Showing 15001 words to 18000 words out of 104658 words
hakanne ya sata tasowa ta shige jikinsa tana magana cikin shagwaɓa.
“Oh My BB kayi ƙyau sosai”.
Shiru yay mata, bai kuma rungumetanba shi.
hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, ta kai lallausan hannunta tana shafa fuskar tana murmushi, “BB kamin murmushi mana”. ‘Ta ƙare maganar da sumbatar laɓɓansa’.
Duk da saƙonta ya shigesa hakan bai hanashi ture hannunta ba daga fuskarsa yana ƙoƙarin janyeta a jikinsa, amma sai ta ƙankamesa tana bubbuga ƙafa cikin shagwaɓa.
Iska ya ɗan huro da ga bakinsa, a daƙile yace, “Wai mikikeyi haka kamar wata tata Hudah? Ki bari karkimin Squeezing kaya”.
“Sai ka sake fuskanka to” ‘ta sake faɗa a raunane’.
Kansa ya girgiza kaɗan yana riƙota sosai jikinsa, hakan ya saka Shahudah ɗago fuskarta cike da annuri ta kallesa, shima kallonta yake cikin ido yana kuma narke idanunsa dake ƙara tsundumata a ƙaunarsa.
“Idan kinaso ki sameni yanda kike buƙata Hudah ki canja kamar yanda nima nake buƙata”.
Yay maganar a hankali tare da sauke laɓɓansa akan nata da keta walƙiyar janbaki, ya sumbata.
Kafin ta samu zarrar magana ya cireta a jikinsa ya nufi hanyar fita yana saka baƙin Eyeglasess ɗinsa a ido ba tare da ya sake koda kallonta ba.
Murmushi Shahudah tayi tana wani juya idanu, tabbas tana ƙaunar Jawaad fiye da hasashen mai tunani, dan shine namiji da ta fara so a rayuwarta, so kuma na haƙiƙa mai cike da tsagwaran sadaukarwa, kuma tana fatan ƙare rayuwarta da ƙaunarsa. Matsala ɗaya da ke tsakaninsu shine banbancin ra'ayi, Jawaad ɗan gayune mai aji da cikar haiba, duk yanda kake tunanin haɗuwarsa ya zarta nan, amma tana mamakin yanda kansa yake a tukunya game da rayuwa irinta manyan yara, ta ɗan taɓe bakinta tana komawa cikin kujera ta zauna, tasan canjawarta ta koma ra'ayinsa abune mai matuƙar wahala da iyawarsa a gareta zaiyi wuya, su dai tafi a hakan kowa da ra'ayinsa zaifi basu zaman lafiya, kan ya matsa sai ta canja ɗin dai-dai da buƙatarsa.
★★★★★★
Ya isa Office ɗinsa da ya ƙawatu da kayan more rayuwa, sai ƙamshi mai daɗine ke tashi a ciki, ya zauna cikin kujera yana mai miƙa hannunsa domin karɓar takardun hannun wanda suka shigo tare. Shafin farko da ya buɗe ya maida ya rufe yana ɗago razanannun idanunsa, “Ina na farkon?”
Ya faɗa cikin karsashi.
Cikin ɗan ruɗewa da tambayar bazata Aminu ya shiga kame-kame, “S...o...so...sorry sir!, dama Sir Qaseem ne ya karɓa, sai yace na kawo maka waɗannan”.
Gira ɗaya Jawaad ya ɗage sama, ya janye idanunsa da ke neman fara canja launi ba tare da ya tankama Aminu ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Computer ɗin da ke saman desk ɗin gabansa.
Tsawon wasu mintuna da basu gaza biyar ba Aminu na tsaye, babu abinda jikinsa keyi sai tsuma, zufa ta hudo dukkan ƙofar gashin da ke jikinsa.
Jawaad dake aikinsa ya kallesa ta wutsiyar ido yana faɗin, “Tsayuwar ka zaɓa ko komawa dasu, idan ka karɓo waɗancan ka haɗa ka kawo min?”.
Sosai tsantsar firgici ya kuma bayyana a fuskar Aminu, ya sharce gumin da ya tsatstsafo masa a goshi tare da gyara tsaiwa zaiyi magana.......
Wani mugun kallo Jawaad dake ƙoƙarin miƙewa ya watsa masa, ba tare da yace uffanba ya zagayeshi ya fice da ga ma office ɗin gaba ɗaya.
Da tsantsar sassarfa ya biyo bayan Jawaad da ko kallonsa baima sake yiba.
Mutanensa biyar na amana suka take masa baya zuwa Office ɗin boss ɗinsu, yayinda Aminu ya bi hanyar da zata sadashi ga ubangidansa Qaseem Ali.
Yardar dake gareshi ga manyansa sam ta hana masa shamaki da neman izinin shiga ofisoshinsu, kansa tsaye yake shiga ba tare da jiran iso ba. Sai da yay masa sarawar girmamawa tamkar yanda al'adar jami'an tsaro take, kafin ya zauna a ɗaya da ga kujerun gaban ƙaton tabirin.
“Jay!”.
“yes sir”.
“Ko kasan maganar sace Alhaji kokino tana neman shigo da shugaba ƙasa a ciki”.
Cikin rashin fahimta Jawaad yace, “Sir! Kamar ya kenan?”.
Shiru ogan yayi na wasu sakwanni, kafin ya ɗago kansa daga wayar da yake dannawa ya maida kallonsa ga Jawaad, wayar ya miƙa masa yana faɗin, “Ɗazun nai magana da shugaban ƙasa kai tsaye babu shamaki kowa a tsakaninmu”.
Idanu sosai Jawaad ya zaro waje, “Sir, miya ce?”. ‘Jawaad yay maganar a hankali, mai nuna alamar tsorata’.
Kaɗan Sir Ahamad barewa ya buga tebirin gabansu yana huro iskar bakinsa, ya miƙe tsaye tare da maida dukkanin hannayensa baya ya goya, sai da yay taku biyu zuwa uku kafin ya juyo ga Jawaad, “Jay! Adadin lokaci, lokaci shugaban ƙasa ya bamu na gaggauta samo Alhaji Sadi kokino, abinda ya bani mamaki annan yanda ya tsaurara, mika fahimta?”.
Jawaad dake bin ogansa da kallo kamar ya samu magiji ya sauke numfashi, tare da taɓe bakinsa yana murza yatsun hannunsa da ke bada ƙarar ɗas-ɗas a hankali, zuwa kusan sakon goma sha biyar sai kuma yaɗan zabura, cikin ƙanƙance idanu mai nuni da na tuno, yace, “Sir sai naga kamar yana tunanin ana zarginsa da hannu a ciki....”
“Exactly my dear!, nima wannan shine tunanina, Jay kana da ƙwaƙwalwa, shiyyasa a komaina nake sonka a gaba” ‘Sir Ahmad ya ƙare maganar yana komawa a kujerarsa ya zauna’.
Jawaad dake murmushin jin daɗin yabon da ogan nasu yay masa, ya sauke numfashi yana gyara zama, “Sir inada shawara”
Sir Ahmad dake kallonsa yace, “ita mukafi buƙata ai ayanzu Jay”.
Jawaad ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana jinjina kansa, “Zan turo maka a rubuce Sir”.
“Okey babu damuwa Jay, yaya maganar zaɓin haɗa runduna?”.
“Sir zanje na zauna dasu Asim yanzu insha ALLAH, zuwa yamma zamu aiko da jadawalin sunayensu”.
“Okey, amm......”
Maganar Sir Ahmad ta kakare dalilin Knocking ƙofa da akayi, haɗiye maganarsa yayi ya bada izinin shigowa........
_____________________________________
BILKEESU
_____________________________________
Sakamakon tashi da hayaniyar yaran gidanmu a kowacce safiya, sai yau muka tashi da hayaƙin sigari a gidanmu.
Gashi rashin samun isashen barci ya saka mafi yawancinmu makara sallar asubahi. Hakanne ya kawo go slow ɗin shiga banɗaki. A ɗarare kowa ke komai saboda dokar rashin yawan motsi da yaran Jazuuuga suka kafa mana, a cewarsu yana barcin safe, duk wanda yay ƙwaƙwƙwaran motsin da ya tashi to lallai sai yaji a jikinsa, kuma komai tsufarsa basu ɗaga masa ƙafa.
Hakanne yasa mafi yawan mazan gidanmu ficewa da ga gidan da wuri ba tare da ko wanka sunyi ba, wasu kuma suka ɗauki kayan wankan zuwa gidan wanka.
Mukan dama maman firdausi ta mana dabara, wani tsohon bokitin ƙarfenta da hannun ya ɓalle tuni ta koma saka kayan tarkace a ciki ta ɗakko mana, a ciki mukai alwalarmu, bayan mun kammala muka fita muka zubda ruwan. Hakama da zamuyi wanka saita yi dabarar saka labule jikin murfin ƙofa da bango tace muyi cikin ƙatuwar bahonta. Muna kammalawa shirin makaranta nayi, babu zancen zaman karin kumallo, baba ya bani naira ɗari akan idan naje makaranta sai na karya, dan ita firdausi ta gama secondary tuni. Godiya nai masa na amsa na fito cikin fargabar waɗanan shaiɗanu da suka wargaza mana farin cikin gida a cikin kwana ɗaya kacal.
Sosai gabana ya faɗi, dan kuwa ina fitowa da Jazuuga na fara tozali, yana gaban fanfo tsaye, daga shi sai gajeren wando, hannunsa riƙe da brush alamar baki zai wanke, sai yaronsa ɗaya a gefensa riƙe da kofin ruwa.
Nai ƙasa da kaina, yayinda nakeji har lokacin shi nasa idanun na yawo a jikina. Tamkar munafuka naɗan risina kaɗan ina faɗin “ina kwana”.
Ban jira amsarsa ba nai ƙoƙarin wucesu.
“K zonan!”
Naji an faɗa cikin wata sautin murya mai ban tsoro, sosai ƙirjina ya shiga sama da ƙasa, na rimtse idanu ina karanto *Hasbinallahu wa ni'imal wakil.*
“K dan ubanki kurma ce?!!”
Aka kuma faɗa cikin sautin da yafi na farko razanarwa.
Juyowa nai garesu, nazo gabansu na tsaya kaina a duƙe, dan bazan iya kallonsa haka babu rigaba, duk da kasancewar gidanmu gidan haya ne bamu saba ganin haka da ga mazan gidanba.
Shareni yay tsawon lokaci yana cigaba da brush ɗinsa, yayinda idonsa ke kaina ko ƙyaftawa bayayi, sai da ya gama tsaf ya raɓa ta gefena ya wuce yana faɗin, “biyoni”.
Ba ƙaramin firgici na tsinci kaina a ciki ba, dan marata wani ƙugi tayi kafin ta ɗaure tamau tamkar zata fashe. A cikin zuciyata kuwa ina tunanin na bisa nai masa mi? To. Ban gama samo amsar data dace da tambaya taba naji an fisgi hannuna, duk iya ƙoƙarin tirjewata da magiyar roƙonsa ya sakeni da nakeyi bai saurareni ba, sai da ya kaini har cikin ɗakin nasa sannan ya wurgar dani saman lallausan kafet ɗin da aka shinfiɗa yana huci.
“K kin sanni kuwa? Kinsan wanene ni? Dahar zaki ringa sakani maimaita miki magana!!”.
Jikina na rawa naja da baya dajan ɗuwawu ina girgiza masa kai, ga hawaye na gudu a fuskata tamkar fanfo, ya kuma zaromin manyan idanunsa jajaye, cikin nunani da ɗanyatsa tamkar zai tsokale idona yake faɗin, “Karki bari na tsaneki a gidannan, inba hakaba wlhy saina fatattaka rayuwarki, tashi maza ki gyaramin ɗakinnan”.
Cikin rawar jiki nake amsa masa da “to” na ajiye jakkar makarantana na fara gyara ɗakin, duk abinda nake yana tsaye a kaina tamkar wani dogari, niko sai hawaye nake zubarwa ba tare da samun zarrar gogewa ba.
Cikin mintuna ƙalilan na kammala gyaran ɗakin, dama ba wani datti yayba. Ba tare da na kallesa ba nake ƙoƙarin magana, duk da nasan shi ni yake kallo, “N...na..gama”.
“Saura shara” ya faɗa yana juyawa ya fita.
Tsintsiya na ɗauka nai sharar ina cigaba da kuka, ina gamawa na fito daga ɗakin, ALLAH ya soni ya shiga wanka, yaransa kuma wasu sun fita sai mutum uku kawai.
A gudu-gudu na fice da ga gidan, duk da naga mafi yawancin matan gidanmu na laɓe ta jikin labule suna kallona, wasu kuma ta Windown ɗakinsu.
A yau kam inhar nace na fahimci wani karatu a makaranta to nayi ƙarya, abinda ya faru tsakanina da baƙon gidanmu ya tsayamin a rai, babu abinda nake sai fargabar komawa gidan ma, malamin mu na Geography har buguna yayi akan yana darasi ina duniyar tunani. Dai-dai da yunwar cikina ban tuna da itaba har aka tashi, haka na nufo gida cike da tsoro dan bani da inda nake dashi da ya wuce gidan, kuma dama can ban saba da yawo ba, da an tashi daga makaranta gida nake nufa, shiyyasa yanzu ma naji can kawai nake buƙatar zuwa dukda kuwa tsoron dake cike fal raina................✍🏻
Page 8
............Shigowata soron gidanmu yaɗan sakamin nutsuwa kaɗan, dan yau babu mahaukacin kiɗannan, sai da nai addu'a kafin na shiga da sanɗa tamkar wadda tazo yin sata.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na kuma saukewa ganin ƙofarsa a rufe, sannan babu kowa a cikin irin yaransa, sai wasu a tsirarun matan gidanmu dake ƴan aiyuka a tsakar gidan.
Abinda ya bani mamaki yanda duk suka zubamin ido kamar wata baƙuwarsu, ni dai sannu nai musu na wuce ɗakin innar Firdausi kai tsaye.
Sannu Firdausi da inna dake zaune sukaimin, na amsa ina ƙirƙiro ƴar fara'a akan fuskata tare da bin tarin kayanmu da aka jibge gefe da kallo.
Kafinma na tambaya firdausi ta fara min bayani,
“Bilkeesu kayanmu ne baba yace mu kwaso da ga baca mu maido nan, dan babu dacewa zamanmu acanɗin saboda canjin da gidan ya samu”.
Murmushi nayi sosai wanda ya bayyana farin cikina yanzun kam, na zauna kusa da Firdausi ina faɗin, “Amma inna idan mun dawo nan baba fa?”.
“Karki damu kinji Bilkisu, babanku zai cigaba da kwana a bacar shi, kwananku acan babbar barazanace a garemu da mutuncinku, waɗannan yaran sam zukatansu basusan yaren tsoron ALLAH ba, abinda ransu keso kawai suke ji da gani a gaba ɗaya duniyarsu”.
“Hakane inna, babu abinda zance daku nidai a wannan duniyar, ALLAH ya yalwata rayuwarku da dukkan farin ciki har cikin aljanna, kun haska fitila a rayuwata lokacin da tsatona suka kashe domin hana kansu ganin hanyar da zasu riskeni, kuɗin masu zinariyar zuciyace mai haske fiye da ta dayimon (diamond), na.......”
Katseni inna tayi saboda kukan daya sarƙe harshena, ta jawoni jikinta tana bubbuga bayana alamar lallashi
“Ya isa haka bilkisu, kema ɗiyarmu ce tamkar Firdausi, ki daina kallonmu a waɗanda sukai miki alfarma, muna yin abinda ya dace muyine kinji”.
Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye.
Kusan tsawon mintuna uku tana lallashina, kafin na miƙe na cire Uniform ɗina naje naɗan watsa ruwa, bayan na dawone na iske Firdausi ta ajiye mana abinci.
Munacin abinci inna na zaune gefe tana ƙullin kayan sana'arta, Firdausi ta haɗiye abincin bakinta tana faɗin, “Bilki akwaifa matsala”.
“Tsayawa nai da ga ƙokarin kai abincin bakina ina kallota a tsorace”.
Inna ta harari Firdausi tana faɗin, “K Firdausi bana son ƙirƙire-ƙirkire fa, ya zaki ɓata mata zuciya? Wannan ai shirmene”.
“Kiyi haƙuri inna” Firdausi ta faɗa a sanyaye.
Kallon Inna nayi nima a raunane, “Inna dan ALLAH karki hana ta sanarmin, da inji a wani waje ai gara naji daga gareku, dama tunda na shigo naga matan gidannan namin wani kallon ƙurullah daya tsoratani”.
Murmushin takaici Inna tayi tana girgiza kanta, “Suma son zuciyane ke ɗawainiya dasu, dan abinda ya shafi kowane a gidane ai”.
“Dan ALLAH Inna miya faru?”.
“Karki tada hankalinki Bilkisu, baƙon gidanmu ne ya tara taro ɗazun bayan fitarki makaranta, ya kafa sharuɗa ne a gidan, wai bayason hayaniya, sannan kafin ya tashi barci a share tsakar gidannan a wanke tare da bayi, lokacin da zai fito kuma karyaga kowa sai.......”
Tai shiru cikin haɗiye wani takaici daya zame mata ƙululu a maƙoshi.
Cikin ƙaguwa da tsorata nace, “Inna sai me?”
Shiru tai ta kasa bani amsa, sai Firdausi dake sharar hawaye tace, “Wai sai mu ƴammatan gidan kawai, kece zaki ringa masa gyaran ɗaki, ni kuma kai masa ruwan wanka, su Aina'u ma kowa da aikinta, kinsan miya bani takaici Bilkisu?”.
Kaina na girgiza mata saboda hawayen da suka fara gudu a kumatuna. Ta goge nata itama tana cigaba da faɗin, “Bayan wannan dokokin harda sharaɗi mai barazana ga duk wanda yace zai bar gidannan ko zai sanarma hukuma, wai amma dukda wannan ruɗanin sai su Zee ke murna, harma suna ƙokarin yin kwarkwasa a gabansa”.
Kasa cewa komai nayi, sai tsame hannuna danai daga abincin da mukeci na koma gefe, hakama Inna da Firdausi kowa yay shiru yana cuɗawa da kwance abinda yakeji a ransa.
★★★★★★★
Kamar yanda Jazuga ya kafa dokoki a gidanmu haka kowa ke bi, ba komaine yasa hakanba sai tsoro, dan ba gidanmune kawai ke tsoron Jazuga ba, gaba ɗaya layinmu a tsorace suke dashi da yaransa, babu wani mai sukuni, dan yaran Jazuga sun addabi kowa a anguwar, gashi sai ƙara jan yara matasa ya keyi masu rauni cikin tawagarsa.
Abinda zai baka mamaki Police kansu tsoron shigowa anguwarmu sukeyi, ballema muyi tunanin zasu iya kamashi ko ƙwatar mana ƴanci daga mulkin mallakarsa.
Tun ina damuwa da bautar gyaran ɗakinsa har abin ya zame min jiki, ƙa'ida kullum sai na gyara sau uku, safe, rana, yamma.
Abinda kawai ke damun rayuwata dashi shine kallo, duk motsina a gidan idonsa na kaina inhar yana gida, duk da kuwa a koyaushe cikin Hijjab muke ni da Firdausi inhar zamu fito tsakar gida.
A cikin ƴammatan gidanmu kuwa wasu sai dai addu'a, dan kuwa sosai ake zargin Jazuga na lalata dasu yana basu kuɗi, hakanne ke ƙara tada hankalin iyayenmu.
Muna cikin wannan halin ne kuma saiga ɗan uwansu Firdausi wanda yake matsayin zaɓin iyayenta yazo daga can asalin garin su Firdausin, canjin daya tarar a gidanmu ne ya tayar masa da hankali, dan haka ya roƙi baba akan kawai a saka musu ranar aure.
Na taya Firdausi murna, sannan na taya kaina kuka, dan kuwa koba komai itakam ALLAH ya tsameta, niko da ko saurayi ban taɓa yibafa? Kunsan samarinma sunfi son ƴammatan masu ƙyale-ƙyale, niko bani cikin jerin masu shi, wadda suturar sakawa bata wadaceta ba ina taga kayan ƙyale-ƙyalen burge saurayi.
Saurayin Firdausi bai bar garinba sai da aka tsaida maganar aurensa da Firdausi wata biyu kacal..
Rayuwa a gidanmu ta cigaba da tafiya a ƙuntace, komai yabar mana daɗi saboda su Jazuuga, abu mafi ɗagamin hankali shine saka idonsa a kaina fiye da kowa a gidan, wani salon iskancima da ya ɓullo dashi shine danaje gyara masa ɗaki shima zai shigo ya zauna yana kallona kamar wata tv, narasa miyake kallo tare dani, ni dai sam baza'a sakani a jerin ƙyawawa ba, dan kuwa baƙace ni, bani da dogon hanci, bani da kayan ƙawa na ado da zasu fidda ƙyauna ga kowa. Shiyyasa lamarinsa ke ban mamaki da al'ajabi.
Babban abinda na riƙe shine addu'a, dan itace babban makamina a gareshi.
Yauma kamar kullum na tashi da wuri saboda zanje makaranta, dukkan abinda ya dace muyi ni da firdausi munyisa, hatta da aikinta da Jazuuga ya bata nakan tayata, saboda ni nawa saiya