shiru tamkar mai barci.
        Tun yana iyajin motsin wasu daga jama'ar gidan da hayaniyar yara har gidan ya koma yay tsit alamar dare yaja sosai, baka iya jiyo komai sai kukan karnika na gidajen makwafta, da yake akwai wuta kuma sai anguwar ta kuma samun nutsuwar yin shiru babu ƙarar Generators dake hana kunnuwansu zama lafiya.
     Tashi yay zaune sosai ya kwantar da kujerar da yake ya ƙara yin Balance ɗin samun yin tunanin da ƙyau, sam baya sha'awar shiga sashen nasu saboda ƙunar da zuciyarsa ke masa.
       A watannin daya ɗauka na aurensa da Shahudah bai tsinci komaiba sai takaici da ɓacin rai, kullum da salon fitinar da take kawoma rayuwarsa, ga hargitsin aiki gana cikin gidansa.
     Ya tuna maganar kakansa daya taɓa faɗa masa lokacin aurensa da Shahudah.
       *_“Jawaad naso ka auri irin wadda rayuwarka keda buƙata, amma tunda haka ALLAH ya tsara muna maka fatan alkairi, sai dai ka sanifa shi ubu mai ƙyau abin san kowane, sai dai ba kowanne ƙyaƙyƙyawa bane kake samunsa ciki da waje mai amfani da amfanarwa, dakamar wuya asamu cikakken farin ciki tattare dashi inhar akwai tangarɗa tun fil azal, wani lokacin daga yanayin ginin abunne a zuciya da kuma rayuwa, wani lokacin kuma tun usul akwai rashin nagarta musamman idan anci karo da sakacin iyaye wajen rashin yin ginin da addini ya koyar, bazaka fahimci komai daga zantukana ba Jawaad sai nan gaba kaɗan, irin waɗannan yaran abinda zaku haifane abin tausayi dakai kanka da za'a jefa cikin garari ba suba, amma dai ALLAH ya sanya albarka da alkairi a ciki, ALLAH yasa muce gamma da akayi”._*
       Nannauyan numfashi Jawaad ya sauke yana rumtse idanu da ƙarfi, wato irin waɗannan tashin hankalin da jahilcin ne kakansa ya hango masa tattare da auren Shahudah, wanda shi a baya tunaninsa bai kawo kan hakaba, kawai yafi kallon rashin isashshiyar tarbiyyarta zai tsayane ga taɓara kawai, kuma zai iya canjata da wuri tunda tana sonsa.
     A irin kima da nagartar Dad ɗinsu bai ƙyautu ace zuri'arsa ce a wannan yanayin yahudancinba da sunan wai ƴancin kai, shikenan dan ƙaddara ta shigar dakai cikin wata rayuwar da ba takaba saika mantar da kanka da zuri'arka tushensu da addininsu da al'adunsu?, ansan a shekarun da suka ɗauka cikinsu dolene a samu raunin al'adunsu, dan yau da gobe ta wuce wasa, ballema ba zuwa gidan sukeba su, to amma bai dace a duk inda ka tsinci kanka ya zam ka manta da addininka da koyarwarsa ba, dan ako ina kake ALLAH ya wajabta maka yinsa da kuma neman ilimin sani a kansa.
        Lallai yana ganin anzo gaɓar da zai tunatar da Dad da Mummy abinda suka mantan kokuma son zuciya ya sakasu maidashi baya saboda son ƴaƴa ko sakacinsu.
        Haka Jawaad yayta tunani bai fargaba sai kiran sallar asubahi yaji, nannauyan numfashi ya sauke tare da kallon agogon dake a tsintsiyar hannunsa.
       Ya ɗan matse idanunsa da sukai masa nauyin buƙatar barci, da ƙyar ya yunƙura ya tashi zaune sosai, ya buɗe motar ya fita ya nufi ciki.
     Ji yake tamkar yabar gidannan gaba ɗaya yau ɗinnan.

_________________________
BILKEESU
_________________________

             Sosai na samu nutsuwar zuciyar zama dasu Ummie, dama can ni a rayuwata inahar zaka nunamin ni mutumce kamar kowa mai daraja tuni nake sakar maka jiki, to yanda su Ummie suka amsheni sai hakan ya dasamin ƙaunarsu.
        Nazifa ce dai har yanzu muna sama-sama ne, niko halinta bai dameniba ko kusa, abinda ya kawoni ma nafi son maida hankali kansa ba matsalar wani ba.
     Dan na tabbata a halin yanzu wannan ilimin dazan nutsu na samune babbar katangata kuma gatana koda anan gaba idan ALLAH yasa muna a cikin masu tsahon rai.
      Su dukansu babu mugunta suke nunamin karatu, hatta da Nazifa da batayina tunda na fahimci mayyar mathematic ce sai nake raɓarta ta koyan abinda ban fahimtaba.
      Zakusha mamaki yanda takan zauna ta koyamin dukda anayine ana dizgani.
       Ahankali sai na fara fahimtar halin kowanne a cikinsu har ita Nazifar kuwa, tunda na fahimci yanda halin kowannensu yake saina ƙara ɗaura ɗammarar zama dashi a yanda yaken danna ribantu da hakan.
        Bani da lokacin hatta tunani a yanzu, na maida dukkan hankalina ga karatun sai ko bautar ALLAH dake a gaban komai, kullum kuwa ina ƙoƙarin miƙama UBANGIJI kukana.
       Abinda ya kuma sakamin nutsuwa da Nazifa sam bata wasa da salla, lokuta da dama ma ita kema su Ummie faɗa akan su tashi suyi akan lokaci, idan har zan tashi da daddare da taji motsina itama zakaga ta tashi tayo alwala tazo kusa dani ta shinfiɗa abin salla.
       Hakan dasu Ummie sukaga munayi sai suma ya fara tasiri a ransu, sai suka fara cewa suma mu tashesu dan ALLAH.
       Daga nan sai muke tashinsu, itama Rebecca sai take tashi taita addu'oinsu, dan bata iya barcin da muma mun tashi, fatanmu dai ALLAH ya tabbatar da nasara a garemu akan wannan jarabawa.
       Kusan halin ƙuruciya, a irin wannan shekarun namu dama zakaga daga harkar makaranta saina samari ke tasiri a rayuwarmu, dan idan mun zauna hira su Zuhrah kanta hirar samarinsu, nidai bani da abin faɗa, dan ko'a mafarki ban taɓa saurayiba, na tuna sanda ina gidanmu na haya har habaici akema innata akan banda farin jinine, bata cewa komai, iyakarta murmushi kawai.
      Sai zuwa yanzunne nima nake gasgata maganarsu, lallai banida farin jinin, dan nidai ba'a taɓa cewa ana sonaba, ko irin soyayyar nan ta ƙuruciya ban taɓa yiba, sai dai naga ƙawayena nayi harma a bani saƙon musayar wasiƙar soyayya na kai.............✍🏻

Page 25

.............Wanka ya samu yayi da ruwan ɗumi danya rage nauyin jikin, sannan yay alwala ya fito, jallabiya kawai ya  saka ya fito zuwa massallacin gidan dake a ƙofar kiga.
      Ana idar da salla ya fice abinsa, dama yau a makare yazo, dan haka yay sallar a ƙofa-ƙofa, bai yarda tsayawa gaisuwa da kowa ba har kawunansa, ya gudo gida ya kwanta.
          Duk yanda tunanin yaso masa tasiri barcin da ya keji sai yaci ƙarfinsa, kafin kace mi ya fara sauke numfashi a hankali alamar dai yayi nisa cikin barcin.

        A makare ya tashi zuwa office, dan haka yayta komai cikin hanzari harya samu ya kimtsa, yayi ƙyau sosai, ya fito yanata baza ƙamshi kamar ko yaushe.
        Gimba da tun ɗazun yake gewayensa da tunanin ko lafiya?, yay saurin miƙewa daga wajensu mai gadi ya nufosa.
        Sam babu walwala a fuskarsa, ɗaure take tamau babu sauƙi,  kusan biyar daga matasan ƴammatan gidan da suka fito zasu wuce makaranta suka shiga gaishesa kowacce zuciyarta a narke da ƙaunarsa.
       Hannu kawai ya ɗaga musu dan baijin zaima iya motsa bakin balle aje ga magana, da sauri Gimba ya buɗe masa motar saboda yau dai yasan babu wargi a wajen boss.
        Shima sai da ya zagaya mazaunin direba sannan ya fara gaishesa.
     Shiru Jawaad ɗin bai amsaba, Gimba ya kallesa ta mirror, yanda ya gansa kwance a jikin kujera idanu a lumshe ya tabbatar masa lallai akwai matsala.
     Bai sake cewa komaiba ya tada motar suka fice daga gidan.
      Sai lokacinne Jawaad ya amsa masa gaisuwar, tare da faɗa masa inda zasuje kafin Office.
       Jin asibiti ya saka gimba tunanin ko baida lafiya ne?.
         A ƙofar gida sukaci karo da motar yaran da aka bama Jawaad ɗin yanzu a Office saboda tsaro su huɗu, gilas ɗin motar kawai Gimba ya sauke suka matso suna gaisheda Jawaad ɗin cikin girmamawa.
        Idanunsa ya buɗe yana ɗaga musu hannu, bayani ɗaya yay masa akan Sir Ahmad yace yau zasu fara gudanar da aikinsu, daga yanzu duk inda zai saka ƙafa dolene sai da su.
      Numfashi kawai ya basu, yay musu nuni su shiga mota kawai.
      Umarninsa sukabi, su ka rabu biyu kowacce mota mutum uku, ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta Jawaad tana a tsakkiya.
    Shi sam baya buƙatar wasu securitys tare dashi, amma Sir Ahmad ya matsa sosai akan yabar barin Jawaad ɗin na yawo haka tun randa abin nan ya faru tsakaninsa da Qaseem.
     
         Shigarsu asibitin suka samu waje sukai fakin, kasa daurewa Gimba yay ya juyo a ɗarare yace, “Boss ko baka da lafiya ne?”.
     Idanu Jawaad ya buɗe a hankali kan gimba, sai kuma yay masa guntun murmushi yana girgiza kai alamar (a'a).
        Duk da Gimba bai gamsu ba haka ya fito, Security ɗaya kuma ya buɗema Jawaad ɗin motar, yaja kusan seconds ashirin sannan ya zuro ƙafarsa ƙasa ya fito.
         Baƙin eyeglasess ɗinsa ya ɗora saman ido alamar dai babu sassauci kenan, yana tafe suna take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.
        Ganinsu kawai ya isa ya baka tsoro, gasu duk sunsha baƙaƙen suits da eyeglasses, fuskoki kam ba'a cewa komai saboda ɗaurewa.
        Sun samu girmamawar mutane musamman ma'aikatan asibitin, duk da fuskarsa ɓoyayyar fuskace da ba kowa yasan matsayinta ba, amma yanayinsa da kwarijininsa sun saka mutane ganin girmansa a idanunsu, sannan yanayinsa ya tabbatar da ba ƙaramin mutum bane koda a hasashe saboda mazajen dake rufe da bayansa harda masu binduga a hannu su uku.
     Sai ƙalilan da ba'a rasaba da zasu iya sanin fuskar, musamman tsananin kamar da yake da mahaifinsa.    
        Tsaye yay dai-dai saitin matar da ke a reception ɗin, duk sai ta rikice, Jawaad ya kalli gimba dake gefensa a ƙasan maƙoshi yace, “Office ɗin Doctor Tayyeb”.
       Gimba ya juya ga matar yana maimaita mata.
   Kai ta shiga gyaɗa masa baki na rawa tana faɗin, “Ok ok Sir” tai maganar tana ƙoƙarin kiran wayar ogan nata Doctor Tayyeb.
       Basu san mi ake cemata daga canba, tanata dai ƙoƙarin masa bayanin dazai fa himta amma da alama cewa yake bazai samu ganinsu ba....
      Tsawa ɗaya daga securitys ɗin Jawaad ɗin wani ya daka mata, hakanne ya sakata sakin wayar jikinta na tsuma, Gimba yace ta haɗasu da wanda zai kaisu Office ɗin ko ita ta fito ta rakasu.
      Duk fa wannan dambarwar da ake Jawaad na tsayene yana saurarensu hannayensa duka biyu a cikin aljihu, nazarin asibitin da mutanen dake kaikawo a cikinsa kawai yakeyi, duk da ma tun shigowarsu kowa ya nutsu waje guda dan yanayinsu ya nunama kowa dama ba ababen wasa bane balle a gansu a ɗauke kai.
        Wata Nurse ce tai musu rakkiya har Office ɗin, tana ƙoƙarin yin knocking Jawaad ya ɗaga mata hannu alamar kar tayi.
     Ja baya tai kanta a rissine alamar girmamawa a garesa.
     Gimba ya tura ƙofar Jawaad ya shige kansa tsaye, yayinda yaransa suka jeru a ƙofar kamar waɗanda sukazo kama ɓarawo😂.
   
       Takun takalman Jawaad suka saka Doctor Tayyeb saurin matsawa daga jikin budurwar daya ƙwakume a Office ɗin yana lalubewa, itama Nurse ce, sanye takema da Uniform ɗin asibitin.
        Wani wawan tsaki Jawaad yaja yana ɗauke kai daga garesu, Budurwar dukta ruɗe sai duƙar da kai take cikin alamun jin kunya da firgici, shi kansa Doctor Tayyeb ɗin a firgice yake, ganin Jawaad a asibitinsa da kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login