Showing 75001 words to 78000 words out of 78068 words

Chapter 26 - Mikiya Book 2 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

1287

adda'an samun lafiya da sauka lafiya_

_kana ina tunanin loƙacin dawowar AK Nigeria yayi da kuma barinta na har abada da zaiyi da sunan aiki, se dai inda ziyara kamar in ya rako matarsa lol😁😀_


*Byeeeee*










*🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍
39&40

# Hot Romance scene
# Real life
# Hot love scene
# Ak meerah
# A.k.a AMMEYLAYLERH👍👉


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Cikin ƙanƙanin loƙaci se gashi a gidan kusan tare suka shigo shida jami'an daya ƙira a hanyarsa na zuwa. Tun daga bakin get na gidan suka fara cin karo da gawawwaki.
Haka har suka dire ga Kamaal ɗin dake kwance babu rai jikinsa da kuma marria da itan ma dai babu numfashin tattare da ita.
Cikin hanzari suka raba marria da jikin Kamaal nan aka tattaresu zuwa asbiti domin duba lafiyarsu duk da cewar sun san kamaal ɗin ya riga da ya mutu. Amma dole a matsayinsa na jami'a a duba ainihin abinda ya faru dashi duk da sun san abinda ya farun ganan halamar hakan.
Baki ɗaya su kuma wadan da suke kwance aka kwashe ana zubasu wota motan na daban, baki ɗaya suka tattara bindugun su kamaal ɗin dama na sauran ƴan ta'addar.
Bayan isansu hospital duk wani bincike daya danganci case ɗin mutuwar sunyi, kan marria suka koma duk wani taimakon gaggawar daya kamata sun mata amma bata farfaɗo ba. Cikin ƙanƙanin loƙaci ƴan uwan su kamaal daga rano suka cika hospital in tare da gidan shi. Kuka kuyi na ladamar wofan tar dashi da sukai sunyi har ba adadi, Ga kuma halinda marria take cikin na rashin farfaɗowanta, haka suka tattara suka koma ana barin mamanta tare da ita.
A gidansa aka may wanka, bayan an sallace gawar kamaal haka aka miƙa shi gidan sa na gaskiya.
(Allahu Akbar rayuwar duniyar kenan haka dai- haka dai loƙacin da kake kan ganiyar jin daɗinta, sai kuma mutuwa tazo ta riske ka a yayin da baka yi zata ko tsammani ba. ka shirya ko ba shirya ba taɗauke ka Allah yasa mu yi kyakyawan ƙarshe Ameern ya rabb,Ubangijii yaji ƙan Aliyu shureim)
Bayan mutane sun dawo daga maƙabarta haka zaratan matasa suka rinƙa shigowa cikin gidan suna gaisuwar kamaal ciki kuwa harda jami'ai abokan aikinsa. Dsp daya zo haka ya zube gaban kwarya kwaryan cikinsa yana matsan hawayen munafunci. "Allah ya jiƙan kamaal yaron kirki dashi wllh. Kai duk wanda ya kashe wannan yaro Allah dai ya toni asirinsa cikin gaggawa" daga cikin zuciyarsa yag saurin cewa (Yaseen ba ameen ba) lol☺😁 kunji shege mugu fa.
Haka akaci gaba da karɓar gaisuwar kamaluddeen bawon Allah, daga ko ina daga ko wacce duniya yabone kawai ke tashi akan kamaludden ɗin, kasancewar shi mutumne shi na mutane babu ruwansa da girman kan nan irin matasan yanzu da suke ɗorama kansu da zafi. Don malam bahaushe kance kowa ya ɗebo da zafi to bakinsa tabbas wannan haka yake.
haka dai Kamaal ya ringa shan yabo daga bakunan mutane maban banta, musamman ma talakawan da yake shige musu gaba yayin da wani iftila in ya afka musu. Rayuwa keñan in kayi dakyau kanka haka za inma akasin hakan ne kanka.Kamaal kam Saidai muce alhamdulillah ya sami tarin shedar mutane sai fatar hamdala kammm.
Kuka kuwa jama'a da dama sunyi kuka iyaka kuka sosae. Kakarsa iya Inno se kuka take cikin kukan take furta.
"Allah ya jiƙanka kamalu kamaludden, mutum me daraja da kamala me halin tattako da ban girma, Allah sarki Allah beyi zan rayu dakai ba kamal amma insha Allah zan rayu da abinda ka bari a duniya kamalu" tayi maganar tana shaftar ruwan hawaye me tafe da majina.

Se da marria tai kwana biyar kana ta farfaɗo wannan karan mikin dayay mata tsai arai shine ya fara faɗo mata. Ahankali ta shiga bin ko ina da kallo harta dangana da kallon mum nata dake sallah ta kalli alkibla, Saurin fusge ledan ruwan tayi a jikinta tuni jini ya fara yarara a hannunta data fisge canular dake hannunta.
"Ummata ina *YAAYAA KAMAAL NAAAA?* kinsan mafarkin danai ummata?wai a cikin mafarkin se ga wasu ƴan daba suka zo zasu kashemin Aiy'n, Wai shine na dauki bindigar nima na ringa kashesu, amma fa wai shiɗin ya mutu inata kuka kinji mafarki da soko ko umma" Tay maganar tana ta kallon ummanta dake ta sallar kwallan daya riga da ya cika idanun mum marria tasa bayan hannunta ta share don batason marrian taga tana kukan. Miƙewa tayi tana nufar inda marrian take, zama tayi gefen gadon da take zaune ga kuma hannunta na ɗigar jini.
Kanta umman ta janwo tana ɗorawa kan ƙafafunta sumar kanta ta soma shafawa a raunace tace "Marria kamaludden kam ya rigamu gidan gaskiya se haƙuri" wani irin kwace jikinta tayi a na ummanta, se kuma ta shiga ja da baya baya tamkar wata sabon kamun hauka.
Ummace ta riƙota ganin abinda takeyi cikin tausasa murya ta shiga faɗin. "ki daure!,ki daure, ki nutsu, nutsu Marria ki danni zuciyarki don Allah. Maza nutsu nasan da matuƙar ciyo hakan dole kiji matuƙar ciwo ki kuma fi kowa jin ciwon mutuwar kamaal duba da cewan har yanzun ko shekara baku ƙarasa rufawa da auren kuba. Amma hakan ba shi zai ba ki dama ki mance da cewar ubangijin daya bamu kamaal shi ya karɓi abinsa duk mai rai kuma mamacin. Kana mutuwa dolece a wuyan kowanne ɗan Adam kamaal kam ya riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta masa!, Ubangijii yasa yayi kyakkyawanr ƙarshe yasa aljannatul Firdausi itace makomar kamaludden"Mum marria ta ƙarasa maganar haɗi da goge kwallar data cika idanunta taff na tsananin tausayin ƴar nata. Cikin ɓacewar tunani na ɗan wani loƙaci muryarnta na rawa tace. "ummiey meya faru naga kina kuka"?
Daga har nurses dake tsaye akanta babu wanda maganar marrian bata girgiza ba, meya faru fa take tambayar su?. Kenan me hakan ke nufi badai tayi loosing memories nata bane?. Ummanta ce ta janyota jikinta tana ɗora kanta saman ƙirjinta cikin dakewa da shanye ciwon dake sukar ƙirjinta umman ta dubeta tare da cewa. "Marria kamaal mijinkine ya rasu!, ya tafi ya barki yabar gudan jininsa a tare dake ba tare daya ganshi ba, ya tafi yabar kowa da kowa na cikin duniyar ma baki ɗaya saidai Allah Ubangijii yaji ƙan kamaludden domin ya riga mu gidan gaskiya, gatan da zamu masa shine binsa da tarin adda'oinmu!" wani irin murmushi ta saki irin mai ƙona zuciyar nan tace, "kin yarda keñan? dama kema umma ashe kin yarda bakiji me nace miki ba cewa nay miki nayi mafarkin wasu sun shigo gidan mu sunyi harbin bindiga shine suka kashe min yaya kamaal na a cikin baccin nima kuwa duk sena kashesu. Barama ki gani ina wayana take na ƙirashi nace yazo yanzu kuwa zaki ganshi dan ma ki tabbar da cewan a mafarki nake" tayi maganar tana lalubar inda wayanta yake. "Innalillah wa'inna ilaihir raji'un"²
Ummanta, nurses,dama Zayd suraj da tun farkon fara sambatunta ya ƙame ƙamm ya kasa shigowa dan ji yay ƙafafunsa sunyi may nauyi.
Wani irin matsanancin tausayin marrian na kama shi cikin son gasgata mata kamaal kamm saidai wani ba bashi bane. Zayd suraj ya furta "Kamaal yatafi kamm marria wannan abu da kikeyi bashi zai sa yadawo gareki ba, da ana mutuwa adawo marria da yanzu mun dawo da kamaal cikin wannan duniyar kodan ɗorawa daga inda ya tsaya!, kodan ya ƙona zuciyoyin maƙiyansa sai dai kash wannan kalmar ta *Kulli nafsin za'ikatuol maut* ta jima da hawan kansa. Saidai haƙuri! Adda'a juriya da jajircewa kamar yadda ya ce dake"
A tsorace marria ta ɗago dara-dara idanuta masu kaifi ta ɗora akan zayd ɗin, kafin ta shiga girgiza kai hawaye na fita a idonta tace. "A ina ya mutum? Muje ku nuna min, wllh idan na farka daga wannan baccin baran sake komawa ba, sedai naita zama ido biyu.idan kuma da gasken kuke to wllh Nima binsa zanyi idan ya mutu sai muje cenñnn muyi rayuwar aurenmu a maƙabartarma, harda babynmu ma da zamu haifa ai shikenan kooooo Ummata"?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai suka shiga ambata ganin kamar ma marrian bata a cikin hayyacinta da nutsuwar tane. kallo ɗaya zaka mata kasan cewar Samm bata a hayyacin tane, cigaba tayi da kallon zayd da kuma ummanta ganin kowannensu hawaye yake daukewane daga idanusa, ya sanya sosae tsoro da zallumi haɗi da tashin hankali wanda ba'a sa masa rana na lulluɓeta Wanda tunda take tsawon rayuwarta bata taɓa irskar irin sa ba ya ziyarci zuciya da gangar jikinta, ji tayi wani irin abu yasoma ratsa baki ɗaya ilahirin jikinta . sai kawai jikinta yafara rawa kamar mazari.Cikin muryan da yay ƙasa sosae tace "Shikenan yaya kamaal na yatafi ya barni, ya tafi ba tare da yaga babyn da zan haifa mana ba?, ya tafi ya barni da kewa da maraicin rashinsa? na tabbata nima nayi ban kwana da farin ciki kenan ko?, wallahi umma ba zan iya rayuwa ba tare da Aiy'n ba nima mutuwa zan yi domin ban ga amfani rayuwata ba in ba tare da aiyn ba, kinga ƙara kawai na bishi idan mukaje can sena haifa mana baby'nmu muyi rayuwanmu mu kaɗai ko dan Allah Ummalolona?" se kuma ta fashe da dariya tana soma riƙe cikinta seta fara faɗin "Dan jinjirinmu ai dan Allah Abiey'nka ba ragon namiji bane ko? Kuma babu wanda ya isa harbinsa ma ina nannnnnn........
$e kuma komai ya sake tsaya mata chakkk tana sake sumewa.
Fashewa da kuka mum marria tayi tana ta ambatar duk wasu adda'oin da suka zo bakinta tana jijjiga marrian.
Cikin ƴan mintuna kaɗan ta kuma farkawa, amma wannan karon kammm ko damar sunbatun bata samu ba, sedai bin kowa da take da rinannun idanun da suka jeme sukay jaaaaaa sosae.
Da wani kalan saurin tashin hankali zayd suraj yabar wurin don bazai iya ci gaba sa sauraren zararrun kalmomintaba. Ko kallon gabansa baiyi kai tsaye motansa ya faɗa yana mata key ya kwasheta da wani mugun speed na hauka.
Shi kaɗai a zuciyarsa yake raya duk masu sautsayin da Allah yasa ya gano da kwai sakun hannunsa a mutuwar abokinsa babban amininsa kamal Rano, ya rantse shima seya raba shi da nasa numfashin. Yanxu dai dan Allah dubi yacce suke ƙoƙarin haukata matarsa a sanadiyar mutuwar mijinta. Sun maida mishi ɗa ko ƴarsa marayu tun kamin su zoma duniyar da ba komai cikinta banda tarin kunci, hasaada, cin Amana, rashin kishin ƙasa, zanba cikin aminci. Da dai duk wasu abubuwa marasa kyau, to mema mutum zeyi a cikin wannan duniyar kamm uhmmmm? Ya tambayi zuciyarsa hakan. Wani ɓangare na daga cikin zuciyansa yace {babu}
Yau kwanaki biyar kenan daya rasa abokinsa kamaal ɗin, kuma tun a daren ranar ya fara gudanar da wasu bincike tare da ƙwararan hujjoji domin gurfanar da mara gaskiya maciya amanar ƙasa da kuma aikinta.

Tun daga wannan loƙacin marria ta koma kamar wata zararriya ita kaɗai ka ganta tana dariya wani bin kuma ka ganta tana kuka. Ga kuma wani sabon al'amari daya kunno kai shine na juyewar magana daga yadda gaskiyar lamari yake zuwa ƙarya, wai marria itane ta gayyaci ƴan dabar nan da su kashe mijinta in ba hakaba meye yasa ita ko kwarzane bata jiba? Me yasa ba'a sameta da karzanen ciwo bane. Wannan abu shiya sake rikitar da duk wani makusanci nasu marria, sedai zayd tsaye akan komi tun a daren jiya ma yay magana da AK yace lallai dole akwai buƙatar ya dawo neja. Hakan kuwa akayi a washe garin ranar AK ya dira a nigeria.
wanda yay daidai da ranar dasu mah suka miƙa meerah ga sashin AK ɗin.
Yana zaune kan wata farar royal coution dake gaban pool nashi na nigeria. Tsaye ya miƙe cikin tsabar tafasan da zuciyansa ke masa hannunsa riƙe da guns. Seti ya dauka tare da harba bindigaf a irin abin gwajin nan. Ta farko seta goce,
Kallonsa arms yayi tare da furta "Baka samu ba!" shade dake idonsa ya cire tare da faɗin "Wannan ze samu" ya faɗi yana sake harba ta biyu da uku duk suka harbi tsakiyan paypay ɗin inda suke ya kalla tare da furta.
"Gotawar seti sam ba ɗabi'ar *ABDOUL-MALEEK AK* bane. Kamar yadda Ak be kamaci ya zamo abin setin wani ba. Kamar yacce aka wayi hari har wasu sun fara cin dunduniyata"
Milea ne y kalla AK din tare sa faɗin, "bara na ɗan zaga Boss" kansa ya jinjina masa tafiya ya fara taku daya ana biyu sejin sauƙar harsashi yay a tsaƙiyar gadon bayansa. A ɗan razane duk suke kallon AK ɗin.
"Amma Boss me yasa?" Arms yay tambayar tunda yasan boss ɗin nasu baya taɓa aikata ba daida ba.

"Shiga hurumi! Arms duba" ya faɗi yana sake harbin setin kafar miles ɗin. da sauri arms ɗin kuwa ya isa ga miles yana duba ƙasan shoe nashi kamar yacce AK ɗin ya buƙata. A take kuwa se gashi hannunsa rike da plash camare wacce ya dauƙo daga cikin takalmin miles ɗin.
Cikin wani kalan taku har wani ɗan rausaya yake ya sake furta.
"Kada ka yarda da kowa ka kashe koma waye ka zama naka kai kaɗai.Yare ɗaya ne a duniyar nan wanda kowa yake fahimtarsa, shine kada ka yarda da kowa wannan shine"
daga haka ya yasanya kansa yana barin bakin pool ɗin kai tsaye. Kuma Zaid Emaar's yana nan a ƙasar naijan shima.

Bedroom nashi ya wuce kai tsaye duk wasu sauran hujjujin da zayd ya kawo mishine ya gama haɗesu wuri guda. A kuma daren ranar yabi jirgi zuwa Kano don a gudanar da shari'an dashi. Xuwa loƙacin kuwa duk wanda yaga marria seya tausaya mata.
Don abin a tausaya matace don kuwa kalmar nan ta taɓin hankali na neman tabbatuwa akanta. Wai hakan ma dan tsaye mahaifinta yake akanta ga kuma zayd da kuma jajircewarshi garesu, duk wani nauyi da dawainiya da su ya ɗauke da kansa. A randa kuma ta haihu a ranar Insha Allah za'a sake ɗaura Aurenta a karo na biyu da *ZAYD SURAJ SHUREIM* kuma sunyi na'am da hakan domin kai tsaye roƙo na ƙarshe da Kamaal ɗin ya masa kenan kuma a gaban AK ne se kuma ita marrian, Tunda ta fara dawowa cikin nutsuwanta shiru ya zama shine abokinta, fuskan nan me yawan fara'a da ban dariya duk sun gudu nasu wuri. A loƙacin kuwa da Babanta ya sameta da zancen loƙacin ma wajen wata biyu da rasuwan kamaal ɗin bal tace samm ita bata yarda ba. Ai ita da kuma auren wanin kamaal har gaban abada.

Anan kano sukay zaman farko, inda ido da ido suke neman danne gaskiyar abinda ya faru, daga karshe ma zayd se ɓoye iyayen yarin yay a gidansu. Domin barazanar mutuwa da wasu manya keyi dole ya daukaka ƙara zuwa *ABUJA* dan yace Insha Allah seya cikama kamaal muradinsa na amsarwa wadan nan mutane haƙƙinsu. Babu zata mataimakin gwamnan kano yaga sammacin ɗaukaka ƙara zuwa babbar kotu ta gaba shida ɗansa fayel. Nan da kwanaki uku don haka ya shirya shedun ƙarya da kuma manyan mutane domin bashi kariya shida yaronsa kodan kada sunan ya ɓaci da kuma rashin kujerarsa da yake matuƙar ƙauna. Haka dai sukay duk wasu shige da ficensu kuma sunyi ƙoƙarin ganin kota wacce siga sun kwato wannan dayan ƙarshen da marria ta harba, wanda kai tsaye shine ya sanar dasu wadan da suka aikosu su kashe kamaal ɗin har dama matar nashi. A lokacin kuwa da Dsp yaga takardar sammaci na biyu harda ƴar guntuwar gudawarsa yay don kuwa abu ne baiyi zata ba.
_A yau ranar Asabar 5/10/2024_ babbar kotun maƙil take da jama'a ta ko ta ina ciki kuwa harda shegaban kasar A..K...K dasu Ak shida Zaid Emaar's amma dun ɓoye fuskokinsu ne cikin mask, duk wani wanda masu gidan rana suka zauna masa daram to kuwa yana a cikin wannan kotu don wanke dan uwansa Hon Iliyasu maitama da yaronsa fayel maitama.
"KOOOTU!"
Alƙali ya buga ƴar hidimarsa tsittttt kuwa kotun ya dauka.
Nan ya umarci da masu kare fayel dasu fara gabatar da shari'ansu. Nan suka shiga zayyano manyan hujjojin karyar da suka tanaja domin kare kansu.
Mutum ɗaya ne daga cikin masu kare fayel ya miƙe yana furta.

"Ya me girma me shariya kamarrrrrrr"

Hhhhhhhhh to muci gaba ko? Amma a fage na gaba.

To nake ga mu dakata a nan

_Shin zamuga su waye zasuy nasara?_

_Shin Zayd suraj ne zeyi nasara ko kuwa su Hon iliyasu maitamanae da nasarar?_

_Tammm ƙaƙa kara ƙaƙa karfa ku manta yau kam ga AK ga kuma A..K..K shugaban kasar nigeria kenan, wanda yay shijira daga ƙasar sa KUWAIT zuwa tamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login