Showing 18001 words to 21000 words out of 78068 words

Chapter 7 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1279

tarun mata "kuma fa kasan idan har bada chocolate naci ko miye ba ba zama yake mun a ciki ba zanyi aman sane Aiyn"
"Mrs Aiyn dawo nace badai chocolate bane ganan wani nazo miki dashi"
Ya faɗi yana tashi ya dawo da ita yana zaunar da ita kan ƙafafunsa...
Shida kansa ya bata abincin duk lauma bayan laum saiya haɗa mata da wannan chocolate ɗin don haka shine wanzuwar zaman lafiyansu su duka tunda ta sami cikin nan kuwa.
"Sannu da zuwa Aiyn"
Ta furta bayan ta gama ƙoshi abinta tukunna. "Uyummmm saida kika gama cika ciki kana kika tuna damin sannun really?"
"To ai zuwa loƙacin ko kallon gabana banyi sosae ne aiyn"
Ɗan shafa gefen fuskanta yayi yana faɗin "Babyn Aiyn rigima"
Haka dai suka shashance abinsu aikin dabai koma ba kenan.
★★★
Ta buɗe baki kenan da niyar sake wata maganar, amma maganar da maƙale a bakinta sakamakon tozali da idanuwanta suka mata da merrah.
Wani irin tsuma tare da yankar zuciya ta tsinci kanta a ciki da kallon meerah ɗin, jinin jikinta kuwa a take ya shigawani irin hautsina mata wanda hakan kai tsaye ke tabbatar mata da tafasa jinin jikinta yake. Ido Oum ta kafe Mah dasu domin ganin reaction nata, Sammm ta gaza janye idanunta akan meerah ɗin da ƙyar ta samu ta fusgo kalmar
"Easherh? DIDINA!!!"
Da sauri itama merrah ɗin ta juyo da kanta zuwa inda tajiyo irin muryan Anne'nta masoyiyarta sakk. Itama chakkk ɗin ta tsaya tana kafe matar da ido babu wata tantama zata iya rantsewa wannan fuskan Anne'ntane wllh. Saidai ita wannan ɗin tsantsan hutu da jin dadi daya gama huda fatar jikinta da kuma tsananin hasken fatar ta.
To amma wannan kamannin ai sunyi yawa kuma dai tasan Anne'nta bata da alaƙa da matar dake tsaye a gabanta. Domin kuwa tasan basa da alaƙar gari ɗaya ma bare kuma ta jini.
Hannuwanta suna rawa ta matso ga Merrah ɗin tare da shafan fuskanta cikin wani irin raunin murya ta furta.
"Irin kamar ki ɗaya da DIDINA! saidai a yanzu duk inda take nasan tafi haka zama ta iya haifar yake"
Hannunta tasa tana kifewa saman na matar da ganinta ya bugar mata zuciya, wllh zata iya rantsewa da'@ Nig taga matar nan babu abinda zai hanata kamata tace itane mahaifiyar Anne'nta duk da kuwa cewan wannan matar baici ace ta haifi ya Annenta ba.
Muryanta yana rawa itama ta furta "Da'a ce a ƙasarmu na ganki babu abinda zai hanani cewa kene mahaifiyan Anne'ta"
Saurin rungumeta Merrah Mah tayi tana furta "Allahu ahad!! Allahu ahaad!!! Wllh irin muryan Queen Lajja na ce dake"
Kamar daga sama taji Mah taji muryan Oum tana faɗin.
"Taya barewa zatai gudu ɗanta kuma yayi rarrafe ita ɗin JININKICE! Ƴar gidan Easher'nkice RAZEERNERH"
Da wani irin bala'in ƙarfi ta sake rumgume Merrah ƙa ƙam a jikinta tana fashewa da wani mugun kukan daya kusan sarƙe numfashinta.
"A ina? A ina MARYAM? Kar dai kice min itane MATAR ABDOUL-MAKEEK? Inkuwa hakane lallai Allah da girma yake kuma shine buwayi gagara misali shi yasa tun a ranan data sanwo ƙafanta cikin wannan gida bugun zuciyana ya sanja, Sanyin da nakeji a tare da Easherh na wllh shi naji tun a ranar"
Sai kuma tayi shiru tana ɗan ɗago fuskan merrah idonta bai sauƙa akan komi ba sai kan wani ɗigo da yake kan gefen wuyan merrah ɗin wanda yake tamkar zanen tatto.
Sake rungumeta tayi sai kuma sukayi luuuuuuu sakamon sumewar da Mah ɗin tayi.
Merrah kuwa dama bata san mike faruwa ba ita dai tasan mafarkine kawai take wanda a cikin mafarkin jinta da ganinta suka jima da shuɗewa, shi yasa ma loƙacin da sukayi bayan itama tabi ta kawai a tunanin ta duk a cikin mafarkin ne
Kafin takai ƙasa Oum tayi saurin tararsu itada Jesrah da shigiwarta kenan room ɗin Ak din don ganin Pa'pa'nta. Dawowarta daga wurin aiki kenan don Zaid ne ya isheta akan tayi maza ta dawi zata may wasu abubuwa kafin wannan kayan fushi da bacin ran ya dawo gidan wato AK.


Tana zaune bata san sadda ta miƙe tsaye ba zumbir tana furta "Wacce Easher'n ?"
Ta tambayi hadimar nata wanda dama shigowarta kenan ta dawo daga fitar da tayi tun da sanyin safiya. dog year rigace a jikinta abaya wacce aka narka manyan kuɗaɗe kafin a siyeta ,saikuma gyalenta data yane kanta sai jakarta da kuma takalminta suma duka designer ne.
Damƙar wuyanta tayi tana me sake faɗin"Nace miki wacce Easher'n?,ba tambayarki nake bane wai?"

Ta faɗa cikin ɗaga murya wanda hakan saida ya razana Hadimar daganin yanda yanayin Moh jiddon ya sanja loƙaci ɗaya.
"Umm ummm dama dama.....
"Ummm dama me ki buɗe baki kimin magana dama me?
Ta faɗa tana sauƙe wani irin wahalallen numfashi mai nauyi haɗe da dunƙule hannunta A lokacin inka ganta zaka kasa gane inda yanayinta yake,shin baƙin ciki take ji kokuma tsoro da fargaba Ko tashin hankali ne?
"Ke beenanxeer wai ko kunnuwanki sun daina aiki yadda ya kamata ne na dawo miki dasu daidai.?"
Haka Moh Jiddoh ta sake rikirkita beenah cikin rawan jiki da dama yawanci a kawoma wani gulman wani kake cin ubanka jikinta baki ɗaya bari yake ta buɗi baki cikin sarƙewar numfashi ta furta.

"Wllh da gaske ne nazo wucewa ta cikin balcony ɗin Oum jesrah naji tana zance da dukkan alamu ma waya take yine, shine fa na lafe naji tana cewa ƴargidan Mah data batace ta bayyana amma anan ɗin ba ita bace ƴartane ma wacce aka ɗaurama Boss Aure da ita wai Merrah!"

Wani irin wulgar da beena ɗin moh tayi duk kuwa da cewar jikin tsufa gareta amma kai dama kallo ɗaya zaka mata kasan cewa irin tsofin najadun nan ne maƙirai. Wata sakakkar ijiyar zuciya ta sauƙe tana jin duniyar ma baki ɗaya na juya mata, kanta kuma na neman juyewa zuwa na masu ta6in hankali.

Wayanta dake gefen Royal chiar ta ɗauka tana dannawa da alama wani ko wata take nema a wayar cikin gaggawa.
"Hello Hussein? Maza ka bincikamin yanzu shin da gaskene matar da aka aurama Aboul-maleek aure da ita ƴar Easherh ta bayyana kokuma watace ne daban?, ina son bayanai yanzu yanzu sannan ka tabbatar babu wanda ya zargeka don nasan halin haukarka idan ya motsa kana iya kwa6emin aiki"
"To shikenan Moh yanzu kuwa zan bincika ɗin"
"Idan har ya tabbata haka ne to da akwai gagarumar matsala! don shirin da mukayi tsawon shekaru gaba ɗaya wargajewa zayyi,dan haka ka taka tsantsan ka ganomin komai, Amma ta wata hanyar da sauƙi domin idan harya tabbata Yarinyan itace, kuma ita aka aurama wannan shegen kaga kenan babu Aure tsakanin su, tunda da uwar yarinyar dashi tantirin uba ɗaya suke."

Daga tacen Hussein ɗin yaja ijiyar zuciya hankalinsa na ɗan dawowa jikinsa sai kuma ya furta.
"Wai to garin ya haka ta faru a bazata taya ma zakice haka duk shirin da mukayi na 6atar da Ita a duniya saida ta dawo? mtswwww aikin banza nikam ba samm ban yarda ba wllh moh"

"Karka yarda dan mataccen ubanka! Nace karka yarda hussein a kana kallon yadda abubuwan dai suke kwa6e mana a cikin ƙaramin loƙutan nan"
Kitttttt ta datse kiran tana wani irin runtse ido tareda jijjiga kai Kai tsaye Center table ɗin tsakiyar ɗakin ta fasa raga raga tana kuma tsaye, zuciyarta na neman faso ƙirjinta tabbas ta yarda sai yanzun abubuwan da suka faru a wancen ranar komai ya dawo mata a kuma ranar ne ita yarinyan ai tazo, kana a kuma ranan tayi poisoning na me martaba.
"Wllh bazan yarda komai ya kwa6e min da wuri haka ba! Meyasa za'ayimin haka? duk Uban tsawon waɗannan shekarun dana ɗauka kenan a banza wllh bazan ta6a yarda nayi faɗuwar baƙar tasaba dole ki mutu yau _Jaddern Ashaan_ Duk kece sanadiyar komai kene kika shigo cikin rayuwata kika 6atamin ita wllh na tsaneki Na tsaneki Keda zuriyarki tsanar daban ta6a ma kowa ba a duniya"
Tana faɗin hakan ta miƙe ko kallon gabanta batayi babban burinta kawai taganta a gaban jaddern Ashaan ɗin. Taku take me kama da sassarfa idonta har bata gani sosae zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
Haka ta ringa shiga tana fita ta cikin wasu 6oyayyan hanyoyi wanda haka har saida takai kanta ga wani surƙuƙun bakin ɗaki me tsananin duhu sosae. Wanda dattin ƙura da yana baki ɗaya suka baibaye ɗakin, da hannuwanta tayi amfani wajen fara share gefe da gefen tsakiyar ɗakin, take wani wuri da aka masa alamar zEr0 ya bayyana. Numbobine tsoffi irin na da ɗin nan suka bayyana a jikin wannan wurin bayan ta danna wata jar alama, numbobin da suka daɗe da zama haddattu akanta ta shiga daddanawa, a take tsakar tilen moples ɗin yaja gefe da gefe saiga wani da ɗaɗɗen gini ya bayyana kai tsaye ta shige ginin cikin ƙarƙashin ƙasar. Wata azabar shi kansa ginin wani ginin ne a cikinsa haka ba tare da tsoro ko fargabar komai ba ya faɗa dakin ƙarshen. Bin bayanta yake cike da fargaba mai cunkushe da tsoro,ita kuma ko waigowa bayanta bata yi kawai tafiya ta ke
cikin sassarfa ta ban mamaki wanda hakan yasa dole Mahboob fara haɗawa da sauri-sauri gudu-gudu dan
ya cin mata amma ina sai ƙara sauri ta ke harta shige cikin wani surƙiƙin dogon gini. Kai tsaye cikin dogon ginin ta shige shima ya mara mata baya
cikin sauri, yana shiga yaga ƙofa ta samu da kanta ta rufe gidan kai tsaye nan ta ke wani uban duhu ya mamaye
gidan baki ɗaya tamkar wata yayi nisa, Nan take hankalinsa yayi mugun tashi domin ko tafin hannunsa bai iya gani tsabar duhun cikin duhun ɗakin.
Kai tsaye inda Jaddern Ashaan take a ɗaɗɗaure ta nufa wani irin yankawa gabanta yayi ya faɗi zuciyarta na barazana wa gangar jikinta ta hanyar fasar kirjinta ta fito.
Cikin wani mugun tashin hankali da ƙinƙinar da bata san tana da ita ba sai yau ta shiga faɗin.
"Me me me za zan ga gani hah ha ka ni Hauwa'u?, komai ya gama ƙare min ɗin kenan dai ko kuwa yaya ya?, to kadai mutuwa tayi ta bushe ta zama wannan burbuɗin kasan?"
Ta faɗi tana me wawurar kasan da ta ɗan turu wuri ɗaya. Wata walƙiya taga ta gitta idanunta da wani irin hasken daya kashe mata idanunta sai kuma taji kamar an buga mata wani, Sai kawai ta tafi luuuuuu tayi ƙasa a sumeeee........



To masha Allah ai shikenan saimu gimtse anan ba?

Hhhhhhhhhhhh



Kai wllh nama rasa ta inda zan fara da tamboyinku da kuma yawan sharshinku mutanena.
Kawai dai muje zuwa game rabo za'a warware komai dashi.

*AMMEY LAYLERH taku ce*







*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

11&12

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

**☆✭ ★ You Are My Dream Come True _Meerah AK 😊🙃🥰😍_**

_MADINAH_

A ɗan tsorace Ash ya janye wayar a kunnensa wanda har hakan ya sanya queen Lajja dake basa gyaran kumba dago da kanta tana me dubansa a nutse.
"Lafiya Ashfuddern?"
Queen lajja ta tambayi mijin nata, kansa ya ɗan jujjuya mata yana faɗin. "Kamar dai kunnuwa sun ɗan sami raunin jine wllh Lajja, amma kar6a muga ji abinda ake faɗa! Daga lambar Lele Razeerh ne"
Itama jikinta na ɗan rawa ta amsa tana manna woyar da kunnenta tare da jin furucin da Oum ta sake maimaita mata itama.
"Kunnenka be samu raunin jiba Rahul hakane abinda kaji kuma daidaine"
Tsaye ya miƙe har jikinsa na ɗan rawa kaɗan bada yawa ba, "Bani phone na"
Ya faɗi a hanzarce. Bashi tayi kai tsaye number'n Zayeet Ash kai tsaye yayi calking.
"Ina buƙatar jet yanzu yanzu maza xuwa Kuwait Zayeet Ash!"
"Ko lafiya kuwa Abana?"
"Ba tambaya nace kamin ba aikin zakamin kona nemi woninka yamin?"
"Afwan Ya abana yanzu kuwa an gama"
Daga haka ya yanke wayan yana cewa lajja ta shirya yanzUn zasu tafi babu jirah. A take Zayeet Ash yayi magana da pilot ɗin dake driver'n nasu duk inda suke so yayi akan ya shirya tashi yanzu zuwa kuwait.
Babu 6ata loƙaci kuwa ya nemi izinin tashi 7 na magrib ɗin, 7:30 jirginsu ya tashi daga madina zuwa kuwait, tafiyan bame tsaho bace cannnn hakan yasa 8:50 suka sauƙa a masarautar kuwait. Kai tsaye Mah dake a sume suka fara gani tun a daren wacce har yanzun bata farfaɗo ba.
Ganin me girma sarki Ash a sallar asba ba ƙaramin kaɗa hantar cikin hussien yayi ba, amma sammm hakan be nuna ba ko'a fuskan shi saima gaisawa da sukai cikin mutan taka da tattako.
Daga nan masauƙi suka sake komawa ita kuwa dama lajja tare ta kwana da yarinyanta. Wacce sai a sanyin asubar nan ta farka da wasu surutai wanda ba masu ma'ana ba, Da kan lajja take a sake mata alluran bacci domin kwakwalwanta ya sake samun relax yanda ta kamata.

★★★

Ak tun a daren ranan oum ta sanar dashi abinda ya faru wand har kawo kwanan yau be ta6a ganin matar nashi ba, kasancewar sa6ani suke samu kuma ko zaid Merreh bata taba haɗuwa dashi ba. Hakan kuwa yama Oum daɗi domin kakaf labarin abubuwan da suka ringa faruwa tsakanin AK da MEERAH saida fulani ta bata labari wanda hakan shine abinda gafi rinjayar hankalin me marta, ganin duk faɗin duniyar babu mahaluƙin daya taba fira dashi bare batun bayyana kansa wa al'umma, amma ta sanadiyarta ya magantu tun daga nan me marta yasa aka ringa bibiyar masa duk wani motsin Ak ɗin tare da Merrah.
Bama iyaka labari kawai ake bashi ba daga karshe komai ake may video nasu har kuwa ranan data kusan faɗawa ƙasar benen nan, anan maganganun yarinyar da kamu kamanninta suka haska may wani muhimmin sirri da tarun abubuwan mamaki, tun daga nan ya fara neman duk wata hanya da zata sada shi da iyayen yarinyar. Saidai kuma kash a loƙacin daya bayyana sai yayi rashin sa'a don saura kwana uku bikinta ma a loƙacin, Harya fara shirin juyawa wani ƙaddarern lamari ya sake haskaka hasken daya fara kalla tattare da yarinyan Harkuwa hakan ya kaishi ga nasarar haɗa aurenta dana mara jin jikinsa.
Wannan kaɗan kenan daga cikin abinda fulani ta yankama Oum ɗin.
Ak kuwa cewa yayi yau zaiga ƙarshen fitsarar koma wace tada yarda harta amsa sunan matsayin matarsa. Hakan ya sanya kai tsaye ya nufi Sashen mahaifiyarsa duk da kuwa yasan cewarn babu kowa bangaren nata.
Kai tsaye daga yasan bedroom na jesrah nan ɗin ya nufa.
Fitowanta a wanka kenan domin tashinta kenan alluran bacci itama oum tasa aka mata,sai yanxun take farkawa hakan yasa tana tashi ta fara da wanka don tana son jinta Fresh off kafin ta zauna nazartan komai tunda kuwa xuw yanzun tasan ba mafarki bane ba kuma cikin gushewar hankali take ba.
Rigar wankane sanye a jikinta blue colour iyaka cinyanta sai farin towel data naɗe kanta a ciki. Wani mini kuma riƙe a hannunta tana tsane ruwan dake ɗiga daga fuskanta zuwa jikinta. Fararen santala santalan cinyoyinta tar dasu kamar wacce ake wankesu kullum da madara da zuma sai wani colour'n glowing suke. Sammm ita ba ma'abociyan son irin waɗan nan ƙananun kayan bace amma kuma tunda tazo ƙasar dole bata da za6in daya wuce hakan tunda bata isa ɗaura zani ta shiga wonka ba, yoma ina yake babu dama zani ɗayane kakaf kayan kuma tunda jesra daga dashi take amfani idan zatai wanka ta hanata sanyawa amma taƙi. Haka tanaji tana kallo ta ɗauke mata duka zanin harma da rigan akan hakan kuwa har ƙaranta takai wurin oum Amma ta bata haƙuri tace taci gaba da amfani da showel ɗin da kuma bathrobe dele haka take dannewa tayi amfanin dasu ba don taso ba.
Towel ɗin dake ɗaure saman kanta ta ware tana kaɗa kanta tare dayin hajijiya domin idan ba jesra bace a room ɗin bata wani amfani da na'urar busar da gashin kai, tafi gane ta naɗo abinta a showel kana ta karkaɗe abinta ta taje shi tas.
Sake baza gashin kan tayi tare da ɗagowa haɗi da ɗan turo baki gaba haɗi da faɗin "Jes kin gama dan.......

Maganan tane ya maƙale a maƙoshinta haɗi da wani irin zaro manyan idonta masu kalan madara da kuma na ƴan mayen nan. "Ya rabbi.! Ɗan dabar can dai anan?"
Harshen meerah da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri ya suɓuce wajen faɗa batare data shirya hakan ba. Aida wani irin tsalle ta buga sai gata tsaƙiyar bed tare da toshe kunnuwanta da hannayenta tana kurma uban wani ihu.
"Na shiga uku Ni! Maryam, Innalillahi yanzu kai nan ɗin ma saida ka biyoni ko tsoron Allah bakaji?. Ka sani yanzun ni killatacciya na haramta da duk wata haɗawa dakai A yanxun haka ina amsa sunan matar Aur........

"Keeeeeeeeeee!!!"

Ya daka mata wata kafurar tsawar data sanyata ƙamewa, "Ke mahaukaciyan inace hala? Kinyi ƙanƙanta dana bibiyi tatsitsiyar yarinya irinki nevermine har gaban abada"
Duk da cewar a tsorace take kuma kanta a rufe yake da duka tafukan hannuwanta amma hakan be hanata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login