Showing 60001 words to 63000 words out of 104658 words

Chapter 21 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

199

Dama yana hanya, dan haka yace mata ga shinan zuwa a rikice.

      Ba Mummy ba, hatta su Aamila da sukasan tushen komai sun rikice, dan jini bana wasaba ya ɓallema Shahudah, ta jiƙe inda take kwance sharkaf cikin mintunan da basu wuce goma ba, jikinta kam harya fara saki saboda mahaukacin jinin da take ɓararwa.
        A wannan halin Salman da Dad sukazo suka samesu, suma rikicewar sukai, wasu suce a kira Doctor wasu suce a tafi asibiti, daga ƙarshe dai sukabi shawarar Salman da yace akira Doctor kawai, dan kafin su isa asibiti Shahudah zata iya rasa rantama gaba ɗaya.
     Kowa ya gamsu da hakan, dan haka aka dannama family Doctor ɗinsu kiran gaggawa.
         Doctor ya iso akan lokaci, dan haka ya kora kowa a ɗakin ya shiga ƙoƙarin ganin ya shawo kan matsalar sai dai hakan ya faskara cikin sauƙi, dan kuwa tuni Shahudah da dai ta sanƙame masa alamar suma.
      Dole Doctor ya nema taimakon wani abokin aikinsa, babu ɓata lokaci shima ya iso tare da ƙaro musu ƙarin kayan aiki.
      Su Dad duk sun rasa ina zasu saka kansu, Mummy kam kuka take rurus wanda ya kasance da biyu, damuwar halin da ɗiyarta ta tsinci kanta da ɓoyayyen burinsu akan cikin da suka ƙwallafa rai.
       Salman zai kira Jawaad Dad ya hanashi, acewarsa kar a tada masa da hankaki su jira suga abinda zai biyo baya tukinna.
     Dole Salman ya haƙura ya ajiye wayar suka cigaba da zagayen falo, inda lokaci-lokaci Dad kan jeho musu tambaya akan miya kawo sanadin matsalar?.
       Amsa ɗaya Mummy ke badawa “Ita bata saniba, wai Shahudah tana ɗakine tun ɗazun tana barci”.
      Sam Dad bai gamsu da wannan maganarba, amma sai baija zancenba saboda a yanzu damuwarsu a ceto ran Shahudah tukunna.

★★★★★★

        Koda su Rose suka fita suka bar Jawaad shi kaɗai a office ɗin sai zuciyarsa ta kuma ƙuntata da zungurinsa da tunanin Shahudah, abin ya ɗaure masa kai sosai, dan kuwa a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya saboda takaicinta da yakeji ko kawota a ransa bayayi ma sam.
      Yanzunma dai ƙoƙarin sake ingijeta yay a zuciyarsa ya shiga wani aikin, yanayi yana jan tsaki a duk sanda ta sake faɗo masa cikin rai.
         A haka dai har ya samu nasarar janyeta cikin rai baki ɗaya ya cigaba da harkokinsa kawai.

★★★★★★★

       Likitocin nan sunsha wahala kafin su sami nasarar shawo kan jinin dake kwarara a jikin Shahudah, daga nan suka koma ƙoƙarin ganin numfashinta ya dawo, bayan ɗaukar kusan awa biyar a kanta suka samu komai ya dai-daita, sai dai sun zangaɗa mata allurar barci tare da ƙarin ruwa.
       Suka fito kowa na yarce gumi, tare da sanarma su Dad jini da Shahudah take buƙata saboda nata data kwararar.
      A nannefa aka shiga kallon kallo, dan kuwa kaf gidan jinin kowa baima Shahudah sai na Jawaad, ta taɓa samun wata matsala lokacin tana secondary, har takai ana bukatar ƙara mata jini, a time ɗin an gwada na kowa a gidan bai mataba sai Jawaad, lokacin shikuma sunje can tare da kawu Nasiru ne.
         Dad yace, “To amma Doctor kafin muje ga wannan yaya maganar cikin jikinta ne?”.
           “Alhaji ai muma ajiye batun ciki gefe, yanzu dai jinin muke buƙata da gaggawa domin tana matuƙar bukatarsa gaskiya, daga baya mayi maganar cikin”.
       Ajiyar zuciya Dad yayi, ya ciro wayarsa a aljihu yay kiran Jawaad, kusan kira uku bai amsaba, hakanne ya saka Dad tunanin lallai Jawaad yana kan aiki, dan baya taɓa masa kira biyu a ce bai ɗaukaba inhar yana kusa.
      Yana cikin yin zancen zucine sai ga kiran Jay ɗin ya shigo, jikin Dad har rawa yake ya ɗaga.
      Haƙuri Jawaad ya bashi akan yay masa afuwa suna yin sallar la'asar ne.
     Ajiyar zuciya Dad ya sauke, danshi ruɗewar da suka tsinci kansu a ciki bata bari sunji kiran sallarba ma.
       “Babu komai My Son, wlhy wata matsalace ta taso shine nace ALLAH yasa bakan aiki kakeba zan katseka”.
      Gaban Jawaad ya faɗi, dan muryar Dad kawai ta mugun tsorashi,  yay saurin faɗin, “Babu damuwa Dad, kana buƙatar ganinane?”.
         “Sosaima kuwa my son”.
         “Insha ALLAHU ka bani nanda mintuna talatin zan iso”.
      “ALLAH ya kawoka lafiya”.
     Dad ya faɗa yana sauke wayar a kunnensa.

           Jawaad ya rasa mizaiyi hasashe a wannan wayar da sukai da Dad, jacket ɗinsa sky blue daya ɗoro saman baƙaƙen kayan jikinsa ya ɗauka jikin hanga ya fice cikin matuƙar hanzarinsa.
      Gimba na hangosa ya taso da hanzari yazo ya buɗe masa mota ya shiga, ba tare da ya tambayi ina suka dosaba ya tada motar suka fito.
       Saida suka hau kan titi Gimba yace, “Boss ina zamuje”.
         “Zangina road” kawai ya iya furata masa yaja bakinsa ya tsuƙe.
    Gimba daya fahimci ina suka dosa ya ɗauki hanyar da zata sadasu da gidan su Shahudah.
           Tunda aka buɗe gate ɗin gidan gaban Aamila da tasan dokar ya shiga faɗuwa, jitake kamar Jawaad zai gane komai da ya faru a kan fuskarta.
        Jawaad ya shigo cikin bajintarsa da jin shiɗinfa ya isa, fuskarsa sam babu walwa.
          Yanda yaga duk sun nutsu waje guda sun zuba tagumine ya sakashi tsaresu da mayun idanunsa, Ya sauke akan Jack dake zaune kusa da Salman, aransa ya furta “Jack again?”.
       Janyewa yay ya maida ga Dad daya miƙe tsaye yana faɗin, “Yauwa My son ka iso?”.
     Kai kawai Jawaad ya iya jinjina masa yana haɗiye wani yawu mai kauri saboda ganin Jack.
      Mummy ma ta miƙe ta nufoshi kamar yanda Dad yayi.
      Kusan a tare suke ƙoƙarin masa bayani, dan haka ya zuba musu idanu ko ƙyaftawa bayayi.
       Tunda suka ambaci jini da Shahudah ta zubar yaji tamkar an buga masa guduma a kansa, ya wani lumshe idanunsa da suka fara canja launi yana fidda numfashi da sauri-sauri.........
       Maganar Dad dake cewa, “My Son yanzu haka sunce tana buƙatar jini da gaggawa, inba hakaba zamu iya rasata” ta katse tunaninsa.
        Buɗe idanunsa yayi yana buso numfashinsa, ba tare daya cema su Dad ɗin komaiba ya juya ya kalli likitocin dake tsaye tsuru-tsuru suna kallonsa.
     Takawa ya farayi a hankali cikin nuna halin ko in kula zuwa garesu, ya zauna cikin kujerar dake wajen yana harɗe ƙafafu tare da miƙa musu hannunsa kawai, saboda t-sheat ce jikinsa baƙa wadda ta fidda dukkan ainahin surarsa, sai jacket dake samanta itama tsawon hannun iyakarsa gwiwar hannunsa.
         Yanda Doctor yaga Jawaad ɗin duk sai ya dabarbarce, a harzuƙe Jawaad ya kallesa, cikin daka tsawa yace, “Jinin zaka ɗiba kokuwa kallona zaka tsayayi malam?!”.
         “A'a yallaɓai, ALLAH ya huci zuciyarka” Doctor ya faɗa jiki na ɓari.
         
      Su dai su Dad duk sun zuba musu ido, tsawar da yay ko ai har cikin hanjin cikin Aamila da Salman ta shiga, shi kansa Jack baisan Jawaad bane zaizo gidan da tuni yabar falon ma.
          Doctor ya gama shirin ɗibar jini a jikin Jawaad, dan haka a ɗan shakku yace, “Yallaɓai ko zamu samu ɗaki mu shiga ka kwanta, saboda dokace na ɗibar maka jini a haka”.
       Wani mugun kallo Jawaad ya watsama Doctor ɗin, ya ja siririn tsaki da faɗin, “Kai dokar ta dama, kana ɓatamin lokaci bayan inada abunyi kuma”.
         “Sorry yallaɓai”.
Uffan Jawaad baice dashiba, sannan ko gezau baiyiba dukda allurar da aka surkuɗa masa cikin jijiyar hannu, wayama ya ɗauka yana latse-latse abunsa tamkar baisan mi akeyiba.
        Yana a haka har aka kammala ɗibar jinin, Doctor yace, “Yallaɓai kayi haƙuri karka tashi, dan jiri zai iya kwasarka”.
        Banza Jawaad yay masa bai tankaba, duk da idanunsa na masa yam-yam sai ya dake bai nunaba.
      Dad da yasan kaɗan daga taurin kan Jawaad yace zai tashin yay saurin faɗin, “My son karka tashi kaji, kaɗan dakata ɗin kamar yanda yace”.
         Guntun murmushi ya ɗago yayma Dad ɗin amma baice komaiba, sai kansa daya maida jikin kujerar ya kwantar kawai ya lumshe idanunsa.
      Mummy tazo kusa dashi ta zauna tana miƙa masa abu a kofi.
       “Karɓa kasha wannan”.
     Idanunsa ya buɗe yana kallonta, ta kamo hannunsa ta saka masa kofin, hakanne ya sakashi ɗago kansa daya kwantar yana kallon abinda ke ciki.
        Kofin ya matse cikin hannunsa yana ƙankance idanu, a bazata yace, “Mummy miya kawo sanadin hakan?”.
         Dukda itama Mummy batasan sanadiba sai da gabanta ya faɗi, cikin ɗan in ina tace, “Yaro na santsin ruwane ya kwasheta ta faɗi, kasan Shahudah batajin magana akan saka shegun takalman nan masu tsini”.
       Karan farko daya saki wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa lotsawa, yakai kofin da Mummy ta basa kan bakinsa ya shanye abinda ke ciki gaba ɗaya ba tare da ya bama Mummy amsar maganarta ba.
       Koda ya miƙa mata kofin sai ya maida kansa ya kwantar jikin kujerar yay shiru tamkar mai barci.
      Gaba ɗayansu ido suka zuba masa, gaba ɗaya yanayin da Jawaad yake ya bama Dad mamaki, amma sai bai kawo komai a ransa ba ya danganta hakan da yanayin aikine maybe................✍🏻

Page 24

..............Tabbas ran Jawaad a ɓace yake, amma baka isa fahimtar hakan a kan fuskarsa ba, kusan mintuna talatin ya ɗauka zaune kafin ya miƙe da shirin tafiya, a cewarsa zaije ya dawo.
        Da kallo duk suka bishi, idon Aamila tamkar zai faɗo ƙasa kuwa, gani take tamkar abinda suka aikata zaije ya binciko.
       Salman ya sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Wai miya kawo wannan matsalarne?”.
       Jack da Aamilah suka kalli juna kawai, kowanne na haɗiyar yawu da sauri, dan basusan amsar da zasu bama Salman ɗinba kuwa.

        Dad kam sama ya nufa yace Mummy tazo yana son ganinta.
     Koda suka ƙarasa ɗakinsa sai ya turke Mummy da tambayoyi.
       “Aysha mi kuke ɓoyewane?”.
      “Kamarya Dadynsu?”.
“Ya ina tambayarki kina tambayata? Yanayin yaron nan kawai ya tabbatarmin akwai wani abu dani ban sanshiba, sannan namiki tambayar miya kawo sanadin zubar jinin, kincemin kema baki saniba, tana ɗaki tana barci, amma gashi shi kin sanar masa faduwa tai da takalmi, minene gaskiyar zancen?”.
          “Wlhy Dadynsu nima sai da na faɗa ne na fahimci nayi kuskure, amma kamar yanda na sanar maka bansan minene sanadinba, dan tana ɗaki kwance ne”.  
      Kai Dad ya dafe yana bubbugawa, itama Mummy zama tai ta sake zabga tagumi tana zancen zuci, babban fatanta ace kawai cikin nan bai zubeba.
    Sai dai ita kanta zuciyarta na rawa akan kar dai Shahudah bataji ƙwaɓar da sukai mataba sai da ta aikata ƙudirinta kamar yanda take buri tun farko akan cikin?.
     ‘Innalillahi, kai amma da yarinyarnan ta cucesu wlhy kuwa’.

         Likitocin nan sai da suka samu dai-daituwar komai sannan suka fito, har lokacin Dad da Mummy basu sakkoba.
        Aamilah ta matsa kusa da Doctor ɗinsu, catai yazo zasuyi magana dan ALLAH, tashi yay sukai waje, babu wanda yasan mita faɗa masa, kusan dai mintuna goma sai gasu sun dawo falon.
      Itace ta haura sama ta kira su Mummy, Doctor yay musu bayani cewar cikin jikin Shahudah da dai ya zube.
      Tambayar farko da suka haɗa baki wajen jefo masa shine, “Minene sanadi?”.
        Jimm kaɗan yay kafin yaɗan gyara zamansa, ya ce, “Eto Alhaji matsalar dai kamar daga mahaifarta ne, dan bata da ƙwarin riƙe abu mai nauyi, yanzu kuma cikinta ya shiga wata na uku, shiyyasa ya fara nauyi kaga”.
      Kai Dad ya jinjina daga shi har Mummy sun gamsu da hakan, sai yanzu yakejin zargin da yake ya bar ransa, ya gamsu da bayanin matar tasa, amma kuma tayi gangancin cema Jawaad ɗin takalmine ya kada Shahudah.
     Itako Mummy dai can ƙasan zuciyarta kamar tai hauka takeji, dan gaba ɗaya kalmar zubewar cikin nan ta gama birkita mata lissafi, kallo ɗayama zakai mata ka fahimci bata a cikin nutsuwarta.
        Shi dai Doctor yay musu ƙarin bayani akan idan Shahudah ta tashi, tare da cewa zaije asibiti, idan ya taso aiki zai biyo ya kawo mata magunguna.

★★★★★★

           Koda Jawaad ya koma Office harkokin gabansa ya cigaba dayi tamkar babu abinda ke damunsa, sai ɗan ciwon kai da yake danganta nasabarsa da jininsa da aka ɗiba, maimakon kuma ya samu nutsuwa ya huta sai hakan ta gagara, dan bayan kamar awa biyuma Asibiti sukaje shi da Hafeez duba Alhaji Kokino da jikinsa yay ƙyau Alhmdllh.
      Dukkan iyalansa na wajen, Shema'u ganin Jawaad jikinta har ɓari yake, shiko batasan yanada abinda kecin ransaba, koda ta gaishesa hannu kawai ya ɗaga mata ko kallon arziƙima bata samu daga garesa ba.
    Basu wani jimaba suka baro asibitin, kasancewarsu ƴan sandan farin kaya, ba kaki suke sakawa ba sai babu ruwan kowa dasu, babuma wanda ya kawoma ransa ƴan sandane su, sai dai iyalan Alhaji Kokinon da suka sani.

     Bai sake waiwayar gidansu Shahudah ba sai da ya tashi aiki, daga nan ma ɗin gida ya wuce, yay wanka ya kimtsa bayan yasha tea daya zame masa amini yanzu, ya fito cikin kayansa masu taushi farare masu tambarin Adidas, ƙamshinsa yake fitarwa a hankali.
      Yauma da kansa ya tuƙa motar zai fice, a gate sukai karo da yaron Kawu Saminu Mas'ood, sauke gilas ɗinsa yayi kamar yanda Mas'ood ɗin yay shima, cikin mutuntawa suka bama juna hannu kowanne yana daga mota bai fitoba sukai musabaha, kowa na tambayar iyalan ɗan uwansa.
         Daga haka Jawaad ya fice Mas'ood kuma yay ciki.
         Redio ya saka yana saurare harya isa anguwar su Shahudah dake shiru babu hayaniya, duk da babu wutar lantarki ko wanne gida zaka samesa da hasken janareto tunda anguwar duk irinsune masu hannu da shuni.
        Yanayin Horn mai gadi ya buɗe da hanzari, dan cayake burkutaccen nanne Qaseem.
        
         Salman da jack na zaune a harabar gidan can gefe, Dukansu kowa da sigari a hannunsa yana zuƙa suna fira.
       Salman yay saurin jefar da tasa ya take da ƙafa saboda ganin motar Jawaad.
        Nesa dasu kaɗan yay fakin, dukda ya gansu ko kallo basu ishesaba ya rufe motar yay ciki abinsa.
          Babu kowa a falon gidan, amma tv nata ɓaɓatu, tsaye yay yana bin falon da kallo kamar wani baƙonsa, hannayensa dukansu na cikin aljihun wandonsa.
       Aamila ta fito daga kicin hannunta ɗauke da kofin tea da kuku ya haɗama Shahudah ta amso mata.
      Sosai ta firgita da ganin Jawaad, yanda tai bayama kaɗan ya rage ta zubda shayin.
    Ɗauke idonsa yay daga kanta tamkar baiga halin data shigaba.
        Sannu tai masa, bai amsaba sai kansa kawai ya gyaɗa mata, cikin in ina tace ya hawo sama Shahudah nacan.
       Duk da yayi ɗan mamakin miya maidata sama bayan yasan ɗakinta a ƙasa yake, amma sai bai ce uffanba yabi bayan Aamilah.
        Aamilah ce ta sanarma Mummy da zuwansa, Mummy taɗan ɗaga murya tana faɗin ya shigo mana.
      Jawaad dake ƙofar ɗakin tsaye duk yana saurarensu tura ƙofar yay ya shiga da sallama.
       Kallo ɗaya yayma Shahudah dake kwance a gadon dan bata daɗe da farkawa ba, ta daiyi wanka dan ɗaure take da tawul fari, daka ganta kasan batada lafiya dan tayi zuru-zuru, ta ƙara haske sosai ga idanuwa sun kuma yo waje.
          Gaisar da Mummy data miƙe yayi, ta amsa suna ficewa ita da Aamilah daga ɗakin.
     Tunda suka fita saiya shiga bin ɗakin da kallo tamkar ya ajiye wani abu a ciki, hakan ya saka itama Shahudah ta bisa da kallo ƙirjinta na wani bugawa kamar zai fito.
       Kusan minti ɗaya yana kalle-kalle kafin ya koma baya. jingina yay da bango hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa, ƙafarsa ɗaya ajiye a ƙasa ya tokara ɗayar jikin bango, ya tsurama jojo karen Shahudah dake kwance kusa da ita ido ko ƙyaftawa bayayi, sai faman cizon leɓensa na ƙasa yakeyi.
        Shahudah da duk jikinta babu ƙwari ta miƙe zaune da ƙyar ta jingina da filo, kofin gefenta ta ɗauka tana juya cokali cikin shayin da Aamilah ta kawo mata, ta ɗago idanu ta sake kallonsa, “Bb ka zauna mana” tai maganar a matuƙar sanyaye.
     Ƙala baice mataba, sai ƙafarsa daya sauke yana cigaba da kallon jojo.
       Ya tako a hankali zuwa gaban gadon ya tsaya a kanta, sai kuma ya ɗora tsaftatacciyar ƙafarsa saman gadon yana zuba mata idanunsa da suka canja launi baki ɗaya.
        A bazata tajiyo muryarsa kausashe yana faɗin,
       “Wane likitane yay wannan aiki?”.
     Dakewa tai cikin nuna halin ko in kula tace “Wane ai kuma Bb? Kainefa ka bani jini, kuma doctor ɗinmu ne ya ɗiba, wane kuma aiki kake buƙatar sanin wanda yay bayan wannan?”
       Ƙafarsa ya sauke ƙasa yana sakin wani murmushin daya saka zuciyar Shahudah harbawa da ƙarfi.
      Kujera ya jawo ya zauna, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, ya kuma tsuke fuskarsa yana kafa mata rikitattun idanunsa, “Hudah kinsan sunan aikin ɗan sanda kuwa?”.
     Kanta ta girgiza masa a hankali, yanayin da fuskarsa take ya sake ruɗata.
       Sauke ƙafarsa yay ya ɗan ranƙwafo yanda zasu ƙara samun kusanci, cikin magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login