Showing 24001 words to 27000 words out of 78068 words
madai ganan alaman kore alamun har duba message ɗin tati kenan. Amma ta ƙi bata amsa _Hii Yesmeern lafiyan?_ Ta sake tura mata kuma yayi two tick kuma ta gan story ɗinta amma bata duba message ɗin nata ba sauƙa tayi tare da switch data'nta tayi ma baki ɗaya.
Maganar da Moh tayi ne ya sanyata maida dukkan hankalinta thought bata ɗago kai ba akan Moh ɗin
''uhm Umaymah kenan ae shiyasa naso tun a wancan loƙacin naso mu gama da komai amma abun ya gagara gashi kuma a halin da ake ciki yanzun babu damar hakan!'' shiru Umaymah tayi na ƴan seconds da alama tana sauraren abunda Moh jiddoh ɗin ke faɗa mata ne
''Duk da ance shi icce tun yana ɗanyensa ake iya lanƙwashi, to amma ni duk da bushe ɗin zan iya lanƙwashin! Idanma ta kama da karyewa to kuwa karyashin zanyi don buƙatan kaina ya biya Moh'' duk da a karkace tayi maganar amma tasan inda maganar ta dosa.
Murmushin gefen baki moh ta saki sai ta ɗago batare da nuna komai ba ta furta "Uhmmm dakyau ki kula sosae wajen lankwasar dai kar yazam mu ta sake kwabewa"
Wani kallo ta jefa mata wanda kai tsaye jiddon ke ankare da ita, itama wani shegen murmushi tayi ita kaɗai tasan abinda take kwancewa da saƙawa.
"Zan kula sosae karkj damu Jiddoh komai zai tafi a tsarinane tafiya a tsarina kuma baya nufin kwa6ewar aiki irin na wasu!"
Kai tsaye jiddo tasan maganar nata ne kuma ta amsa kamar yadda umayman ke buƙata dama, "Aha Allah temaka na ce saimun sake haɗuwa". Dama kamar jira umayman take ko irin wacce take akan ƙayar nan haka ta miƙe zimbir tana barin parlou'rn a zuciyarta take faɗin.
{Mayyar mata kawai kullum tana kan sallaya kamar wata mutuniyar kirki nan kuwa sai shegen iya ƙulla makirci da haɗa tuggun tsiya...}
Tana tafe tana duba wayanta loƙaci bayan loƙaci kuma tana jan tsuka, kamar daga sama kuma sai ganin ƙiran yasmine tayi ya shigo wayanta. Saurin peak call in tayi gudun kada ta katse mata ƙira don tasan kaɗan ne daga cikin aikin Yasmine ɗin.
Daga ta can bangaren cikin harshen larabci yasmine ta furta. "Hala akwai abinda yake tafiya ba daidai ba tunda naga saƙonninki harta email!ok?"
"Loƙacin zamanki America ya ƙare yasmine don loƙacin fara farautane wannan! Amma ya kamata ki taho haka nan my be not my be forever kuma"
"Kina nufin A maleek na Emaar's a yanxun haka Mommah?"
"Yana a harma da tsarabnan wifey a tare dashi"
Daga kwancen da take ta mike tsaye zimbir tare da faɗin "Ma me? Kamar fa mata naji kin ambata mom a taya A maleek zaiyi min haka? Shikenan kitsimayi zuwana Later"
Daga haka ta datse ƙiran tare da dafe kanta da taji loƙaci guda ya balain sara mata. "A wannan karon dole ka faɗa hannuna Abdoul-Maleek Emaar's ko kaki ko kaso mata ne bisa kanka wanda ake mana laƙabi da gangar shaiɗan"
_Amma wait! Nidai nace babu ni Ammey Laylerh tare da duk me karanta littafin Mikiya Uhummmmm_
★★★
_Some late_
Karon dataci da wani abu kamar gini ne yasata saurin ɗagowa tana yin one step back hannunta dafe da hancinta data buge tare da forehead ɗinta amma hancin yafi mata azaba
A hankali ta soma ɗagowa dan son tabbatarma kanta wanda ke tsayen saboda wannan unique ƙamshin da bata ta6a jinsa jikin kowa ba sai jikinsa ɗin.
Kallon kallo sukewa juna ita dashi kasancewar sa mutum mai tsayi sosai kuma dai kunsan tsawon mace dana namiji yanda suke hakan yasa ta koma wata ƴar karama. ''Halan kai makaho ne?'' da ƙarfi tayi maganar dan ganin yanda yawani mata tsaye a gaba tamkar wani bijimin sa. Idan inda suke tsaye yayi magana to shima Ak yayi, jin yaƙi ko tanka mata ne ya sanyata sake faɗin
''Malam nace baka gani ne? kokuwa iccen daka buge baiji maka ciwo ba?'' ta faɗa tana hayayyaƙo may ta buɗe baki kenan da niyar sake magana muryan Jesrah ta dake tahowa ta katseta.
Cikin shegen rainin hankali ya dubi jesrah tare da faɗin''dalla malama hold it na ce miye wannan aka kawowa mutane gida'' da sauri jesrah ta duba ak ɗin tare da faɗin
''Akie Merrah ne fa''
Wani kalan yamutsa fuska yayi tare da furta''miye wani Merrah kuma?'' yanda Yake yatsina fuska kamar yaga kashi ne sake hasala Meerah ɗin itama.
''Akiey Matarkane fa wanda aka ɗaura ma aure da ita already tuni'' wani irin shegen murmushi yayi yana yuja kai ya tabe baki irin anzo wajen Nan.
''Au cemin zakiy kaskar data maƙale tace saini, wacce tabi duk wani lungo da saƙo don ganin ta shigo rayuwana. Fine amma bara na tuna miki wani abinda basu faɗamiki ba nan gidan ba kowane mara aji ko jani talau ne yake iya shiga ba bar ganin kin samu shigowa fitan ma ba wahalan zaiyi ba kamar shigowanki EMAAR's......
Ɗagowa Merrah tayi a karo na farko tunda suke tsayen ta kalleshi straight in the eye. Tare da furta.
"Who are you? How dere you?"
Ta faɗi in a low dangerous voice, kafin taci gaba da faɗin. "Saidai gidan ma ai beyi kama dana mutane tunda ba'a daidai ɗinsa yake ba, Kuma a kallon farko ma gidan beyi kama da gidan da mutane ke rayuwa a cikinsaba baki ɗaya duhu da duhuwa ne kewaye da durƙushashshen kangon ginin daya yake a baybay"
Da wani kalan kallo ya bita me kama dana rainin hankalin nan.
"Idan ma dalilin wani abu yasa kika nace saikin shigo gidan nan toh ki sani bakida muhalli a yanzu dan the house is full with children's no more room for you''
Yana faɗin hakan ya wuce abinsa bayan ya mata wanna shegiyar alaman datafi tsana fiye da komai daga gareshi. "Babu wanda besan halin Akiey ba so inaga hakan ba abinda damuwa bane dear!"
Taji muryan jesrah tana jan hannunta lips nata taɗan ciza bada yawa ba tana bin bayan jesran don dama wurin oum suka nufa data aiko ƙiranta.
Oum ɗin ta tarar zaune tare da jesrah wacce ta labartama oum ɗin komai daya faru. Cikin ƙarfin halin Oum tace "$higo man Meerah kinzo kin tsaya a Kofa? Zonan kusa dani kinji ta faɗa tare da nuna mata gefen da take zaune,murmushi ta yi tare da karaso ta zauna kusa da itah kamar yadda oum ɗin ta buƙata ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da faɗin.
"Oum good afternoon" Murmushi Oum ta saki tare da da amsata da "Lafiya Alhamdulillah baki biyo bayan iyayenki nema zance ns ko kakanni nema"
Ɗan murmushi kawai meerah ta saki tana jinta a takure da zaman da sukeyi ɗin, dan har yanzu ta gaza sakin jikinta da oum don sosai take kunyar matan yanzun ma jinta take kamar ta gudu haka taji aranta.
"Jesrah kuje ku gaida mutanen cikin gidan"
"Tomm Oummuh"
Jesran ta faɗi ko kafin ta miƙe kuwa tuni zaram har meerah ta rigata miƙewarma, kai tsaye bangaren Umaymah jesrah ta fara raka Meerah ɗin. da wannan shegen makircin nata da zagon ƙasa ta tar6esu faran² Allah'n baka. Basu wani jima ba sosae suka mata sallama wasu manyan arabian jallabiya tare da Alkyabba da turaruka masu tsada sosae ta haɗa meerah dasu. Ko kallon kayan batai ba jesra ne ta amsa tana mata godiya.
Daga nan bangaren Moh jiddoh suka yi a loƙacin tana zaune ne akan caution tayi crossing ƙafafunta tana karkaɗasu idanunta a lumshe ita kaɗai tana aikin saƙawa da kwancewa. Wani kalan buɗe idonta tayi tare da juyowa zuwa wani mummunar faduwa gaban moh jiddoh yayi zuciyarta ya shiga harbawa da sauri-sauri idanu ta rufe ganin wani irin haske mai bala'in karfi ta cikin idanun meerah ɗin batayi auni ba taji muryarta na cewa
"Innalillah wa'inna ilaihir raji'un meke shirin faruwa dani ne haka ni jiddoh yau na shiga uku!"
Da sauri jesrah ta fita a ɗakin tana cema Meerah tana ɗan zuwa don wayan da aka ƙirata.
Wata nannauyar ijiyar zuciya Moh ta sauƙe tare da furta "wllh shegiyar yarinyar nan tsoro ta bani kodan jinin mayuce masu shegen ƙarfi jinin tsiya tirrr dai wllh har abada ba'a taba sarki biyu a guri ɗaya" tayi maganan tare da buɗe idonta ba kuwa su faɗa ko ina ba sai cikin na meerah. Baki ta buɗe mata tare da daƙune fuskanta sai kuma gata zaram akan jiddon.
"Da kina yarinya bakiy karatu bane? Cokali ɗaya na nonon sa yafi daro ɗaya na nonon jaki, uhmmmm dama saida nai tantamar ba'aje makaranta ba. duk aukin jakuna ba zasu taba kama ƙafar doki a gudu ba. Kuma har abada zakara shi kaɗaine sarki Moh ɗinmu ta ƴan gayu"
Ta waske abinta tana kamar gyara mata rufin hulan kanta tayi ganin shigowar jesrah. Saƙeƙe haka moh tayi tana me bin meerah da ido kawai fakar idon jesran tayi tare da ƙyafta mata ido ɗaya da kashewa. "Ina ganin mutafi haka nan ko dear?"
"Ehhhhh hakan ma yayi. Moh sai haɗuwa ta gaba yanzu ta wuce sauri muke ki kwana cikin sauƙin zuciya Allah kuma yaja da ranki kisha kallo my kakas"
(Yau naga yadda ake bariki ni mai jiddah, to kodai akwai abinda yake ba daidai ba ko yake a baybay bana da masaniyar hakan kuma?)
Ta ayyana a zuciyarta tana jinjina ƙarfin halin yarinyar, {kai ina wllh ma tana da aljanu yarin yarnan}
ta sake maimaitawa tana faɗawa bedroom nata.
Haka Moh ta kwana datunanin abunda ya faru tsakaninta da Meerah sosai abun ya tsaya mata a rai,tunda take bata ta6a ganin makaman cin haka ba a iya tsawon rayuwarta duk me hakan ke nufi?, ya zama dole ta shirya ma zuwan waɗan nan jerin abubuwane ma zata ce ko ƙaddarori ne ma oho da wanan tarin tunanin bacci ya ɗauketa.
A ta bangaren meerah kwana tayi da tarin abubuwa maban banta wanda suka farun min dama wanda suke kan faruwan. Ruɗani,mamaki, al'ajabi sun taru sun hana Meerah runtsawa a wannan dare. Kanta ya gama kullewa dangane da abinda duk suka faru ɗazun tsakaninta da Moh da kuwa wannan Aljanin. Shin mutumin nan ɗan dabar ne da gaske? Kokuwa wani abu daban da bata sani ba. Babu abinda ke mata kaikawo a zuciya sai kalan yadda ya ringa yaba mata maganganu da kuma haɗuwarsu na jiya daya bita har ɗakin ta me hakan ke nufi kenan?
Ita kam al'amarin wannan gida ya fara birkita mata lissafi tun a farkon shigarta komai ya gama bayyana kansa gareta.
A lissafin ta dai Moh jiddoh itace uwar masu gidan to amma ta ya ya Akai ta kasance me fuska biyu. Abubuwa sosea ya hango tattare da matar baƙaƙe ba masu lissafuwa ba. Zuciyarta a ƙone take babu ko ɗigon rahama idan har lissafinta ya bata daidai Kenan 6atar da Annenta akayi a cikin wannan masarautar? A tunaninsu ita ƴar gidan ce kenan miye silar mutuwan matan me martaba ga biyu? Zancen daya faɗa a baybay ita tuni ta gama fayyace abinta filla filla tun a ranar. Kuma ita kaɗai tasan abinda taga ni ta kuma ɗaukarma kanta alƙawarin bibiyar kowa da kowa na wannan masarautar har zuwa kan dalilin da yay bacewar annenta. Kenan Anne ita bama ƴar nig bace Sarki Ash dai shine cikakken mahaifinta Allahu ahaad lallai Allah da girma yake.
? Sai wajajen ƙarfe biyun dare bacci yay ciki da ita cike da tarin wasu mafarkai masu ban tsoro.
A hankali hasken rana ya bayyana a sararin samani.
Wanda haka yayi dai-dai da farkawanta tare da bayyanan ciwon da taji maranta ya harba mata, ya mamaye duka har sassan jikinta da zuciyarta.
Wani irin rumtse idonta tayi tare da tashi zaune cikin wani irin gigitaccen ciwon da ya mata dirarn farat ɗaya tace.
"Sheehhhhhhh Wayyo! wayyo!! wayyo Allah Anne na ciwo zafi wayyo Raiha wayyo kowa da kowa na cikin duniyar ma baki ɗaya. Wayyooooo"
Ta faɗi da ƙarfin daya farkan da jesrah a zabure don babu jimawa da komawansu bacci bayan sunyi sallar subhi.
"Subhanallahi Aunty meerah mike faruwa?" ta tambayeta cikin muryan bacci tana mikewa tare da nufo wurinta, wani irin juyi haɗi da murƙususu meerah keyi wanda hakan kai tsaye ya sake firgitar da jesrah kai tsaye ta fita a dakin da gudunta domin sanarma da Oum.
★★.....★★★
A ta bangaren umaymah tun a daren jiya ta gama shirya komai na tarbar dolky'nta tun daga kan abincin da takeci har zuwa tsaftar sashen ma a yau ta kasance ta musamman duk da a kullum a tsaftace yake. An shirya kalolin abinci da ƙamshinsu ya gama cika ko'ina na sashen har maƙwaftan shashen ma ka iya jiyowa. Duk ata dalilin son ta farantama dolly'n.
A mugun guje rantsatsiyar baka wulik ɗin lafiyayyar motar da dolly ke ciki ta tsaya gab da ƙofar shashen umaymah, cikin rawar jiki ɗaya daga cikin Hadiman ya buɗe mata motan, sauran kuwa tuni sun zube ƙasa kan gwiyawunsu kawunansu a ƙasa domin kai tsaye sun san dokar madame dolly'n DA'DAH. Tun a farkon shigowan motanta kuwa cikin Mention ɗin hadima suka dinga tsere don gujema haɗuwa da ita bare takai ga yi mata laifi.
A ƙalla taja Sama da mintuna goma batafito ba duk da kasancewar an buɗe mata, sai da taga dama dan kanta sannan ta ziro ƙafarta fara tas dake a cikin ƙyaƙyƙyawan blue ɗin takalmi mai tsananin taushi da ɗaukar ido da zai iya birge duk wani mai kallo, Wanda yaci uban naɗi da igiyoyin dake jiki, kusan sakan biyar a tsakani sannan ta ƙara zuro ɗayar cike da ƙasaita.
Tashin ƙamshin turarenta da takun sawayenta ya tabbatar ma duk wani rai mai numfashi ata bangaren isowarta. Wanda hakan kai tsaye ke sanya su rusuna kawunansu ƙass gudun haɗa ido da ita kayi laifi. Cikin wani shegen taku take wucesu hancinta ɗage a sama tana wani huhhurashi sama ita ga ƴar zafin kai.
Wasu shegun ɗamammun riga da wando ne a jikinta na jeans iya ma'alwantarta kan nan naɗe cikin swear band me shegen kyau da tsaɗa, da wani irin maɗaukakin farin ciki umaymah dake zaune ta miƙe tana rungumar yarin yar nata.
Kafin da hannu taima dukkan amintattun hadimanta dake zagaye da ita nunin su fice. Har rige-rigen bin ƙofar da zata kaisu falon farko dazai fiddasu ta ainahin ƙofar sashen nata suke. "I miss u my dolly'n Dada"
Wani iska taja tare da jan numfashi ta fesar a hankali.
Idanunta ta ɗan ƙankance da jinjina kanta tana sakin ɗan karamin murmushi domin Dada ɗinta da tafi kewa fiye da komai har ita kanta momman kuwa.
Ita kuwa Umaymah da take jin duk wannan ranar tanajinta rana ta musamman ne a gareta, sakar mata kiss a goshinta haɗi da zaunar da ita tamkar bata baby.
"Mommah Kina lafiya?".
"A zahiri dai lafiya nake, amma a baɗini cike nake da tarin damur dake cinkushe a raina first"
Umayman ta faɗi fuskanta na sauyawa daga yanayin farin cikin da take ciki zuwa kishiyarta.
"Uhhm!" Yasmine ta faɗa da ɗan lumshe idanunta ta buɗe Still a lokaci guda.
"Kai tsaye ki faɗin damuwar don nima yanzun haka a cikinta nake saidai jin wannan lamarin ya shafe wancan ɗin don shi serious bane kamar wannan ɗin"
Kai tsaye ta ɗan tsaƙuri lamarin a ciki ta bata. Idanunta a lumshe suke buɗesu tayi tare da fesar da numfashi ba tare data bata amsan tambayar data mata ba ta furta.
"DADA fa?".
Tay maganar a fisge tamkar yinta ya zama tilas ne a gareta. "Yana mashel kotra" Wani kalan zaro idonta tayi wanda suke a bugu wanda kai tsaye inkai mai fashimtane a take zaka fahimci ba'a daidai suke ba.
"Be dena zuwa Mashel kotra ba har yanzun kenan?"
???...........
*BY AMMEY LAYLERH*
*🦅 MIKIYA 🦅*
_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________
*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~
✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*
BOOK Two…………………………✍
15&16
_DEDICATED TO ALL WRITERS ALL OVER THE WORLD_
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
**☆✭ ★ Hot Reletionship scene
**☆✭ ★ Hot love
**☆✭ ★ Romance scene
**☆✭ ★
❤️❤️❤️❤️❤️
"Ehhhhhhhhh"
Ta bata amsan tambayan data mata tsaye ta miƙe ranta a bace har zata wuce sai kuma ta tsaya chakk tare da faɗin.
"Wannan ɗin duk laifinki ne Mommah"
Daga haka ta wuce side ɗinta sai ƙamshinta kawai data barma Mom ɗin nata itama tsayen ta miƙe tana me nufar nata side ɗin don ƙiran Hussein.
Taƙira wayansa yafi sau cikin kwando amma yana Ring baya ɗauka haka ta hakura badon taso ba.
Ko cikakken five minutes batai ma sai gata ta sake fito sanye cikin 3ter ɗin bakin wanda da bakar riga hannunta riƙe da car key sai uban glasses ɗin data rufe idonta dashi, kota kan mom dake mata magana akan ina zata je bata biba bare abincin da take mata tayi.
Wata Mota ƙirar Mercedes Benz 2024/2025 ta ɗauka kota kan hadiman dake famar zube mata