Showing 45001 words to 48000 words out of 147628 words

Chapter 16 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

gefe da zai zauna a wannan matsayin.



"Hamma wannan saqonnin barazanar basa da alaqa da faruwar wannan abun kuwa?". Kai yake jinjinawa sanda yake takawa a hankali yana matsawa daga wajen



"Definitely......but I'll make it clear im not Intimidated" Ya fada da wani irin qwarin gwiwa yana dora top saman rigar t.shirt din jikinsa.



"Let's go.....ka kira William kace ya samemu a can....."



"Amma hamma.....flight isn't ready"



"We'll take the road" Ya furta yana riga saddiq yin gaba.



Kafin sukai ga isa lagos ya gama shirya dukkan abinda ya kamata ace ya tsara din. Suna dab da shiga garin har a sannan idanunshi biyu,ko daya baiji wani buqatar bacci ko kuma ya huta ba. Yaja qaramin tsaki sanda suka dauki hanyar kamfanonin. Ya fahimci ita kalmar SO ko a meye ta shiga wahala ce kawai da walagigi da ruhi,wannan ya sanya banda soyayyar family dinsa bai taba saka soyayyar komai cikin ranshi ba,sai yanzu gashi kwatsam......kamfanin ya shiga ransa har baisan adadi ba......gashi kuma ya zama abu na farko da son nasa keson zame masa wahala,da wannan ya qara ji a zuciyarsa lallai tabbas ya kamata ya nisanci soyayya iyakar iyawarsa.



Duk da sun nuna matsayinsa yafi ya taso da kansa amma ya kauda wannan. Ya karbi duk wani bincike nasu ya dora da nashi. Da gaske an samu wani dan qaramin store cikin kamfaninsa cike da qwayoyin da inda wani me qaramin matsayinne ba shakka sai ya tafi dauri gidan gyaran hali,amma da yake a nigeria muke.....kuma kura ma tasan gidan me babban sanda sai ya zamana dakatar da kamfanin kawai akayi sai bincike ya kammala.



Bayajin zai iya bari maqiyansa su kalli faduwarsa da wurwuri haka,wannan ya qara masa qaimin shiga binciken da kansa gadan gadan.



Ya fuskanci tarin abubuwa masu yawa cikin case din,wannna ya qara masa qaimi,bai kuma yarda yayi handling case din ma kowa ba.



Duka da bacci da cin abincinsa qalilan ne. Amintattun experts investigators din daya aminta dasu kawai suke aiki ka'in da na'in,ba dare ba rana. Bai gayawa kowa abinda ake ciki ba banda anni da yace ta tayashi da addu'a,akwai matsala amma qarama ce ba wata babba ba,haka ya gayawa abba da farouq. Saidai sam hankalin farouq ya gaza kwanciya,don yana dawowa daga seminar dinsa ya biyo bayasa a washegari.



Yadda ya ganshi ya tabbatar abun ba qarami bane,don ya nuna har a jikinsa don kuwa ya dan rame kadan saboda rashin bawa abinci muhimmanci. Ya sake sallamawa da miqa wuya kan muhamnadun yaci sunan muhammad din,namijin gaske ne da gaske......daga yadda ya tunkari komai yake gabatar dashi da dukka qarfin gwiwarsa da jarumtarsa kadai ya qara tabbatarwa NAMIJIN DUNIYA NE.



Yanata qoqarin dodging komai farouq ya dubeshi.



"4weeks without me dude.......have you noticed your appearance?.....check your reflection" Ya fada yana kama hannunsa zuwa gaban concealed mirror din dake wajen.



Ya kalli fuskar tasa kaman yadda farouq ya buqata,sai ya saki murmushi ya miqa hannu yana shafa fuskarsa.



"Chill out mana dude,nayi settling komai,It's come to an end......My evidence supports my claim....and it speaks for itself,all the fact are on my side,na gama komai gobe zasu saki kamfanin.....abu daya ya rage na gano shine,who's pulling the string" Hannunsa farouq ya riqo yana girmama qarfin jarumtarsa,yana jin inama ya samu irin wannan jarumtar tasa



"We'll leave no stone unturned,we'll find him together" Rungume kafadar farouq yayi,yana sake jin qaunarsa cikin ransa.



A gaba ya sakashi ranar,yasa ya ajiye komai tunda bincike ya kammala. Da kansa ya zauna ya masa gyaran fuska da sauran wasu abubuwa,yana masa suna hira yana bashi labarin nasa progress din da aka samu bayan seminar din. Duk duniya da farouq kadai yake irin wannan sakewar. Ranar duka tare suka qarar da ita,sai dare sannan kowa ya wuce makwancinsa,da zummar gobe da kamfani yaci gaba da aiki jibi tabbas dole su wuce gida,wanda sam bai fahimci meye ma'anar matsawar da farouq din yayi bama.



Ya dauki wayar da zummar kashewa ya tarar da tarin miscalls da kuma saqonni,guda daya ya duba ya fahimci wacece. Fareeda ce....saqo bayan saqo kamar bata da wani sauran aikinyi sai tura masa da saqon.



"How did she get ahold of my number?" Ya tambayi kansa da kansa. Tunawa da yayi da mahaifinta ya sauqaqe masa wahala,yasan samun numbersa zai zame mata wani abu kenan me sauqi. Tsaki yaja ba tare da yabi takai ba,ya kashe wayar ya kwanta.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_ZAFAFABIYAR_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 29





29





&Cikin kwanakin har ruwan jikinta takeji kaman ya qare saboda tsabar wani irin kadaici da dumbin tunani da yake cike a kanta. Sati hudu cur tana a cikin gidan......ba motsin kowa ba gilmawar kowa,ba hira da kowa,ba waya,daga ita sai tv sai karen gidan dake haushi nesa da muhallinta. Ada ko parlor din bata fitowa tana qunshe a daki,daga bisani ta fahimci depression na loneliness zai iya kamata,don haka da kadan da kadan ta fara fitowa tana zama.



Saidai daga zaman sai bacci,sai wanka sai wata kwanciyar. Gyaran gidan kansa bai wani dameta ba,don tana ganin ba wani muhalli bane da zata damu kanta a kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu... Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan.



A kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida hankalinta sam sam.



&"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan.



Shirya kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa.



Gidan duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area dinsa na sama yana fatan samun wani abun.



Wuta ce 24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage mintunan da zaiyi jiran furar.



Kadan kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma batajin tana da wani abinciii bayan shi.



Fargaba taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo.



Sai data masa daidai sannan ya kashe tv din,ya dauketa ya hada da cup da spoon ya wuce daki.



Sake kasa kunnenta tayi da kyau,a yanzu ba sound din,saita lumshe ido tana qoqarin saita nutsuwar kanta. Bata taba sanin kadaici masifa bane sai yanzu,bata taba sanin haka yake taba ruhi da rayuwar mutum ba sai yanzu. Wasu hawaye suka biyo ta lumsassun idanunta suka gangaro kan fuskarta. Gaba daya ta koma wata raguwa a kwanakin,zuciyarta kwata kwata ba wannan qwarin da tsaurin sai wani irin rauni da ya sake cikata,sai kawai ta kifa kanta saman pillow din ta saki siririn kuka,fried egg din da bata iya ci ba kenan.



&Bacci yayi sosai wanda da qyar ya tashi sallar asuba wadda duk tsanani zai wahala ta kubce masa. Koda ya koma yunwa ce ta tadashi,cikinsa gaba daya kamar an masa yasa. Yadan yamutsa fuska kadan yana tunanin me zaici?. Inda ameh yana nan ya tabbatar yanzun da yake qarfe sha biyu na rana ya gama breakfast yana jiran umarnin hada lunch da za'a kai company ko kuma ya jirayi zuwan dafa dinner.



Brush ya fara shiga yayi sannan ya fito,ya dauki wayarsa guda daya a ciki ya kunnata. Kamar jira akeyi sabbin saqonni suka shiga turereniyar shigowa,baibi takai ba ya lalubi number ameh,bai sameshi ba,yaja dan qaramin tsaki,wala'alla ya lalata wayarsa kaman yadda ya saba,waya bata fiya dadewa a hannunsa ba zakaji ta fadi ko kuma ta lalace,wannan dalilin ya sanya ameh din kansa baida cikakken number boss din nasa,wanda dama kusan duk wanda ya mallaki number wayarsa ya cancanta kuma yana da connection dashi nakai tsaye irinsu ameh din dame sunan malam.



Amna ya kira,bugu biyu ta daga.



"Hamma......barka da dawowa"



"Barka kade amna"



"Good morning hamma......ya hanya ya gajiya?"



"Alhamdulillah......ya makaranta?,kun fara shiga lectures?". Kai ta gyada



"Mun fara hamma......ba dadi hamma ba supporter.......BB farouq yace na cika shirme......ya saddiq tsokanana yake koda kuna nan......nayi missing ya musaddiq har yanzu bai dawo ba......please hamma kace ya dawo haka?" Ta qarasa maganar a shagwabe.



"Zai dawo soon" Ya furta badon yana nufin ya barshi ya dawo nan kusa ba. Tun tuni ya aike da musaddiq din wani aiki don ya nisantashi da maamah,bayason zamansa a nan ya tabbatar idan yana nan watarana maamah zataci galaba a kansa. Hakanan baison fitowa kai tsaye ya nunawa musaddiq komai akan maamah



"Allah ya dawo dashi lafiya....."



"Ameeen amneee......ki hadani da anni idan kin fito.....ki gayawa ameh lallai lallai yazo yau"



"In sha Allah hamma" Tana shirin tambayarsa sabreen ya ajiye wayar.....saita bari kawai ta shigo gidan da kanta tayi mata barka da dawowa.



Yadda taji yunwa na kama mata cikinta da gaske ya sanyata miqewa bisa dole. Yau kam sanye take da silk sleeping dress maroon color,riga ce iya cinya da wandonta dogo har qasa,saidai kuma tana da dan budadden wuya kadan. Duk da ramewa data danyi hakan bai hana rigar mata kyau ba,ta kuma zauna cif a jikinta. Jikinta ta jawo ta sauka daga saman gadon,tasa hannu ta tattare gashin kanta waje daya a qeyarta,ta taka a haka zuwa gaban madubi,ta jawo dan madaidaicin jewelry organizer din dake saman madubi ta budeshi,hair clip guda daya babba ta maqaleshi sannan ta samu vintage scarf ta daure kanta,wanda jelarsa dankwalin ta zauka kafadar hagu da damanta. Akwai socks a qafarta,wadda sanyin ac din gidan ya sanya dole take sakata saboda yadda marbles din yake daukan sanyi sosai,kwata kwata batasan ya ake controlling duka Airconditoners din ba bare ta daidaita shi,hakanan kawai take haquri. Sauqinta daya ana cikin yanayi na zafin farkon kasancewar damuna,banda haka ta tabbatar ba qaramar illa zatayi mata ba.



A nutse ta murda qofar,ta fara leqo da kanta tukunna tana tuna motsin da taji jiya,sai data tabbatar shuru wajen yake ba alamun komai sannan ta fara fitowa a darare tana sanda hannunta dauke da plate din soyayyen qwan.



Yau haka nan ya sauko da qafafunsa bai sanya takalmi ba. Fara tas din qafarsa dake da dogayen yatsu yake takawa a nutse yana sauka daga stairs din hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa ta William,yanason sake tabbatar da komai na company din yana tafiya lafiya lau.



Sanda ta buda qofar da zata sadata da parlor din farko ta sanya qafarta lokacin ya kusa da stairs din qarshe,wannan ya bashi damar ganin wulgawar mutum ba tare daya tantance waye ba.



Dan tsam yayi da ransa sai kuma yadan qara hanzarin saukowar don yaga waye ya gilma din,sam zuciyarsa na masa nisa da tuna tana cikin gidan.



Da wani irin sassarfa take qoqarin fita a falon ta sada kanta da falo na biyu na gidan ta boye kanta a kitchen. Murya takeji sosai tana sake kusanto inda take,tsoro ya sake cikata,kenan wani ne ya kwana a gidan akayi mata kwanton bauna?,har sai da akaji fitowarta sannan ya bayyana?. Ta shiga uku,su waye suka shigo?,abu daya ta sani ko zasu yankata su cinye ba wanda yasan sun shigo saboda tazarar dake tsakaninta da security din gidan.



Tana saurin isa ga kitchen don ta buya yana sassarfar shan gaban macen daya gani. Kusan dukansu sai abun yazo musu lokaci guda,yana dab da cimmata tunaninsa ya dawo kansa. Ashe yabar wata cikin gida......akwai yarinyar dake rayuwa cikin gidan,wannan tunanin ya sanyashi tsaiwa cak,tsaiwar tasa ta bata damar wucewa kitchen din cikin matuqar sauri ta maida qofar ta kulle harda murza key.



Qofar yabi da kallo yana zare wayar daga kunnensa. Mamaki kadan yana kamashi,anya qwaqwalwarta lafiya qalau take kuwa?. A nutse ya xura wayar a aljuhunsa yana dage kafadunsa cikin I don't care manner,sai kuma ya koma saman daya daga cikin kujerun ya zauna yana canza channel,kadan kadan kuma yana kallon falon. Ba wani tarkace bane ko wani abu a ciki,amma tsaftarsa bata masa ba. Ya saba duk inda ya wurga idanunsa ya ganshi fes yana qyalli da daukan idanu,amma a nan din idanunsa suna iya ganin qura a wasu guraren. Qaramin tsaki yaja can qasan ranshi yana fadin bazai dauki qazanta ba. Minti biyar yana jira yaga ta bude qofan amma ba alama,yunwa yakeji sosai,yana buqatar wani abu me nauyi da zai sanyawa cikinsa. Baya wasa sam da cikinsa,mutum ne me son lafiyayyen abinci musamman wanda ya dace da tsarinsa.



Miqewa yayi ya taka a hankali ya isa bakin kitchen din,har a sannan tana maqale bayan qofar tana tunanin yadda za'a yi ta kubuta daga hannun mutumin da batasan yadda akayi ya shigo gidan ba. Knocking din daya fara yi a hankali ya sake gigitata,ta qanqame jikinta guri daya tana runtse idanunta hankali a tashe. Sau biyar yana bugawar ba wani motsinta,ranshi ya sake baci,sai kawai yabar wajen yana takawa a hankali ya nufi wata qofa daban da zata sadashi da kitchen din ta baya.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_ZAFAFABIYAR_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 30





30





Jin an dakata da bugun ya sanyata sulalewa a wajen tana dafe qirjinta. Bata ankara ba hawaye ya balle mata,dama ta yaya za'a barta a gida irin wannan ita daya idan ba dama anyi shirin salwantar da rayuwarta bane da gangan. Tunda take a rayuwarta bata taba sanin tsoro na ainihi irin wannan ba.



Qofar data hanga ya sanya taji relief,ta goge fuskarta ta mmiqe a hankali cikin sanda tana nufar qofar ko zata samu wata hanya da zata fice daga cikin gidan zuwa bakin gate.



Tana miqa hannunta tana riqe handle din da zummar bude qofar daidai lokacin shima ya bude qofar da dan zafin nama,abinda ya sanyata ta biyo qofar takuma yi kyakkyawan masauki a jikinsa.



Dif

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login