Showing 36001 words to 39000 words out of 78068 words

Chapter 13 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1288

sanda bakinsa ya buɗe har ya furta sunan.
*☆MIFRAH!♡*
Wanda hakan yay daidai da faɗawanta ruwan tumjim. Cikin abinda bai wuce ƙiftar ido ba shima sai gashi ya faɗa cikin ruwan yana danna iyo a cikin ruwan domin sai yanzun ya tuno da _ORCAS FISH_ ɗin dake cikin ruwan wanda kai tsaye zasu iya cutar da ita. Cikin wani irin mugun salo ya sake yin ƙasa luuuuu a can ƙasan ruwan loƙacin daya hangeta yayi daidai da sanda wani ƙaton Orcas yayo kanta.
Wani kalan zillo yayi tare da bugar kan fikin da ƙafarsa ai kuwa kifin yayo kansa gadan gadan. Cikin rashin tsoro da sabawa da wasan da yayi dasu dama can tun husil ya jefa may ƙafarsa kifin kamar wani mutum ya buɗe manyan idonsa like na mage akan AK. Ƙafar ya sake shura masa yana yin ƙasa daidai ta ƙarasa ƙarshen ruwan jikinta na sakewa baki ɗaya.
Rungumota yayi a jikinsa ya fara tafiya da ita a cikin ruwan. Yanajin jikinta babu alamun numfashi akan wata chiepgago catasiam chiar ya shimfiɗeta tare da zuba mata idanunsa da ruwa suka shiga ciki. Yana gaza tunanin ma wanda taimako ya kamata ya fara bata kawar da kansa yayi tare da ɗora hannunsa saman ƙirjinta setin wuyarta ya fara dannawa 6ull saiga ruwa ta hanci ta baki yana bulbulowa ci gaba yayi da danna kirjinta nata idonsa ba'a kanta ba gashin kanta a tarwatse band tayi nata wuri tare da ribboms ya baje har saman ƙirjin nata.
Fara fat haka fatar ta yayi a take saida ruwan ya gama fita tsaff amma kuma bata kawo numfashi ba alamar somewa tayi kenan ta tsorata da ya hala. Yi yay kamar ya ƙyaleta amma kuma wata zuciyarta na faɗa masa ko ba komai ai tana da haƙƙi akansa. Idanunsa yaja ya lumshe tare da ɗora bakinsa saman lips nata ya fara hura mata numfashinsa me ɗumi.
Wani gwairon numfashi tayi tare da soma tari saurin ruwan na ƙarasa fitowa. A zabure ta ware dukan girman idanunta jikinta na kakkarwar tunowa da kifin da yayo kanta. Buɗe baki tayi da niyar Kwalla ƙirar sunan Anne'nta amma sai taji wani al'amari na daban ƙarasa sauke ganinta a kansa tayi lips nashi cikin nata idanunsa a lumshe eyelashesh nashi na ɗigar ruwa da gashin kansa shima, Ash ɗin rigar dake jikinsa armsless na ɗigar ruwan itama.
Jin alamun ana kallonshi da motsin farkawar da tayi ne ya bashi damar buɗe idonsa da har yanzu ruwan kmda sukar shigar masa na ciki. kafe cikin nata idanunta yayi da nasa cat eyes ɗin masu matuƙar girma da yalwar gashin da haryanzu ke ɗigar ruwa, kif-kif kawai ta shiga yi da idanunta  gefe guda kuma sai faman kokawa take da numfashina dake seizing.
         A matuƙar wahalce ta samu ta kwace lips nata daga bakinsa tana sakin doguwar ijiyar zuciya tare da buɗe bakinta da niyar masa tsiwa da karta masa rashin m akan kada ya sake shiga harkanta.
Chakkk maganar da take niyar yi ɗin ya maƙale mata a loƙacin daya jefa idanunsa cikin nata, maƙut ta haɗiye maganar nata dan duk yanda ta ƙudiri niyar masa tsiwa da karta masa rashin m kasawa tayi.Don shi Mutum ne mai masifar kwar jini da cika wuri ALLAH ya azurtashi da wani irin baiwar da duk tsagerancinka baka isa yi may ba a loƙacin da yasa idonsa a cikin naka koda ace ya fisa a shekaru kuwa. Wani irin kwarjini gareshi na ban mamaki don tin muna nigeria saina kuɗiri niyar may rashin mutumci amma samm bana iyawa sai a bayan idonsa ko ya ɗauke ganinsa akallona. Ƙoƙarin janye idona nake a kansa amma ya hana hakan ta hanyar sarke nawa idon a cikin nashi. Wani kalan smile ya saki tare da janye jikinsa daga gareni.Yanda yay murmushin ne yasa har ban san yadda akai na kafesa da mayataccen kallo ba.  Idanunsa ya ɗan waro min waje da ɗagesu alamar kallon fa?. Cikin sauri na kauda fuskata gaba ɗaya ina murguda masa baki tare da faɗin "Miye abin kallon ma a wurin crim irinka?" ƙasa ƙasa yadda nasan bazai jiba.
Amma ɗan bawar Allah'n nan tamkar kunnen maciji ashe saida yajini saijin sauƙar deep voice nashi nayi daf da fuskana yana me faɗin.
"Kuma a haka dai kika gani har kika mato kika ce Inba ɗan ƙasar kuwait ba sai bakim rijiya" wani kalan zaro idanuwa gaba nai tare da furta. "Wllh ƙarya kakemin uhumm jannnn toma nayi me dakai?"
"Abinda ake yi mana"
Saurin kallonshi nai gabana na mugun bugawa tare da faɗin. "MII YE A AH KEYI ƊIN?"
Na faɗi cikin rarrabewar murya saida ya kwashi wasu second kamar kuma daga sama naji sauƙar muryansa yana furta "Nima ban sani ba"
(Ɗan ikka)
Na raya a raina kallon yadda fitar numfashina da kuma sauƙarsa yayi saiji nayi baki ɗaya ya dawo jikina tare da feɗin.
"Waye ɗan ikkan"
"Innalillah ni yaushe ma kaga nayi magana?"
Na faɗi cikin marairaice murya kamar wata ta gari. "Nan ne ya faɗi kuma na tabbata baya ƙarya" Ya faɗi yana me ɗora hannunsa akan dede setin maƙogwarona.
"Wllh ni banason sherri kuma saina haɗaka da Oum!"
fuskana yaɗan lakace tare da furta "Really? Kuma me zakice mata? ce mata zakiy mijinkine yay........
Ai ban ma san sanda na rufe masa baki da hannu naba ina wani zazzara ido irin an kama barowon nan yayima sarki sata.
Kamar kuma an zabure na tattaro duka ƙarfin daya min saura na turashi gefe ina kwasa a guje ba tare dana bi kota kan sauran kayayyakina ba. Da wani kallon kallo yabi bayanta yana me sauƙe ijiyar zuciya. Ɗagowar da zaiyi yaga gittin mutum halamar kar a ankare da koma waye kenan. Zuciyarsa yaji tana tafasa namomin jikinsa na ɗaukar tsuma kenan duk yadda yake taka tsentsen da rayuwar da kuma sirrinsa se ankai ga wani ya gani kenan. Lallai anason kaishi bango ne kawai domin suna daf da ƙarasa balle ramin kurane da kansu. Wanda daga karshe kuma farautar da zaiyi bame kyau bace.
Jikinsa na ɗigar ruwa yabar wurin yana bi ta ƙofar daya shigo ƙebantacciya.
Kai tsaye jerin floor'n dake zagaye a Downstairs ya faɗa cikin ɗaya be ɗau wani loƙaci me tsayi ba ya fito babu riga a jikinsa sai wani farin trouser dake jikinsa guntu.
      Upstairs nashi ya koma first floor inda nan ne bedroom nashi yake kai tsaye bathroom ya wuce yana me sakarma kansa shower, Jikinsa sanye da bathrobe ya fito se wani mini towel ɗin da yake amfani dashi wurin tsane gashin kansa. Cikin zafi zafin da zuciyarsa ke masa ya shirya kansa cikin wasu halp armanian caftan, second floor ya nufa sumar nan ta baje ta rufe duka kusan fuskan shi. Cikin master bedroom nashi ya faɗa inda nan ne ɗakin nu'urorinsa a nan yake gudanar da duk wasu ayyukansa. Kai da ganin ɗakin ka iya rantsewa dan ijiyar na'urori kawai aka yishi. Don ita kanta ƙofar babu wani mahaluƙin daya isa shigarta idan har ba me ita ba duk kuwa da yadda kakai da iya bin kwakwaf ɗinka.
     Ɗakin ƙaton gaske ne na ban mamaki yana shiga ƙofar ta rubuta _Welcome to A...MALEEK linor_
       Da silver and golden metals masu sheƙi wanda ke ɗauke da salon burgewa akan wata casion sofa ya zaune nan ya shiga jona na'urorin yana kunna kowacce. Na duka sassan garden ɗin don so yake yaga tun yaushe aka fara masa irin haka. Abin mamaki kuma footage camera ɗin bata nuna may komai ba se shigan Moh da kuma yadda ta fita kamar a tsorace daya gani. Sai kuma Shigan Meerah tun daga ranar farko har zuwa yau da yanda take zuba shirmenta. Be murmusaba be kuma ɗaure fuskan ba don shi ba mutum bane da ake iya fuskan yanayinsa kai tsaye.

*****
Meerah ____

A nutse take cira ƙafafunta amma kuma daga can ƙasan zuciyanta tsoro ne fall na yadda al'amura suka faru cikin abinda basu wuce seconds ba. Tsabar kanta ya rikice taka mai mai seta rasa hanyar da zata komawa bangaren oum ɗin. Don gini ne masu yawa kuma kusan iri ɗaya wanda dole idan baka saba rayuwa a cikinsa ba kanka ya ringa rikicewa wajen banbantasu.
Wani matsananci faɗuwar gaba ta tsinci kanta a ciki. A ranta tana rasa miye dalilin daya sa duk sanda zan haɗu da matar nake tsintar kaina da faɗuwar gaban. Saima na rasa ta yanda zan saisaita tunanina na gane ainihin abinda yake haifarmin da hakan. Maganganun da kunnuwana suka jiyomin daga gareta ne suka sanya ƙirjina wani irin dokawa wanda kai tsaye hakan ya dirar min da wani matsanancin ciwon kai tare da zazzabi me zafin gaske.
A take jikina ya shiga rawan sanyi dama kuma gani da jiƙaƙƙun kaya wanda dama nasan babu tantama sai hakan ya haifarmin da zazzabi ko mura nayi ta atishawa ba kakkautawa shi yasa sam bama ga maciji da ruwa, Da baya na soma ja idanuna nason rufewa daga kallon gabana amma ƙarfin hali da taurin zuciya ya sanya naki bama hakan dama ta hanyar hanasu kullewar, ga wata shegiyar jirin dake ɗibana amma haka nake takawa inaja cikin ƙarfin hali.
Daf da shiga ƙofar palon tayi baya luuuuu anan jirin ya sama galabar kayar da ita. da sauri Aafia ta fitowarta kenan daga sassan oum ta tarota tana ɗora hannunta saman hancinta taji koda sauran numfashi. Jin babu alamar numfashin ne ya sanyata Komawa passess na oum ɗin, babu daɗewa sai gata sun fito tare da oum da jesrah.
Tub fitowar oun bayin dake jere a layi Suke duka mata wasu na zubewa idan sun ganta saboda girmamawa saidai Sam hankalin ta bekai garesu ba saboda da tashin hankalin da take ciki akan meerah.
"Kama min ita Aafia mu kaita ciki" da "to" aafia ta amsa ta suna shigar da meerah can cikin bedroom na oum.
Zama tayi a gefen lallausan gadon ta Wanda yaji ado da tarin mayafai irin na sarauta ta cire alkyabbar dake jikinta. Wayanta ta ɗauka hankali tashe kai tsaye gargalion tayi calling.
"Gaga maza yanzu kazo duk abinda kake ka fatse shiiii Maerayamah ce babu lafiya!"
(Maerayamah) ya maimaita sunan acan ƙasar ranshi yana tuna waye ma me irin wannan sunan a gidan, ba tare daya ko tuna me sunan ba ya datse ƙiran yana fitowa daga cikin computer room ɗin daya ɗebi loƙuta masu tsayi a cikinsa yana charking out na duka ma abubuwan da yake da buƙatar ganinsu.

Cikin abinda gai gaza Five minutes ba sai gashi ya shigo har bedroom na oum ɗin. Akan wata chalkia sofa ya zaune me launin L yana me fuskantar gadon. "Da buƙatar ka fara rage mata kayan jikinta da dukkan alamu shine ya bata damuwan" yaji muryan oum na bashi umarnin hakan kai tsaye. Kallo ɗaya yama inda take kwance ya ɗauke kansa a kallonta. Tsammm ya miƙe tsaye be ko kalli inda oum take ba ya ɗaga ta cilak yana fita da ita baki ɗayanta tamkar wacce ya ɗauka jaririya. Lallai sai yau na sake tabbar da cewar mutumin nan ba ƙaramin ma'abocin gym bane duk ilahirin jikinsa a mummurɗe yake alamar ƙarfi sosae ta bayyyana a jikinsa.
Cikin wani eltia room ya shige Kana buɗeta za ka tadda upstairs wadda ta yi sama, in ka bi ta za ta kai ka dakunan bacci ne guda biyu dake jere. Ploor ne me girma haka amma ba irin girman nan sosae ba, wanda ya qawatu da kujerun fata masu taushi da santsi, gefe guda kuma na’urar dumama daki (room heater) Akan doguwar caugh ya kwantar da ita. Jiƙaƙƙun kayan jijinta ya fara zare mata tare da ɗaura mata towel ɗin daya gani. A hankali yakai lips nashi saman lips nata, saurin zame bakinsa yayi jin yadda ilahir jikinta ya ɗauka wani kalan zafi sosae me turara jiki. Meyarwa yayi tare da fara zuƙo numfashinta ya jima kafin ya samu tadakyar taja wani gauron numfashi. Fatar idontane ya soma motsi alaman tana son buɗe idon ne amma kuma yaji² da raɗaɗin dake mata ne ya sanyata gaza buɗe idon.
A hankali bakinta ya fara motsi wanda bakajin abinda take cewar, ido ya tsurama bakin nata take ya soma fahimtar maganganun da dake faɗi cikin can ƙarshen sauti. "Anne! Wannan gidan ba gidan zama bane domin kuwa sonkai da zalumcin dake danƙare a cikinsa ya zarce sanin me tunani! gidane da yake daf da tarwatse wanda ƙarfi da yaji ake son zalimci yazam shine gaba da komai na gidan. Oum! Anne don Allah karku bari hakan ya taba faruwa don Allah Oum me kika ma waɗan nan mutanen suke son ganin bayanki har ƙarshe? Oum.......
Bakinta ya rufe da nasa bakin yanajin abinda ya tokare ƙirjinsa ɗazun yanxun na shirin dawo masa.
Sai kuma a hankali ya zare bakin san tare da tsareta da dukka manyan idanunsa A kanta, "Mene yaba jonalist kamarki tsoro har haka?"
Haka taji sautin muryansa ya daki ƙirjinta. Saidai babu halin ta kuma wata maganar don me makakon taji afwa saima sake tsanani da jikin nata ya sake yi. Wanda hakan ne ya tilas tashi fita a room ɗin babu jimawa sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da first aidbox. Ruwan allurai ya haɗa tana kwance a inda ya kwantar da ita se oum dake zaune a gefenta wacce fitarsa data gani ne ya sanyata shigowa. Allurarn ya mata yana gama mata ya fice bayan ya nunama oum yadda zata bata magungunan.
Anan ɗakin tayi jinyarta har wajen 3 days abinta shikuwa Ak tun daga ranar be sake ko waiwayar inda take ba. Alhamdulillah jikin nata kuma yayi sauƙi sosea se atishawar da take fama kuma. Shi yasa kullum zaka taddata riƙe da tishu a hannu, Tafiyace ta gama Ak ta gaggawa zuwa ƙasar Swizland. ganin kuma yanayin jikin Alhamdulillah hakan ne ya bashi ƙwarin gwiwar tafiyan. Kafff gidan babu wanda yasan da tafiyar nashi idan ka ɗauke oum kawai don ko jesrah bata sani ba bare meerah wacce take ta kanta. dake ma ba wani daɗewa zeyi ba 1 week ne kawai zeyi ya dawo.



Today is just like any other day, karar alarm ɗin dana seta ne ya tadani ƙarfe biyar daidai kamar yadda na saba.
Ban tashi ba illa mistike idanuna danay tareda addu’an tashi a barci ina haɗawa da salati. Sosae nakejin Though abubuwa sunyi min yawa amma bana raba ɗayan biyun harda maganganun danaji wanda na tabbata sune suke sake relax nawa tight. Yau a ɗakinmu na kwana tare da jesrah kallon bed ɗin da take kwance nayi har zan tada ta na tuna tana fashin sallah tuna hakan danay ne ya sani fasa tashin nata. Jiki a mace na miƙe tare da shigewa bathroom tsarki nayi tare da ɗauro alwula na kalli alkibla.



_SWIZLAND_

Katafaren two storey building gida ne mai matukar kyau da tsada iya haɗuwa gidan nan ya haɗu kai da ganin gidan kasan masu rayuwa cikin wan nan gidan ko dai wani babban ƙusa ne wanda yaci yasha harya tada kai. ko wani babban ɗan kasuwa gate ɗin gidan kawai abin a tsaya a kalla ne ɓangaren biyu ne a cikin gidan ga wani ɗan madai dai cin pool a tsakar harabar gidan, daga gefen hagu katafaren parking space ne mai ɗauke da katon rumfa da suke ɗauke da wasu shegun manyan motoci kusan kala biyar a wajen ƙirar *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll (R) Royce boat Tail* *Bugatti* *Gtf cruiser land* motocin kawai abun kallo ne daga gefen dama kuma shuke shuken fulawowi ne awajen masu matiƙar kyau da ban sha'awa launin ja da yellow daga ɗan gefen parking space wani Katafaren wajen hutawa ne dake kewaye da glass wajen ɗauke yake da wasu fitattun kujeru masu numfashi set ɗaya launin sky blue a tsakiyar kujerun kuma wani haɗaɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen da gefe guda kuma ga wani katon deep freeze a wajen dake ɗauke da lemukan sha kai ko ta ina gidan nan Ƙarshe ne ya haɗu ba karya.
Daga cikin gidan kuwa wani dankaramin terrace ne wanda kai tsaye mutum yake iya hango unguwar da motoci a bakin titi da kuma kai kawon jama’a tsilli tsilli. Wanda Wurin akwai taga mai girma a wajen da ke rufe cikin farin kyakkyawan labule terrace ɗin na ɗauke da doguwar kujerar hutawa (sofa) ta zaman shan iska, Se wani Ƙaramin table na glass a gabanta wanda koda yaushe za ka same shi cike da kayan marmari cikin dankaramin basket babu dare babu rana. Se gymnasium daga gefen wajen wanda yane shaƙe da kayan motsa jiki babu abinda babu kama daga nayi a zaune, a tsaye, a kwance, daga rigingine, na gudu. Duka dai babu nau'in da babu. Anguwar _ISLAMABAD_ kenan Ƙerarriyar anguwa wacce take cikin jerin rukunin mangan anguwannin birnin Swizland kena. Anguwace da duka tsarinta yake na manha masu ji da gidan rana wato (NERA, DOLA da HIROF)
Wacce baki ɗaya jerin rukunin gidajen irinsu ɗaya ne daga waje sai daga cikine abubuwa suke banbanta. Wanda acan ne manyan ƴan siyasarmu ke barar da kuɗin su ta hanyar kama irin manyan anguwannin wasu ma kuwa siye gidan suke kai tsaye. Wanda inda kuɗin zasuzo su baza bana a tamu ƙasar da talauci beyi zurfi da ƙarfi har haka ba amma rashin kishin kai da suna lallai su ɗin wasu shegune a ƙasar suke fita yawon outing Manyan kasashen wajen suyi Challing abinsu.


A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login