Showing 45001 words to 48000 words out of 104658 words
Chapter 16 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete
ɗumin hawaye kawai nakeji suna bin kumatuna, duk da naga rashin jin daɗin iyalansa hakan bai hanani ƙwaɗayin binsu ba, koba komai burina nayin karatu mai zurfi ashe zai cika a duniya, insha ALLAHU zanyi haƙuri da kowane irin halin daza fuskanta daga garesu domin samun cikar burina”.
Abu kamar wasa sai ga magana ta zama babba, dan kuwa dai Kawu Ali cayay nai shiri mu wuce, ba kuma saina ɗauki komi ba, ni kaɗi suke buƙata.
Tashi nai nayi wanka kamar yanda Yaya Shu'aibu ya umarceni, sai gani na fito tsaf cikin irin kayan da Sani ɗan gidan Uwargida ya bani kala uku.
Yanda na ɗanyi tsaf na kula ya sakasu mamaki, dan sanda nake ɗazu kam tamkar an kwatonj da ga bakin kura ne.
Kewar Yaya Shu'aibu kawai naji, amma Inna da Lawusa banji komaiba kam, Yaya Shu'aibu ya kwantarmin da hankali akan ai tunda inacan zai dinga zuwa dubani, da dai kam baya zuwa, dan sau ɗaya ma ya taɓa zuwa gidan, tunta kuma matar Kawu Alin tai masa wulaƙanci shi da inna bai sake zuwa ba koda wasa, amma yanzu darajar zan zauna a gidan zaike zuwa insha ALLAHU.
Yamin nasiha yanda zanyi ƙoƙarin zama da kowa lafiya ba tare da anyi kuka da niba, ya sake maimaitamin muhimmancin haƙuri a duk halin da zan tsinci kaina.
Godiya nai masa cikin share hawayena.
Da zamu wuce har mota suka rakomu, Kawu da matarsa suna a mota ɗaya, yaransuma motarsu daban, to nima sai akace na shiga motar yaran nasu.
Ina kallon namijin baiso hakanba, dan harda guntun tsaki yaja, macenma tanata ƙunƙuninta da ba kowa kejiba.
Suna gaba niko ina zaune a baya a maƙure tamkar wadda aka sace, a haka muka bar anguwar su Inna na ɗaga mana hannu, niko ina share hawayen sabo dana farayi dasu.......
________________________
JAWAAD
________________________
Koda suka baro gidan Alhaji kokino station Gimba ya nufa dasu, Jawaad kawai ya fita a motar amma banda Aliyu, dan ɓoyensu akeyi ba kowa yasan da dawowar tasuba.
Gimba ya juya da mota domin maida Aliyu gida, yayinda wani ya ƙaraso da sauri ya amshi kayan hannun Jawaad bayan ya gaidashi cikin girmamawa.
Fuskarshi da ɗan murmushi ya amsa masa, yana gab da shiga Office ɗinsa ya hango Qaseem na fitowa daga Office ɗinsa cikin hanzari, da alama dai wani uzirin zaije, baki Jawaad ya taɓe ya shige abinsa.
Aiki garesa danƙam a office ɗinan, harma tunanin ta ina zai fara yakeyi, ya zauna yana sauke numfashi bayan ya rataye rigar suit ɗinsa jikin kujerar.
Yana duba sabbin files ɗin daya iske a saman tabir ɗinsa yana murmushi sai kace wani zararre, shi kaɗai yasan mi yake tufƙawa a zuciyarsa.
★★★★★★
Saboda ayyukan da yayi sosai, ga mitin da suka zauna bai bar office da wuriba, lokacin da suka hau titi gimba ke tambayarsa ina zasuje? Sai kawai ya bashi amsa da suje gida, dan haka kawai yakejin sha'awar zuwa gidan yau kodan yaga ɗan tayin cikinsa yaji sanyi, duk da bashi da tabbacin Shahudah bata aikata abinda tai niyyaba, tunda yasanta da taurin kai.
Gidan gaba ɗaya babu wuta, hakanne ya bashi mamaki, dan koda babu wutar nepa akwai ƙaton janareto da ake kunnawa da daddare.
Ba tare da ya fita a motarba ya cema gimba yaje ya duba mike faruwa da janareton, dan yasandai ba lafiya ba, tunda dama kullum shike hidima akansa, koda baya gari jan... Ɗin ya samu matsala basajin kunyar kiransa su sanar masa duk da kuwa ALLAH ya basu arziƙi gwargwadon ikon da suma zasu gyara matsalar.
Sai dai bazasuyi hakanba, saboda ɗunbin dukiyar da aka barma Jawaad ɗin itace kawai idonsu ke gani.
Gimba da ya dawo yaɗan risino daga waje yana kallon Jawaad dake danna waya harken ya haske kamilalliyar fuskarsa.
“Boss waifa kaji yaƙi tashine, tun ɗazun ojo yake ta fama, yanzu hakama na iskesa yana ƙara dubawane koza'a dace”.
Janye idanunsa yayi daga kan wayar ya maido kan gimba, fuskarsa da ɗan alamun ɓacin rai yace, “Shine kuma dan wulaƙanci bai faɗaba tun ɗazun a ɗauki mataki?”.
“Wlhy Boss nima namasa wannan faɗan, amma sai ya nunamin ya faɗama kawu babba tun wajen 6, amma sai yace masa yaje sashenka idan ka dawo ya sanar maka, shikuma yazo madam tace bakama kwana gidaba”.
Tsaki kawai Jawaad yayi, ya buɗe motar zai fito, hakanne ya saka Gimba matsawa baya ya bashi hanya.
Yay gaba gimba kuma ya ɗauki ƙaramar jakkar dake gefen Jawaad ɗin ya bisa da ita, kafin ya ƙaraso gareshi harya shige falonsu.
Shahudah na kwance a falo tana kallon tasharta da tafi so saboda waƙoƙi da ake sakawa, sai dai yau anyi abin arziƙi sifikun can ƙasa aka sakasu babu ƙara sosai, kallo ɗaya Jawaad yay mata ya janye idonsa yana fara taka steps ɗin benan.
Tamkar sokuwa haka Shahudah ta bisa da ido, idanunta harsun fara tara ƙwalla......
Ƙwanƙwasa ƙofa da akaine ya sakata maida kallonta wajen, kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa da yes.
Jawaad na step ɗin ƙarshe yaji Gimba ya shigo falon yana gaida Shahudah da cewa ga jikkar boss, tsayawa yay cak saboda wani abu daya taso masa a maƙoshi na ɓacin rai, bakomai bane face tsantsar kishi mai gauraye da baƙin ciki, saboda kayan da yagani a jikin Shahudah, amma dan rashin mutunci ta bama Gimba damar shigowa ba tare da yunƙurin suturta jikinta ba.
Kasa jurewa yay sai da ya juyo ya kallesu, gani yay kan gimba a ƙasa ya juya zai fita, yayinda Shahudah ke tsaye zata je ta ɗauka jikkar a inda Gimba ya ajiye saboda yanda ya ganta bazai iya ƙarasawa gabanta ya bata ba.
Sosai idon Jawaad yay jajur, babu tsammani ma yaji ya cika da hawaye saboda tsabar kishi, juyawa yay kawai ya ƙarasa hayewa batare da yayi mata magana ba.
Yana tsaye gaban mirror yana saɓule rigar saman suit ɗinsa Shahudah ta shigo, baiko kalleta ba ya jefa rigar kan sofa ya fara sassauta tia ɗin wuyansa.
Itama bata tanka masanba taje ta ajiye jakkar saman tebir ɗin gaban gadon sannan ta zauna fuska a ɗaure, ita a dole yanzu tabar sakar masa fuska.
Daga inda take take hangosa ta cikin mirror yana ɓalle maɓallan rigar sa ta ciki kalar bulu, harya gama farar best ɗinsa ta bayyana bata iya janye idonta ba, ya kunce belt ɗinba da saɓe dogon wandon ya faɗi ƙasa sannan yajawo stool ɗin mirror ya zauna ya saɓile ƙafarsa daga cikin wandon, yana fara cire takalmi ne Shahudah ta fara magana cike da gadara kamar yanda ƙanuwarta Aamila ta bata shawara, dan tace inba haka takema Jawaad ba bazai dana cin tuwo akanta ba, itama dai ta yarda da hakan ɗari bisa ɗari, shiyyasa farawa tun daga yanzu.
“Ban taɓa tunanin baka ƙaunata ba sai akan wannan ɗan iskan cikin, wai yau harni kake ƙwatanta zaɓa da ciki bb, walhy ka bani tsantsar mamaki, ni son gaskiya nake maka, dan haka bazan danganta martabarka da ciki ba, zan haifesa kamar yanda ka buƙata, sai daifa ka tabbatar tunma daga yanzu wlhy bazan shayar dashiba, dan ƙirjina bazai zube a banza ba, kaima baka samuba balle wani ɗanka, sannan lokacin da ciki yakai haihuwa sai dai amin cs bazanje wajen haihuwa na buɗe a wofi ba ka samu zarrar bin wata, danku mazan hausawa yanda kuka san bunsiraye akan mata haka kuke.....”
Ba ƙaramin sukar Jawaad maganar Shahudah ta ƙarshe tayi ba, da har zaice mata harda ubanki ma bunsurunne kenan saikuma ya haɗiye abunsa kawai yay shiru yana miƙewa bayan ya zame safar ƙafarsa, dolene ya koyama yarinyarnan ɗanyen hankalin da ƙwaƙwalwarta zata dawo aiki tamkar ta kowa, wlhy ya yarda wayewar da babu ilimin addini a ciki ba ƙaramin daƙiƙanci take kawowa mai itaba.
Ƙala bai ce mataba, baima ko kalli sashen da takeba yay shigewarsa bayi domin samu ya watsama jikinsa ruwa.............✍🏻
Page 19
..........A wannan tsakanin kam sai abubuwa suka sake rikice musu a gidan, dan salo-salo na rashin mutunci Shahudah ta ƙaro take tsulama Jawaad, shiko sai ya watsar da ita tamkarma bai san da ita a gidanba, yama koma ba kullum yake kwana a gidanba, gara yaje gidansa da su Aliyu suke yay kwanciyarsa acan, idan suka takura masa da tambayar lafiya yace Shahudah bata nan ne.
Tun suna yarda da zancensa har suka fara zargin akwai dai wata a ƙasa, amma tunda bai basu damar saniba sai basu takura ba, sun dai ɗauki aniyar tayasa da Addu'a.
Cikin hikimar UBANGIJI sai yay ma Jawaad maganin Shahudah ta hanyar jarabtarta da laulayi mai azabar tsiya, dan takai yanzu ma sai da taimakon wani take iya wasu abubuwan, shi sai bai duba abinda take masaba, a duk lokacin da ta nema taimako yakan taimaketa inhar yana gidan.
Abu ɗayane har yanzu ta kasa samu a gareshi, shine sakin fuska, gaba ɗaya tabar ganin haƙoransa a waje, baya wata doguwar magana da ita, idanma yanaji da shariyar sai yazo gidan ya fice bai tanka mataba, tun abun baya damunta harya fara yanzu, dan kuwa tana tsananin buƙatarsa a kusa da ita kuma, sai dai dukkan damar hakan ya toshe mata ita.
Inhar a gidan ya kwana da safe zai leƙa ɗakinta yaji yaya jikinta?, zai kuma tambayeta abinda take buƙata, inhar ta faɗa zaisa a sayo mata.
Idan kuma da dare ya dawo koda ya isketa a falone zai tambayeta yaya ta yini? tana buƙatar wani abu? Iya amsar data bashi zai saurara yay wucewarsa ɗaki, yana shiga yake kullowa dan karma ta shigo masa. Ba ƙaramin zafi hakan yake mataba, harma tanaji tamkar taje ta zubar da shegen cikin taga ƙarshen iskancinsa.
Sai dai zuciyarta na tuna mata gargaɗinsa na ranar, yayi rantsuwa da inhar ta zubar ta tsinka igiyar aurensu duka uku, tasan wanenen Jawaad, tasan kuma zai iya tunda har ya hau dokin zuciya akan hakan..
Ita shaida ce akan haƙurinsa, sannan kuma tasanshi inhar yay zuciya da abu akansha fama kafin ya waiwayesa, a zahiri mutane sukaga sauƙinsa yayi yawa, amma saika nutsu dashi zaka fahimci murɗaɗɗen halinsa na ra'ayin riƙau, mahaifiyarta kace mata haka mahaifin Jawaad yake, dan haka dukkan hallayar Jawaad na ubansa ne, ya kuma kwaso wasu daga uwarsa, dan itama lumbu-lumbu take wutar ƙaiƙayi.
A yau dai kam lamarin nasa ya mata tsanani, dan ko mama Atika tabi duk hanyar da zataga Jawaad yaƙi bama kowa damar hakan hatta da kawun nansa, saima Qaseem ne ya samu damar gaggaya masa magana a kan Shahudah a office, sai kuma Jawaad ya manna masa hauka ya sharesa tamkarma bai san da shiba.
Waɗannan abubuwa suka taru akan Shahudah sukai mata yawa, dan haka ta shirya zuwa gida kozata samu sassauci dan yau tana ɗan jin jikin da sauƙi.
Dama ita babu tambayar fita a tsarinta, shirin ta tayi ba tare data nema izininsa ba, shi dama baya gidan, a office ya kwana yau.
Shirinta tayi cikin wando da riga jeans da top baƙa mai adon stones an runbuta *Beauty* da manyan baƙi da su, tayi ƙyau dan ƙyau, saboda farar fatarta na ɗaukar wankan ƙananun kaya da kalar baƙi, cikin a lafe kamar babu ɗa a cikinsa, yau dai ba'a samu damar zane fuska da kwalliya ba, fauda kawai aka shafa sai lipsgloss, ƴan arziƙin na kusa kuma, aka saka kimono tare da yafa siririn gyale akai, sai dai an saki rigar ba ɗaureba, hakan yasa taketa jan ƙasa a baya, ga glasess baƙi da aka toshe fuska dashi, ta dai fito asalin ƴar gayenta lamba ɗaya kuma shafin farko a jaridar manya.
Da kanta taja motar, yayinda kiɗa mai taushi ke tashi daga sifikun.
_______________________
BILKEESU
_______________________
Tun a harabar gidan nake tsarkake sunan ALLAH, dolene akira dukiya jarabawa ga bawa, yanzu mai wannan muhallinma dan yace ya manta da danginsa ai bakaga laifinsa ba, wani dai saikaga tamkar alƙalamin rubuta ƙaddarar rayuwarsa a hannunsa yazo.......
Zungurata da akaine ya sakani dawowa hayyacina babu shiri, harara ta gallamin da jan tsaki, “K dalla baƙauyar banza ki wuce muje, kin wani zauna kallon gida, halan yau kika fara ganin irinsa?”.
Bance komai ba, sai bin bayanta da nayi kawai.
A falonma dai akwai abin kallo da bakima bazai iya lissafowaba, abinda kawai zan iya faɗa hotunan masu gidan da aka ƙawata adon falon dasu, a yanda naga hotunan da alama yaran nasama sun zarta biyu, dan kuwa bayan waɗan na gani ga mutane uku kuma a hoto, namiji haɗaɗɗen saurayi maiji da kansa, sai ƙyaƙyƙyawar budurwa da tafi dukkan ƴan gidan asalin ƙyawu, saikace wata jinin larabawa, dan nikam bazan ce baturiya ba, dan ba ƙyawunsu nake ganiba, sai dai shigar tatace kam sak ta turawan ce, sai hoton namiji again da bazai wuce shekaru goma sha biyarba, hoton dai da gani tsohon hotone.
Na sake waigawa ko zanga inda yake babba sai dai babu.
Tunda muka shigo kawu saman bene ya haye, hakan ya saka hajiya binsa itama.
Suma duk sai suka shige ɗakunansu aka barni ni kaɗai a falon tamkar mayya, hakan baisa naji rashin daɗiba, koba komai nasamu damar yima falon kallon tsaf ai.
Sakkowar hajiya daga saman bene ranta a ɓace ne ya sakani kallonta, sai kuma na duƙar da kaina saboda mugun kallon data jefeni dashi, kafin tace wani abu sai ga Kawu ma ya sakko fuskarsa babu walwala.
Ni dai dama a ƙasa nake zaune, sai na ƙara ladabtuwa domin girmamawa a garesu.
Kawu yace, “Ɗiyata taso muje kiga ɗakinki kinji”.
Cikin girmamawa na amsa da “to” ina miƙewa, yana gaba ina biye har ɗan lungun dake falon, ɗakuna ne a jere guda biyu, muka isa har gaban na ƙarshen ya buɗe ya shiga, nima shigar dai nayi.
Ɗakine babba sosai, akwai komai a ciki na amfani tamkar ɗakin matar aure, matar aurenma ƴar gata ta gaske.
Da ƴar ƙura a cikinsa kaɗan, alamun dai ba amfani ake dashiba, komai na ciki kuwa kalar ja da fari ne.......
“Bilkisu nan ne zai zama ɗakin ki kinji, shi ɗin ɗakin ƴar uwarkice datai aure kusan wata tara kenan, yanzu kinga saiki maye gurbinta, inason ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki ɗauki kanki tamkar kowa na cikinsa, yanzu dai idan kin huta zuwa dare zamu zauna dan ki san kowa da sunansa kinji”.
“To kawu nagode sosai, ALLAH ya ƙara buɗi da haske na alkairi”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “Amin ɗiyata, amma daga yau ba kawu ba, ki kirani Dad kamar yanda ƴan uwanki suke kirana dashi, kema yanzu baki da banbanci dasu a gareni kinji”.
kaina na ɗaga masa nima ina murmushin jin daɗin dajin tsantsar ƙaunarsa a raina, shine mutum na shida da arayuwa bazan manta da suba, domin sunji tausayina a lokacin da nake buƙatar hakan ga kowa, sun ƙyautata mani lokacin da jama'ar duniya suke guduna, na share hawayen da suka ziraromin a fuska.
Jinai kawai an kama hannuna, na ɗago na kallesa aɗan firgice, “Haba ɗiyata, banason na sake ganin waɗannan hawayen a fuskarki dan ALLAH, nasan bazan iya ɗauke miki dukkan matsalarki ba a rayuwa, amma insha ALLAHU zan kamanta kinji, ki daure ki saki jikinki, zanji daɗin hakan”.
Murmushi nai masa, “Insha ALLAHU Dad bazaka sake ganiba”.
“To Alhmdllh ƴar gidan dad” yay maganar yana rungumeni.
Duk saina rikice, miye hakan kuma kawun yay min?, nashiga ukuna.
Shima fuskantar abun yazomin wani iri ya sakashi sakina yana faɗin, “muje na nuna miki yanda zaki amfani da banɗaki”.
Komai sai da ya nuna min shi, yakuma tabbatar na fahimta sannan ya fita ya barni ina ƙara gwada fahimtar komai yanda bazan manta ba.
Daga baya kuma na zage na gyara ɗakin tsaf, sai naga ya sake ƙyau saboda gyara na musamman daya samu sosai.
★★★★★★★★
A daren ranar wajen cin abinci na sake sanin kowa na gidan, dan kuwa duk Dad yaymin bayani a kansu da sunansu.
Duk na fahimta, duk da dai na kula shi kaɗaine ke ra'ayin zamana a gidan, dan ko babban ɗansu da alama ban cikin tsarinsa shima, sai kallon ƙurilla yake bina dashi a yatsine, wanda hakan ya tunomin da Jazuga a zuciyata, koda na koma ɗaki sai da na zubda hawaye saboda tuno firdausi da su inna da nayi, ina kewarsu sosai, inason sanin halin da suke ciki kuma.
Naci kuka a wannan daren har na rasa hawayen tsiyayarwa, dukkannin komaina na baya ya shiga dawomin daki-daki, ganin ina neman cinye daren da tunani sai na tashi na ɗauro alwala nazo naita nafilfilina ina miƙama ALLAH godiya da kukana game da sabuwar rayuwar dana sake shigowa.
Tabbas rayuwar wannan gida tasha banban da duk inda na rayu, ba'a ɓangaren jindaɗiba kawai harda yanayin zamantakewa da tarbiyya.
Gashi dai ina samun komai na buƙata, dan ko sutura kwana na ɗaya a gidan dad ya kawomin masu yawa, sai dai kumafa duk ƙananune, dan babu ko ƙyallen atanfa.
Abincin da kowa zaici nima shi nakeci, babu wani banbanci tanan ɓangarenma.
Sannan bana aikin komai a gidan, kamar yanda yaran gidan suma basa komai sai ƴan aiki, ko gyaran ɗakina ma sai da nai magana mai aikin gidan ta daina min.
Yanayin tarbiyyar gidan ce dai sai addu'a, dan