Showing 30001 words to 33000 words out of 78068 words

Chapter 11 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1276

mugun yanayi. "Amma dake Allahu ahaad yake sai ya bayyana muku ikonsa ta hanyar kawo wanda ma ba ɗan ƙasar ba yake seta muku hanyar ƙasar taku. Ba don haka ba da tuni ni nagama da babinku na shafe har labarinku a ƙasar saidai bana ma allah shishshigi a cikin lamurana duk da kasancewana ba mutum bace kuma ba musulma ba don haka zanbar mutumin kwarai yaci gaba da aikinsa na barku dashi shine daidai daku daidai da ƙugun ko wannenku domin shi mutum ne da aka haifesa don ƙawar da zulumci da maƙiya musulincin ku. Ni yanzu zan tafi my be ku ƙara gani na my be not my be for ever"
Babat ta fa ce bayan ta gama gwara musu Jiki da haɗa musu jini da majina.

Zaman da basu yi ba kenan ko wannensu ƙafa me naci ban baki ba suka ranta ana kare ko wanne sai maboyarsa.
Wannan kenan.

☆✭ ★***
**☆✭ ★
★★★***

Tsaye suke duka hankalinsu a tashe yake gashi ƙiran duniya oum tama Ak amsma wayan switch off. Sake kallan Meerah oum tayi bayan cike da tsananin tausaya a loƙacin da take sanar da ita cewa ta kwantar da hankalinta wannan ɗin ba wata matsala bace me girma don duk watan duniya tana fama da wannan ciwon.
Har shashen oum babbar likitar dake kula da Emaar's tazo ta dubani tare da bani magun guna harda sadakar Injectoin na samu wanda dama kai tsaye nasan bazan shallake shanta ba tunda duk wani watan duniya saina amsheta.
A wurin ne naji tana waya ita da mah wacce nake jin komai ta cikin wayar da yanda aka sha fama da Annena kafin
ta amince ta yafe musu bayan bata labarin da sukay na yanda aka nemeta aka rasa har zuwa yanzun kuwa.
A raina nake jinjina hali irin na anne na don dama nasan za'a rina wai karuwa tayi bari.
Wuni guda kawai har na faɗa kasancewar dama haka jinyana yake loƙaci guda jikina ke komawa na majinyantan gaske.
Da taimakon jesra na gyara jikina ina fitowa oum na shigowa hannunta riƙe da mug sai turiri yake dafaffen shayine irin nasu na labara wanda yake fidda wani irin daddan ƙamshi me rai da lafiya. Daga gefen bed ta zauna tana cewa na tashi nasha kana na kora da magani, Da ƙyar da lallamawa ta samu nasha saida da tabbar nasha kana ta fita. Data na kunna na shiga whatsaap bayan saimin sim card na ƙasar da jesra tare da phone wanda duka umarnin oum ne.
Seta abubuwana nayi bayan nayi copy'n duka number's nawa na gida nigeria. Kamar wacce dama nake akan ƙaya abu na farko dana fara dubawa bayan gama seta komai na shine fara duba Sabon littafin _AMMEY LAYLERH_
Wato wannan ƴar baiwar marubuciyar tawa *MARYAM NASEER MIRRAH* wacce duniyar rubutu sukafi saninta da. _AMMEY LAYLERH_

♡SPECIAL✯
_Ta Daban_
Wani mugun ihuuu na saki wanda ya sanya jesrah fitowa daga bathroom babu shiri, "Lafiya Uktiey?" ta ƙarasa fitowa jikinta duk kumfa tana tambayana. Banyi duba da kumfar dake jikinta ba na maƙalƙaleta ina sakin dariya kamar ba wacce take jinya cikin wani mugun farin ciki na tsantsan murnan da ya shige ni na shiga faɗin.
_AMMEY LAYLERH! AMMEY LAYLERH!! AMMEY LAYLERH Ceeeeeeee"
Kanta ta ɗan shiga jijjiyawa tare da kallon meerah ɗin tana faɗin. "Waye kuma Ammey Laylerh?"
Dariya na sake saki tare da faɗin "Ki tayani farin ciki ta fara sakin wannan sabon littafin nata ♡SPECIAL✯
_Ta Daban_. ita dai jesrah kallon ikon Allah ta tsayayi sakinta tayi tana niyar komawa na sake riƙo hannunta ina faɗin tsaya ki gani.
A take ta shiga cikin profile tare da group nata na facebook nan take ta fara nuna mata abubuwa. duk da ba ganewa sosai jesrah keyi ba amma ta ɗan fahimci abinda meerah ɗin take nuna mata. Tambayarta tayi sunan da take using dashi a facebook nan take ta faɗin mata. Bathroom ɗin ta wuce tana ce mata bara ta fito a bathroom ɗin itama sai tayi seach nata. Kamar da wasa kuma ta shiga telegram kamar wanda akace mata tayi seach na AMMEY LAYLERH tanyi saiga AMMEY LAYLERH ta bayyana dp nata ɗauke da hoton Wannan tsuntsuwar wato *MIKIYA*
Sallama ta mata tare da bayyana mata cewar ita ɗin babbar masoyiyartace don Allah ta taimaka ta kulata, duk da kuwa cewar ta ganta a online amma sam bata sa ran zata amsataba. Amma kuma cikin abinda bai wuce 5min ba saiga reply ta amsa cikin mutumci. Wani kalan waro ido meerah tayi tare da riƙe baki ganin abinda ta rubuta mata itama tsabar ta shiga ruɗani sai kawai ta tura mata emoji na 😮 alamar buɗe baki da zare ido. A take ita kuma ta tura alamar na sakin dariya tare da rubuta yadai ƴan mata? _kawai nayi mamaki ne wllh_
_Na me fa?_ Ammey laylerh ɗin ta tura mata. _Yadda akai kika kulani haka ba tare da wulaƙanci ba_
Alamar zaro ido itama ta tura mata tare da mata rubuta sosae. _pls zan iya samun Number whatsaap naki pls don Allah!_ ta tura mata tare da emoj na abin tausayin nan. Number'n ta bata haba wa nan fa meerah ta sake sakin wani tsallen na tsabar farin ciki sai kawai tayi copy na no in takai cikin phone nata tare dayin sev da *Ƙauna* Whatsaap nata ta koma Sunan ƙauna ta nemo tare da mata sallam da gabatar da kanta itace meerah wannan masoyiyar tata. Dp na whatssap nata ta duba sai hotonta dake kai yayi saurin sauƙa na wata beauty girl ya bayyana tana tsaye Jin gine daga jikin bayan ƙofar parlour, screenshot ta mata ta tura mata tare da tambayarta wannan gurl in wacece?
_MY LAYLERH_ ta bata amsa _Masha Allah ubangiji ya raya mana ita cikin aminci da yardarsa Aunt_
_Nagode_
Ta rubuta itama taga nan suka fira fitowar jesrah ne ya katse musu firan nan ta shiga bata labarin maganar da sukayi yanzu.

Daga nan suka fita don merrah tace su fita su ɗan zaga ta gaji da zaman nan haka nan. gidan suka shiga zagawa tare da shishshiga ko ina har bangaren moh suka je. daga nan sukayi bangaren Ak suna daf da shiga oum ta ƙira jesrah a waya tace taje yanzu, cewa meerah tay tana zuwa amma ta ƙarasa ta sameta a ciki.
Nan na kutsa kaina cikin ainihin side ɗin zuciyana na buguwa da sauri² ina jin gabana na faɗuwa sosae Nan fa ƙokofi suka rarrabe min nama rasa inda zanbi amma haka na shiga kutsa kaina cikin ƙofofin nan. Nanfa kaina ya juye nama rasa ta inda na shiga sai kawai na nemi hanyar komawa, amma itama ta bacemin batttt. Jikinane ya shiga rawa na shiga tafiya a tsorace ko ganin gabana bana yi chakkk na tsaya sakamakon tuntu6en da naji nayi da wani abu da bansan ko miye ba..........





To ai shike nan a gimtse👌

*By Ammey Laylerh*






*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

17&18

_DEDICATED TO ALL WRITERS ALL OVER THE WORLD_


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

**☆✭ ★ Hot Reletionship scene
**☆✭ ★ Hot love
**☆✭ ★ Romance scene
**☆✭ ★


❤️❤️❤️

Wani kalan runtse idanuna nayi ina jin natsuwata na barin gangar jikina haka zuciyata ma na wani irin harbawa tamkar zata fice daga cikin kirjina. Jin na shiga tangal tangal ɗin faduwa ban ƙarasa dawowa daga duniyar ruɗanin dana faɗama naji an wani irin shatalan ƙafafuna ai kuwa na tafi ƙasa wanwas. Difffff dudif ji da gani na suka ɗan kauce na wani ɗan loƙaci.
A hankali na shiga ware idanuna da suke cike da tsoro, A sannu gani na ya fara washewa tasss na sauƙe gani na a kanshi yana zaune fararen sawayen nan a miƙe, Gefensa kuma pipe ne na shisha da yake zuƙar abarsa hankali kwance.
Wani yunƙuri nayi don bansan sanda wani shegen ƙarfi ya zomin ba "A uzibillahi minash shaiɗanir rajim!" na faɗa loƙaci guda kuma ina miƙewa tsaye sai dai bankai ga miƙewar ba na gan shi tsaye a gabana hannunsa riƙe da pot na shishan yana zuƙa da fesarwa, Hannuna na sanya da niyar rufe hancina ya sa nasa hannun ya fincikoni tare da sanya ni a tsaƙiyarsa ya tokare jikin bango yana fesa min hayaƙin bakinsa akan fuskana tare da tsareni da rinannun idanunsa da suka sanja colour.

Bakina na rawa zuciyana na bugawa na girgiza kai tare da rumtse ido da ƙarfi a tsawace na furta "Mene haka wai?"
Shiru yayi har loƙacin kuma be dena fesa min iskan shishan ba.
"Wanne kalan rashin mutumcin ne wai kake haka? Malam ka janye jikinka a nawa ya dena taɓa fatar jikin Meerah don ba zan taɓa yafewa kai na ba idan hakan yaci gaba da faruwa, da babbar murya ina me faɗa maka ni Maryam Abdullahi Gwani har gaban abada jikina yafi ƙarfin wulaƙantaccen jikin.....

Tsitttt nayi sakamon hannuwansa daya sanya ya zagaye jikin ginin da nake tokare har numfashinsa na sauƙa gefen wuyana. hayaƙin daya zuƙa ya sakr fesa min a fuska tari naɗanyi ganin wulaƙantani kawai yake son yine ya sani nai yunƙurin tureshi a jikina amma ko gezau beyi ba baki na buɗe da niyar yi may bala'i gabaɗaya na haɗiye hayaƙin daya sake buso min. Ai kuwa da wani irin sauri na fisge jikina a nashi tare da tattaro duk wani salive na cikin bakina na tofa may a saman fuskanci. Cikin duban ƙasƙanci na dube shi cikin tafasar zuciya "Allah wadai da duk wani me hali irin naka! Ko dan babu tantama ai dama dan ka zama ɗan shaye² ɗan daba irinka dama ai babu abinda bazai iya aikatawa ba ciki kuwa harda aikata sabon Allah".
Hannu yasa ya hargitsa tulin gashin kansa kana ya furzar da iska me zafi daga bakinsa wani irin tsuma jikinsa keyi yayinda jijiyoyin kansa suka tashi ruɗu-ruɗu dasu tabbas tunda yake babu wani mahalukin daya taɓa yaɓa mishi magana kotankwacin wannan.
{ABDOUL-MALEEK!!!}
ya ji kamar zuciyarsa ta ƙiran sunan sane. kiran da sai daya ja numfashi ya haɗiye abinsa zuwa ciki ba tare daya fesar ba, yana jin hucin zuciyarsa na keto rufin fata bakwai da Ubangiji ya halitta a jikinsa. ja yayi ya tsaya a gabanta tare da ƙura mata idanunsa da suke lumshewa, har yanzu jikinsa ɓari yake numfashi yake sauƙewa a gwame kalmomin data jefashi dasu na neman suyi crosing mind nashi gaba ɗaya.
A take idanunsa suka ita jirkicewa wani mugun bacin rai na dirar masa loƙaci ɗaya. Taku ɗaya tayi a na biyun taci ya damƙi ƙugunta tare da cirata sama ƙafafunta na wutsil² ɗin kwacewa. "Yau zan nuna miki hasalin yadda ɗan daba yake irin nasa aikinsa na dabancin, ki sani ko wacce ƙaddara tana da nata mafarin ke yau naki mafarin zai fara!. wannan shine mafarin taki ƙaddarar na kuskuren da kika tafka na shigo min har cikin bedroom na ba tare da neman iso ko izinina ba.
Kana ki rubuta ki ajje to make you clear, tunda kikayi kuskuren shiga cikin kebantacciyar rayuwana don haka ba ki da wasu yara sai na wannan crimals ɗin, ba ki da wani miji sai wannan ɗan dabar, Kana ba wanda za ki yi wa takaba sai wannan dai shi ɗan dabar Ƴar Jarida Maryam Abdullahi gwani ta Abdoul-Maleek Hassan Al-hassan Emaar's ce har gaban abadan abadaaaaa!!!"
Cilli yayi da ita kanta ya bugu da jikin rug ɗin ɗakin ta saki wata wahalalliyar ƙara riƙe da hannunta data bige sosae a hannun. Tsaye ta miƙe hannuntan na mata wani mugun zugi "Allah ya tsari gatari da sarar shuka! Har abada nafi ƙarfin mashayi ɗan daba irinka mugu! Azzalumi"
Tana faɗar hakan ta kwasa a mugun guje ja da baya baya ya shiga yi yana komawa ya jingina da jikin caution ɗi dake ta bayansa. Wani shegen feshin iska be zafi ya fesar yana kaima iska naushi "Ouch!!!" ya furta yana sake kaima center table glass ɗin wurin naushi A take table ɗin ya fashe hannunsa kuma ya nutse a jikin gilasan ya fara zubda jini sosae. "Ohh shittt. Dom itt" Ya ɗaga hannun zai sake kaima table ɗin wani naushin yaji an riƙe hannun.
"Subhanallah! Gargalion mi ka aita haka? Me kake shirin aikata be a man mana habeebty" juyowa yayi da sauri jin muryan oum saurin wurin da pot na shishan shi yake yayi ƙafansa yasa yayi saurin tura shi ƙarƙashin table ɗin.

Hannun ta sake kamawa tana nufar ƙofar fita dashi hannunsa na tsiyayar da jini. Har bedroom nata ta shige dashi da kanya tayi dresing na hannun kana ta dubeshi cikin mugun ɗaure fuska.
"Mene na gani a ɗakinka wanda ka tura da ƙafarka?"
Saurin ɗago kansa yayi ya kalleta wani mugun kallo ta wurga may tare da faɗin. "Mene kake son maida kanka haka? shayeshaye har cikin gida ko kunyar mahaifinka dake cikin halin ciwo bakaji. Me kakeson komawa Abdoulmaleek?"
"Oum!!"
Ya faɗi yana ƙoƙarin kamo hannunta buge hannun tayi sai kuma ta juyo idanunta cike taff da kwallar da suka tara. "KO wacce ƙaddarar rayuwa tana zowa ɗan Adam ne ba tare da yashirya mataba, dalilin bashike da ikon Juya tarin ƙaddarorinsa ni kuma wannan itace tawa ƙaddarar. Ƴaƴana sune ƙaddara ya Allah ga bayin kanan ka shirya min su!!!. Ka tseratar min da imaninsu daga dukkan wani abu batacce ka tsare min su daga sharrin masu sharri ka musu katanga daga dukkan laifukan da suke aikata maka! Ya Allah kar kaci gaba da ba makiya damar cutatarmin da yara na YA RAHMAN........ Tayi maganar tane me rushewa da kuka.
Wani irin tafasa jinin jikinsa ya soma tare da tsuma yana jin zuciyarsa na dunƙulewa wuri guda, Ja da baya da baya ya soma yana fesar da wani kalan zazzanfan numfashi. ko zogin hannunsa dake naɗe da bandagee baigi haka yasa kai ya fice zuciyarsa na tururi. Kai tsaye special room ɗin da pa'panshi yake ya nufa wanda yake a sassan nashi, zama yayi tare da tonƙoshe ƙafafunsa agaban mahaifinsan ido ya zuba masa yana jin abubuwa da yawa nason suyi losing nashi out.
"Papa komai ya kusan zuwa ƙarshe a yadda kake ɗin nan babu ruwanka dama duniyar bare abinda yake cikinta da wasu ko kullum burinsu shine wawason abinda ke cikin duniyar. Ba mamaki zomo ya haifi kurciya, kurciyar kuma seta iya kasancewa unguluce wannan zoman kuma ba mamaki a wayi gari aji yayi gurnani kamar zaki!!!pa da kanka nake son ka tashi ka tunasar dasu cewar loƙacinsu ya riga da ya soma daga yanzun"
Ɗan numfasawa yayi tare da sake riƙe hannun pah sai kuma yaci gaba da faɗin.
"Duk da an shiga tsakaninmu dakai amma hakan be faru ba kamar yadda sukay zata! Drunker's kuma kaɗɗara tace bawai sawarsu ba kamar yadda sukai zata Zaid be lalaceba pahhhhhhh.....
Kamar yadda duniya da ƙasarsa ke kallonsa duk a cikin salon aikinmune hakan domin yaƙar shege dolo ya kasance kaima shegen kan kane. Pahhhh!!! Zaid be taba koda kwatankwacin shan wani abu na maye ba domin nabi duk wata hanya na toshe hakan duk kuwa da nasan cewar ba wai iyata ce ta sanya hakan ba. Nima wannan ɗin shine ƙaddara amma komai da yake faruwa da bawa yana da nasa sanadin. Sanadin nawa an cutar dani tun ina ɗan ƙarami tun shekaruna basu kai ake bani wine as matsayin Coffee tun ba gane hakan ba harna gane daga ƙarshe naci gaba da siya da kuɗi. Amma hakan be taba gusar min da hankali koya fitar dani a hayyacina ba domin jinin dake gudana a duk wani sassa na jikina me ƙarfine kuma a tafashensa yake, A kullum kwanan duniya inama wine kallon lemu ne shisha kuma kallon flovour nima ɗan shaye shaye bane kamar yadda oum ta faɗi paaahhhhh kace mata "ABDOUL-MALEEK HASSAN AL-HASSAN EMAAR's KUWAIT ba ɗan smoker's bane ka faɗa mata papahhhhhh.......
Kwallace ta zubo daga cikim kwarmim idon paaah hannuwansa suka fara motsawa a hankali sannu ahankali hannunsa ke motsawa harya ɗaga zuwa saman kan AK.
"Na sani!!!"
Paaah ya faɗi cikin muryan dayay low sosae da sosae wanda shima Ak ɗin iya motsin da lips na pahh ɗin yayi ya fahimta abinda yace ɗin, saurin jimƙe hannun yayi a ƙirjinsa hawayen da rabon da yayi harya manta na gangaro masa. A hankali paahh ya soma magana. "A loƙacin da duhun ke mamaye dani wani haske yazo ya haska min hanya! Daga nan shi wannan hasken ya disashe yabarni har gaban abada tun daga loƙacin na fahimta komai babu laifi hakan dan _SANYI YA HAIFA WUTA_ koba komai shine zai shige cikin wannan ɗayar wutar ya yaƙeta harma ya cita da yaƙi bayan ka gama kuma shi wannan sanyin yazo yamaka rumfa ya harma ya baka GARKUWA ko a yau a Yanzu raina yabar gangar jikina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login