Showing 48001 words to 51000 words out of 104658 words

Chapter 17 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

203

kuwa na kula dai tsantsar rayuwar turaice da ɗabi'unsu ke wanzuwa ga jama'ar gidan.
      Duk kayan daga gadama zaka saka babu ruwan wani da kai, babu mai maka faɗan rashin dacewarsu, rungumar juna tsakanin mazan da matan hakan ba komai bane, shima Dad ɗin dazai tsawatar rungumemu yake, rashin girmama na gaba matsayin na yayanka wannan sam babu shi, ɓangaren ibada ba damunsu tayiba idan har ka cire Dad da ba kullum yake zama gidanba, bazan ce maka arana suna cika salla biyar babu tsallake ba har Mommy ɗin, maganar Qur'an ma ban gansa a gidanba tunda na shigo, amma akwai ɗaki na musamman domin karatu, cike yake da kowanne nau'in littafin daya shafi boko harma dana labaran turanci, komai kayi a gidan sunansa ƴanci kawai, babu mai cemaka akwai kuskure a ciki.

       Duk ɗabi'un nasu sunmin girma, na kasa kwaikwayon ko guda ɗaya a ciki balle na riƙesa matsayin cigaba.
    Hakan yasa a kullum suke hantarata da suna baƙauya ko bagidajiya, bana damuwa dan bana samun sakewar fuska daga kowannensu dama idan ka cire Dad, idan baya gida babu maimun magana sai hantara da harara.
     Iyakar nan dai tsananin ya tsaya min, shiyyasa bai cika damuna ba sosai.
     A ƴan kwanakin dana samu a gidan jikina harya fara nuna alamun canji, dan kuwa fatata ta fara gogewa, sannan jikinma dai da alama ƙiba zai fara, baƙina da kullum suke zagina a kansa ya fara korewa, dan duk sanda Yah Qaseem zai hantareni yakan kirani da suna baƙar banza.
      A kwai ranarda Yah Salman ke faɗin wai dama na taimaki kaina nazo ya kaini asibiti anmin allurar da zan koma fara ko nayi ƙyan gani, danshi wlhy har kunya yakeji suzo suyi baƙi aga ɓaƙar fuskata a cikinsu, ni da kwalta ta titi bamu da maraba.
     Dariya Aamila da Mummy sukaita tuntsurawa akan wannan zance, harma Mummy ke faɗin, “karka damu, sonake mu fita shopping ai na haɗo mata mayukan da zata kore wannan mugun baƙin, ni kaina baƙin nan nata har tayarmin da tsigar jikina yakeyi, anya Bilkisu nama taɓa ganin mai baƙinki kuwa?”.
         Murmushi kawai nayi ina haɗiye kukan da yake shirin taho mani.
    Yah Qaseem yaja tsaki shima daga inda yake zaune yana cewa, “Ku baƙin kawai kuke gani, ni wlhy nafi tsanar naniƙaƙƙen hancin yarinyarnan, sai kace tana gudu aka saka mata, wannan ko farin tayi an faɗa muku fasali zatayi? Indama ALLAH ya sota ya bata jiki mai ƙyau, gashi dan jaraba kullum tana fama da wannan hijjabin sai kace akanta aka fara addini, idanma zaki sauƙaƙama kanki ki sauƙaƙa yarinya, larabawanma tushen musuluncin sha'aninsu sukesha balle ke jinin wahala”.
           Nan ɗinma dariyar sukayi, hakan ya sakani kasa jurewa sai da yawayen da nake riƙewa dai suka zubo, hijjab na saka na share kawai.
      “Tofa, wai kuka kikeyi dan an faɗa miki gaskiya? Tab kinada aiki wlhy” Yah Salman ne mai maganar yana miƙewa zai fice.
        Haka suka cigaba da cimin fuska kowa na faɗin albarkacin bakinsa, dawowar Dad ce ta ceceni na samu sukuni, shikuma ganin yanayina ya sakashi tsareni da tambayar lafiya?.
     Nace masa babu komai daga barci na tashi

★★★★

           Ina sati na huɗu a gidan da safe kowa ya fice, daga ni sai Aunty Aamila da mummy ne a gidan, kuma duk suna ɗakunansu suna barci, niko bana iya dogon barcin nan hakan ya sakani fitowa falo na zauna ina kallo a tv, ɗauke wutar da sukaine ya saka ni miƙewa, ga shirin gidan kuma yasaka  naji duk kaɗaici ya taso mani, tashi nai na koma ɗaki na kwanta duk da nasan ba barcin zanyiba.

★★★★

        Da ƙyar Shahudah ta iya isa gidansu saboda rashin jin ƙarfin jikinta, tai hon mai gadi ya buɗe mata, yana ma gaisheta amma bata sauraresa ba ta shige, koda tai fakin ma kanta ta kwantar a sitiyari tai shiru na wani lokaci, kusan mintunanta biyar sannan ta samu ta fito zuwa cikin gidan.
       Yanda gidan yake shiru tasan su mummy basu tashi barciba, gashi tana buƙatar hutawa, tsohon ɗakinta ta wuce danta samu ta hutama ranta, dama inhar tazo gidan takan zauna acannane.

     Takun takalman da najine ya sakani kallon ƙofa, har aka buɗe aka shigo.
       Idanuna suka saukakan ƙyaƙyƙyawar matashiyar mace cikin ado na ainahin zubin wayewa ta shigo ɗakin babu ko sallama.
       Tozali dani ya sakata zare baƙin glasess ɗin idonta da ya rufe kusan rabin fuskarta tana min kallon sama da ƙasa, nason sanin ke kuma wacece haka?.
       Nikuma cire glasess ɗin natane ya bani damar ganeta duk da a hoto na taɓa ganinta, ɗiyarsu Dad da aka bani ɗakintace mai suna Shahudah kamar yanda ya sanarmin ce, yauce ranar farko dana ganta a zahiri, dan kuwa tunda nazo gidan bata zoba, dama Dad ya sanarmin batajin daɗin jikintane tana fama da ƙaramin ciki shiyyasa, amma ita bata iya sati ɗayama batazo gidanba.
     Takun takalminta ya sakani dawowa hayyacina, ƙoƙarin fita take tana sake bina da kallo, sai yamushe fuska take tamkar taga wani kashi ko abin ƙyanƙyami.
       Da ƙyar na iya fusgo magana a harshena nace, “Sannu da zuwa aunty”.
        Banyi tunanin ta amsa mani ba, ta dai fice da ɗan gudu kamar cikin fushi ko tunanin takalmin ƙafarta zai iya kadata bataiba kuwa......

______________________
JAWAAD
______________________

             Ɓangaren Jawaad kuwa yau gidan Alhaji Kokino ya sake kai ziyara, inda ya samu damar ganawa da dattijuwar nan da wancan zuwan ta kawo musu kayan breakfast.
        Wannan karon ma itace ta kawo masa ruwan sha, dan shi kaɗai ya zo sai gimba.
      Koda ta ajiye ruwan bayan gaisuwa sai tai yunƙurin juyawa zata fice abinta.
           “Da alama dai a ranar sha uku ga watan bakwai, dai-dai da washe garin rasa Alhaji wani abu ya faru wanda ganinsa ko jinsa ya jawo Accident ɗin faɗuwa a gareki har kika samu ciwon da har yanzu kike jinsa a jikinki, kuma tabbas wannan abun da kikaji ko kika gani yana da nasaba da Alhajin”.
        Cak ta tsaya, ita bata fitaba bakuma ta dawo da baya ba, ba komai ne ya jawo hakanba sai kalaman Jawaad masu saka rikici ga duk mai alaƙa dasu.....
     Jawaad dake ƙoƙarin zubama kansa ruwa a kofi ya sake katseta da faɗin, “Abin bana dogon tunani bane mama, abin kawai na sani zan cigaba da riƙe Yazeed har sai nasan dalilin faɗuwarki a wannan ranar, miya tsorataki?, abu na gaba ki taimaki kanki kije asibiti a duba ƙafarki, dan naga har yanzu kina ɗangyasata”.
     Ya kai ƙarshen maganar yana takowa inda take a tsaye.
    Hakanne ya sakata kallonsa ta kauda kanta da ƙoƙarin haɗiye hawayenta, tace,
        “Miyasa zaka sakamin yaro cikin al'amarin da baisaniba?”.
        “Mama idan har kina buƙatar na sanar masa komai a yanzu ai bamu makara ba”.
     Idanunta jajur ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yake, amma sai ya janye nasa idanun ganin tana neman rikicewa, yay murmushi yana sake matse kofin hannunsa na glass, rashin ƙwarinsa ne ya saka kofin tarwatsewa  sauran ruwan ciki ya jiƙe masa hannu ya zuba a ƙasa, guntayen kofin kuma sukai ɗai-ɗai a ƙasan suma.
      Dattijuwa ta sauke idonta akan hannun Jawaad har zuwa kofin da yaya kuci-kuci a saman tayis tamkar ba shiba, sake maida kallonta tayi gareshi a wani yanayi mai nuni da tsantsar damuwarta.
        Jawaad ya zaro handkherchief a aljihunsa ya goge hannunsa tas sannan ya turasu a aljihu duka biyun yana ja da baya fuskarsa na ƙara tsukewa.
        “A duk lokacin da aka zuba ruwa a glasscup yana da matuƙar ƙayatarwa, har kakanji bakason ɗauke idonka wajen kallonsa koda zaka kwana a haka, amma da tsautsayi zaisa wannan kofin fashewa a hannunka zaka iya gamo da haɗarin yanka maisa aji zafi, shi kuma ruwan dake ciki idan har ya zuba a jikinka ƙoƙarinka kawai ka goge, damshin da ya rage iskace kawai ka iya busar maka dashi, wanda yake a ƙasa kuwa sai kaga dukansa ya zama haɗarine, musamman akan abu mai santsi irin tayis. Na tabbata duk wanda zai shigo falon nan a yanzu zaiyi ƙokarin ganin bai taka wannan ruwan da glasess ɗin nanba, yaron da hankali bai gama bin jikinsa bane kawai zai maidashi abun wasa. Mama bansan yaya zaki rarraba zantukana a jujuwan da suka cancantaba, ni dai kawai abinda raina ya bani komai tsanani zansan gaskiyar zancen....”
       Ya raɓata ta gefe zai fice, yana saka ƙafarsa ɗaya a waje yajiyo sautin dariyarta.
      Dakatawa yay tare da juyowa yana kallonta.
       Tace, “Yarona idan kwalba ta fashe a hannun mutum zafinta kawai zaiji saiko fitar jini da zai gani, amma idan zuciya ta samu suka har abadan wannan tabon baya gogewa komi adadin shekarun da aka ɗauka bayan jin wannan ciwon, ruwan da zai zuba a jiki a goge iska ta busar bashi da banbanci da hawayen dake kwarara daga idaniya zuwa fuska a goge iska ta busar da sauran, inda ake samun banbancin kawai shi wannan ruwane, daya zube labarinsa ya shuɗe, suko waɗannan hawayene koda sun bushe ba'a daina iya ƙididdige su a tsarin da sukazo na farin ciki ko akasinsa har ranarda fitar numfashi zata yanke, ka cancanci a kiraka da suna *Ƙwai cikin ƙaya* sannan kuma lallai kai *Yarone ɓata hankalin dare kayi suna*, duk abinda kake buƙata daga gareni zaka samu, amma ba'a nan gidanba, mu haɗu a gidan daka ɗauki yarona Yazeed.............✍🏻

Page 20
............Tunda suka baro gidan Alhaji kokino maganganun tsohuwar ne kawai ke yawo a zuciyar Jawaad, gaba ɗaya ya kasa fahimtar alaƙar ɓatan Alhaji kokino da kalamanta, ya rarrabasu ajujuwa daban-daban amma basa bashi ainahin abinda ya dace, yay guntun tsoki yana cigaba da shafa gemunsa a hankali, yayinda idanunsa ke kallon hada-hadar jama'ar gari.
Daga nan office ya koma, inda ya tarar da baƙuwa zaune tana jiransa.
Rose da tunda Jawaad ya fito a mota ta dasa masa idanu ko ƙyaftawa batayi ta sauke nannauyan numfashi lokacin daji ƙarfin ƙamshin turarensa gab da ita.
Ta bishi da kallo tana sake yabama kwarjininsa da cikar zati da ALLAH yay masa, tasan sarai ya ganta, amma jiba yanda ya basar abinsa.
Murmushi tayi ta miƙe tana gyara zaman wuyan rigarta.
Itama ƙyaƙyƙyawar ce ba laifi, gata doguwa masha ALLAH, yanda take tafiya cikin zafin nama tana juya dukkan illahirin jikinta zai tabbatar maka da tasamu isashen training wanda ya haɗu da ainahin halittar yanga ta ɗiya mace.
Kanta tsaye ta nufi Office ɗin Jawaad, wanda kowa yasan bata da shamaki da hakan.
Yana zaune a kujerarsa yayinda wani ke tsaye a kansa yana masa bayani akan aikin daya sakashi, har Rose ta zauna bai kalleta ba, dan idonsa nakan wasu takardu ne, itama batace komaiba ta dai zauna tana saurarensu.
Sai da wancan yakai aya sannan Jawaad ya ɗago yana kallonsa da rikitattun idanunsa da mafi yawan lokuta ke tsorata duk wani maison kawo masa wargi.
"Aikinka yayi ƙyau, sannan yana tafiya dai-dai, yanzu dai kafin dare a tababbar an kamo min Ɗan Lawan da yaransa baki ɗayansu, sannan itama kanta Kande barikin a kamomin ita tare da wiwi ɗin dasu ɗan lawan ɗin ke kai mata ajiya".
"Okey sir" ya amsa yana mai sara masa, takardu biyu Jawaad ya miƙa masa, ya amsa yana ƙara sara masa sannan ya fice.
Lokacinne Rose ta miƙe tai salute ɗin Jawaad dake haɗe takardun daya baza bisa tebir ɗin waje ɗaya, fuskarsa ta sake tsukewa alamar babu wasa, a dake yace,
"Ban saniba yanzu ko zaki maida hankalinki ga aikinki, kokuma zaki cigaba da ɓata lokacinki akan farautar soyayya?".
Ido Rose ta lumshe tana sakin murmushi mai sauti, ta kuma ƙamewa tare da sarama Jawaad a karo na biyu, "Boss duk zaɓin daka bani zan riƙe".
Ɗago ido Jawaad yay ya kalleta, mikuma ya tuna sai ya saki wani guntun murmushi yana girgiza kansa. Ya jawo drawer ɗin gefensa ya fiddo bindiga ƴar ƙarama mai ƙyau, saman tebir ɗin ya ajiyeta idonsa akan Rose da itama kallonsa take ko ƙyaftawa babu, yaɗan bugi bindigar kaɗan sannan ya turata gabanta cike da salo.
Itama cikin nata salon ta ɗauka ta wurwurata tare da buɗeta. Babu komai a cikinta, hakan ya sakata sake kallon Jawaad daya maida hankalinsa ga latsa Computer ɗin saman tabir ɗin.
Ba tare daya kalleta ba yace, "Riƙe soyayya a wajenki tamkar riƙe bindiga ne babu bullet a cikinta, kinsan kuwa a garemu jami'an tsaro sam bindigar bata da amfani, domin ba bindigar bace ƙarfinmu harsashin cikinta ne, shima kuma yana amfanine idan an samu ƙwarewar iya harbi. Karki yarda a karo na biyu kiyi sakaci da damarki, Jawaad akwai mai shi".
"Hummm" ta faɗa cikin ƙunar zuciya ba tare data iya cewa komaiba.
Shima bai sake cemata komanba tsawon lokaci kafin ya miƙe zuwa ga wata kanta, yabi tarin files ɗin cikinta da kallo, da alama dai kwanan wata yake dubawa, har idonsa yakai inda yake buƙatar zuwa sannan ya zaro wata takarda, mazauninsa ya dawo fuska a tamke ya miƙa mata, "Ki samu su Jabeer da wannan file ɗin zakuyi magana".
"Okey Boss" ta faɗa cikin rissinawar girmamawa gareshi tana amsar file ɗin. Sai da ta sake salute nashi sannan tai ƙoƙarin ficewa.
"Ji mana" Jawaad ya faɗa yana bin Rose da kallo.
Juyowa tai ta kallesa, da ido yay mata nuni da harsasai (bullets) kusan goma daya ɗora a tebir ɗin.
Dawowa tai da baya ta kwashe tana faɗin, "Thanks you boss".
Baice da ita komaiba, saima maida hankalinsa yay ga kallon Computer harta fice.
Aikinsa ya cigaba dayi, duk da zuciyarsa na tunanin halin da yabar Shahudah jiya da dare, tana bashi tausayi saboda wahalar da cikin yake bata, amma bayason nuna mata hakan koda a fuska ne.

Ƙarfe huɗu da wasu mintuna ya fito massalaci ya zarce office ɗin boss ɗinsa domin amsa kiransa.
Bayan nuna girmamawarsa garesa ya zauna kamar yanda ya bashi izini.
"Jay yaya dai? Na jika shiru, ko akwai matsala ne?".
"A'a Sir, babu wata matsala aiki yana tafiya dai-dai, a yanzu haka zancen da nake maka insha ALLAHU ƙiris yama rage".
"To Alhmdllh, banason aikinnan ya shige satinnan, dan yanzu hakama wata ta taso kuma".
Kallonsa Jawaad yayi da son jin ko minene?.
Ya cigaba da faɗin, "Akwai wani mai kayan miya anguwar ƴan kilishi daga can ƙasan layin, majiya mai ƙarfi ta kawo mana alamar tambaya a kansa, saboda gagarumin fashin da akayi satin baya gidan Alhaji Sulaiman, Qaseem aka ɗora akan case ɗin, sai dai naga baiyi wani serious ba sam, yamafi maida hankalinsa akan wannan case ɗin da ayanzu nasan kai kama kusa kammalashi".
"Okey Sir, yanzu mikakeson nayi ni akai?".
"Case ɗin nakeso ya dawo hannunka Jawaad, dan waɗannan ƴan fashin bincikenmu ya nuna sunada laifuka masu yawa, amma basu barin kowacce damar da za'a gane sune, sai yanzune muka ɗan samo bakin zaren".
"Na gane sir, to amma an buɗema case ɗin file ne?".
"No, nabar komai a hannunka, dan banida shakku akanka sam".
Kai Jawaad ya jinjina masa, "To amma sir kozan iya sanin wanda ya kawo sirrin?".
"Mizai hana Jay".
Murmushi Jawaad yayi, dan har zuciyarsa yana ƙaunar ogan nasa, ALLAH ne ya ɗaga darajarsa a hukumarsu, da kuma ƙoƙarin ogan nasa, dan ƙarancin shekarunsa basukai ace yana a kujerar da yakeba a yanzu, amma saboda manyan ayyukan da sir Ahmad Barewa ke bashi yaketa samun cigaba, har takai yanzu yana cikin jami'an da hukumar ƴan sanda ta DSS ke ji dashi saboda ƙwazonsa, da salon aikinsa, duk da kuwa ta wani ɓangaren yana zagayene da maƙiya masu burin taɗosa ƙasa a kullum.
Ya daɗe a Office ɗin suna tattaunawa kafin ya fito.


_________________________

"Ke kuwa yaushene zakiyi hankali mamana?". Hajiya Humaira ta faɗa saboda faɗowa kanta da Shahudah tayi tana barcinta.
Baki Shahudah ta zumɓura tana faɗin, "Ni Mummy inada hankalina, wai wacece a ɗakina kuma?".
Baki Hajiya Humaira ta taɓe tana sakkowa daga saman gadon tare da jan tsaki, "Ƴar uwarkuce".
"Ƴar uwarmu fa mommy? Waccan baƙar yarinyar?".
"Ita ɗinfa, ɗiyar ƙanwar dad ɗinkj Gurguwarnan da kika taɓa ƙonawa da shayi wani zuwa data taɓayi kuna primary lokacin, koda yake dawuya dai ki tuna ma".
"Tab wlhy mummy ban mantaba, shine Dad ya jajubo mana ƴarta? Itama gurguwarce halan?".
"Ko ɗaya, lafiyarta ras itakam, mamar tata ta rasune ai, shine ya kawota nan wai tayi karatu".
Dariya sosai Shahudah take kwasa harda kwanciya, cikin dariya take faɗar tab ɗi, "Wannan mummunar ce za'aima gatan karatu? Irin waɗannan ko a makarantar ma mi suke ganewa yo? Amma kuma shine ama rasa inda zata zauna sai ɗakina" ta ƙare maganar da kumbura baki.
"Uhm, ke bakisan tsiyar da mukasha akan hakanba da shi, yanzu dai karkice komai ki bar mata ɗakin, ke sai a gyara miki na kusa dani, dan idan kikace wani abu akanta komai zai iya faruwa, ya ɗauki son duniya ya aza a kanta waishinan mai riƙon amana".
Sosai lamarinnan ya zafi zuciyar Shahudah, harda ma dad ɗinsu wani maganar rashin tarbiyya, na zata Hajiya Humaira zata kwaɓeta sai naga kawai tayi dariya.

Tunda ta fita sai nima na kasa daurewa na fito falo na zauna, kusan awa ɗaya ina wajen zaune duk damuwa ya rufeni, dan bansan dalilinta na fita da gudu ba.
Aunty Aamila ta fito daga ɗakinta cikin figigiyar rigarta ta barci, wadda kaɗan ta zarta cinyarta.
Kallo ɗaya taimin taja tsaki ta wuce tebirin cin abinci.
Lamarinta baya damuna nikam, hakan yasa ko sashen da take bamma kallaba.
Ina zaune a wajan Mummy da baƙuwarmu suka fito, na gaida Mummyn cikin girmmawa kamar yanda na saba.
Amsawa tayi itama cikin nuna halin ko in kula, aunty Shahudah kam bamma isheta kalloba, hakan ya tabbatar min itama dai bazan samu karɓuwaba a gareta kenan, ban damuba, dan ba yaune karon farko dana fuskanci hakanba.

Zuwan Aunty Shahudah gidan yaɗan sake takurani, saboda wulaƙancin da takemin yafi na kowa muni, ko abu na taɓa ita bazatayi amfani da shiba, a cewarta karna gogama ɗan cikinta Munina, nakanyi murmushi aduk lokacin da naji furucinta.
Takai inhar tana falo zaune takance bazan zaunaba wlhy, banaja da ita saina tashi na fita kona koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login