Showing 9001 words to 12000 words out of 104658 words

Chapter 4 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

188

gwamnati ta saya, shi kuma Abdul yana da ilimi, sai yazama shine ya tsayama jama'ar ƙauyen da duk abinda ya shafa har sai da aka biyasa haƙƙinsa, ya kuma basu shawarwarin su sake sayen wasu gonakin dan ga damar yin noman rani ya sake samuwa, ɗari bisa ɗari suka amince da shawararsa da ga manyansu har matasansu.
Turawan da sukazo wannan aiki sai al'amuran Abdul-aziz suka matukar birgesu, hakan yasa suka jashi jikinsu ya zama abokin hirarsu duk da kuwa ba ko yausheba, dan shima yanada harkokinsa da yakeyi.
Turawan ba cikin ƙauyen suke kwana ba, zuwa yamma suke tashi su koma cikin birni inda suke da masauki, hakan yasa suka sake jan ra'ayin Abdull har yasan mazauninsu, suma kuma sukasan nasa.
Kafin kace mi shaƙuwa ta shiga tsakaninsu sosai, halayensa na neman nakai da dattako na sake birgesu, gashi dai ba wani babba ba can amma akwai halayyar manya, kafin su kammala aikin ƙaton dam ɗinnan da ko Abdul baisan iyakarsa ba shakuwarsu ta wuce misali, dan har bilkisu ya kaimasu suka gaisa, sannan wani lokacin yakan sakata tayi abinci ya kai misu, acewarsu suna koyon cin abincin arewacin Najeriya.
Bayan kammala aikin nasune sukai haramar komawa, dukansu sun fuskanci halin kewa na tsantsar sabo, sai kowanne ya tsinci kansa a damuwa, lokacin da zasu tafi suka damƙa gidansu kacokan ga Abdull ƙyautar ALLAH, dama saya sukai dansu zauna harsu gama aikinsu, ganin sun kammala kuma sai suka bashi da zasu tafi, rasama mizai faɗa musu yayi dan susan yaji daɗi, dan gidane mai azabar ƙyau da tsari, kowa yasan dai yanda turawa suka amince da gyaran muhalli, to shima wannan ya ɗauki tsari na musamman, gashi a anguwar manyan mutane.
Duk sai da ya ɗauki ƴan uwansa ya kaisu suka sanya albarka da matan babansa, hakama dangin mahaifinsa dake ƙauye, mota biyu suka ciko sukazo suka tayasa murna. Sannan ya maida iyalansa can, harda mama maryam yaso amma mijinta da ita kanta suka ƙi, aganinsu yaya zasuje suyima ƴaƴansu zaune dukda dai gidan babbane. Dole Abdul ya haƙura amma ya ɗauke ƙannen Bilkisu biyu da suka rage ya maida gabansu, dan ɗaya a cikinsu itama tayi aure.
Shekara ɗaya kacal da faruwar hakan saiga turawannan sun dawo Najeriya, ashe zuwa sukai tafiya da Abdull, dan su dai yamusu har ƙasan zuciya, bayan ɗan kace nace da aka samu akan tafiyar tasa dai da ga karshe ALLAH ya amince su mama maryam suka barshi ya bi turawannan, sai dai yabar matarsa a nan gida Nageriya.
Wannan tafiya itace ta sake canja komai da ga rayuwar Abdul-Aziz Yusif Tafida, cikin ƙankanin lokaci ya bunƙasa, dan kuwa acan ƙasar turawannan ashe sun jashine akan harkar noma da kiwo irin nasu, suka sake wayar masa da kai, shima ya sake wayar musu da kai akan nasa sanin da ALLAH yay masa, dama su kunsan komansu da tsari, tamkar kamfani nasu yake, sai suka dirasa matsayin babba mai kula da komai, a duk bayan wata uku yake zuwa gida Nageriya yay wata guda ya koma can ƙasar, sannan anan Najeriya ma ya kafa jijiyoyi musamman a ƙauyensu, dan kuwa ya tallafa ma matasan ƙauyen da magidanta akan noman da kiwo, harma ya kwashi wasu acikin matasan suma sunacan turai ɗin tare dashi.

Rayuwa ta matukar sauyawa, duniya ta bama Abdul-Aziz babban filin fantamawa a cikinta, abin birgewa kuma yana amfani da damarsa sosai wajen gina kowansa, tamkar ƴan uwansa da abaya suke ganin sun fisa yanzu ya zamar musu runfa, dan kuwa dukkan dukiyarsa da ke Najeriya su ya ɗaura akanta, dukkan sirrinsa sun sanshi, duk abinda kaga bai sanar musuba to lallai sai dai sirrin da ya shafi matarsa ko mahaifiyarsa, wannan kam da ga shi sai su sai ALLAH, har zuwa yanzu kuma basu haihuba, kuma bai taɓa yunƙurin sake aure ba, hakama babu wanda yace masa ya sake auren ko za'a dace. Yana son matarsa sosai, dan haka bai taɓa nuna mata ya damu da rashin samun ƴayansu ba dukda yana kwaɗayin son ganin tsatsonsa a duniya.
Ba a cikin ahalinsa kawai yake taimako ba, hatta da mutanen gari ta kowanne fanni amfanuwa suke da tagomashin arziƙinsa, ya zama bango abin jinginar kowa, sannan runfa mai lulluɓe zafin rana ga kowa, dukda hakan kuma bai isa zama mai ƙyautata zukatan kowa ba, dan ko UBANGIJI daya hakicci ɗan adam baya iya masa............✍🏻

Page 5

...........A yanda Abdul-Aziz ke bautama al'umma da hidimarsa, sai ka ɗauka bai ma san ciwon dukiyarsa ba, kokuma a banza ya sameta ba da guminsa ya taraba. Abubuwa yake na bajinta ko tunanin kuɗin zasu iya ƙarewa bayayi, kafin kace kwabo sunansa ya zauna ɗam abakin mutane, ko yaro ƙarami ka ambatama sunan Alhaji Abdul-aziz tafida da gudu zai amsa maka harma yay maka sharhi gwargwadon fahimtarsa.
     
        Rayuwa ta ci gaba da shurawa, yayinda wasu da ga cikin jama'a suka fara kafa dandalin kiranye ga Alhaji Abdul-aziz zuwa ga siyasa. Duk da yana jinsu, kuma yana ganinsu, sai ya maida kansa makaho kuma kurma akan batun, dan shi sam siyasa bata cikin tsarin tafiyarsa ko burinsa.
       A na cikin wannan yanayinne ya fara ginin wasu katafaren gidajen gona guda biyu, amma a jihohi mabanbanta. Sai wani katafaren family house da zai haɗa dikkan ahalinsa waje guda, kuma kowa da ɓangarensa babu ruwanka da shiga sabgar gidan ɗan uwanka, Wannan aikinne ya kauda hankalinsa ga nacin jama'a na son ganinsa cikin siyasa.
        Lamarin kuɗi sai mai su, kafin kace wani abu gidajen gona sun kammala, hakama gidansu, matasa da yawa harma da magidanta sun samu aikinyi a ciki, abubuwan alkairi harsun fara fitowa ta gidan, sannan suma sun koma sabon gidansu shi da duk sauran ƴan uwansa da iyalansu, mama maryam ce kawai taƙi tunda dai aure takeyi, sai Alhaji Abdul-aziz ya sayi gida kusa da su suma suka koma.
     
      Duk yanda Alhaji Abdul-aziz ya so zamewa siyasa lamarin ya faskara, dan kuwa sosai ake masa bibiko da naci harta hannun aminan mahaifinsu da mama maryam kanta da mijinta.
       Rana ɗaya suka ware wajen ritsashi, dan gangami akai masa na musamman tare da manyan mutanen da zuciyarsa kejin kunyar bijiremawa. Ba da son ransa ba dole dole ya amsa da addu'ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.
   Kowa ya amsa da murna da farinciki, tare da masa addu'oin na musamman wajen bashi nasarar jagorancin al'umma cikin sauƙi.
       Ƙyawawan halayensa ne yasa shi kasancewa mai kishin jama'ar sa, har suma sukeji a ransu zasu iya sakar masa ragamar rayuwarsu ya mulka, babu ɓata lokaci rana tsaka ya afka siyasa bisa jagorancin abokai da matsawar mutanen gari da suke ganin ya cancanci zama jagoran nasu.
     Koda ya tuntuɓi ƴan uwansa sai suka bashi goyon baya, dan duk ya riga ya gama siye zukatansu, zuwa yanzu ƙauna ta haƙiƙa suke masa da bashi kulawa wajen jansa jikinsu, (kowa yasan ziciya da son mai ƙyautata mata), dama kuma suna cikin waɗanda aka kama ƙafa dasu harya amince da batun.
      Mama maryam ma sai ta bashi goyon baya sosai, tare da binsa da addu'ar alkairi, sai dai sam Bilkisu abin bai kwanta a ranta ba, amma babu yanda ta iya tabi ayarin ƴan binsa da addu'a tunda taga kowa ya bashi goyen baya, bai kamata ita ta zama ƴar ta wareba a cikinsu.

            Shekarar da Abdul'aziz ya shiga siyasa a shekarar Bilkisu ta sake samun ciki a bazata, ai farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu bashi da kwatankwaci sam.
      Bilkisu tanata rainon cikinta hankali kwance, ga kulawa tana samu ga kowa, watanta tara cif da wasu kwanaki ta haife ɗanta namiji sargaɗeɗe, inda ranar suna yaci sunansa *Jawaad*.
            Jawaad ya tashi cikin kulawar dangi da mahaifa, gashi yaro abin san kowa a zuciya, dan danan ya fara wayo, gashi da jikin girma masha ALLAH, shekararsa ɗaya da rabi Bilkisu ta yayesa, dan yana tafiyarsa ko ina, ga haƙora reras a baki, sai dai kumafa baya magana, dan har Jawaad ya kai shekara biyu da wasu watanni baya magana, bayama yunkurin yinta, hakan yasa kowa yake ɗauka ko bebe ne, dan sun tabbatar yanaji da kunnensa, tunda idan akai masa magana yana fahimta, bakinsa ne dai baya furtawa. Tunma Bilkisu na damuwa harta daina ta maida komai hannun ALLAH, dan koda Alhaji Abdul-aziz yace zai kaisa asibiti itace ta hana, acewarta a jira aga zuwa wani lokaci dai.
     Domin farin cikinta ne kawai ya so barin zancen sai dai kuma da ga baya saiya kasa hakan, dan abin na damunsa, ga dai Jawaad da wayau harma na tsiya, amma yaro bai da maraba da dutse a fannin faɗin albarkacin baki. Kuma zama yay ya lallaɓa bilkisu akan kai Jawaad ɗin asibiti, da kyar ta yarda dai aka kaishi, sai gashi kuwa an gano yana da matsala ne a ƙasan harshensa da maƙoshinsa, nan akai masa aiki yay tsawon sati uku yana jiyya kafin ya warke su dawo gida. Ba'aja wani dogon lokaci ba Jawaad ya fara magana, zo kuga murna ga wannan ahali, kowa na sake miƙa godiyarsa ga ubangijin al'arshi buwayi gagara misali.
         Babu daɗewa da samun lafiyar Jawaad, a cikin matan Alhaji Yusif ɗaya ta rasu, Wannan rasuwa ya mugun girgiza wannan ahali sosai, musamman ƴaƴanta.
         Bayan wucewar komai na rasuwar jama'a suka takura ma Alhaji Abdull akan ya fito takarar shugabancin jihar, sam ki yayi, danshifa dama bai shiga siyasa dan yazama shugaba ba, ya shigane kawai dan ya zama jagora da zai tsaya kan masu mulkin su tallafi talakawa kawai, amma badan yay mulkiba.
     Nanma dai caa aka sake masa, babu yanda ya iya sai ya amince kawai yabi ayarin ƴan takara.
     Abin zai baku mamaki idan nace muku komai yimasa akeyi, duk da talakawa sunsan yanada kuɗin da zai iyama kansa komai haka suka tattalafa da kansu sukai komai, acewarsu ai sune sukace yayi, dan haka sune zasuyi masa komai.
      Wannan lamari ya sake girgiza duniyarsa, dan yarasa miyasa jama'a suke masa irin wannan makahon soyayyar?

Ni ko nace Alhaji Abdul ai masu iya magana kance (Nagari na kowa, mugu sai maishi).

       Bayan kammala duk wani hatsaniya da ruguntsumi na kamfen akai zaɓe, tunma ba'ai nisa ba kowa ya fahimci Alhaji Abdul-aziza Yuseef ya bige abokin takararsa,  tunkan sakamako ya fito mutane har sun fara shagulgula, ana faɗa gari ya sake harmutsewa.
     Shi Alhaji Abdul-aziz ma ana faɗan yaci kuka ya kamayi, dan haka kawai yaji zuciyarsa ta karye ya shiga share ƙwalla.
      Lokacin Jawaad na jikinsa yana wasansa, sai ya tsirama mahaifin nasa ido yana kallo duk da baisan mike faruwa ba, murmushi Alhaji Abdull yayi ganin kallon kurilla da Jawaad ke masa, ya ja kumatunsa kaɗan yana faɗin “Haba ɗan sanda kallon fa na minene? Yau nauyi ya haye Abbanka mai girman gaske, kai min addu'a ALLAH ya bani ikon saukewa”.
       Duk da Jawaad baisan ma'anar maganarba sai ya ƙyalkyale da dariya shima yana jan kumatun abbansa kamar yanda yay masa.
     Murmushi Bilkisu da ke gefensu tayi kawai, dan batasan dalilin da yasa mijinta keson kiran ɗan nasu ɗaya tilo police ba, tun baima kai hakaba yake kiransa da suna JAY -P!, tunma bata fahimci ma'anar sunanba har dai ta tambayesa ya gaya mata.
    Ko a lokacin batai masa jayayya ba sai fatan alkairi yazama ra'ayin Jawaad ɗin kenan idan ya girma shima.
    Tun a lokacin ya fara amsa wayoyin taya murna har ma kansa ya nema fara ciwo.

         Bayan abubuwan da suka biyo baya dai a ƙarshe aka rantsar dasu, Alhaji Abdul ya koma gidan gwamnati shi da iyalansa, sai dai su mama maryam basu bisuba, sunce zasu rayu anan gidan da ya saya musu.
      Harkar mulki ta fara gudana, inda Alhaji Abdul yazoma duniyar ƴan siyasa da sabon salo mai ban mamaki, gaba ɗayan albashinsa ya sakashi a taskar gwamnati, an ware aiki na musamman za'ayi ma talakawa aiki da kuɗin, sannan ya dage tsayin daka wajen gyara jiharsa ta kowanne fanni, dandanan sunansa yay amsa kuwwa a ƙasar, komansa ya zama abin koyi da alfahari ga al'ummar da yake jagoranta, ya zama zakaran gwajin dafi sannan tauraro mai haskawa da zamaninsa.
     Gashi sam bashi da girman kai, kowa nasane, babu ruwansa da wani banbancin jam'iyya ko yare, tsakaninsa da ALLAH yake aikinsa cikin ƙwarewa da jagorancin UBANGIJI.

         Adadin shekaru na hawan farko suka cika ga duk waɗanda suke kan mulki, mai makon Alhaji Abdul-aziz ya koma sai jama'a suka nuna shugabancin ƙasar gaba ɗaya suke bukatar ya karɓa. Wannan lamari yaso gigitashi sosai. A fili ya nuna sam bazata yuwuba, amma ina jama'a sun tsaya kai da fata suna masa magiya da kai kukansu wajen ALLAH.
     To duk abinda ALLAH ya hukunta sai ya kasance koda bawan da abin ya shafa bayaso, kana nakane ALLAH yana nashi, nashiko shine gaskiya.
       ALLAH ya ƙaddara sai ya zama shugaban ƙasa, sai ga shi kuwa ya zama, dama wanda yake kai ya gamane gaba ɗaya.
     
      Zuwa yanzu Jawaad ya girma, dan shekarunsa bakwai a duniya, yaro mai wayo da ƙyawawan ɗabi'u, kamar yanda ƴaƴan talakawa ke makarantar gwamnati sai ga Jawaad ma a ciki, dan mahaifinsa yace ita shima yayi, a ma ƙauye, to ɗansa ma can zaiyi babu tantama. Aiko hakance ta kasance, dan sai ga ɗan shugaban ƙasa a makarantar gwamnati, abin ya burge jama'a, tare da jan hankali ga sauran masu mulkin suma duk sukaita maida ƴaƴansu can.
       A gefe kuwa Alhaji Abdul nata sake cusama Jawaad son aikin ɗan sanda, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi yayi tasiri a ran yaron, dan babu sunan da yake ƙauna a ransa kamar *JAY-P!* da Abbansa ke kiransa dashi, ma'ana *_(Jawaad Abdul-aziz Yuseef police)_*.
      Ko kayan wasan Jawaad duk zaka samu suna kamanceceniya ne da kayan jami'an tsaro, abin ya riga ya shiga yaron jini da ɓargo.

      Shekarar Alhaji Abdul-aziz ɗaya akan mulki ALLAH ya jarabcesa da ciwon da har ya kwanta, ashe hawan jinine bawan ALLAH, kwanansa uku kacal da wannan ciwo zuciyarsa ta buga yabar duniya😭.
     
     Tashin hankali kenan wanda ba'a saka maka rana, wannan lamari harma bansan a yanda zan musaltashi masu karatu su fahimta ba, dan kuwa ƙasarce baki ɗaya ta harmutse tare da komai na cikinta, mutuwar Shugaban ƙasa Abdull-aziz ba batun iyalinsa kawai akeba, maganar al'umma kawai akeyi, waɗanda sukeji basu taɓa gamo da rashi mai taɓa zukata da aiyuka irin wannan ba.

       Tunda wannan rasuwa ta gudana bilkisu ta rasa hankalinta, sam an kasa gane kanta, hauka take tuburan wanda ya kai ga har an rufeta a ɗaki ma.
     Mama maryam tsohuwa mai tawakkali da hakuri, baka ganin hawaye saman fuskarta sai dai na zuci kawai.
     Ƴan uwansa kam su kansu ka kalla abin tausayine, lamarin yay masifar ruɗasu, dan Abdul mai biyayyane a garesu tare da ƙyautata musu, suka tuna irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa da bajintar da yay musu a rayuwa sai suji hankalinsu ya kuma ƙololuwa a tashi, sunyi kuka harsun godema UBANGIJI.
        ALLAH sarki Jawaad, duk da bai kai hankalin da za'ace ya fahimci komaiba ya ɗanyi kukansa ganin kowama yanayi, musamman ma halin da mahaifiyarsa take ciki na hauka, sai dai zuwa wani lokaci kuma sai ya saki ransa, yakan dai zo ya tambayi mama maryam ina Abbansa? Yaushe ne zai dawo?.
    Sam bata ɓoye masa, takan ce masa Abbansa ya tafi inda ba'a dawowa.
     Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin kuma yay zugum yana tunani kafin kuma ya saki ransa ya koma wasa cikin yara sa'oin sa.

       A haka aka share wasu watanni, riƙon Jawaad ya dawo hannunsu mama maryam, bilkisu kuma ana cigaba da nema mata magani, dan bata ma ƙasar an kaita asibiti.
     Haka rayuwar ta cigaba da shurawa, an maido Bilkisu gida, kamar taji sauƙi sai kuma abu ya dawo sabo, lokacin har Jawaad ya fara wayo, yana shekara ta goma sha huɗu, ajin secondary js2, ranar wata juma'a sai aka wayi gari Bilkisu ta bar gida, nema iya nema anshasa amma babu ita babu dalilinta, lamarin ya girgiza mama maryam har itama ya zama sanadi a gareta.
      ALLAH yayma mama Maryam rasuwa sakamakon ɓatan bilkisun itama, wannan karon kam Jawaad yaji zafi sosai na rasuwar kakarsa da ɓatan mamansa, yayi kuka har abin ba'a cewa komai.
    Ƙanwar bilkisu taso riƙon Jawaad ya dawo hannunta amma dangin mahaifinsa suma suka ƙi, sai Abba Naseer babban yayansu Alhaji Abdull na farko a gaba ɗaya gidan ya amshe shi ya koma hannunsa da zama.

        *★★★★★★★*

      Gata sosai Jawaad yake samu a wajen ahalinsa, dan a ganinsu  lokacin da zasu nuna jin daɗin ƙyautata musu da mahaifinsa yayi kenan, ɗan gatane ta kowanne fanni, riƙonsa ake tamkar yana gaban iyayensa, ƙilama idan sune bazasu masa wani gatanba irin haka.
     Kamar yanda marigayi Alhaji Abdul ya ajiye burinsa akan Jawaad na zama ɗan sanda sai ALLAH ya amince masa yasamu cikar burinsa ta hanyar cusa son aikin ƴan sanda a zuciyar Jawaad, sosai ya ke son aikin ɗan sanda, wannan shine burinsa, mafarkinsa, kuma fatansa. Lokaci ƙanƙani ya samu cikar burinsa kodan tsatson da ya fito, da dattako irin na mahaifinsa da baza'a taɓa mantawa ba.

*______________________________*

        Shekaru sun shuɗa, komai ya sauya, Jawaad ya zama abinda yay fata, ya girma ya zama babban mutum kamilallen saurayi mai aji da tarin cikar kamala da kwarjini na haƙiƙa, komansa na nagartattun mutane ababen koyi da dubi, gaba ɗaya halayen mahaifinsa sun dawo jikinsa, sam bashi da damuwa sai ta aikinsa tare da ƙyautatama jama'a.
    Mutum ne da bai damu da abinda bai shafesa ba ko ba'a sakashiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi, idan har bakai ne ka sakashi a lamuranka ba bazai taɓa shiga ba, bashi da son hayaniya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login