Showing 21001 words to 24000 words out of 78068 words

Chapter 8 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1277

murguɗa masa baki ba tare da furta.
"To nidai ko miye na haɗaka da girman Allah ka fice a gidan nan baki ɗaya kaga nan gidan sarautane ba kamar nigeria bane daka saba dabanci wllh idan Mijina ya ganka zai iya halakaka! Tunda naji kowa na gidan tsoron shi yake ance ɗan zafin kaine wllh tsaf zaisa bindiga ya harb......

"Keeeeeeeeee!"
Ya sake sakar mata wata tsawar yan faɗin "Allah ya kiyashe na harbe wani saboda mace macen ma ke irinki marar aji"

"Wllh zanyi maka ihun ɗan iska tunda ba zaka fita ata arziƙi ba"
"Uhumm Aha bara to na matso yadda zakifiyin me dalili ihun da kuma lasisi ganin dai da gaske gadan gadan nufo tan yake ya sanyata miƙewa a guje tayi hanyar data fito wata bathroom. Taku ɗaya tayi ana biyun taji ya ɗamki tsintsiyar hannunta, "wayyo Allah na wayyo Oum kina ina kizo wani ya shigo har cikin gida zai keta min haddi!"
Wani mugun bugu ya kaima bakinta a take gefen lips nata yaɗan fashe ba da yawa ba kaɗan, "Idan kuma nine mijin sai kiyi yaya kuma?"
Tuf ta tofar da miyau wanda jini ya ɗan biyo kaɗan "Allah ya rufa asiri ma ɗan daba irinki yazama mijina, kasani nan ɗin gidan mutumcine da masu mutumci kuma ka sakarmin jiki domin jikina me darajane me tsadane ba kowanne datti da ƙazamin jiki ne ke haɗa nasa da nawa ba na bayama ban yafe ba wllh"
"Sai kuma Akayi katari _ABDOUL-MALEEK HASSAN EMAAR's nine nan a matsayin mijin naki! Idan har baki haɗiyi zuciya a daren yau kin mutu ba ke ɗin baki cika babbar mara kunya ba kuma naki _ZAFIN KAN_ kaɗan bame yawa bane"
"Allah ya rufa asiri wllh dana zauna da ɗan ta'adda marar kishin ƙasar sa kalanka kara na haɗiya zuciyan na mutu tirrrrrr da mugun fata"
Tana faɗin haka ta yanka masa cizon da yazo may a bazata wanda hakan shine ya bata daman guduwa tana Mirza ma bathroom ɗin Key. Numfashi ta shiga sauƙewa a hankali tanajin yadda zuciyanta ke bugawa, "Mugu! Azzalumi!!"
Ta faɗi tana durƙushewa a wurin wani abu me zafi da narka Zuciya na dunƙule mata wuri guda. Cikin muryan kukan taci gaba da faɗin "What do you want?,why did you bring me here?, leave me I can't Meerah yanzu ni ba merrah ɗin da ka sani bace ada ni matan wani ce sunan matar aure nake amsawa azzalumi ɗan daba me satar mutane I hate you."
Ashe ma bata sani ba ita kaɗai take abinta don tuni yabar bangaren ma baki ɗaya.
Da kyar ta iya fitowa a bathroom ɗin tana jin yadda zuciyanta yake a cinkushe, Sallah ta gabatar anan idda take bacci me nauyi yayi awon gaba da ita duk wainar da ake toyawa kuwa bata sani ba har zuwa washe garin ranar.
Da misalin biyu da rabi na rana baki ɗaya duk wanda yake da kusanci da waccen maganar sun gama kammala a babban palon Mah, Harda Sarki Hassan Al-hassan kasancewar jikinsa da sauƙi sosae taron zayeet ash ya buɗe musu da adda'a kafin Sarki Hassan ya furta, "Alhamdulillah Ahar kullum Allah shine abinda godiya me bayarwa da kar6ewa a sa'ilin da yaso!, Ayau ma shine ya sake haskaka mana wani hasken da muka jima da rasashi ta hanyar disashewar daya mana ya bace mana battt! Amma kuma cikin ikonsa da buyawarsa da kuɗirarsa ya bayyana hasken da muka jima da fidda rai da wannan Hasken kwasan kuma da yaso a rana guda, a wuni guda ya haskaka mana shi kansa asalin wannan hasken wato ya bayyana mana ƴarmu da muka jima da cire tsammani daga gareta wato Eash.......

"Be kuwa bayyana muku ba wllh"
Suka jiyo muryan moh jiddoh tamkar wacce aka wullo daga sama. "Idan har ina numfashi hakan bame yiyuwa bane! Kuma idan harda gaske ne yarinyar itace wacce aka ɗaurama aure da wannan tantirin kenan babu Aure a tsakaninsu kenan?, tunda uwarta yayar Abdoul-maleek ce"
"Ba yayarsa bace"
Nusassiyar muryan Sarki ash ya daki duka kunnuwansu tare da ratsa tsakiyar ƙirjin kowa.
Gaba ɗaya kallo ya koma kansa ciki kuwa harta ita ƴar tijarar wacce dakyar mahboob ya samu ya cetota daga wannan shegen ginin ƙasar.
"Kwarai kuwa ba yayarsa bace hasalima basa da wata alaƙa saita musulinci!"
Cikin muryan nan da yake fita da kaushi kaushi da kuma hargagi ta furta "To saika mana ƙarin bayani tunda daduk kan alamu daga sama ta faɗo ba haifarta akai ba"
Moh jiddoh ta faɗi tana wani harare hararenta. "_EASHERH ASH MAYESH_ , Ita ɗin cikakkiyar ƴata ce ta sunna kuma ƴar Auta ta"
"Rainin hankali taya ƴar da na ni ce mutum ta farko na fara amsarta da hannuwana Loƙacin da Razeenerh ta haifeta yanxu kuma don son cika wani mugun nufi kace ba ƴarta bace?, to wllh inma auren kuke son halastawa to kuwa tabbas haramtaccene"
"Moh Easherh kwarai ba ƴar dana haifa bace ƴar Ash ce"
Wani mugun kallo ta data cillama Hassan ne ya sanya shi shanye maganarsa.
"Uhummm tell me ina jiran ka sanar dani ta yadda aka haihu a ragaya"
"Ganin a waccen loƙacin MATATA RAZEENERH bata haihu ba har shekaru biyar da aurenmu ne ya sanya sarki ash ƙirana ya sanar danj cewar, Idan har queen lajja ta haihu mahaifiya ga Razeenerh kenen ya bamu duk abinda ta haifa halak malak. amma karna sabarwa ma kowa tun kuma daga loƙacin Zeenerh ta koma can madina da zama da nufin tana laulayi me zafine moh idan baki manta ba a loƙacin haka na sanar dake?"
Ya faɗi yana kallar moh ɗin kanta ta gyaɗa mishi alaman ehhhhh ta tuna da hakan, ci gaba yayi da faɗin.
"Bata tashi dawowa ba sai a daren ranar da queen lajja ta haifi Autarta mace wacce suma haihuwar taso musu a bazata. A kuma daren naje nazo da zeenerh sai tayi kamar a masarautar ta haihu sai mukayi amfani da hakan gashi kuma dama babyn kamanninta ɗaya da Razeenerh kasancewar uwa ɗaya uba ɗaya ba ƙarya ba. a haka tayi rainon babynta saidai tarin wani abin mamakin sammm babyn taki amsan mama a wurin Razeenerh dole muka renata da madara har takai yaye ba tare da kowa ya fuskanci komai ba.
A haka har takai shekaru takwas kwasam kuwa dare ɗaya rana ɗaya sama ƙasa muka Nemi Easherh muka rasa, wanda wannan shine tushen komai har bayan wasu shekaru tun muna san ran wata rana zamu ganta har muka haƙura muka fawwalama Allah komai. A haka mukaci gaba da zaman mu ba tare da zeenerh tayi ko 6atan wata bane, ganin hakan ya santa cemin nayi wani auren ko allah zai bani haihuwar, haka har auri Yasmine wato mahaifiyar Adeenerh abin mamaki ko wata biyu bata cika ba ciki ya bayyana a wurinta wanda kuma wata ƙudirar na allah saiga itama Razeenerh'nan da nata cikin.
Kusan loƙaci ɗaya suka haihu fikonsu kwana biyar a tsakani, A kuma ranar da zeenerh ta haifi ɗanta namiji a kuma ranar Yasmine ta rasu. Bayan ta faɗamin wasu maganganu masu girma da nauyi.
Rasuwanta babu daɗewa sarkin kano na nigeria ya bani auren ƴarsa wacce ada naso bijerama hakan saida zeenerh ta tunasar dani kana na amince,cikin ikon Allah kallon farko nama maryam naji soyayyarta tsantsa a zuciyana. Ashe Allah ya soni da rahamarsane da naso bijire masa ashe itace cikon mahaɗin garkuwan haskena.
Bikinmu babu dadewa sai gata da ciki wacce ansha gwagwarmaya ba laifi baga Moh ba ba kuma ga matar biyunina ba matar hussein kenan domin kiri² suka nutsa tsanarta a fili babu ko kara. Daga inda ta haifi ƴan biyun ƴaƴanta duka maza wata _ABDOUL-MALEEK_ da kuma _ZAID_ Daga nan mabuɗin wasan ya soma har kawo kwanan yau kuwa!!!"

A fusace ta miƙe tana furta "lallai na yarda gyaɗa mayaudariyace tunda akayita da kwanso amma ba komai ko anan A-Hassanu ka nuna min ban isa dakai ba na haifekane ban haifi halinka ba"
Fuuuuuuuuuuu ta fice tana barin ɗakin domin wasan ai bezo karshe ba dole saita cika burinta kota kuwa shine ƙarshen numfashinta.

Daga nan suka sake tattaunawa a tsakaninsu maganganu masu sarƙaƙiya kana daga nan xuwa gobe insha Allah zasu wuce nigiria don ganin cikon miradinsu su duka wato _ANNENMU_ kenan.
Da da meerah za'a tafi amma Oum tace su barta suje saisu zo da annen, dake ma har yanzu babu wanda yasan da maganar ko jalal Ash be sani ba so suke sai komai ya kammala kana su bayyanama duniya. Drecly da sarkin kano sukayi maganar kuma dama acan zasu fara sauƙa.
7:50am jirginsu ya lula nigeria kwarya kwaryar liyafa aka haɗa masu a fadar kano kasancewar yau babban sarkine a kasarmu wato sarkin madina da kansa ba aike ba, ƙara kwana sukayi sai a washe garin ranar agains suka sake bin jirgi zuwa lagos kai tsaye kuma sarkin kano yayi magana da Malam Abdullahi gwani tun a daren jiyan.
Da misalin sha ɗaya da rabi jirginsu yayi dirar Mikiya a garin lagos nan ma a gidan gwamnan lagos suka sauƙa wasu shegun manyan motoci kusan guda talatin aka shirya wanda duk na rakiyan me girma Ash Mayesh ɗin MADINA ne.
A wani irin tsare aka shiryama fitan motocin kansu iri guda ne kasancewar duk wanda yake da labarin sarautar madina yasan cewar basa fita a mabanbanta motoci ko kuwa sunkai ɗari ne ko.
Gaba ɗaya motocin Rolls R Rayce ne bugun 2024/2025
Blue black masu ting glass ga wani irin ƙawatan da aka ma motocin da ado irin na zaratan manyan sarakuna, Ko wacce bayan mota tana ɗauke da tambarin _ASH MAYESH_ ne wanda duk a iyaka daren jiya aka shirya hakan. Kwara ɗayace fara wacce ta kasance bullet proof ce, Duk inda suka gimla sai kaga anabinsu da video kasancewar labarin sarautar madina ba boyayya bace.tuni matasa ƴan zaman banza watk media trend suka fara baza video'n tare da ɗan short rubutu.
_kome ya kawo Me girma sarkin madina sarki Ash mayesh zuwa nigeria me girmane don haka I'm waiting_
A jiraye suke dajin kome ke faruwa da abinda ya kawo shi ɗin.
Tunfa daga farkon layin har zuwa ƙarshen baka isa ganin iyaka motocin ba, don kuwa bama masu lissafuwa bane dama jama'ar anguwa kuwa harma da wasu anguwannin sun fito dan ganema idonsu dill da dill. Duk kuwa da kasancewar birnine babu ruwan wani da wani to amma wannan batu ake na zaratan sarakuna wanda sukayi zarra sukayi fice a bangaren sarauta.
Ganin inda motocin suka fakane yafi jan hankalin jama'a fiye da baya. A cikin masu leƙe kuwa harma da fitowa harda matan gidan. Amma banda Anne su kuwa sunce baza'ayi babu suna ko iyaka motar suka kalla wata rana sun bada labari suce sun taba ganin motocimsa. Saidai me? Tsaiwar da motocin sukayine a gaban ƙofar gidansu suma yaja hankalinsu. Wannan farar motan ita kaɗaice aka shiga da ita har bakin bishiyar settline ɗin dake ta gaban gidan. Wasu zaratan larabawan hadima maine suka kewaye motan tare da fara wata kalan busar sarewa wanda jin wannan busar ne ya sanya Anne tsayawa chakkk domin jinin jikinta taji ya ɗauka wani kalon tsuma tamkar irin wanda yayi kewar wani gi6i daga cikin rayuwarsa loƙaci guda kuma ya samu ko ya gani ko ji haka jikinta ya ɗauka tsuman.
Cikin harshen labarci suke kirara wa sarkinsu su kuma fadawan kano na fassara musu, Malam Abdullahi gwani da kanshine ya buɗewa ma sarki Ash mayesh motan. Kyawawan fararen sawayensa da duk tsufa besa sun sanja bane ya fara zirowa cikin wasu shegun almurun bakaken halp cover irin sarakunan nan. Shine ya masa gajora har zuwa babban palon Anne domin yace baya da buƙatar ko ina muhallin Autarsa anan yake da buƙatar ganawa da yarinyansa.
Cikin sauri sauran matan suka tari malam Abdullahi suna cewa ya haka duk sauran sassan gidan beyi masa ba sai a sashen Annen kawai zaikai baƙo me girma irin wannan?.
"Babu inda mahaifi yafi dacewa da ya gana da ɗiyarsa inda ya wuce ɗakinta!"

Wani mugun zabira sukai su duka biyun suna ja da baya tare da faɗin.
"Ahhh Rainin hankali dai duk ƙasar nigeria bata isheku wasan kwaikwayon ba saikun haɗa da sarki me girma irin wannnan dan zubar masa da mutumcinsa kome?"
Wani kalan yunƙurowa fadawan kano sukay dake sune masu jin duk abinda suke faɗan. muryan da sukaji ya dakatar da sune ya sanya su juyowa su kalli wurin, Ai da wani mugun bala'in gudu sukaja baya suna sandarewa.

Don wani mugu mugun kaman.....
.


_To ai shikenan mu gimtse kawai nima bansan ko miye ba suka hango ɗin_

*BY AMMEY LAYLERH*

_MIKIYA_








*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

13&14

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

**☆✭ ★ You Are My Dream Come True _Meerah AK_ Friendship 😊🙃🥰?
?_**


Don wani kalan mugun kamannin Anne'n tsantsa da suka gani tattare da wannan kamilallar fuskan dattijon, basu sake rikicewa ba saida queen lajja dake bayan sarki Ash mayesh ta bayyana gabansu itama wanda kai tsaye kamannin Anne'nma duka natane. Ja da baya da baya suke jikinsu na rawan tsoro. Mah (Razeenerh) ce da taji shiru su basuy gaba ba basuyi baya bane ya sanyata leƙo da kanta don ita baki ɗayama tsoron gidan ne ya kamata don gani take taya ace ƴa mafi soyuwa a zukatan iyayensuce ke rayuwa anan wurin. Alhalin su suna can cikin daula da daula ƴarsu na nan na rayuwa a irin wurin nan.
"Wllh yau munyi gamo ne Maman Abdallah nafsi nafsi"
A haba sai aka shiga tsere tsakanin Matan biyu d0n ganin Mah ɗin ya ƙarasa juyar musu da kai baki ɗaya. Cikin anguwa kuwa kafin kace mene har tayi tafff da jama'a ƴan son ganin dill.
Tun tana danne ƙoƙarin danne bugun da zuciyanta ke mata harta gaza dannewa, Raiha ce kwance a gefen Anne'n kasancewan yau weekend ne babu school. Sama take kalla busar sarewan da ake ci gaba dayi na sake bugar da ƙirjinta, Shin sai yaushe ne wai zata dena ire iren waɗan nan mafarkan masu cike da yaudara. don ba yau take ire iren mafarkan ba. Ba yau ba ba jiya ba, ƙofan da taji an taba ne ya sanya zuciyanta bugawa da ƙarfi Malam Abdullahi ne a gaba kafin Mah sai queen lajja me martabane ƙarshe. A nutsenta ta ɗago kanta don gastata kanta. Faɗawa da idonta yayine a cikin wata me balain kama da itane ya sanya jinin jikinta tsinkewa. Tafiya take hannunta yana nuna Anne wasu hawaye na ambaliyan ruwa a saman kyakkyawan fuskanta. "Ke ke kece DIDINA? Lajja wllh Easher'nmu ce wllh itane duk inda jininmu yake baya iya buya don a tafashe yake ba'a daskare yake ba! Har abada jinin Ash ba tauyayye bane ko wacce magudana ta jikinmu tafasa yake jinin mu a tafashe yake Ya abana"
Haka Mah ta shiga faɗi tana kuma ƙara kusanta kanta ga Anne, hannu takai da niyar taba Anne'n ai kuwa taja da baya tare da ƙarema ma mah kallo tun daga kan suturar dake jikinta har zuwa ƙarshe. "A ahhh kada hannunki yayi yunƙurin ta6a wannan jikin, gudun kada ki bata naki jikin"
"Ka gani ko Abaah ai dama na faɗa ma duk inda jinin Lajja da Ash yake baya taba buya har gaban abada wllh Easher ce itace itace itac.........
Sai kuma luuuuuu tayi baya da sauri Raiha ta kwalla ƙara don idonta a kulle suke tin arbar da tayi dasu mah ɗin, ita a zaton tama gamo ne tayi buɗe idonta kuma daidai da faɗuwan da mah ta tafi zatayi.
Kafin kowa a cikinsu yayi wani yunƙuri tuni Anneh takai gwiwowinta ƙass mah ɗin ta zube a jikinta,wasu hawayen ta bata san kona miye ba na saƙƙo mata.

Da sauri Malam Abdullahi ya juya da niyar fita. "Ina ka nufa yanzun?"
Muryan Ash ya katse shi daga shirin fitan da yay niya. "Tana da buƙatan ganin doctor ne"
"Ba buƙatan hakan" kai tsaye queen lajja ya kalla tare da furta ki bata taimakon gaggawa" Ko kafin ya rufe bakinsa harta isa garesu

★★★
*KUWAIT*
_drems

''Aslm!'' Umaymah ta gajarta sallaman tana tsaye daga bakin parlour'n tana kallon Moh Jiddoh dake zaune akan prey mad, Ahankali moh ɗin ta juyo ta kalleta ko second batayi ba ta ɗauke kanta, zama tayi gefen kujerar da Moh ɗin take Zaune tana ajiye wayarta a kusa da ita tace
''mun kwana lfy Jiddo?"
Banza Moh ɗin tamata duk da tajita kuma in da sabo yaci ta saba da halin Jiddon dan mace ce ita mai jin kai har yaranta yiwa take waima a haka ƙaunar umayma'n take. Ringing da wayar moh ɗin ta fara ne yasa ta kalleta miƙewa tayi taje gun dressing mirror ɗin ta ɗauko mata Asaad ne me ƙiran wanda t take kira Autan ta dake England miƙa mata wayan tayi ta gagaya tana zama tare da ɗaukar tata wayar whatsApp ta shiga tana duba messages kallon message ɗin data turama Autarta yasmine tun friday da dare ta kalla, yanzun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login