Showing 84001 words to 87000 words out of 104658 words

Chapter 29 - Kwai Cikin Kaya Book 1 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

214

inda ka cire irinsu Qaseem da suka gaza ɓoye hassadarsu akan maganar.
      Dan kuwa dai kowa yasan badan matsayin kujerar Jawaad ta kai bane ya samu wannan cigaba, cancantace kawai da ƙwazonsa ya kaisa.
      Da yake tafiyar gaggawace sai basu wani zaman ɓata lokaciba suka fara shiri, horarwas zata zama ta shekaru kusan biyu ce, amma bawai lallai su cika biyunba cif-cif, dan a ƙa'ida ma shekara ɗaya da rabine, sauran watannin da zasu biyo baya na wani tsarine daban.
     Hakan yasaka su Aliyu duk da iyalinsu zasu wuce, Rose da Jawaad ne kaɗai babu mahaɗi🥴😂.
          Ya sanarma Uncles nashi gaba ɗayansu, sun masa fatan alkairi kuma tare da addu'ar samo nasara.
     Sai kuma shawarar mizai hana ya zaɓi ɗaya a yaran dangin a ɗaura musu aure ya tafi da ita, dan ba girmansa bane zama babu mace sam gashi har yana a shekara ta biyu da rabuwarsa da Shahudah, musamman a ƙasa irin wadda zaije yanzun akwai damuwa.
     Bai wani jasu da nisaba ya nuna musu suyi haƙuri, maybe zuwa nan gaba idan bukatar hakan ta taso koda yana a cannne zaiyi magana.
       Aiko wannan furuci nasa ya sakasu rabama ƴaƴansu lambarsa suyo farautar zuciyarsa bayan wucewarsa daya kirasu ya tabbatar musu ya sauka ƙalau.
     Ko Baba ma sai da yay masa maganar auren kafin ya wuce, dan dama yana yawan masa shi dasu Umma, amma a koda yaushe yakan basu haƙurine da daɗin bakin su ƙara masa lokaci, bayason a sake tafka kuskuren baya kamar aurensa da Shahudah.
       Sun masa fatan alkairi da addu'ar dacewa da mace ta ƙwarai da nasara akan abinda zashi nema................✍🏻

Page 31

............A ɓangaren Shahudah kam taci alwashin sai Jawaad yazo ya nemeta har inda take, dan a nata hasashen gwala rayuwarsa take a haka.
     Tasan ɗunbin son da yake mata dolene ya jigatu da rashinta, shekaru biyar ta ɗiba masa cif, sai ya koma ƙaramin mahaukaci a kanta sannan ta bayyana a garesa.
       A shirmenta ko ganin ta cinye shekaru biyu bai nemetaba baisa taji a ranta akwai matsalaba, a'a a ganinta kawai ya rasa hanyar da zai iya ganintane, tunda Mummy ta tabbatar mata Jawaad baisan inda takeba har yanzu.
       Ita kuma duk motsin Jay Mummy tana sanar mata komai harma Aamilah da Salman, wani lokacinma harda Qaseem, ko dangane da tafiyar Jawaad Qaseem ne ya sanar mata komai.
        A duk sanda akai mata zancensa danne zuciyarta kawai takeyi, amma kewarsa da ɗunbin begensa kullum sake mamaye zuciyarta yakeyi, batason ya kalleta matsayin mafi arha a mata shiyyasa tai dauriyar riƙe ajinta gam tunda ta ƙetaro kasarsu tai kunnen uwar shegu dashi, sai dai a kullum hotonsa shine abin kallonta, hakama duk wata kafar yaɗa zumunta datasan yanada accaunt a wajen tana bibiyarsa da sunan da ba nataba.
       Ta kasa kula kowane saurayi, ta dai yarda kuyi abota amma ba soyayyaba, to kuma dama can dai gaskiya Shahudah bata iskanci, koshi Jay shaidane akan cikakkiyar budurwa ya sameta, dama can iskancinta baya wuce shan minti, amma bata yarda tarayya da waniba, takance wannan mallakin Jay ne tunma a wancan lokacin, to a yanzunma dai da harma yanzu take ɗauka da aurensa kanta tana taka tsantsan, sai dai fa iya shege da duk wani dandali na taruwar wayayyu tana a wajen babu abinda ya dameta, tunda bawai muhimmancin auren ta saniba balle ƙa'idojinsa, a ganinta duk abinda takeyi ƴancinta ya bata damar yin hakan, balle ta dawo inda babu ruwan wani da wani.



A gurguje⛹‍♀😏

_________________________
       BILKEESU
_________________________

             Rayuwa tai nisa, sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun zama yini, yini ya rikiɗa dare, kafin wani dogon nazari daren ya haɗa kwanakin da suka bada satittikan da suka dunƙulle wattani, sai gamu da shekara ɗai-ɗai har huɗu cif a makaranta, yanzu haka jarabawa biyu kacal ta rage mana kammala jarabawar ƙarshen zangon karatunmu na.
     Abubuwa da dama sun faru, wasu a iya tunawa, wasu ko zuciya ta manta saboda hidimomin yau da kullum, mun kwankwaɗi madarar ilimi wadda muke addu'a da fatan ta zamewa rayuwarmu dana ƙasa damu alkairi.
     Zakusha mamaki idan kukaji a cikin baƙin al'amuran da suka zoma rayuwata ciki harda soyayyar Yah Qaseem datai ƙarfi a tsakaninmu,
      Hoo duniya makarantar makaho, kai mai idonma ba ɗage masa ƙafa takeba, wai ni Bilkisu ƴar baƙa mummuna ƴan ƙwalisar samari masu ji da ƙyawu da ƴan canji a aljihu irinsu yaya Qaseem keso? To lallai dai abin da mamaki, sannan yana buƙatar alamar tambaya, shin sone na gaskiya? Kokuwa sone na sha'awa?.
      A wannan kaftawar da zamu farane kawai kowa zai iya fahimtar hakan, danni dai har yanzu baiji amsa tayinsa daga bakina ba.
     Dan duk wani salon rayuwa da iya zama da jama'a a yanzu Alhmdllh na san gwargwadon ilimin da UBANGIJI ya bani.
          Maza da yawa surar da ALLAH ya bani ke ɗibarsu zuwa gareni, ba wai ƙyawuba, duk da ƙoƙarin killace jikina da nake ban tsiraba a wajen mayu irinsu Yah Qaseem.

_________________________

             Uzirin gaggawa ya sakani dawowa gida a weekend ɗinnan domin ɗaukar abinda na manta, babu wanda yasan da zuwana, dan motar haya na shigo.
       Tun isowa gidan namu gabana ya faɗi, dan kuwa da motar ƴan sanda naci karo, na tura ƙaramar ƙofar gate na shi da sassarfa, dama dagani sai handbag ɗita.
        Zan shigo ƴan sandan zasu fita, dan haka suka bani hanya saboda na riga na kawo jiki, koda na shigo sukuma sai suka fice, na bisu da kallo kafin na maido kan Amina dake ta faman kuka ga mamanta itama tanayi.
       Sai Dad da Mummy dake tsaye sunata faman faɗa akan maza su Amina su fice musu da ga gida, inba hakaba zasu bama ƴan sandan da suka fice dama su tafi dasu.
      Gaba ɗaya ban fahimci yaren kowa a cikinsuba, na sake maida dubana ga Yah Salman dake kan mota zaune yana wani munafukin murmushi, Aamilah na daga gefensa tana latse-laste a waya.
         Nai saurin ƙoƙarin riƙo hannun Amina da suke ƙoƙarin fita, amma sai ta fisge a fusace harda bigemin hannu ta fice.
          ‘Lallai akwai matsala’ na ambata a zuciyata ina binsu da kallo har suka fice......
     Kiran da Dad ke minne ya katse tunanina, na sauke ajiyar zuciya ina nufarsu hankalina duk a tashe da tunanin mi akaima Aminar?.
          Ina isowa gabansu Dad abinda ya fara faɗamin shine, “Ƴata rabu da waɗancan masherantan mutanen kinji, dan ba mutanen arziƙi bane masheranta, duk ƙyautatawar da mukaima rayuwarsu sai suka ƙare da nemanmu da sharri”.
      Duk da bansan kan al'amarinba sai naji kalamun dad basumin daɗi ba, dan haka nai murmushin yaƙe kawai ina faɗin, “Wani abune ya faru Dad?”.
     Kafin ya bani amsa Mummy ta katsesa da sauri, “Daga shigowarki Bilkisu, ki shiga ki huta mana koma minene zakiji daga baya”.
        Kaina kawai na iya ɗaga mata, suka shiga ni kuma nabi bayansu.
     Dad dake zama a kujera yay min tambayar lafiya nida nake ƙoƙarin zana jarabawa ta ƙarshe nazo gida?.
        Sai da na durƙusa a gabansu na gaishesu sannan nai masa bayanin abinda ya kawoni.
         Ganin ya gamsu da maganatane ya sakani miƙewa na nufi ɗakina, dan duk tunanina a dagule yake da abinda na gani, sam zuciyata ta kasa yarda su Amina ne basu da gaskiya. Akwai dai abinda tabbas shi Dad bai saniba an ɓoye masa.
      Har nai wanka na fito domin cin abinci wannan lamari na sukata, babu kowa a falon na wuce kicin, a can ɗinma ban samu kowa ba, to dama wa zan gani? Amina ce dai da kuku kuma ga ayanda na iske gidan.
         Babu komai a kicin ɗin, amma da alamun dai anyi abinci, fitowa nai dan na san yana Dani, ilai kuwa a can na hangosa, tunani baisa hankalina ya fara kaiwa canba.
       Ɗiba nai na koma ɗaki kawai, duk da uwar yunwar da nakeji sai kuma nama kasa cin abincin, dan laumata ɗaya jal na ajiye cokalin ina sake karanto damuwar dake tattare da Amina.
     Amina ta taka rawar gani a rayuwata ta gidannan, dan ta soni a lokacin da kowa ya tsaneni, ta ƙaunaceni a lokacin da kowa ke ƙyanƙyami na, to ni tayaya yanzu zan sami nutsuwa a halin da take ciki?.
     Bani da ikon fita gidan a yanzu, amma nayi alwashin zuwa anjima ko a sacene sai naje gidansu Amina.
      Da ƙyar naci rabin abincin dana ɗebo, na zuba tagumi ina cigaba da saƙawa da kwancewa.

         Bayan sallar isha'i na fahimci gidan yayi shiru, a hankali na leƙo falon, babu kowa a ciki, yau ko tv ma ba'a kunnaba, cikin sanɗa na nufi kicin, ta ƙofar baya na fita a hanzarce zuwa harabar gidan, nanma sai da na wawwaiga na tabbatar babu mai kallona sannan na nufi gate.
     Baba mai gadi ya taso yana tambayata ina zanje, saurin masa alamar yay shiru nayi, murya ƙasa-ƙasa nace, “Gidansu Amina zanje baba, dan ALLAH ko wani ya tambaya karkace na fita, duk da nasanma da wuya asan bana nan”.
     Kansa ya ɗagamin, ni kuma na fice da sauri...............✍🏻


Page 32

..............Gidansu Amina yana maƙwaftaka da gidanne, dan duk anguwar kusan shine ginin talakawa, Amina ta taɓa sanarmin Babanta ne ya saidama Dad filinsa kafin ya rasu, ya kuma roƙesa akan dan ALLAH karya bar wani ya amshe gidan dasu Amina suke ciki danya lura masu hannu da shuni duk sun saye gidajen talakawan wajen sunyi gine-gine saboda ƙyawun anguwar, shiko gidansune na gado bayason yaransa su rasa.
      Wannan alƙawarine da dad ya riƙe ya saka gidansu Amina zama zakka a anguwar duk da kuwa ansha ƙulla musu dan a mallaki gidan hakan bata faruba.
          Da Amina na fara tozali tana kwance a ƙofar ɗakinsu lulluɓe da bargo tana rawar sanyi, na ƙarasa gareta ina ambaton sunanta.
     Dai-dai nan mamansu ta fito tana ɗangyasa ƙafarta dake mata ciwo, saurin dakatar dani tai a zafafe.
     Na tsaya cak ina kallonta da mamaki, dan nasan matar tana sona sosai, tana ɗaya daga cikin waɗanda suka koyamin dabarun rayuwa da mutane.
       “Mi kikazo yi mana a gidan, ki fita dan ALLAH, bana buƙatar sake ganin fuskar kowa daga ahalinku, dan haka fita kona miki abinda baki taɓa tsammaniba....”
        Kaina na duƙar ƙasa gabana na sake tsananta bugu, murya na rawa nace, “Mama dan ALLAH kiyi haƙuri, kimin uziri bansan komaiba dangane da abinda ke faruwa ba, babu kuma a wajen wanda zanji sai ku, nasan tunda naga fushi a fuskarki an miki ba dai-dai bane, dan ALLAH ki lamincemin mu raba wannan damuwar tare ko zanji sassauci a raina, da......”
     Saurin dakatar dani tai da fadin, “Damuwarmu ai tafi ƙarfin mu kasaftata wani ya samu wani yanki a ciki, an rigada an cuta mana, saboda bamu da komai kuma an nuna mana fin ƙarfi, Bilkisu jin abinda ya faru bashi da amfani a gareki sam.....”
      “Yana da amfani Mama, koba komai ƙila inada gudunmawar da zan iya badawa”.
        “Baki da ita Bilkisu, dan haka fitar min daga gida”
     Ko motsi kasawa nai, hawayen da nake riƙewa suka gangaro bisa kumatuna, juyawa nai a hankali zan fice muryar yayan Amina malamin islamiyyarmu na tsinkayo yana ma mamansu magana.
       “Mama karki haka mu saurareta, dan muma munsan bata san komaiba tunda batanan, kuma koda tana nan bata da wani ƙarfin ikon sawa ko hanawa a gidan muma shaidane”.
        Mama ta sauke numfashi da cewa, “Hakane, dawo Bilkisu”.
       Da sassarfa na juyo garesu, na tako inda Amina take na durƙusa ina yaye bargon da take lulluɓe, ƙara ta ƙwalla, hakan ya sakani saurin ja baya a firgice.
     Mama ta ƙaraso kusa damu tana mata magana, sai da ta sami nutsuwa ne maman ke cewa, “Kiyi haƙuri Bilkisu haka takeyi wanu lokacin, abu kaɗan ke sakata firgita yanzu”.
       Sosai mamaki ya kamani, na kalli maman ina tambayar to minene sanadin hakan? Dan ni dai nasan Amina mace ce mai tarin nutsuwa a komanta.
          Mama ta miƙomin kujera ƴar tsigunno, amsa nayi na zauna ina mai ƙarajin tausayin Amina.
      Itama zama tayi daga ƙofar ɗakin, yayan Amina ma ya zauna daga ƙofar ɗakinsa.
         Kallon mama nayi ina ƙara jeho mata tambayar abinda ke faruwa da Aminar.
      Mama ta sauke numfashi mai ciwo tana share hawaye, tace, “Bilkisu fyaɗe akai mata a cikin gidanku, sai dai mun gaza tantance wanene yayi?, saboda abu suka bata tasha batare data saniba”.
        Bansan sanda na koma ƙasa daɓas ba nai zaman ƴan bori, har taune harshena nake wajen faɗin, “Mama fyaɗe fa?”.
         Kasa bani amsa tayi saboda kukan da takeyi, sai yayan Amina ne cikin takaici yace,
        “Abinda ya faru kenan Bilkisu, munje mun faɗama Alhaji amma hajiya ta katsatstsare a kan sharri akaima ƴaƴanta, bayan kuma a idon mai gadi suka fiddo Amina cikin wani yanayi ita da Aamilah, munje mun ɗakko ƴan sanda shine suka basu kuɗi mukuma aka ƙaryatamu, wlhy badan mama ta hananiba da saina kaisu kotun musulinci, amma yanzu mubarsu ALLAH ya tsayar damu a kotunsa, dan yafi kowa sanin gaskiyar abinda ya faru”.
      Kuka nake sosai, wanda har su mama sai da suka koma lallashina, ganin dare yayi suka lallaɓani na komo gida.
        A falo naci karo da Yah Qaseem, da alama dai ɗakinama yaje bai ganniba, na share hawayen dake gudu a fuskata, ba tare dana kallesa ba nace masa “Ina yini”.
        Cikin kafeni da idonun da nakeji suna yawo a kaina ya amsa mani, ya ɗora da faɗin, “Ina kikaje haka? Na leƙa ɗakinki nama zata ko kina bathroom ne?”.
      Kaina kawai na girgiza masa amma na kasa magana, hakan ya sakashi takowa gabana dab, baya na matsa dan banason sunamin irin wannan abun haka.
     Kafin yay magana nai saurin faɗin, “Kaina ke ciwo Yah Qaseem, ina daga baya ina shan iska dan ina tunanin zafine”.
      Kamar bai gamsu ba, sai kuma cayay, “Okey to ALLAH ya ƙara sauƙi, kinsha magani ko?”.
    Kaina na ɗaga masa.. 
Yace, “To kije ki kwanta, dama nazo naji miya dawo dake gida keda ke shirin dawowa gaba ɗaya”.
      Sai da na raɓashi zan wuce sannan nace, “Babu komai, da safema idan ALLAH ya kaimu zan koma, dama abu na manta kuma ana buƙatarsa shine nazo ɗauka”.
      Banji amsar daya baniba, dan tuni na shige, nakuma dannama ƙofata key dan karma yace zai biyoni.
      Jingina nai da ƙofar ina kuma fashewa da sabon kuka saboda tausayin Amina, inhar zasu iya cutar da yarinyar data ɗauki tsahon shekara tara tana musu bauta to ni ta yaya zan tsira a wajensu? Miyasa zasuma Amina haka? Duk taka tsantsan ɗin yarinyarnan da riƙon addininta da martaba, Amina ko zama babu hijjab batayi a gidan, duk zafi ta gwammaci haƙuri ta zauna a hakan duk dan gujema irin wannan ƙaddarar, “Wane tsinannene ya aikata wannan aikin? Sai yaushene ƴan sandar ƙasarmu zasu ajiye kuɗi su ɗauki gaskiya? sai yaushene masu kuɗin ƙasarmu zasu fara yarda da kuskuren ƴaƴansu su ajiye son zuciya!!” na ƙare maganar da zubewa a ƙasa ina mai tauna leɓena alamar jin zafi mai yawa a zuciyata.
     Ni kaina bansan tsahon lokacin dana ɗauka ina kukaba, ban taɓajin takaicin sakacin Dad ba irin yau, dan inaji a jikina koni akaima abinda akayiwa Amina bazai ɗauki matakiba, a halin yanzu kuwa ai nice a halin hau, dan kuwa zasu iya min kwatankwacin yanda sukai mata.
        Kuka dai na yisa harna rasa hawayen zubarwa, rayuwar gidan haya da talauci, maraicin iyaye, matsalar Jazuga, haɗarin tsintar kai a matsayin mai kisan kai, faɗawa hannun su Uwargida, kuncin zama gidan Inna zainaba, duk sun faru, yau kuma ga jin daɗin da cigaban rayuwa amma cike take da ƙalubale kala-kala tare da firgicin rashin tabbas, shin mutanen duniyane a haka? Kokuwa duniyarce a haka?, wanene zai bani amsar wannan tambayar ko zata zamemin hasken fahimtar cuɗaɗɗun al'amuran cikinta?.

          Yanda naga rana haka naga dare, sai gabannin asuba barci yaɗan saceni, hakan yasa na tashi a makare, ina yin salla nai shiri a gurguje, banama son ganin kowa a gidan har Dad ɗin kansa, dan haka na rubuta masa text message akan na wuce dan yau ina da jarabawa, naji bazan iya kwana biyun da nai niyyaba sam.
          ALLAH ya soni sanda na fito ana wankema Yah Qaseem motane, bai kai ga fitowa ba.

         Gidansu Amina na shiga, mama na tsakar gida tana damun kunu, na duƙa na gaidata, cikin bina da kallo da takeyi tace, “Bilkisu miya sami fuskarki haka ne?”.
      Murmushi nayi ina haɗiye kukan dake shirin zomin, nace, “Babu komai mama, zan koma makarantane, amma insha ALLAHU baifi nanda kwanaki goma zamu dawo gaba ɗaya ba, akwai wani likita zaizo har gida ya sake duba jikin Amina, insha ALLAHU zai bata dukkan taimako, na kuma muku alƙawarin koba yanzuba saina binciko wanda ya aikata wannan ɓarnar kuma an hukuntashi insha ALLAHU”.
      “Ah ah Bilkisu, karki saka rayuwarki a haɗari kinji, koma wanene mun barsa da ALLAH, zai saka mana, mun gode da nuna kulawarki a garemu”.
       “Mama barin wanda ya aikata yaci bulus shine yake nuna na gama saka kaina a haɗari, dan abinda akaima Amina, nima zasumin kwatankwacinsa ai, ke dai kimin addu'a kawai”.
         Addu'oin fatan alkairi mama ta shiga jeramin, kafin tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login