Showing 39001 words to 42000 words out of 78068 words

Chapter 14 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1297

K★
Tsaye yake ya ɗan rankwafa daga saman terrace ɗin yana kallon duk wani shige da fice na manyan motoci dama ƙananunsu. Sanye yake cikin wasu guntayen ƙananun kaya kansa babu komai sema gashin kansa daya baje wata har tana zubowa da saman goshinsa. Kana ganinsa ba indiye sakk hannunsa riƙe yake da wani glass cup wanda pineapple juice ke ciki yana sipping a hankali. Idanunsa a lumshe yake kunnensa manne da bluthoot yana bada jar danja da ƙoriya. Wanda hakan kai tsaye ke nuni da cewar waya ce yake ko kuma yanajin music ne.
Ware manyan idanuwansa yayi a bazata maganar da aka faɗa may na sake bugun ƙirjinsa amma sammm hakan be nuna ahalaman hakan a tattare dashi ba.

_KUWAIT_


*BY AMMEY LAYLERH*
(Mirrah)






*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

21&22

_MEERAH_

A loƙacin dana buɗi ido na gama tabbatar da AK shine mijin da aka ɗauramin aure dashi na ci alwashin sai nayi sanadiyyar rugujewar rayuwarsa gaba ɗaya. Saidai ashe lamarin ba haka yake ba mutumin da akema kallon ɗan ta'adda ya rikiɗene wa al'umma duk da kasancewar shiɗin ba haifaffen nigeria ba.
Mutumin da zuciyarsa take a tsarkake kallum kwanan duniya yana yin sane cike da tarin yaga ko wacce al'umma bata cikin matsala. Mutum na farko kenan dana fara ganin irinsa me wankakkiyar zuciyar da babu algus a cikinta, Mutum ne wanda kai tsaye zamu iya ƙiransa da me zuciyar zinare koma nace lu'u lu'u ko zarce haka.
Tun daga loƙacin dana gama fuskantan komai shi kansa na gama fahimtar rayuwarsa abar tambayace don cike take da tarin sarƙaƙiya wanda badan tsayayyar zuciyar da yake da ita ba wanda da wannan tsayayyiyar zuciyar ne yama ƴan uwansa katanga ga dukkan tarin ƙalubalen dake fuskan tosu. Wanda da ace zuciyar ba a dake take ba da anjima da kaita ƙass anyi dumumu da ita kai tsaye. A ranar dana gama tabbatarma kaine cewar ehhhhhhh lallae shiɗin abin a tausaya masa ne a wata rana a wani dare dare mafi tsananin duhu wanda magauta sukayi amfani da loƙacin don son cikon muradinsu amma dake babu haƙƙin kowa a kansa sai Allah ya sauya musu mugun nufinsu ta hanyar katangar da Allah ya gina tsakaninsa da zina.

_A Ranar A kuma loƙacin_
★♡♡♡
A hankali Iskan ke kaɗawa gwanin birgewa yanayin weather'n garin gwanin ban sha'awa me cike da dadɗan yanayi. ga yanayin garin da hadari yama samaniya ado ta hanyar mata ƙawanya a hankali a hankali iskan ke kaɗawa me tafe da ƙamshin ƙasa amma hakan bai hana kaji daɗin iskan dake kaɗawan ba, A hankali Ak ke tattako staircase yana saukowa jikin sa sanye da wando 3 Quiter blue da Sweaetshirt mai laushi mara nauyi fara ƙal kamar Auduga. Se ɗaukar ido take tamkar yanzu ne ya fito da ita daga cikin kwalin ta saboda haske Se ya ɗaura danim jacket blue color mai ɗan girma a saman farar rigan, hannun sa na ɗaure da tsadaddar gold watch mai bala'in kyau da tsada sai kyalli yake yana ɗaukan ido, ya haɗe kyakyawan dogon gashin san nan nashi daya sha gyara ya ɗaure a can ƙarshen ƙeyarsa sai wani daya zubo kaɗan ta gaban goshin sa kamar mace, fuskar nan a ɗaure tam kai da ganin sa kaga Lion ɗin ne da gaske don yaci a ƙirasa da gargalion ɗin.
Tafiya yake cikin majestical takunsa na isa da kuma izza kai tsaye dining room nashi ya nufa, jigba jibgan Bodyguard nashi zagaye da ploor'n har zuwa dining area ɗin. sanye suke cikin suit baki da glass baki a face nasu fuskar nan tasu kamar hadari a ɗaure tamau babu alaman imani ko ɗigo a ransu, sun jeru yali gefe da gefe sun sanya table ɗin a tsakiyar su sunyi ma wurin zobe.
Tun AK bai iso wajen ba suka fara sara masa ko kallon in da suke bai yi ba ya nufi saman kujerar table ɗin, a sukwane ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya ja masa kujerar baya. Zaune yakai yana crosing ƙafarsa ɗaya akan ɗaya haɗi da ɗakilar woyansa. Da hannu yama ɗaya daga cikinsu nuni da Wata luxury warmer's me ɗauke da Hot Grilled chicken, nan take ya fara serving na shi tare da tura may gabansa. A nutse yayi cheak upp na cikinsa yana miƙewa tsaye bayan wanke hannunsa dan ba ɗabi'ar sabace cin ko wanne irin abinci da spoon. A nutse ya bar wurin drectly yana me nufar garden nashi ta kebantacciyar hanyarsa.


A nutse take durfafar garden ɗin yanayin wajen na sake burgeta sosae musamman yadda yake samun kyakkyawar kulawa. Sanya ƙafafunta kenan sautin muryarsa shine abu na farko daya fara ziyartar kunnenta,kafin daga bisani idanunta su sauƙa a kansa,dai dai loƙacin da shima ɗan motsin da yaji ya sakashi ɗaga kai idanunsu suka sarƙe wari ɗaya,yana daga tsaye dan shigowarsa kenan shima hannunsa guda ɗaya cikin aljihunsa ɗayan kuma mug ne na tea party dabai gama sha yana sipping nashi a hankali....
Wani kallo ya wurga mata ganin yadda ta kafeshi da mayun idanunta. Bakinta ta murguɗa may tare dajan ƙaramin tsaki tana ɗauke kanta a kallonsa. Chakkk ya tsaya da sipping tea ɗin dayay niyar yi.Lumshe idanunsa a nutse yayi yana jin wani irin bacin rai na taso may,idan har dai dai kunnuwansa suka jiye masa kamar sautin tsaki ya jiyo wanda yaga alamun fitarsa daga ɗan ƙaramin bakinta data turoshi gaba loƙacin da take hada sautukan tsakin. Ba tare da tayi aune ko tunanin hakan ba kawai sai ganinsa tayi gabanta yana binta da wani irin kallon data kasa gane masa. Haka kawai taji gabanta yayi mummunar faɗuwa kowanne sashe na jikinta yayi sanyi saboda yadda ya zuba mata mayatattun idanunsa,yana jifanta da wannan kallon da har ayau bata san ma'anarsa ba.
Numfashinta ne ya soma ƙoƙarin sezing ganin irin kallon da yake binta dashi ga kuma daf da daf ɗin da sukay ya mugun takura mata. Sake waiwayowa tayi still har yanzu ita yake kalla kallon dake sake tunatar mata farkon ganinta dashi.
Sake janye idanun nata tayi ta maida dubanta wani wajen daban, gaba ɗaya kallon da yake mata ya wuce ƙa'idar da jarumtarta zata iya ɗauka uwa uba kuma shirin rikicewa takeyi gaba ɗaya,saboda yadda tsananin kwarjininsa yake sake cikata.
Da wani irin hanzari ta nufi hanyar barin garden ɗin da zummar fita,amma kuma kafin ta isa har ya isa ya tare hanyar ya kuma sake tsareta da shegun idanunsan nan.
★ "Wa kika ma tsaki?" Ya jefe mata tambayar kansa tsaye cikin izza da ƙasaitarsa "Ta yadda makaran kunnuwanka suka jiye maka yanzun ma se su baka amsarka!" kai tsaye ta jefa masa amsar tambayar bayan ta ɗauke kallonta daga gareshi.
"Ko?" Ya faɗi wani shegen murmushin gefen baki na subce masa, Na irin mamakin yadda take iya jefanshi da duk wata maganar da tazo bakinta. Amma kuma ba abin mamaki bane idan yay duba da yadda ta mu'amulanceshi a gidan jaridarsu. Da yanda duk wata haɗuwa tasu basa taba wanyewa lafiya seta jefeshi da duk maganar da yazo bakinta .Fuskanta yake duba yanason gano daga inda ta samo wannan qwarin gwiwar Kyatt take iya tsaiwa a gabansa ta gwada masa rashin kunya,yayi imanin har zuwa yanzun bata gama sanin ko waye shi. Amma a yadda ya lura akwai ƙuruciya sosai tattare da ita Idan yace zai punishment nata ɗan ƙaramin abu kawai zaiyi da zai bata zazzafan warning,ta yadda ba zata sake marmarin maida masa martanin ko wacce iriyar magana bace nan gaba.

Ganin abinda yake shirin aikata mata ne ya sanya ta fakar idonsa ta tunkuɗi mug dake hannunsa a taje tea ɗin ya bare masa a jiki. Ita kuma ta ranta ana kare tana barin duka garden ɗin. Dake yanzu kamar ya zame min izini saina shiga sasaan Moh da kuma Umaymah haka kai tsaye na biya ta duka passess nasu.
Tsaye naga Yasmine wacce nake ma fuskan kallon kamar na taba gani kodai na taba saninta. Kuma tunda tazo gidan so biyu muka haɗu sammm yarinyar bata da ɗabi'u masu kyau, kodan dama haka gidan yake ohon musu dai can ta matse musu. "Ki tabbar a daren yau yasha wannan lemon! Don shine kaɗai hope namu akansa na tabbata duk inda yakai ga kamewarsa da wani jiji dakai nasa wannan karon dole yazo hannu. Ni kuma daga loƙacin da kika tabbar min da yasha daga loƙacin nawa aikin ze fara bayan lafawan komai. Kana kin tabbata kinsha duk abubuwan nan dana baki kana bana da buƙatar koda Dada'nki ne ya san da wannan shirin namu Akan Wannan shegen yaro"
Daga nan idona ya fara ganin bibbiyu ina tunanin su kuma waɗan nan mutanen har abada a haka zasu ƙare kenan a ya won tuggu da cutatar da mutane. (Ko wanne me tsautsayin ne wannan!) Na Faɗi a raina " Koma waye ubangiji karya baku nasara akansa" na faɗi a bayyane ina barin bangaren zafi biyu na haɗe min a loƙaci guda. Lallai wannan gida se adda'a kowa babu alkairi a zuciyarsa. Maganganun waccan ranar ne suka shiga dawo min turyan turyan. Rasss naji gabana yayi wani irin mummunan bugu inajin zuciyata na dunƙulemin wuri guda. "AK" na ambata a bayyane don ranar ma akan shi ne naji duka maganganunsu. "Tabbas shine" na sake faɗi inajin yanayin bugun numfashina na sauyawa daga matakin da yake zuwa wani matakin na daban. "Ya rabb karka baya waɗan nan mutane cutatar da wannan bawan naka!"
Kawai se tsintar bakina nayi yana me wannan adda'ar. Gaba ɗaya yanzun kam shi kansa tausayi yake bani don yaci a taisaya masan amma shi girman kai da zafin kansa bazai taba bari ya fuskanci hakan ba. Haka na koma sashin oum suƙuƙu har yanayina yana kasa boyuwa na halinda da nake a ciki. Wanda hakan ya kasa boyuwa har oum take tambayana ko lafiya, amsa na bata da cewar lfy lou nake kawai dai banjin daɗin jikinane. Kwanciya nayi babu abinda ke tada ni in banda sallar da nake tashi yi. Haka har akayi sallan isha'i wanka nayi na zira riga da wanda na bacci masu ɗan kauri wandon ba dogo bane caan haka ba rigar. Babu daɗewa da kwanciyana oum ta shigo hannunta riƙe da Tea plask, "Doter te maka kibi min Garga da wannan duk yau ban jishi ba tun fitansa na safe" ta faɗi tana bani tea plask ɗin. gabanane naji yay mummunan bugu sanin cewar mutum ɗayane take ƙiransa da garga ɗin kuwa wato *AK* jiki babu kwari na miƙe tare da ɗora after dress akan kayan baccin dake jikina. Seda naje har bakin ƙofa jesrah ta tsayar dani ban tashi aune ba sai ji nayi tana feshe ko ina na jikima da turare.
Bige hannun nayi ina faɗin "Banson iskanci fa jesrah miye kikeyi haka?" na tambayeta ina janye kwace jikina. "Gaskiyace wa yace miki ana zuwa wurin miji haka sikaukau babu ko ɗan kamshi haka? Kefa nama fahimta nine da kaine zan zaunar dake na koya miki darussan dake cikin aure, irin yadda ake mallake zuciyar mijin nan yaji duk duniya babu macen da takai mace a gareshi inba ke ɗin nan ba. Jeki dawo wllh daga yau zamu fara sabon darasi don da gasken gaske so nake ki mallaki Akiey ta yadda wannan ɗan banzan zafin kan nashi ze ragu"
"Ban haya na wuce jesrah tunda shirmene a gabanki ke" na faɗi ina ƙoƙarin rabata na wuce. "Da gaske so nake ki zama cikakkiyar matarsa Meerah"
Banko sake waiwayota ba duk kuwa da cewar inajin maganganun shirmenta.
Duk inda na keta na wuce se kaga hadimai na rusunar da kawunansu ƙasa wanda hakan samm ni baya min daɗi baki ɗaya. Sedai babu yadda na iya tunda suka san matsayina a gidan kuwa, duk taku ɗaya da zanyi ina jinsa ne tare da bugun zuciyata. Rass gabana ya bada sautin bugu loƙacin da na kusa cin karo dashi, baya nayi zan faɗi yay saurin taroni ina komawa saman jikinsa. Zafi rau ɗin da naji a jikinsa ne ya sanyi saurin janye jikina a nashi tea ɗin na ajje masa a wurin ina faɗin "Ganan inji oum" na juya da nufin komawa ko taku ɗaya banyiba naji sauƙar hannuwansa ƙan ƙuguna abinda bai taba faruwa dani ba yazo min kuma a bazata.

"Don Allah ka sake ni miye hakan ni banso!" na faɗi a rarrabe zuciyata na bugawa sosae.
Bai amsa min ba saima wani lumshe idanunsa da yay yana matse fuska alamar da abinda ke damunsa. Gabana ne ya faɗi tunowa danai da wancan maganganun nasu umaymah zance koma na Moh jiddo. A take kaina ya shiga juyawa inajin wannan karon bugun da zuciyata kemin ya zarta ka'idarsa, don kai tsaye maganganun mutane biyun nan ne sukai tasiri a cikin zuciya. Ita moh jiddoh kai tsaye paisoning nashi tasa ayi ɗaya daga cikin hadimansu mash kula da bangaren kitchen, ita kuma umaymah table desire zasu sa may don ya kusanci ƴarta don cika muradinsu. (Wan ne ne daga ciki kenan?) na faɗi a cikin zuciyata. Haka kuma cikin suɓutar baki na furta "Baka da lafiya ne?"
   Maimakon ya amsamin tambayana sai ma ya wani lumshe idanunsa da matso da fuskarsa kan tawa sosai. Idanuna na runtse da sauri ina ƙanƙame jikina tare da kauda fuskar tawa gefe. Sai kawai naji saukar numfashinsa akan wuyana zuwa ƙasan wuyan nawa da cikin kunnen yana shinshinata can kuma kamar wanda aka tsiƙara se jinay ya ɗaukeni cilak yana fita dani gaba ɗaya daga ɓangarenma baki ɗaya. Ta wata sihirtacciyar hanya yabi wanda take kamar irin ginin nan na ƙasa. Abin mamaki se gamu a wani plat na daban kuma wai duka anan cikin ɓangaren nashi muke nefa.
Tafiya ya shiga yi dani jikinsa na sake ɗaukan zafi wanda na take da tabbacin badan taurin zuciya irin tashi ba da seadai ace ko yana kwance a gadon asibitne ko kuwa dai shima memar irin hakan hake da buƙata a dai irin wannan halin.
A ɗaya daga cikin manyan bedroom na plat ɗin ya shige damu akan wata farar sofa ya zaunar dani yana fesar da numfashi me zafi. Cikin ƙarfin hali yayi amfani da landline na room ɗin maganar second yayi yay ya janye wayar a kunnensa. Kamar ten minutes ya sake ɗaukana ya fita damu compound na plat ɗin nidai se aikin rarraba ido kawa nake don shine nawa. cikin wata lafiyayyar mota blue black ya sanyani shima ya zaga yana komawa mazaunin driver. Babu kowa a harabar wurin da dukkan alamu kuma babu me rayuwa a wurin dama. Revarsw na car ɗin yayi tare dajanta da wani kalan mugun gudu na tsiya,wanda hakan ya firgitani ido na rumtse da ƙarfi har bansan sanda na ɗamki ɗamtsen hannunsa. wanda ni kai tsaye    bansan hakan abinda ya haddasa masa. Wani kalan jan burki yayi harda saida kaina ya daku da sterring na motan. Shi kuma wani kalan rumtse idonsa yayi don ji yayi a loƙacin saura kaɗan numgashinsa ya rabu da gangar jikinsa. Sake dakar haban motar yayi yana sake bata wuta ko kallon gabansa baiyi, kai tsaye a hadadden gidansa dake _MASHATLE SHUWAIK_ ya taka wani kalan wawan birki. Take motan yayi da balain ƙarfin tsiya cikin kiftar ido da buɗewa na'ura ta tantanceshi.
A compound na get ɗin ƙarshe ya taka birki. Ƙafofina na zubo ƙasa da niyar fitowa se jinai anyi sama dani tare da tafiya dani a nutse cikin yanayinsa na kamewa. Ta wata ƙofar glass yabi damu sai gamu a wani ƙayataccen bedroom. Jikinsa kuma    zuwa loƙacin ya sake ɗaukar ɗumi sosae.
   A zabure na mike ganin yadda loƙaci guda yanayinsa ya sanja baki ɗaya. Hannuna ya kama tareda janyoni na faɗa saman kansa daman already ya rigada ya zauna saman sofa. Kan ƙafafunsa na faɗa ya haɗeni da zazzan jikinsa yana rungumeni gaba ɗaya na.A hankali ya ciro da shuɗaɗɗun idanuwansa kaina yana me bina da Wani kalan kallo me nakasta gangar jiki. Faɗuwa gabana yayi na ɗago na sake kallonsa a karo na biyu ganin irin kallan da yake min yasha banban da waɗan can na baya. kafin na sake wani yunƙurin tuni ya sake matseni a cikinsa sosai akan gafafun nasa mukai kyakyawan haɗewa muna fuskantan juna kirjinmu a haɗe.
Yadda yake jin bugawan zuciyata ne yasake gigita tinaninsa ya zagayota da hannuwansa Yana saka Kansa cikin wuyana yana Jan numfashi me ƙarfin gaske, Wanda ya sake bugarmin da zuciya da ƙarfi hakama numfashinsa me dumi yake sauƙa akan fatan wuyana tini suka tayar da tsigan jikina.
"Wayyo ni Allah na shiga uku! dan Allah Yaya *AK KUWAIT* ka rufa min asiri ka ƙyaleni, wai minene haka kake yimin kamar wani maye" Na faɗa cikin yunƙurin miƙewa da ɗan sauran ƙarfin daya rage min. Gocewa yay daga kyakykyawar rungumar da yay min ya koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login