Showing 27001 words to 30000 words out of 78068 words
bata biba domin babban burinta takai ga inda Dadanta yake a yanxun. Gudu take sharawa tamkar ba mace ba cikin ƙanƙanin loƙaci sai gata takai cikin harabar wajen shakatawar. Don gudu tayi bana wasa ma tamkar motar zata tashi sama.
A daidai table ɗin wasu mutane ta taka birki wani shegen birki.
Suna zaune a gaban wani table su kusan biyar sai mace ɗaya. wanda samansa ke ɗauke da kwallaben giya dukkansu su biyar ɗi. su na sanye da kayane na shan iska.
Cikin fushi haɗi da zafin zuciya ta banko motar ta buɗe loƙaci ɗaya ta fito da gangar jikinta tamkar wata kububuwa, basu an kara ba tasa ƙafa ta tashi table ɗin giyar nasu dukansu suka zube ƙasa .
Ɗaya daga cikinsu ne ya ɗago kai don ganin isshashshen daya musu hakan, saurin faɗaɗa fuskansa yayi da murmushi wanda ba yaro bane ba, kallo ɗaya za ka yi masa ka gane zai iya bama shekaru 60 baya ya gama mallakar hankalin sa sai dai kashhh! wannan wajen girma yayi gardama ya kuma faɗi.
Dan zungurin dada wannan mutumin yayi wanda ya ɗago kansa Cikin murya ta wanda yake cikin maye ya lumshe ido ya tare da sakin murmushin yaƙe "Dolly'n Dada! Sauƙar yaushe babu sanarwa babu komi kuma gashi ina hurin rihazal nefa na koyar rawa. Don wllh so nake nafi wancan ɗaya a cikin biyun iya rawa da waƙa. Kinga idan ban sami sarautar Emaar's ba zan tsira da waƙar kob......
Maƙale masa maganan yayi sakamakon , Cikin ƙarin baƙin ciki ta dakatar dashi shi Cikin fushi kamar zata wanka masa mari ta fara magana
" Dada what's wrong with you are you out of your mind? na tabbata duka abubuwan da kuke aikatane yake bibiyanmj ɗaya bayan ɗaya kaico da zuwa danai ba'a ƴar sa'a ba I will......
"Yasmine!!!"
Dadan ya faɗi a tsawace tamkar ba wanda ya gama magana cikin maye ba "muje gida"
Ya faɗi kwalbar giyar dabe ƙarasa zubewa ba ta ɗauka tare da kwankwaɗeta a take. Wanda Dadan nata yabita da kwallon tashin hankali "yasmine kinsan abinda kika aikata kuwa wine giya giya fa kika sha?"
"To maye don nasha ina kaima sha ka gama yanxun kuma dama shi sharri a ɗan aike nd duk inda yaje saiya dawo ma da amsarka don haka ka amshi wannan as matsayin amsar aikenka Dada"
Wani kalan jar birki yayi ita kuwa ci gaba da takunta tayi ta shige cikin motan ta tare da bata wuta tana barin harabar wurin......
_NIGERIA_
*Lagos*
Wani gwauron numfashi Mah ta kawo tare da ƙamƙame hannun Anne dake cikin nata cikin ƙasa da murya cann take faɗin.
"Easherh ki yafe min ni yafe ma DIDI'NKI BODDO'NKI Komai daya faru ba laifinta bane. Hakan rubutaccen jarabawarmune tun daga rabbis samati karki yanke mana irin wannan hukuncin Easher'n Didi!"
A hankali take zare hannuwanta ana mah ɗin.
"EASH ASH MAYESH?"
Taji dakakkiyar nusassiyar muryan dattijon ta ratsa har tsaƙiyar ƙirjinta. Bata da kwarin gwiwan bijirema zuciyarta ga abinda take shirin aikatawa. Don haka ta miƙe jikinta a matuƙar sanyaye ta isa har gaban Ash tare da kafe shi da idonta da nashi sakk ta gani kamar nata. "Shin wanne irin laifi na muku dana chanchanci wulaƙantarwarku har haka?, Ko makaho ya laluba tabbas yasan jinin dake gudana a nawa jinin nakane. Amma me yasa? Me yasa kuka aikata min haka shin ashe idan wani laifin na muku ban chanchanci da ku yafe min ba, na buɗi ido na ganni inda bansan ko wacece niba nayi kukan rashin wani ko wata dazan ƙira da nawa ko tawa ƴar uwa ko ɗan uwa na nesa kona kusa. Shin a rayuwa kunsan irin ƙalubalen rayuwar dana fuskanta a cikin wannan duniyar wannan jinin dake gudana a jikina an buɗi baki an ƙirashi da najasa haramtacce ma'ana har ƴar karuw.....
"EASHERH ASH......."
Queen lajja ta furta da ƙarfin daya sanya har na bakim palon toshe kunnuwansu. "Jinin AsH jinin AShaan Jinin lajja ake ƙira da jinin karuwa me yasa beyi zafi ba? Me yasa be tafasa? Me sa beyi aikinsa akan masu faɗawarsa don har gaban abada kinin AsH da Lajja Yafi ƙarfin a wulakanta yafi ƙarfin tozarci jininmu me zafi ne a tafashensa yake har abada ba'a taba ɗaga mana yatsa mu ƙyale! A in.......
Shiru tayi sakamakon riƙo hannunta da ash yayi da ido ya mata alama da tayi shirun haka nan, Tattausan carpet ɗin da yanzu baffansu Raiha ya shimfiɗa musu suka zazzauna. Har zuwa loƙacin kuwa Anne kukan take a nutse lajja ta Janyowata tana ɗora kanta a kan ƙafafunta. Wata nannauyar ijiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji hannun sarki Ash ya dafa saman kanta a karo na biyu masu hawahen suma sake balle mata wanda da gaza fahintar na tsananin daɗi ne ko akasin hakan.
Da hannu Mah dake kwance kan ƙafafun Anne itama taya fito Raiha a nutse ga ƙaraso ga matar me tsananin kama da Annenta. Kwantar da ita tayi akan jikinta tana shafa gashin kanta da yake a tsefe. "Ƙawa bani labarin Ningeria"
Mah ta faɗi cikin juyayyar hausanta da abin ma abin dariya. "Amma kafin nan miye sunanki?"
Ta sake tambayarta ijiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin. "Mu biyu ne ƴaƴan Anne nida Didi Ita sunanta Maryam ni kuma Razeenerh amma tana ƙira na da Raiha ma'ana kebantacciya. ita kuma Didi ta tafa faɗa mana cewar kamar tanaji a jinin jikinta kamar ta taba rayuwa dame irin sunan haka nan"
Wani irin sake rungume Raiha Mah tayi cikin jinjina iko irin na ubangiji kenan harda sunan lajja da nata Didinta ta sanyama ƴaƴanta. Duk kuwa da cewar ba duka bane ta gane abinda Raiha ɗin ta faɗi.
"Allahu Ahaad! Allahu Ahaad!!Abaan lajja kuji wani ikon allah ko lallai jinin dake yawo a tsakankaninmu me ƙarfine"
Wani tattausan murmushi Sarki Ash ya saki wanda yaja hankalin lajja itama ta saki nata murmushin.
"Nifa kun gindayar dani gaba ɗaya kaina ya ɗauke wuta. Wai me ke faruwane ku sanar dani"
Suka jiyo muryan hajiya umma da shigowarta kenan wanda daƙyar aka barta ta shigo don anguwar cike take maƙil da soldier's.
Ta faɗi tana zama kusa da Anne hannunta anne ta matse a nata bappa da kansa ya mata bayanin komai nan itama ta shiga jinjina ikon Allah da karfin zatinsa.
Nan Anne ta gabatarma dasu mah Hajj umma. mafi yawanci sarkin kano shike fassarar musu maganganun shi yasa firan nasu beyi tsaho sosae ba. Daga nan bappa yaje ya shigo da abokanan zaman Anne habawa zokaga yadda ake rarraba idanu tsakaninsu. Wannan fa shi ake da tsammaci abinda baka tsammata ba ashe ita ɗin ƴar sarautace jinin sarautace gaba da baya haba no wonder take da shegen kwarjinin tsiya da rashin ɗaukan no nonses.
A kunyace suka gaida su sarki ash ɗin da zancen kurame don basu ma san mine zasuce tunda ba karatu me zurfi sukayi ba, a loƙacin kuma malam ke koya musu sukace sun wuce ajin a koya musu yanzu yanxun kuma ga ranar ajin yazo babu ajin.
Kafin kace mene saiga labarin zuwan ash nigeria da dalilin zuwansa nata zama trend a media. Haba wa tuni duk wani me alaƙa da gidan malam abdullahi yayo maza ya garzayo, saidau wata sabuwa anguwar kanta waɗan nan soldier's ɗin sunyi block nata sunyi crossing motocinsu ta ko wanne shashe na anguwar.
Saida sukayi sallan zuhr wanda zayeed ne yajasu kana suka koma wani shegen estate guda governor ya basu. wayyo allah zo kaga yadda masallacin yayi wani kalan cika a ranar har bakin anguwar sabida balaraben da ya jasu sallah.
Kwanansu biyu suka fara shirin juyawa tare da Anne har dama hajj umma da Bappa don sunce a can ƙasar su zasu bada labarin yadda rayuwar annen ya kaya. Da da farko taso bijirewa amma kuma malam abdullahi ya bata kwarin gwiwan tafiyan kodan taje daga ƴan uwanta na jini ita taji tana da ƴan uwan da kuma dangi kamar kowa wannan shine mafarin komai.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Duk inda tura takai bango wannan shegun samudawan Ak ɗin sunƙi bayyana kansu haka kuma sunƙi bada wata ƙofar da za'a iya cimmusu. Don Tight security legency'n Ak ɗin will forever live in nigerians mind. Don he's a legend and a here.
Kuma duk wannan abin yana faruwane tare da sa hannun Kamaal Rano da Ak ɗin ya damƙa komi a hannunsa. Haka har suka gama haukarsu tare da nemansa da akei ruwa a jallo,
Shi kuwa bangaren salman abu kamar wasa saiga ƴar ƙaramar magana na neman zama babba don duk wata na belin ɗinsa a toshe yake wanda kai tsaye suma umarni suke amsa daga sama wanda kuma saman basu san waye ba daga ina yake. Tun Isa manu na boyar kansa harya bayyana don wannan videorizeeng ba ƙaramin bacin suna ya janyo mishi.
Wanda har saida General A..K..K shugaban ƙasar ganzu ya magantu akan wannan maganar.A a nan fa suma hankalin su mom surry ya fara dawowa jikinsu don tun tana zaton itace ta musu ɗaurin talala sai take ashe suma su duka harda ita aka ma ɗaurin talalar baki ɗaya ga kullum surry cikin kuka da ƙorafi dake mata akan itafa lallai mijinta take da buƙata sakamakon abubuwan data kinsa mata. Iyaka wannan kaɗai kan tashi hankalinta matuƙa Momen salman kuwa abu ya haɗu ya haɗe mata goma da ishirin gashi tashi ɗaya ƴar aikinta zeey ta bace bata battt tayi batan dabo dade da no nata baya tafiya.
Gashi yanzu isa manu shi kansa yana cikin tention yake na kulle masa yaro. Babu shiri Audu bashasha ya baro ƙasar india don dama ya gama warkewa tsoron aran gamarshi da Ak yake tsoro. yaga kuma komai ɗin na shirin sake kwabe musu, don kenan hakan ma salon wani yaƙin ne aka ballo musu wato da niya aka bar Isa manu aka garƙame masa ɗa yadda abin zaifi sukarsa gashi dai yana da duk wata dama saidai sammm damar taƙi samuwa a gareshi harda ma magoya bayansa.
Lallai sai yanzun suke sake yarda kuɗi ba komai suke iya saya ba a duniya indai akace da adalci babu son kai to kuwa har abada gaskiyace gaba da ƙarya duk girmanta koda takai tekun maliya a yawa. Gashi daga ƙasar poland sai daga company'n (E) group sai ƙiranshi suke akan lallai idan salman bai je a cikin week ɗin nan zasu janye shere ɗin da suka sanya hannu. Shi kuwa ko karen haukane ya cijeshi bazai ta6a bari ya rasa hannun jari a (E) Group ɗin ba ganin yadda yanzun shi ake yayi duk wani sabbin news da zaka samu ana yin sane akan (E) Group companie's.
Audu bashasha kuwa a daren ranar yama Nig dirarn mikiya don shima yana da nashi taskon tunda yaronsa Farouq har yau Ak ɗin be sake shiba yana a hannunsa. Kuma tunda Su Ak ɗin suka ɗauke shi kome kama da labarinsa basu kuma jiba bare gani ko a news. Iya tashin hankali Ak ya tashi hankulan mutanen nan fiye da zaton me tunani.
Gashi kuma duk inda jami'ai suko so gasgata fitan Ak a ƙasan hakan ya gagara don Inspector kamaal Rano tsaye yake akan hakan. Don indasuka fuskanci cewan ak baya ƙasan shikenan komai ka iya faruwa komi muninsa kuwa.
Don kuwa komai ahannunsa Ak yabar komai kuma kwatsam rana tsaka saiga tantirin zaid ya dawo nigeria a matsayin Ak wanda ko yaransa basu gane ba tunda su dai ba sanin ƴan biyu bane suka. Kuma dama ba yau ak ɗin ya saba musu haka ba don komai nashi zaid babu abinda be iya ba kuma babu lungo da saƙo da ak yake zuwa wanda shima be sani ba nan fa aiki ya sake daukan zafi.
Don a iya shegen zaid wanda yafi ak ɗin rawan kai da kuma zafafa kansa akan abu tuni ya matsama waɗan can bayin Allah'n lamba akan komai nasu, Iyaka kamaal ne kawai yasan ba Ak ɗin bane sai kuwa Arms da suka dawo tare da shi sai Riyya itama wanda kallo ɗaya zaid ya mata ya mato akanta. Kuma duk wani aikin daya danganci fita da ita ya datse sai dai in tare dashine kana yake barinta.
Sosae wannan abu yama arms daɗi harda ma boss ɗin don kuwa dama da biyu ya turoshi naijan.
Kamar dai yadda kuka san zaid baya taba aikinsa a gidan ko anan ɗin ma bata sanja zani ba don saiya ma zabi wuri mafi shegen taka yake gudunar da wasu manyan ayyukansa.
Baki ɗayansu suna zazzaune ne a ƙayataccen babban ɗakin taronsu wanda suke gudanar da zama irin haka fuskan wasun su ko alamun rahama babu. Isa manu ne ya buɗe zaman jugurin ɗin da sukayi ta hanyar furta. "Billahil azeem ko kaffara ba zanyi ba dasa hannun wannan shegen yaron a kulle min ɗana"
"Wa wai kana nufin _ÊÃGLÉ ÆK?_"
Sukayi wata kakkausar murya ta faɗi wacce ya sanya suka shiga waige waigen ganin ta inda muryan ya fito hantar cikinsu na ɗurar ruwa.
Kamar walƙiya haka suka kalla gimlawar abu shuuuuuuuu. A razane suka curo wuri gudu idanun kowannensu kamar ze faɗo ƙasa don tsoro, wata shefiyar dariya aka sake cekewa da ita tare da faɗin.
"Hhhhhhhhhhhhh to kuwa tabbas kunyi kuskure don yanzune zaku fara girbar abinda kuka shuka Hhhhhhhhhhhhhhh"
tayi dariyan tare leƙo da iya rabin kanta ta saman silif ɗin ɗakin Wata razananniyar ƙara suka saki haɗi da dunƙulewa wuri gudu duk cikinsu kuma babu me iya furta koda adda'a ce. "Duka a yanzu ne zasu fuskanci ainihin gaskiyar abinda kuka aikatawa mutum me daraja mutumin kwarai me zuciyar lu'u lu'u irin Naseer Baita Makole"
A tare a sukane suka ɗago daga kawunansu duka ido kamar ze faɗo ƙasa, cikin wani kalan mugun firgici haɗi da tsoro da tsantsan tashin hankali yama ƙawanya suke duban saman silif ɗin saida battt babu ko alamar wata halitta.
Kallon kallo aka shiga yi tsakaninsu ko wanne zufa na karyako masa, domin kuwa har gaban abada mutum ne da bazasu taba mantawa dashi ba a cikin wannan duniyar.
"Yaki ya riga daya soma! ya kamata a nemi makamai domin yaƙar maciya amanar ƙasa, amma kafin ka soma kai ma kanka saika zamo makami. Bayan ka gano gaskiya to saika cika aikinta yazamo wajibi agareni domin ɗaukar fansar mumunin ruhin da kuka zalunta daga karshe kuma kuka sheƙe don haka yanzu loƙacine na girbar tarin abubuwan da kuka shuka"
Baki ɗaya wutar ɗakin ne ya ɗauke
A take wani mugun duhu ya mamaye ɗakin dulum ko tafin hannunka baka isa gani ba. Ihu suka shiga yi suna faɗin ta yafesu sun dena ta musu afwa ta musu rai.
"Ba ko wanne kuskure akema afuwaba kamar yadda ba ladama ce tasa kuke neman afuwa ba kuna nemane sabo da tsira daga mutuwarku, Kunyi babakere a ƙasa kun hana matasanmu aikin yi wanda tsabar zalincinku yake sanyawa mutumin kirki ya koma bata gari, mata kuma suna faɗawa harkar zinace zinace duk ata dalilinku shin koda iyaka wannan alhaƙin aka barku ba'a barku da tarin zunufai masu nauyi ba. kun bata mana ƙasa kun sanya ƙasarmu ta zamo koma baya a ko ina akan sauran ƙasashen duniya kun kawar da iyalan da babi adadinsu. Kun kawar da shugaba na kwarai wanda tarihinsa bazai taba shuɗewa haka kuma bazai taba maimaituwa kun kawo wanda bama ɗan kasar ba kun bashi shugabancin ƙasarku! Wanda sammm babu koda ɗigon imanine a zuciyarsa wanda ƙasar sa mahaifarsa sukayi tirrr dashi ya gudu ƙasarku mara ƴancin kai me boye shegu a cikinta har kuka bashi mulkin da yake jagorantar al'ummarku ku burinku kawai kuga jama'a cikin mawuyacin hali. Inda kuke dariya a yayinda da kukaga mutunmin kirki ya koma mutumin banza bata gari cikin al'umma kuna ɗaukar manyan matsayi ku naɗa manyan malaman mu na addini a yayin da kukaga ya taso da ƙarfinsa, idan kuka bashi wannan matsayin shike nan kun gama dashi bashi da kata bisss ɗin daya isa aikata wani abu a kanku duk meye haka shin me mukai muku ne?.....
Kusani awannan zamanin hatta tsuntsaye Allah wadai suƙe da wannan zamanin don kuwa laifinku na shafarsu ta hanyar ƙafewar koramai da Allah keyi su suka suna faɗuwa suna mutu da ƙonewar bushiyu gadai abubuwan nan birjik wanda duk nayuinsu ya ta'allaka ne akanku, wasu wuraren kuwa mutuwa mutane suke akan yunwa saboda da tsananin rayuwar da kukayi sanadiyyar jefasu. A yinin yau wani bawan Allah yaje har gaban shagon wani akan da ya temaka may kodade da sarakar garine amma haka wannan me shagon ya masa korar kare gefen shagon ya nema ha zauna tare da kife kansa akan ƙafafunsa!!!.....
Kunsan meye faru? mutumin na zama Allah ya amshi ransa sai bayan mutane sun taru kana wannan me shagon ya dinga birgima yana kuka yana cewa wllh sai allah ya tambayesa don yasan
mutuwarsa ta rataye a kansa. Kuma kumsan duk su waye sanadin hakan kune! Kune!! kun maida mutane masu Taurin zuciya da zafin rai kowa najin haushin ɗan uwansa duk su waye sanadi ku bani amsa ku bani amsa ku bani amsan tambayana mana su wa ye sanadi????......"
"Mune wllh mune mune zamu gyara zamu gyara!!!"
Suke faɗi a gala6aice cikin shiga ruɗu da