Showing 72001 words to 75000 words out of 78068 words
waliman inda meerah tasha ado da gwala gwalai, gefe guda kuma ga wasu shegun Kit masu shegen kyau da tsada har set shida ko wacce kalo ɗaya me bakwai ce haka oum ta haɗa kayan. wanda kuɗaɗen da aka narka kawai wajen siyanta se abin ya baku mamaki na gaske bare azo kan uban kayan da aka zuba wanda ya lashe kuɗi wajen kimanin Billions of nera. Dom ina ambatar kuɗin nan kwakwalwan wasu ka iya juyewa kawai kuui emeg akwatu set ɗeɗe har bakwai, kana ko wacce set ɗaya tana dauke da guda bakwai.
Sosae suka gudanaf da taron walimarsu cikin aminci da jin daɗi daga nan meerah aka dangan tata da ɓangaren Ak, kuka sosai tayi kan itafa ba zata zauna anan ba seda ta koma wurin OUM,ko ita mah ɗin. Ko Jesrah seda mah ta mata jan ido kana ta saduda tahaƙura......
★
_Nigeeia
*Kano*
Tun daga bakin shi ga Countrol Room ɗin zaka fara jin kayaniya ta mutane daban², sedai wasu muryoyin sunfi wasu muryoyin yin sama.
"Lallai tabbas ya zama dole mu kawa ƙarshensa a cikin wannan tafiyar domin duk aikin da fara ƙarshe shine yake fara ɓata mana, da wannan baƙar zuciyarsa! To Allah na tuba ma yanxun waye yake tsayawa yay ma mutane aikin tsakani da Allah?, Su mutanen da kake fara karewa daga ƙarshe suna masu kwayema baya ba zasu duba irin talin halacci da sadaukarwan daka musu ba.
to duk miye amfanin wannan kunga kuwa kwara ka tsaya ka mori ƙuriyarka da loƙacinka amma ya zama dole mu kawo ƙarshen Kamaal a wannan karon." Dcp ya faɗi ransa na sake ƙuna domin wani aiki da suke yi akan case ɗin wata yarinya da akayi rep nata. So kuma ɗan gidan mataimakin gwamna shi ne yayma yarinyan fayɗe daga bisani kuma ya kashe ta, shine fa iyayenta suka shigar da ƙara, su kuma gwamna da mataimakin gwamna suka baza kuɗi kan karsu yadda sunan ɗansu ya ɓaci.
Shine shi kuma kamaal ɗin ya jiƙa musu aiki ta hanyar fara binciken sirrin daya fara, kasancewar sune gwamnatin ya sanya tuni maganar ta shiga kunnuwan gwamna da mataimakin gwamnan, shine suka bada umarnin asheƙe shi kawai kai tsaye.
★
*Kamaal Pov*
Kasancewar duk ranar yau be fita bane kasancewar hutu da suka bashi na 2week. Haka suka wuni ƙauna shida mariyanshi da kuma onborn ɗinsu da bai riga da yazo ma duniyar ba. Kamar yanzu ma tana kwance kan ƙafafunsa basu jima da dawowa daga gidan suba da kamaal ɗin shiya buƙaci da suje da kansa. hannunsa dake kan cikinta da yasoma girma itama ta ɗora nata saman nasan tana sakin ijiyar zuciya. Fuskanta ya ɗan shafa yana ajje Littafin *MIN HAJJIL MUSLIM* dake hannunsa yana gyara mata kwanciyarta a jikinsa. "Kwana biyun nan fa duk mrs aiy ta damu Aiy nata da son jikin nan nata sosae"
"Kawai nima naji inason hakan hakan! Jikina ne nake jin duka babu daɗi a cikin kwana kin nan wllh, ga yawan faɗuwan gaba duk sena ji jikina yayi sanyi sosae wllh Soyayyata!!!"
Ta faɗi cikin raunin murya har wasu guntun hawaye na saƙƙo mata. Wani ɗan guntun murmushi yayi yana faɗin, "Ba wani nan kedai kawai son jikinki ya motsa dai ne madame" sake kanƙamesa tayi tana sakin kuka kawai tare da faɗin "Allah da gaske nake ba da wasa nake ba Yaya Kamaal! Samm sammm bana jin daɗin jikina da yanayin, se nake jin tamkar woni abu daga sashe na jikinane ke shirin barina ko rabuwa dani na har abada yaya"
Ta yi maganar in serious hawaye na zubar mata.jin sunan yaya data ambata ne ya sanya shi ɗago kanta cikin wani tattausan sauti ya furta "Miye kuma na kukan? Kuka baya miki wuya ƙo mr aiy?na rasa dalilin dake sanya min mata kuka" kanta ta sake jijjagawa dan ita kanta bata san dalilinta nayin kukan ba kana ba zatace ga abinda yake sanyata kukan ba. Hawayen fuskanta ya shiga share mata yana faɗin.
"To bana son wannan kukan don Allah kimin alƙawarin ba zaki min wannan kukan ba adda'a itane maganin koma menene ba kuka ba. A duk sanda kikaji tsoro ko faɗuwar gaba ba kukan ya kamata kiy ba yi koƙarin danne su da ambatar Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un wannan kalmar yana samar da nutsuwa mrs aiy!" ya yi maganar
yana jin yadda gabansa ya buga a loƙaci ɗaya amma seya shanye hakan yana kawar da tunanin dake son bijiro may. Don ma gudun kada ta fahimta komai tattare dashi ne ya sanya shi miƙewa bayan ya gyara mata konciyarta yana me ce mata
Bara yaje mosque ya dawo. Har yana tsokanarta wannan
Ko kafin ya dawo cikin ƙarfin hali ta ɗan shirya masa wani guntun kirki sama sama shima ta soya may wainan kwai da tea. Daga nan wanka tayi itama ta gabatar da sallar isha'i ta sanja kayanta xuwa wasu riga da wando dogaye marasa nauyi sosae sky blue. Palon ta koma tana zaman jiran ya shigo babi jimawa kuwa se gashi ya dawo, daga zaunen da take ya cirata ita da jikin jikinta yana zaunawa mazaunin da take yana ɗaurata kan ƙafafunsa ita kuma.
Da ƙafanshi yayi amfani wajen janyo dining ɗin data gama shirya may dinner. Haɓar ta ya ɗago tare da kallon cikin tsaƙiyar idanunta dake azabtar dashi. "Me abin mamaki ko?" ya faɗi yana lakuce hancinta. Duk yadda yaso da taci ta gaza cin abincin shi kuwa yaci abinsa daga nan ya ɗauketa kai tsaye yana yin bedroom da ita, yana faɗin. "Zo muje yau daren na musamman muje mr aiy taji da mrs aiy ɗinta" ƴar dariya kaɗan tayi waccs kawai ta yake ce don ita kaɗai tasan kalan gashin da take amsa daga cikin zuciyarta ƴan kawanakin nan. Sosai suka raya daren da tsabtatacciyar soyayyarsu me rai da lafiya. Washe gari ma haka ta tashi da yanayin mutuwan jikin nan har yake tambayanta kodai cikinne ke sanyata jin hakan se kawai ta faɗa jikinsa tana sakin kukan da duk tayi yake jin tamkar yankar zuciyarsa ake.
Ko a wurin aikin daya fita wanda yaune ya dawo bini bini ta ƙirashi taji wai ko lafiyansa kalau. Se kuma ta kara wayan da cikinta tace motsi yake shima yana son yaji sautin bugun nimfashin abiey'n shi. Ya kan yi dariya mara sautu ya kashe wayan kawai duk yay wanda ya kallesa da wannan murmushin yake kallonsa, Duk wasu shedu kuwa ya gama tattare abinsa wuri guda a ranar ya tafi dasu gidansa bayan ya biya ta wurin office ɗin Dsp. Inda dsp ɗin ya sake gargaɗansa akan ya janye batun case ɗin nan na yarinyan ma da bata raye bare ayi shari'an har gaskiya tai halinta me ita ya ɗauka.
"Kai a ganinka kenan, ni barazana wa mutuwata ba baƙon abu bane a wurina!, don ba jiya ba ba yauba na saba fuskantan barazana daga wurin mutane maban banta. Don haka tunda har na riga na fara aikin nan nake ga babu barazanar data isa sawa na janye batuna akan masu gaskiya se ko in mutuwa nayi bi ma'ana kuka sanya aka raba numfashina da gangar jikina!" se kuma ya ɗan dakata tare da fesar numfashi.
"Se dai kashe ni a tafiyar ba shike nufin kawo ƙarshen azzaluman mutane da gurɓatattun jami'ai irinku ba sir' akwaisu akwaisu akwai dubinsu masu zuciyar lu'u lu'u da ɗanyen gwal, duk da shi baya da runduna ko ayari domin kawar da magauta azzalumai amma a ko ina bila adadin wannan kamaal ɗin dake tsaye gabanka har abda shi kaifi ɗayane kamar yadda zafin kansa be taɓa barin ya aikata ba daidai ba. Kashe kamaal kuma na nufin kun gayyatoma kanku da kanku goran gayyatar tonuwar asirinku da mutuwar kune wa AK!!!"
"Tabbas se a yanxun na fuskanta komai malam kamaal kace ashe linkin ba linkin ɗin maƙudan kudaɗen da muke amsa daga matai makin gwamna fiye da hakan shi kake amsa daga wurin babban crime irin Wannan tantirin AK ɗin" dsp ya faɗi yana wani shafar munafukin ƙasimbarsa da katon cikinsa dake rawa shima, sw kuma ya kece da wata kalan dariya yana furta "Ashe dai masu fatar akuyan yawa garemu kawai ka faɗo cikinmu kaima sunanka yay shura da ƙauri a baki ɗaya jahar kano harma da kewayenta kamaal"
Idanunsa ya rumtse da ƙarfin balai tareda da bugar teburin gaban dsp cikin ƙarajin murya ya furta.
"Har abada In banyi adalci wa ƙasata da kuma aikina a matsayina na jami'a ba, zuciyata bazata taɓa samun nutsuwa ba a yayin dana buɗi ido na kalla ana aikata wata ɓarna, kasa cin abinci nake haka kuma kasa barci nake ni banyi kama da jami'a ɗan rufa ido ba ni ɗin *KAREN TSAYE NE* wanda baya lankwasuwa ta daɗi se anci kashi domin duk wanda yay ko yunƙurin lankwasa shi ne to ku sani gefe dashi akwai gidan rinar dake dabaibaye dashi domin bashi kariya daga gurɓatattun ƙasa irinku!!!"
"Waye shi?" dsp ya tambaya.
"*THE MAN WHO CANNOT DIE🙄* *AK, EAGLE Mutumin da baya mutuwa, haka baya da tsoro domin shi kansa tsoro AK firgitashi yake"
Yana faɗin hakan ya fice a mugun fusace yana banko masa ƙofar office ɗin, wata mahaukaciyar dariya Dsp ya saki bayan yayi ya gama kana ya ɗauki wayarsa ya ɗanyi waya me tsayi kana ya ci gaba da dariyarsa yana barin office ɗin shima.
_A wannan daren komai ya faru rubutacciyar ƙaddarar da aka sanya alƙalamin da baya ƙarya aka zana wa'aɗin da aka ɗibarma wannan ruhin ya cika sedai akwai sanadi!!! Ehhhhh tabbas akwai sanadin hakan mujeeeee_
*A DAREN RANAR*
Suna kwance da misalin ƙarfe biyun dare taji ya farka a firkice wanda itama hakan ya sanyata farkawan a tsorace don dama duk a tsoracen take. Cikin muryan bacci da kuma tsoro ta ce "mra aiy lafiyanka kuwa?" ta tambaya. "Mra aiy na jiwo ƙaran buɗe get ne"
"Get kuma da daren nan kodai kunnen kane, duk ina baba me gadin yake" tayi maganar a sukurkuce don duk ma ta rasa gane kanta. Jikinta kawai rawa yake mata tace "Dan Allah karka fita kasan da me suka zone? kawai ka ƙira jami'anku suzo amma kai karka fita yaya kamaal kawai mu buɗe ƙofar baya mu gudu"
"Mrs aiy ina son ki sanya wannan yaƙinin a ranki cewar har gaban abada matsoraci baya taɓa zama gwani, don haka zan fita duk abinda zakiji karki yarda ki fito ko dan wannan ya rayu" Ya faɗi yana ɗora hannunsa akan cikinta daya ɗora hannunsa akan cikin daidai da motsin da cikin yayi. riƙeshi tai ta maƙalƙaleshi tana kuka sosae "Don Allah karka fita yaya tsoro nake ji "
"An haifeni ne badon naji tsoron mutuwa ba MARRIYERHTOU!" An haifenine domin kawi ƙarshen baragurbin cikin al'umma ki sani kowanne zaki mafaraucine a dawa yayinda aka shigo gonarsa, inason ko wanne irin tsoron dake ranki ki kawar dashi domin ni *KAMAAL RANO* ba matsoraci bane samm banma haɗa hanya da tsoro ba bare nasan ya kalansa ko kamanninsa suke, har abada inason ki kasance jarumar mace ko bayan babu raina Mrs aiy!!!" Yana faɗim hakan ya rungumota jikinsa da ƙarfi. ijiyar zuciya dukkaninsu suka sauƙe zuciyoyinsu na bugawa,A hankali kuma ya sake ta yana sakin wani murmushin da tunda take dashi bata taɓa ganin yayi irinsa wanda yay mai kyau kamar na yau ɗin ba. Sake faɗawa jikinsa tayi hannuwa na rawa ta sake rungume shi ƙam.
Bakinsu ta haɗe guri guda inda take jin numfashinta nayin sama sama, da sauri ya janyeta a jikinsa ya na fita.
Numfashi me ƙarfi ta saki loƙacin daya fice a bedroom ɗin.
A hankali ya fito ya soma tafiya cikin sanɗa, ga mamakinsa duk seya tarar an kashe duka bubls ɗin gidan har zuwa lungu nan dake bakin get, can ya hangin me gadinsa kwance cikin jini ga kuma karensa dake a daddaure bakinsa rufe da seltif.Motsi yaji ata gefenshi da babu hasken bubls a wajen,ahankali ya maida dubansa yana ƙurawa gurin ido sosae. Inuwar mutum ya gani tsaye a wurin da sauri ya waiga ɗayan gefensa seya kuma hango ɗaya inuwar mutum ɗin.da baya da baya yay hanzarin komawa ciki da sauri ya shiga bedroom ɗinsa, hannuwansa ya sanya yana janwo wata drower ya ɗauko bindiga a ciki ya maida drower'n ya ɗago yana gyaran riƙon bindugunsa.
Jikintane ya shiga wani kalan rawa loƙacin da kunnuwansu suka fara jiyo musu ƙararn harbin bindigu.
"Koda wasa kida ki sake ki fito koda wasa bazan taɓa barinsu su shigo ciki ba, kinga wannan ƙofar bulletfroof ce harsashi baya fasa ta ki rufe ko ina koda ace sunyi yunƙurin harbi bazai fasu ba ko waye yace ki buɗemar karki yarda ki buɗe idan harba ni bane!" daga haka ya janyeta a jikinsa yana barin bedroom ɗin. Ita kuwa ɗurkushewa tayi a wurin tana sakin kuka sosae.
Riƙon bindigarsa ya gyara nan fa ya shiga sakin harbi takan me uwa dawabi haka ya shiga harbin nan, nan suka shiga musayar wuta shida ɓoyayyun mutanen da duka jikinsu yake rufe. Ganin yadda Kamaal ke zubar musu da yarane ya fusatar da ɓarayin nan, nan fa cikin tafasar zuciya suka shiga kaima daga inda yake laɓe harbi, shima a fusacen ya fito daidai da wani daga cikin mutanen ya sami nasarar harbinsa a gefin ƙirjinsa. Cikin haushi da ƙunar zuciya yay gaba da gaba dasu yana fuskantarsu. Chakkk ya tsaya ganin fuskar miles babban yaron AK wanda daga arms se shi a matsayi. Kafin ya dawo daga cikin duniyar mamakin ya sake jin sauƙar wani harbin a cikinsa. Se kuma aka shiga harbin nasa tau tatau tau tau. Har wajen sau biyar zuwa shida. Ƙarar azaba da raɗin ratsa harsashin jikinsa kamaal ya saki wanda karab a cikin kunnuwan Marria, ɗan cikin tane yay wani kalan motsawa yana mata tambulan a ciki tamkar wacce aka zabura kuma ta mike tana ɗaukar wani shiraminsa ta lulluɓe jikinta. Ka tsaye inda taga ya ɗauka bindigar nan ta nufa guda biyu ta ɗauka dama da hagu tana bude kofan, babu tsoro ko jimamin mutuwa ta ratsa ta cikin palukan gidan tana yin woje, duk da wanda ta haɗu harbin kansa kawai take idanu rufe. Don ita kanta ba zatace ga sadda ta iya harbin ko take harbin ba, tasan dai kawai zuciyanta tafar fasa yake yana mata kuna sosae. Haka cikin wani kalan salo tamkar wata soldier take harbin duk wanda taci karo dashi, kamar daga sama kamaal dake kwance cikin jini ya rumtse idanunsa cikin azaba yana jijjiga kansa "A ahhhh! a a No AIY'N! No mrs aiy kar kiyiiiiii! kada kiyi ki koma" ya faɗi da ƙarfi sosae ina ko jinsa bata yi harbi kawai take kuma idan tay harbin bata taɓa gota seti.
Guntun mutane ukun da suka saurane suka diba a guje suna barin gidan a350 na karshen ta kaima harbi a kasa nan take kuwa ya zube yana kururuwa, bindigun hannunta ta zubar wani kalan jiri na dibanta ta isa gabansa ta zube. Wani irin kuka ta saki ganinsa cikin jini kwance jikinsa ta faɗa tana sake fashewa da wani sabon kuka.
"Sei da nace kar kayi, kada ka fita Amma kaki saurarana mr aiy'n kalla ka gani sun cutatarmin dakai, jikinka yana ta zubar da jini aiy'n bara na kira dactor"
Hannuwanta taji ya damƙa tare da girgiza kansa tare da jan numfashi da ƙyar yana faɗin. "No ba buƙatar hakan aiyn sun riga da sun harben sun gama illatamin rayuwa, nasan bazan rayu ba amma kiyi haƙuri zan tafi ba tare dana ga gudan jinana a duniyar nan ba, zan mutu ne da sonku da ƙaunarku duka ku biyun!"
ya faɗi yana mata nuni da phone nashi, da sauri ta miƙa may bayan ta cire daga security'n daya sev da sunanta.
Cikin wannan ƙarfin halin ya haɗa musu conect shida *AK* da kuma *ZAYD SURAJ* wata magana suka tattauna sosae. Daga haka yana rungume a jikinta ya furta.
"Karki bari little kamaal yay kukan maraici ki tsaya masa tamkar yadda uba yake tsayema ƴaƴansa duk da nasan ban tafi nabar baya lusaraba baya jaruma na bariiiii" se kuma ya saki zancen yana ɗaukar kalmar shahada. Zayd suraj ne cikin ƙarajin da yafi kama dana tashin hankali ya shiga furta. "A ahhh!? A aaa kamaal kada ka tafi karkai mana haka Insha Allah ma zaka ga gudan jininka zaka rayu dashi ba zaka barmu ba KAMAAL YOUSUF RANO" Ina sedai har me afkuwa ta riga da ta afku domin kuwa maganar nan ta *kullu nafsin za'ikatul maut* ta tabbata akan wannan bawa nashi wato kamaal Rano.
Wani kalan ihu marria ta saki tana faɗawa jikinsa itama nata numfashin na tafiya yana barin jikinta.....
Dip dip ƙaran datse kiran da AK yay daga can.
Zayd kuwa da suke gari ɗaya a wani kalan mugun guje ya fice duk da yadda dogarawan gidan sarautar suka so hana shi fita, amma kallo ɗaya ya wurga musu suka bashi hanya. Wani kalan gudu na tashin hankali yake tamkar wanda ya samu cutar taɓin hankali don har tashi sama yake, ta inda Allah ma ya temake shi shine cewar dare ne ba rana ba.
*BY AMMEYLAYLERH*
KUYI HAƘURI!!!
_Duka fages ɗin nan uku abubuwane marasa daɗi ke faruwa_
_Dama haka rayuwa take mu sani wani loƙaci kuka, wani lokaci kuma ayi dariya_
_Ba komai akwai dariyan gaba kuma don Allah mutuwan Kamaal karya zama kamar na *ALIYU SHUREIM* ɗin *QUEEN*_
_kudai kawai ku taya marria da