Showing 54001 words to 57000 words out of 78068 words

Chapter 19 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1285

a call again badon komai ba sai dan ya tabbatar da lafiyarta,video call kuwa yadda suka maida shi kamar cin abinci yafi musu wuya, duk kuwa da cewar muna a tare ne a cikin wannan masarautar dai.
Hakan da yay min ne yasa naci alwashi ramawa akan ita abar son nashi daya fifita akaina, wannan shine silar da yasanya komai yake faruwa na reni Hassan tun daga wannan ranan amma koda da sau ɗaya ban ɗaba jin soyayyarsa. Na rayu ne da tunanin idan ya girma na wulaƙantashi. Hukuncin kakarku shine kuma ya biyo ta kanku na ɓatar da babbar ƴar Hassan wanda ni naɗauka itajin jininsace. Ashe ba haka bane tshohon munafurcin uwarsa Jadderh ya kowa ta hanyar ɓoyemin gaskiyar lamari, nice nan nai sanadin barin Yasmine daga cikin wannan duniyar, (UWAR ADEENERNERH) wacca bayan mutuwar tane sarkin kano ya sake bama Hassan auren ƴarsa Wato jinin mayu (MARYAM) kenan mahaifiyarsu AK da ZAID. ni ce na kasheta da hannuwana kamar yadda na kashe kakanku ni kuma mijina da hannuwana, bana bama kowa aiki nidai karin kaina nake aiwatar da nufi na akan mutum ba tare da samun saɓani ba. Sai dai Ashe nima loƙacin ina ɗauke da nawa cikin ban sani ba.....

"ki ka gyara a wasu zan tukan naki moh cikin tsohon bafaden abaa dai....
Suka jiyo muryar *ME MARTABA SARKI HASSAN AL-HASSAN ASHAAN* wanda yake tsaye daga bakin ƙofar shigowa. A kausashe ta kai dubanta tana nuna shi da yatsa tare da faɗin "Kulll ba'a katseni idan ina kan magana ta"
Ta faɗi tana me ci gaba da faɗin.
"Tun daga loƙacin dana fahimta ina ɗauke da cikin dake jikina nima se nawa hankalin ya kwanta amma kullum kwanan duniya da tunanin yadda zan ɓarar da cikin jikin wannan la'antacciyar nake" ta faɗi tana nuna Jadderh.
A kausashe AK ya miƙe tsaye tare da watsa mata wani kalan mugun bahagon kallo na zakici ubankine. Kafin a zafafe ya furta, "Shedar ke ɗin ba komai bace face dabba. Ki sani kowa yana iya zuwa yai farauta! Amma ba kowane wanda ya iya farauta irinta damisa ba!!!.... Shi kaɗaine wanda aka aifeshi da tambarin farauta a cikin zuciyarsa!.
"Kaiiiiiiiii!"
Moh ta dakama Ak wata uwar tsawa tana sake juyawa ta fuskanci moh
"Amma duk da hakan ban samu kwatankwacin kulawar da jadderh ke samu daga wurin kowa ba wannan dalili ya sanya na haɗa kowa da kowa na musu kuɗin goro kowa na zana shi a matakin da nakeson ya kasance. A haka cikin irin wannan halin Jadderh ta fara nakuda me zafi sosae wacce ta ɗauki kusan Kwana tara tana yi nima kuma a cikon kwana na goman na fara tawa nakudar ɗakinta na kallon nawa haka na haihu na barta cikin halin ciwo da fita a hayyaci.
Yara biyu na haifa duka maza masu masifar kama da juna sedai ɗayan bezo da raiba ina haihuwa norse bata jima da gama gyaraniba na jiyo kukan jariri a ɗakin jadderh, zuciyata a kaikashe na nufin ɗakin da niyar na kasheta na kashe abinta ta haifa sedai kallo ɗaya nama yaron naji ya banaso na kasheshi, inason ne na reneshi tamkar mahaifiya a gareshi daga baya kuma na bayyana masa ba nice mahifiyarsa ita kuma uwar na saceta bayan na maida mata ɗayan yarona da dama bezo da raiba. Ɗaya daga cikin amintattuna na kira nasa aka sace min ita xuwa cannn wani gourdsroom da aka denan shigarsa kwatata saboda irin abubwan da ake gani a cikinsa na al'ajabi.
Babban tashin hankali iyaka tashin hankali waɗan nan family sun shiga barinma dangin jadderh da kuma shi me martaba marigayi. Tun yaran na jarirai na gane baya ɗaukar hussein se hassan.....
"Dama kin taɓa ganin mutum yaso jinin daba nashi ba irindai soyayyar ɗa da mahaifi, ai wannan daban take Allah da kanshi ya faɗi hakan hajiya jiddoh"
Wanna karon muryan jaddern ce ta karaɗe ploor'n. Kana taci gaba da faɗin "Dake a tunaninki soyayyar da uba ze nuna ma ɗansa zeyi kwatanci da wacce ba shine jininsa ba bare ma mu jininmu da duk inda yake a tafashe yake tafarfasa yake tamkar ruwan dake watstsara a tukunya, kuma ki sani tun daga loƙacin da kika shigo naji shigowarki hakan yasa nayi saurin kunna record a wayana har kikai komai kika gama komai na naɗe a cikin nan"
Moh ta faɗi tana ciro wata tsohuwar waya irinta ɗa can ɗin nan ci gaba tayi da faɗin, "A naki banzan tunanin ke kadaice me wayo to ki sani Ashaan sai daya saurara komai dake cikin nan" ta sake faɗi tana nuna mata wayar still.
"Fahimtar danai kamar akwai abinda ya sani dangane da hakan yasa na kawar dashi ba tare da anyi zargin komai ba, ni da hannuwana na sanya pillow na kashe shi tun yana shure shure harya dena. Kinga kenan ko a nan nayi tunani me ƙyau"
Moh ta faɗi tana wani gyara zamanta mandood tsaye daga gefinta. Kana taci gaba da cewa "sedai bansan sanda ke kanki kika rayu har haka ba, shin ina allurar da ake miki?, ina likita oxwa yake? Shin tayaya kika tsirane ma wai Jadderh? Bayan duka uban matakan tsaron dana zuba Niki? ......
cikin wani kalan izzar daya gama mamaye jinin jikinta Jedder'n Ashaan ta furta.
"Ta hanyar gwarzon namijin mazaje Jarumi a filin daga namijin damisa ne ƙwaya ɗaya tak daya tari gungun mayaƙa majiya ƙarfi masu ɗauke da manyan makamai!, TAKWABI Ɗaya tak da zaiyi zarra ya kwantar da dubban takwabban da suka zagayeshi sukai masa ƙawanya, har gaban Abada *ABDOUL-MALEEK HASSAN AL-HASSAN ASHAAN* shi kaɗai ne jarumi ɗaya tak a illahirin Masarautar EMAAR's damisar da aka haifeshi badon ya mutu ba sedan yaƙar maƙiyan papansa, shine shila buɗe ko wanne sabon babin taɓarɓarewar rayukarki Jiddoh.
Kince naci amanarki zanso ki tuna ni dake waye yaci amanar woni! Kodan dama masu iya magana sukance bishiyar da aka dasata domin Allah tafiyin Rassai. Karki manta keda iyayenku duka cin arziƙine ya kawoku ƙasar makka a haka har allah ya haɗamu daku sanadiyyar aikinku. Na ɗauke ki tamkar ƙawa ƴar uwa tamkar Lajja haka na ɗauke ki, Nawuce miki gaba har nasa Pappienmu ya sanyaki school boko da arabic. Min tashi dake tamkar ƴan uku rana tsaka bayan gama sanin sirrikanmu da kikai kika rabani da Ashaan a loƙacin ba shine sarki ba. Kin aauremin boyfreind nawa na haƙura na ƙyaleki, a rayuwa kinyi min abubuwa da yawa duk na dauke ido na toshe kunne amma duk acikin wannan labarin dai ni ce maciya amana? jiddoh"
Jadder'n ta faɗi tana me duban moh ɗin da jikinta ɗauki rawa tun a farkon kirarin da tama AK.
Tabbas idan tace bata ji tsoro ba to kusa tayi ma kanta ƙarya, don wani kalan tsoro ne ya lulluɓeta nan abubuwan da suka faru shekarun baya suka shiga dawo mata daki daki, take tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta, sakk waɗan nan kalaman sune furuci na ƙarshe daya fita daga bakin Ashaan a wancan loƙacin sedai banbanchin suna kawai da aka samu A maimakon *ABDOUL-MALEEK* shi *HASSAN AL-HASSAN ASHAAN* ya ambata tabbas iri ɗaya ne maganar ko tantama batayi.
Bata gama dawowa a hayyacinta ba ta sake jin muryan jadder tana me ci gaba da faɗin, "Daga ƙarshe ma ƙasar na bari na koma wurin Nenne Alayya bnt zubr da zama a ƙasar luponia. Amma dake bawa be isa yanke hukunci ko zartat da abinda Allah beyi niya ba to kuwa wani bawa be isa aikata shi ko hanashiba, kwasan se ɗaurin auren mu kikaji. Rabon se wannan me gurbin tazo tayi nata yaryaɗon kana bi diddiginta zataci albarci, tunda dama shi haka me cin arziƙi yake duk inda yake da wuya beci amana, shi yasa temako yay ƙaranci, sabo da irinku kuke ɓata na gari duka kusa a hadeku a muku kuɗin goro.
Wanna tsayayyen namijin da kika gani gabanki shine maganin kukana dama duka sauran alhlin Emaar's don haka go dn way tun kafin loƙaci ya ƙure miki.

ƙattan mazaje ne guda Uku majiya ƙarfi tsartsaye a bakin Kamfacecen parlor'n na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta kaka gida hannuwansa riƙe da manyan bindugu, A hankali a kuma sanyaye ya fito cikin kamala da kuma nutsuwa kallo ɗaya zaka may kaji ya shiga ranka farat ɗaya, ASAAD EMAAR's kenan shine ɗa na biyu a wurin moh jiddoh. Kuma shine halayyarsa da nata suka sha ban ban tun daga yarinya, tunda ya fito wannan mutane ukun suka mara may baya.
Kai tsaye waɗan nan masu ɗamarar ya fara sallama yace musu suje kawai wannan ɗin aikin cikin gidane kuma zasu magance matsalar da kansu. Amma suka ce dole se sunga moh suna shiga moh ta saki wani kalan kayataccen murmushi tana me furta, "Bismillah ku ƙaraso ga mai laifin ma se kuyi ramm dashi!"
A maimakon taga sun kama Ak ɗin sema wani kalan zaro idanuwa da sukai duna sara masa. Jikin kowannensu na rawa don magana ake *_A general Soldier's nd police Inter pool *_Special anti terroRism squad_*
*_Security squad group_* magana ake ta *~💸 THE BILLIONAIRE 💸_ABDOUL-MALEEK EMAAR's KUWAIT_* wanda kafff duniyar ta sanshi sedai ba fuska da fuska ba.
Kallon kallo aka shiga tsakanin mutanen ɗakin da hannu AK ya musu alamar su fice a ploor'n. Seda suka sake sara may da wani irin salo suka juya suna barin masarautar ma baki ɗaya.
"Da naso daga ke har ƙasusuwan bayan naki zan haɗe na ƙarasa ɓallewa amma sedai cin zarafin mutum ba'a cikin jininmu yake ba, Amma sedai kin ɗanyi kuskure kaɗan mutuwar Grandpaah ba'a hannunki take ba dama can Allah yayi a ranar zebar duniya donke baki isa kisan merai ba"
Ta cikin systerm ɗin da jearah ta ƙira Zaid video call suka jiyo maganar zaid ɗin tamkar daga sama. Ak ne ya dubi zaid daga inda idanunsa yaɗan lumshe tare da buɗesu cikin wannan dakakkiyar muryan nashi ya furta. "Ka taɓa ganin inda mutum ya aikata lefi ba tare da an hukuntashi b@!?. Dole zasu girbi abinda suka shuka da hannuwansa zaid se sun ɗanɗani rayuwa a inda Haskena tayi,ni ban yafe ba ko kowannensu ya yafe dole ni na hukuntasu"
Shigowanta kenan ta furta "Ba kaine ya chanchanta daya hukuntasu ba Garga! Dama duk inda gidan sarauta yake gida ne mai ƙunshe da halittu iri daban daban, wanda ido ka iya gani dama wanda idanuwanmu bazasu iya gani ba, duk inda gidan sarauta yake babban gida ne wanda komai ka iya faruwa cikinta, dik yanda aka ce maka akwai mulki da sarauta toh zai matuƙar wahala ace babu zalunci sai waɗanda Allah ya kiyayesu!. Wasu mutanen sukan nemi mulki da sarauta ta duniya koda kuwa zeyi sanadiyayyar rasa ransu. wasu mutanen babu abinda bazasu iya ba domin kawai suyi mulkin. wanda wasu mutanen ma shi wannan mulkin shine zeyi sanadiyyar shigarsu wutar jahanna. Annabi muhammad (S'A'W) yace mana duk wanda aka be wani muƙami koda kuwa na monitor ne a cikin class to tamkar an ɗauki mukullaine guda biyu an ɗamka masa a hannunsa, wato mukullin gidan wuta dana gidan Aljanna idan kayi alhairi kanka idan sharri ma kanka kaine ka zaɓa mukullin ƙofa ɗaya a cikin wannan mukullan inma *WUTA* inma *ALJANNAH* don me yasa mutane bazamu ringa tuna lahirarmuba a kullum kwanan duniya babban burinmu shine mu samu duniya a hannunmu don haka duk abinda mutum ya aikata kunyar kansa kuma ka barshi da fitowar rana da faɗuwar tama wani babban jafainne, Allah kaɗai Allahu samad shine maganin duk wanda yake jin yakai ya kuma fi ƙarfin kowa to kuwa tabbas Allah shine zaiyi maganinsa ya kuma ji tsoron ranar da zasu gamu ranar da babu gudu babu ja da baya kowa ze amshi sakamakon abinda ya aikata anan gidan duniya. Wasu rashin wayo da aiki da hankali kan jawo su faɗa tarkon mugu! Sabo da sammm Shi mugu idan ya cika mugu ai baya bayyanawa duk mugun da ya baiyana kanshi bai cika muguba. kuma alhamdulillah Insha Allah sunyi ta bayyana kenan bawai iyaka moh ɗin bace..."



Oum tayi maganar idanunta akan AK
Tsitttt kowa yayi a ploorn inda jikin wasu daga cikin masu baƙar zuciya amma tasun bata fito filiba yay sanyi ga son cutatar da ƴan uwansu, wasu kuma ko gezau dama jikkunansu beyi ba bare suji abinda aka faɗi ɗin. Asaad Emaar's ne ya dafa shoulder na Ak kai ya jinjina may alamun yabi yacce oum ɗin ta faɗi. A fusace Moh ta miƙe tsaye tare da furta "Kenan kinyi nasara a kaina kenan jadderh?"
"So kike na sake maimaita miki da baki cewar naci NASARAR ne? Dan nasan ke a karan kanki kinsan cewar naci nasarar! Tunda gashi GUDUN ƘADDARAR da kikay tayi tazo ta sameki har gadon baccinki, kuma gashi kin buɗi ido kinga masarautar Emmar's cike take dammm da JININ JADDER'N ASHAAN ɗin da baki so ba kuma dama ai ɗaurin talala Ubangiji ya miki kuma ki iya bakinki don har yanzu akwai wani babban sirrin da ban bayyana shiba daga gareki! Idan kuma kikace zakici gaba da wannan haukar to kuwa tabbas zaki sha ƙasa, ki sani Inda ba yashi nan ake taƙaddamar kokawa. Kuma shi ramin ƙarya kurarrene in kuma zubawar kikeso ayi to mo zuba mu gani!!!." Jaddarh tayi maganar tana mikewa da shirin palon ploor'n baki ɗaya.
"Wllh baki isa ba. da baki mutu bama yanzu ciwon zuciyar mashayen jikokinki zay karasa kasheki Jadderh, don wllh ba'ayi mutumin da zaici nasara a kaina ba ni jiddoh kuma harya zauna lafiya ba'a haifeshi ba, dagake har jikan naki da kike ganinsa kamar wani malaikan mutuwa senaga bayanku kwarai"
Cakkk jadderh ta tsaya tare da juyowa kafin ko tayi wani yunƙurin yin magana jesrah charaf ta rigata. "Ashe baki sadudaba jiddo wai bakiji abinda tace miki ba kar allura ta tono garma fa ahammm"
Zaram Hussein da ya dade da zama statu a wurin ya chafki hannun jesrah. Kaɗe hannunsa yajj anyi Ak ne tsaye a kansa. "Mafi munin kuskure da zaku sake aikatawa shine ɗayanku ya sake koda yunƙurin taɓa ɗaya daga cikin family nane wannan shine kuskure mafi girma da muni da zaku zake aikatawa" yana faɗar hakan ya wancalar da hannun hussein ɗin yana barin wurin baki ɗaya domin a halin da yake ciki jiyay jininsa na wani kalan mugun tafarfasa ta ciki.

"Duk bana bukatan wasu sauran maganganu haka nan, mashaya kuma da kike magana karki manta mahaifinki tirela² yake siyarwa. Kuma ganan a karkashinki suma da kika zama sanadin yinsu Insha Allahu zasu dena da ikon Allahu ahaad"
Daga haka tasa kai ta fice gaba ɗaya daga ploor'n wani shegen murmushin gefen baki lajja tayi tare da tsayawa a gaban jiddohn, "Kinji ai abinda ta faɗa miki ko a yanzu itace tayi nasarar lashe wasan da dama itace hasalin ƴar wasan. Dan se a yanzu na tabbata lallaie tafashashshen jinin mu shike yawo a jikin duka wadan nan family. toya kika gani? A dama da take ita kaɗai bakiy nasara akantaba bare yanzu da take zagaye a jikin matasan zakuna masu farauta, Idan kuma kikace zakici gaba da waɗan nan abubuwan to tabbas *KAREN BANA* ne zeyi maganin zomon bana idan har baki manta ba ai nasha faɗa miki haka dama moh...
Daga haka itama lajjan tasa nata kan ta fice haka kowa ya shiga ficewa, ana barin moh da iyalanta Al-hussein kuwa tunda moh ta fara bayaninta ya zama mutum butumi, don besha makirci da rashin imanin mahaifiyarsa yakai har haka ba, besha zata iya kisan rai koma yace rayuka ba. Kenan itace ta kashe musu mahaifinsu? Ita kuma mijinta lallai sema yaji duniyar tana ƙarasa fice masa akai. Kallo ɗaya umaymah ta jefama moh ta ɗauke kanta tana ficewa takai ƙofar ita kenan tajiyo muryan moh na faɗin.
"Kema saura ke tunda naki asirin be tonuba! Na tabbata ke idan sukaji kene wacce take poisoning na mahaifinsu to ke saidai hukuncin rataya kuma umaymah. Cakkkkk ta tsaya tare da juyowa "Ke kanki kiji da wutar gabanki keda sakaran ɗanki mara amfani idan ma kin sake buɗar ido kin ganni a masarautar kenan. gadai jikanki nan mandood na barmiki yasmine kuwa dama jininku bace jinin turawace don daga kan mandood ya kasa bani wani cikin duk kuwa da yadda nake maitar haihuwar kodan na gaji dukiyar masarautar nan. Daga loƙacin da kika riga kika bayyanamin cikinki tun daga loƙacin na fahimta nayi kuskure na shigowa wannan masarautar ta hanyarki, tunda kema karerece a karere kike keda jikokin naki, don haka banga amfanin zama da marasa amfani ba nikam na ƙara gaba dama wannan ranar nake jira kuma tazo don haka na tafi mebi forever mebi kuma not...." daga haka taja hannun yasmin (Dolly'n Salman😂😁) suna barin palon suma.
Moh, Al-hussein, mandood, Assad,Asiaa (Matarsa), mahboob, duka da kallo suke bin bayan Umaymah jikin kowa a mace a sanyaye.
Wasu zafafan hawayene suka kwaranyo daga idanun Alhussein, kenan duk zaman zamanin nan amfani kawai mahaifiyars da matarsa sukai ta hanyar cutatar da waɗan nan bayin Allah?. Lallai seyau ya sake yarda tuggun mace duk ƙanƙarta ba kanwar lasa bace, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!!!" ya shiga maimaitawa Assad ne yay ƙiran woya daga bakin get yace duk wanda suka gani karsu barshi ya fita ko waye kuwa.
Daga ɓangaren umaymah kuwa uban tulin dukiya da suka take a wasu manyan trolly lugage suka ɗiba tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login