Showing 48001 words to 51000 words out of 78068 words

Chapter 17 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1290

da jiki cikin wata narkakkiyar murya ya furta. "Me zakiyi da sleeping wear ɗin?" Cikin muryan kuka nace "Sakawa zanyi in kwantama bacci nake ji"
"You don't need to wear anything to night"
Nan take hawaye ya sake ɓalle min idona na zubda ƙolla nace, "Ni bazan iya kwanciya babu kaya ba a jikina!" na faɗi ina son zame kaina daga gareshi. Sake cusa kansa cikin wuyana yayi da wata matacciyar muryansan ya sake furta. ". Don't worry. I will cover your with my body" ya faɗi yana ƙarayin sama dani xuwa kan bedroom nashi.
kuka na sakar masa domin tuna irin baƙar azabar da nasha daren shekaranjiya. Sosai nake sheshsheƙar kuka nasan yau kam idan yace irin abin ranar zaiyi min mutuwa ma kawai zanyi nasan na shiga, I have no way out no escape. Amma ni ban shirya ba tsoro nakeji gashi babu alamar sassauci a fuskarsa. Domin Abinda nake karantawa a idonsa shine yake ƙara bani tsoro,Idonsa ya janye daga cikin nawa.
Cikin wannan sound nashi ya furta "Kuka kuma? tun yanzun? Me kikema kukan wai?, I did not even kiss you fa"
Ya faɗi yana sake shigar dani cikin jikinsa tare da sake kissing na forahead nawa. Still cikin wannan muryan ya sake furta " Amswer mee mi kike ma kuka?". Cikin muryan na furta "Tso ro tsoro inaji!'
Saman fuskana ya shafa tare da gangaro da hannunsa zuwa saman ƙirkijina,"Tsoron me kuma?" ya furta yana sakar min numfashinsa me ɗumi wanda ya sanya tsigar jikina zubawa. Da hannu na nuna shi, sake matseni a jikinsa yayi cikin gajiyayyar muryarsa ya furta "i promise 2 u i will never do like at the last time that fist day" wani kukan na sake saki A gajiye ya sake furta "Me kike so kuma?"
Cikin cracking voice na furta ni dai ka ƙyaleni kawai!" Wani lalataccen murmushin gefen baki ya saki tare da faɗin.
"IMPOSSIBLE"
Kawai ina jin sauƙar lips nashi kan nawa lips ɗin very lightlyya fara kissing nawa out.
Daga nan komai ya ɗauki seti tun ina iya roƙon ya ƙyaleni daga karshe dai harna hakura ina saddarƙawa, don kwarai na daɗe da fahimtar mutumin nan abinda yasa gabansa kawai yake yi, kamar kuwa yadda ya faɗamin ɗin lallai na yarda idan yace zaiyin to kuwa tabbas zaiyi idan kuma yace bazaiyi na yarda babu abinda ya isa sanya shi yayi ɗin koda kuwa menene shi. Zafin da naji bekai na ranar ba amma fa na jigatu ba laifi don ba karya na azabtu iya azabtuwa.
Kaina na saman ƙirjinsa yana shafa sumar kaina a hankali ahankali tamkar wata baby lol.
Se bayan shuɗewar wasu awanni kana ya ɗaukeni chilak yana yin cikin bathroom dani, wanka ya mana a tare kana ya zira bathrobe tare da shigar dani ta cikin nashin ya zaman munyi amfanine da ɗaya. Hannuwansa na yawo a wasu sassa na jikina haka muka fito a gefen bed ya zaunar dani yana sakin rigar wankan dake jikinsa. Saurin chukuykuye duvet nayi ina sauƙe ijiyar zuciya don wllh naga alamun mutumin nan bayda kunya ko kaɗan, ɗauke kansa yayi tamkar besan abinda ya aikata ba a nutsensa ya sanya wasu fitnead rober na bacci irin masu laushin nan farare. Iyaka guntun wandon kawai ya saki yana kwanciya gefena tare da juyo dani muna fuskantar juna, idona a kulle cikin sauƙe numfashin tsoro na ce " zan sa ka kayana"
"Ba buƙatar hakan" naji wannan bugaggiyar muryan nashi ya bugi dodon kunnuwana. Rigima na sakar masa sosae ina dukan ƙirjinsa da babu riga wanda kai tsaye hakan ashe sake kunnoshi nayi, Haba loƙacin da naji yana sake ɗorani akan wata sabuwar hanyar tuni ɗan ƙaramin kukana ya koma na gaske wanda Allah ne ya temakamin ya kyaleni da ƙyar.


Acan masarauta kuwa sosae Alhussein ya nemi daya tada ɗan ƙaramin yaƙi dalilin rashin ganin Ƴar gaban goshinsa dolly. Ga kuma rigarta a ɗakin AK an gani duk wani sassa na ɓangaren sun gama cashe shi tsaff sedai babu kowa wasu wuraren kuma basu isa shigar saba saboda wani gun securityne wani wurin kuma da wani sassa na jikinsa yake amfani wajen buɗeta.
Oum kuwa tana can a gefe abinta taja bakinta tayi shiru tama rasa wanne kalan tunani ne zatayi akan hakan, tasan dai har abada Ak baze taɓa kusantar zina ba duk da baka isa ja da ƙaddarar ubangiji ba amma tana da yaƙinin Insha Allah babu jininta babu aikata zina.
Rashin ganin meerah dadai kam ta damu amma da zuciyarta ta hasko mata wani abu data haɗa da lissafin yasmine da kuma meerah ɗin duk kusan loƙaci ɗaya hakan ya faru se taji nutsuwa na zuwar mata kuma a take zuciyarta a haska mata wani abu. rashin samun AK a waya dama shi yafi komai ɗaga mata hankali har yanzu ma kuwa da wayan ke gabanta still tana trying na no nashi.
Wasu ƙwararrun masana na'ura Da'da ya ƙira a wayewar cikar kwanaki uku, haka suka zo sashen Ak suka shishshiga binciken ɗakin da yasmine take. Anan palon suka ganota da ƙyar sedai duk yadda zasuyi su fiddo da dolly hakan ya gagara sosae hakan ya sake ɗaga hankalin su umaymah. Moh jiddoh kuwa duk wani tujara nata akan Oum take saukeshi tace dama jininta masiface a garesu, Ana haka kuma a daren ranar jirginsu Sarki Ash ya sauƙa a cikin masarautar. Ba a sanar dasu abinda ke faruwa ba an barsu se xuwa washe garin ranan sannan sun tsirga.
Sedai hakan bata samu ba don moh tana jin labarin sun dawo taje har part ɗin da suka sauƙa su dukansu taje ta sauƙe musu wata sabuwar tijarar. sam hankalinsu be tashi ba kamar yadda taso ta haɗa rikici tsakanin iyayen yarinyar da kuma oum. Fitowar Anne kenan daga bathroom bayan ta watso ruwa taji irin tijarar da moh take saukewa iyayenta wanda yanzu a duniya gani take bata da sama dasu har gaban abada tunda har Allah ya bayyana mata su.
Chakkk maganar nata ya maƙale sakamakon ido biyu da sukay da Anne dake binta da wani kalan matsiyacin kallo, don kallo ɗaya tama matar taji sam bada mata ba, Kowa inda Moh ɗin take kallo kamar idonta ya faɗo kasa yabi da kallon don ganin abinda yake neman ruɗar da ita. Wani kalan tattausan murmushi queen lajja ta saki tana me sake zamanta na crossing ƙafafunta datai. "Miye abin firgicewa kuma jiddoh? Bafa *JADDER'N ASHAAN* Bace wannan ɗin EASHERH ASH Ceeee ɓatacciyar ijiyar Allah"


(KAI WLLH SENA TSEYA INA CIKIN RUBUTUN NAN KEWAR MY TEAY NA TA FAƊO MIN I MISS U MY TEAY ƊIN MIIIRAH I WILL MISS U MY TEEMERH NAAAAA! MY TEEMERH'N MERRY)
{HHHHHHH seni masu sunaye da yawa😀😁😂😊}

Wani kalan tsuma naman jikin moh ya fara wata zufa na karyako mata tana biyowa ta duuka sassan jikinta. Ja da baya da baya ta fara yi idanunta na fara gani bibbiyu numfashinta kuma na gwamewa. Karo taji tayi da wani abin da batasan ko miye ba saurin dafe goshinta tayi tana ciro kanta don ganin da me ne taci karo haka?.
Wani kalan dafe kirjinta tayi tare da zaro idanuwanta waje don ganin wacce bata taɓa zata ko tsammanin ganin bace tsaye agabanta. Baki ta buɗe da niyar sakin ihu sai kawai ta tafi luuuuuu tana zubewa some a wurin.....



_Hhhhhhhhhhhhhh ko me ne ya firgitar da moh haka?_

_Tofa mike shirin faruwa ne da meerah ɗinmu uyummmmm?_

_Tofa queen lajjanmu irin wannan yaɓa magana haka? Amma ba komai nidai ina yinki tare da my teay Naaaaaa ma itama tace tanayinki for ever_Ga My kilan ɗina ma tace tana yinki itama ma my piepie'n Mirrah_ Amma ita My Meji love tawa itace tace wai YAYA KUWAIT AK take yi😆😆😆😆 _
_Maman mujaheed da Aysha kuma tace ita ta Meerah ce_ My zeey musa ma ta ɓangaren meerah ce_ Amma ai duk babu ɗamuwa ma tunda mun zama ɗaya da Yaya kuwait Ak ɗin nima na ɗana lol😁😂_
_Allah sarki my Ummeerh musa kekam banma san mine zan ce miki ba keda Hassana Yahuza ƙaunarku ta musammance gareni, ku duka kuka haɗa kuke sonmu DA Yaya kuwait AK ɗin da my Meerah ɗin ba. Ban manta da tarin kaunar da kuka nuna min a duka sauran littattafaina ba kunso JALAAL AREEF kamar ba gobe haka ma MALEEK TOUFIQ, Haka ma ALIEYO namu na gargajiya mutumin Hajjo ɗinmu ta gargajiya hhhhhhh lol itama 😂😁 wllh ta bani ciwon kai ba laifi.....



Laaaaaa nifa na manta irin zazzaga wannan jawabai haka

*END😱*
Amma fa bana littafin fa na fage ɗin don se yanzune ma hhhhhhhhh









*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

27&28

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*


♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Kowa na ɗakin da kallon rashin sani yabi matar dake tsaye wacce suka tabbata ganinta shine yay sanadiyayyar sumewar moh, amma banda queen lajja data ƙame a zaune tana rasa ma wai shin a cikin wacce duniyace take ma takamaimai. Jaddernta dai? Aminiyar nan tata dai wannan ƴar uwartata ƙanwarta jininta biyuninta dai wacce ta riga da fidda rai da sake ganinta har gaban abada wacce ta mace a garin haihuwarta ta farko a masarautar EMAAR's wacce aka nemi gawarta sama ko ƙasa aka nema aka rasa se iyaka yaronta suka gani shima a ma ce. Shi yasa a loƙacin da sarki Al-hussein Ashaan yazo da batun nemawa ɗansa Hassan Al-hassan auren ƴarta RAZEENERH (Mah) taki ta rufe ido tace samm bata yarda ba.
Wanda seda aka kai ruwa rana kana ta amince bisa tilastawar mijinta sarki Ash yace ai ba'a taɓa gudun ƙaddara duk inda kake idan zanen kace seta bika ta zana haka don haka ma kar ɓacewar ƴar uwarta ya nemi da juya mata brain nata. Ita kaɗai ta rufe tayi tayi kuka tayi kuka a loƙacin da auren ƴarta Raneenerh ya ɗauri da Hassan Al-hassan EMAAR's don gani take itama tana iya mutuwar a rasa nata gawar sedai hakan be faru da ƴar tan ba seya faru dai da ɗayar ƴarta wacce a masarautar suke ma kallon ƴar asalin EMAAR's ce. ɓacewar Eaherh Ash a EMEER's shine mabuɗin komai don anan hasashen kowa ya koma kan cewa lallai Jaddern Ashaan ba mutuwa tayi ba ita ma batar da itan akai. Wannan kenan.

Jikinta har rawa yake wajen rarrafawa ga ƴar uwar nata biyuninta kuma babbar aminiyarta jaddernta *JADDER'N ASHAAN* Dinta mace mafi soyuwa a zuciyar mijinta ASHAAN. Wacce akayi bikinsu rana daya aka kaisu ɗakin aurensu rana ɗaya wacce seda tama biyuninta rakiya har ƙasar kuwait masarautar Emaars kana itama aka mikata ga nata mijin sarki ash wanda suka kasance suɗin aminan juna ne. Su kuma sun kasance ƴaƴana ga babban limamin masallacin kaab dake garin maka wato *SHEIKH ALIYULLAH DAWOOD*
Itama jaddern ɗurƙushe takai ƙafafunta ƙasan tana meyin sujjadr sukr, da jan kafa kowa ya isa ga kowa suna wani kalan ƙanƙame junansu kuka da dariya na kwace musu a loƙaci guda. Ɗago kanta queen lajja tayi tana sake duban biyunin tata sai kuma ta sake fashewa da kuka tana sake ƙankameta cikin muryan kuka ta shiga faɗin.
"ALHMADULILLAH! ALHMADULILLAH lallai godiya ta tabbata ga Ubangijin da ke bayar da kyauta ga bayinsa ba tare da duba cancanta ko matsayin su ba a duk sadda yaso, godiya ga Ubangijin da ke ruɓanya ƙofofin rahamarsa ga bayinsa, godiya ga Ubangijin da ke wanzar da farinciki ga zuciyar kowacce halittar rai me numfashi, godiya ga Ubangijin da ke fidda matacce a cikin rayayye,godiya ga ubangijin dake raya rayayye a cikin matacce! haƙiƙa cikekkiyar godiya ta tabbatane ga sarkin da babu kamarsa sarki buwayi gagara misali. Sarkin dake juya dukkan al'amuransa a sa'ilin da yaso. Shukar nan dai da ba'aso ta ruɓanya ba ubangiji yayi alƙawarin seta ruɓanya koda ko ba daga naki tsatson bane Allah yayi alƙawarin se jinin Sheik Aliyullah dawood yayi rayuwa a masarautar nan kodan dattin zunufin da aka jima ana aikata da ruwa me tsarki tsarkakken ruwa"
Queen lajja ta faɗi tana me sake kai goshinta ƙasa.
"Bare ma harda naki jinin cikin wanda suka ruɓanya sukay yabanya a cikin Ashaan mention! Gana nan HASSAN AL-HASSAN ASHAAN shiɗin gudan jininane seda ya huɗa cikin jikina kana ya faɗo duniyar, daɗi da ƙari harda ma harda tukwicin tsarkakkun ƴaƴa dama jikoki"

Chakk ta tsaya sakamon sanyin idaniyarta wato AK daya sarƙafo hannuwansa cikin nata cikin wani kalan mur da face ya furta "Pls duk wannan ba yanxun ma HASKE'n EMAAR's" gashin kansa ta shafa tana me leƙa bayansa Meerah dake ta wani ɓoyewa a bayansa ta kamo nata hannun tana jimƙewa dana AK da natan wasu hawaye masu zafi da sanyi na zubo mata.
"A cikin wannan duniyar har gaban abada kune hasken haske! Kune haske maganin ko wanne kalan duhu, ubangiji ya sanya ma aurenku albarka ya ruɓanya muku da zuriya ta gari nasan a yanzun banda matsala dakai tunda ita ɗin zabin kac......
Da sauri AK Ya toshe mata baki yana wani muzurai yana rarraba ido shi a dole ba zata kunyatashi gaban mutane ba, tattausan murmushi ta saki nasu na manya da sauri queen lajja da se yau take ganin meerah ta janyota tana rungumata sosae "AUTAR AHLI" queen lajja ta faɗi tana sake jin ƙaunar ƴar uwarta da ƴaƴanta biyu da ubangiji ya bayyana mata su duka a loƙaci guda duk wannan abinda dake faruwa sarki ash be sani ba haka ma sarki hassan wanda yana daga can inda yake daidai da shigowarsu AK tare da JADDER'N ASHAAN cikin masarautar yaji zuciyarsa ta wani irin bugawa tare da motsa may da karfin da seta ya tashi zaune daram. "AH!MINHR!" ya faɗi yanajin zuciyarsa na sake motsawa sosae akan muradi da kuma ɗokin ganin Mahaifiyar da sedai ya ganta ta cikin woya. Mahaifiyar da besan daɗin taba, mahaifiyar da aka rabashi da ita ba tare dako numfashinta tare da ɗumin jiki irin na ɗa uwarsa an barshi yaji ba.
Jinsa yay ƙaƙare yake da son ganinta amma kuma komai ze tafine yadda aka tsara ɗin, don haka ya danne duk wani shauƙi da son ganin *AH!MINHR* ɗin nashi zuwa wayewar gari. Kishin giɗen da yake ya koma yana dafe setin heart nashi don jin yadda take may taka da luguɗe harda lillisa.


Queen lajja ce ta mike tsamm tana nufar gaban deep frigde ɗin ploor'n, ruwa me sanyi ta ɗauka tana yayyafama Moh wani dogon numfashi ta kawo tana tashi a zabure. "Ina!!!? Wllh hakan bame faruwa bane har gaban abada, nariga na gama da wannan babin koda ace JADDER'N ASHAAN ce tsaye a gabana dole zata kasance cikin hali na hauka bare ma nasan hakan bame iyuya bane! Haba ni wllh se ma yanzu na tuna ashe fa mafarki nake Hmmmm" taja ijiyar zuciya tana me sake faɗin "Kaidai wannan yaro uwarka ASIA da ubanka ASAAD basu iya haihuwa ba se kuma ta shiga lalabumen neman Inda jaddern ashaan ɗin take don itafa tun waccen ranar se yanzu ne komai yake dawo mata na inda ta tafi wurin jaddern ashaan ɗin mahboob kuma yabita, to tana faɗuwar nan yasauri ya soka mata allurar mantau ta tsahon wani loƙaci kawai data buɗi ido ta ganta ba zata iya tuna kome ya faru ba. Shine dalilin da bata ko sake tunawa da taje ɗaukar jaddern ashaan ɗin ba se yanxun.
Wanda kai tsaye hakan umarnin mahaifinsa ne ASAAD EMAAR's wannan shine tafiyar waccen ranan da muka shallake kenan.
Jindai har yanzun hannunta be kai inda take saka ran bane ya sanyata buɗe idanunta. Tarrr kuwa se akan jadern ashaan da zuwa loƙacin take zaune kan wata cuisine sofa fara. Sake mitsitstsike idonta tayi tayi don ganin kamar ba daidai yake bata ba.
"Ganinki rass yake Jiddoh! Baki sami raunin gani ba tabbas ni *EASHERH SHEIKH ALIYULLAH DAWOOD* {JADDER'N ASHAAN} ce zaune gabanki cikin rai da kuma ƙoshin lafiya, da buƙatar yanzun kam kije ki huta don nima barci nake ji"
Jadderh tayi maganar tana me kallon AK. Shima inda meerah take ya kalla sake shigewa jikin lajja tayi, ita kuwa cike da irin abin nan na jika da kaka ta turota tana faɗin "uhummm nan kike woni maƙale min ina nan kika bi mijin naki kuka guda kika bi kika ɗaga ma baiwar Allah hankalinta" sake lafewa jikin queen lajja'n tayi tare da turo bakinta gaba "To ai naga saceni yayi kunsan jikan naku ya ƙware wajen kizmashin mutane" tayi magananta kai tsaye tana sake ƙanƙame hannun lajja don wllh ta rigada ta rantse ita da mutumin nan se gani se hange se gani daga nesa kuwa.
Jadderh ce ta kamo hannunta ana lajja tana zaunar da ita daga gefenta tana me faɗin. "Ni taho wurina kyale anush laj tare dake zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login