Showing 21001 words to 24000 words out of 147628 words

Chapter 8 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

da matar dake amsa sunan surukarta ta bata jiya. Daga jiya zuwa yau sai takejin komai kamar ya canza. Har a ranta da zuciyarta sam bata jin matar ko kadan.......tana jin wani qaqqarfan abu a kanta da yafi kama da qiyayya......qiyayyar batasan ta mece ba.....saidai koma meye baya rasa nasaba da katsalandan da suka yiwa rayuwarta ita da d'anta. Tanason kiran momma amma batasan me zatace mata ba.....kuma kaman a yanzun ma yayi safiya da yawa ta kirata din.



Yadda taji zuciyarta nason karyewa taji bataso......batason ta karaya tun bata gama fuskantar komai ba. Gidan yayi mata shuru da yawa,duk da dama can ita ba ma'abociyar son hayaniya bace....ko a gidansu zaka samu dakinsu a rufe kirif don rage yawan hayaniyar mutanen tsakar gidan nasu,a mafi yawan lokuta ma tafi qaunar shurun,sai takejin wata irin kewa tana shigarta.....kewar huda.....kewar nadra....kewar haneefa. Takan tsinci kanta a wani yanayi maras dadi idan ta tuna dasu.....ta yaya zasuci gaba da rayuwa?. Tana da nutsuwa kadan idan ta tuna suna tare da momma bahijja,tayi imani zata cika abinda tace din,amma duk da haka bata shirya barinsu a wannan matakin ba.



Yunqurawa tayi ta miqe dauke da tray din don ta maidashi inda ta daukoshi,tako ina tanaji komai da zatayi amfani dashi a cikin gidan na wucin gadi ne kuma na aro ne a wajenta,bata da hurumin zafafa mu'amala da komai na gidan.



A karo na biyu ta sake duban stair case din sanda zata wuce ga qofar da zata sadata da parlor din. Sai a sannan ta sake qare mata kallo sosai. Tamkar gine ginen turawa haka aka tsara gidan,wani irin staircase ne me kyau da aka qawata bangonta da wani irin woods royal frames da shukoki masu kyan launi da fararen furanni qananu qananu. Idanunta ta janye tana jin bata da hurumin maida hankali da wajen,saidai girma gidan yana saka mata shakka da tsoro a ranta,tana kuma cike da shakka da tantamar ita kadai ta kwana ne wai a cikin gidan?. Saidai basket din data gani ajiye saman table din falon bayan ta dawo a kitchen din ya fara alamta mata ba ita daya bace ba.



Tana shirin janye idonta ta wuce ciki taji sallama daga parlor din farko. Da dan tsoro da mamaki ta maida idanunta kan pivot door din cikin tantamar wanda yake sallamar. Tsahon second talatin tayi,sai taji ta wuce ciki kawai,don bata jin akwai wani abu a cikin gidan da take da haqqin lallai saita kula da yadda zai tafi,saidai taku uku kacal ta sakejin muryar na sake jaddada sallamar. Sallamar tayi mata nauyin da takeji bai kamata ta wofantar da ita ta Kuma wuce ba,dole ta dawo da baya tana dosar qofar,ta turata ta bude tana saka qafanta kan step din idanunta cikin parlor din.



Kamilalliyar macace cikin kyakkywar shiga da lullubi,tana a tsaye,gefanta kuma kyawawan kwanduna ne guda biyu ajiye a gabanta. Murmushin data sakarwa sabreen shi ya sassauto zuciyarta,sannan ya zabge kokwanton dake ciki,saita samu qwarin gwiwar ci gaba da saukowa idanunsu cikin na juna



"Ina kwana" Matar data kusan haifarta ta gaidata kafin ita takai ga gaisheta.



"Ga waje ki zauna" Tace da ita cikin qarfin hali ba tare data amsa gaisuwan ba. A nutse kuma cikin girmamawa ta zauna,sai itama ta samu gefen kujerar ta zauna tana maida mata gaisuwar



"Ina kwana?"



"Barka da asuba,mun tashi lafiya?"



"Alhamdulillah......ya baqunta?" Ta fada da murmushi da kuma kulawa a muryarta



"Alhamdulillah" Ta amsa mata har yanxu tana tunanin wace ita.



"Anni ce ta aikoni.....tace kuyi haquri har yanzu akwai baqi cikin gidan,shi yasa ba'a kawo breakfast da wuri ba,amma gashi nan harda lunch don kada ayi delay na kawowan da wuri shi yasa ta hada.... Tace da fatan hakan ba damuwa?" Sunan tadan juya cikin ranta,amma kuma farat daya hankalinta sai yakai kan matar. Murmushi tadan saki tana mamakin damuwar da tayi dasu haka



"Ba komai.....ayi mata godiya sosai" Ta fadi tana jin wani abu na daban akan matar. Miqewa matar tayi



"Sunana baraka.....dadaddiyar hadimar anni ce ni,zan koma,a huta lafiya" Kai kawai ta gyada mata,har ta fice idanunta suna kanta. Sai ta ajiye ajiyar zuciya tana maido kallonta ga basket din gabanta. Tadan xuba masa idanu tana nazarin matar,komai nata cikin dattako.....kuma komai nata akwai alamun nutsuwa me yawa a tattare dashi,waishin WACECE UWA a cikinsu?,wacce mahaifiyar ta ainihi?. Wannan tambayar kusan ita daya ce abar data damu da ita cikin lamarin kaf,sai ta miqe a nutse kaman zata bar wajen,sai kuma ta fasa,ta tsugunna ta dauki basket din,ta taka a hankali zuwa dining area din da aka qawata da wani dunqulalle kuma mulmulallen dining data kasa tantance glass ne ko kuwa dutse?,ta dora basket din kawai akai,sannna ta juya tana sauka ta wuce zuwa dakinta.



Sai daya daidaita komai sannan ya hada connection din duk da yakeso. Bincike ya fara yi a kasuwannin hannun jari na gold da Diamond.......da gaske an masa wani irin mummunar faduwa da bai taba ganin yayi hakan ba tsahon fara kasuwancinsa. Baya ya koma ya jinginar da bayansa jikin kujera yana shafa lips dinsa da yatsansa guda daya. Da gaske akwai faduwa da hasara me yawa data samesu,musamman a irin wannan lokacin da kwanaki kadan suka rage kamfani ya fara aiki. Zai zamana kome xasu fitar ko su samar asara ce a garesu,dole su saidashi a qasa da farashin da aka tsara za'a fiddashi. Saqonnin da aka yita turo masa suka dawo masa akai,ya lumshe idonsa ya kuma budesu yana kiran sunan Allah,sai ya sake maida hannunsa kan system din.



Kusan duk wani ma'aikaci dake aiki qarqashinsa na kusa dana nesa sai daya nemeshi. Ya bata lokaci sosai yana urgent meeting dasu,wanda hakan ya daukeshi aqalla a wanni masu dan dama. Baisan kuma ya jima din a zaune ba sai da cikinsa ya fara qara. System din ya rufe yana furzar da iska daga bakinsa. Ya tabbata babu abinda zasu iya sakeyi......dole su rungumi dukka hasarar data tunkarosu lokaci guda......



Akwai manufa.......kuma anyi ne da gayya,kuma hakan ya sake bashi tabbacin dukkanin saqonnin da aka aike masa da gaske suke.....sun shirya shiga yaqin tare dashi.....sun shirya jan daga shi dasu. Sai ya saki wani qaramin murmushi. Sunyi gangancin fara tsiro irin wannan abun dashi......ya tabbatar basu gama sanin ainihin waye muhammad a kasuwancinsa ba.......wannan abun koma waninsa bazai sauyashi ba......bazai kuma sakashi ya tsaida kowacce harka tashi ba.



Har a jikinsa yakejin a baqon guri yake,banda haka zuwa yanzu da tuni Ameh ya dameshi da batun abinci. Hannunsa ya miqa ya dauki wayarsa ya kunnata daga kashetan da yayi



"Subhanallah" Ya furta da hanzari ganin har azahar ta sanyo jiki. Bai kira anni ba.....bai kira farouq ba,baima kira kowa ba wanda aqalla ya dace ya yiwa kowa bangajiya koda kuwa ba shine ya gayyatosun ba,amma aqalla sabodashi suka zo. Anni ya fara kira amma sai yaji wayar a kashe,yasan har yanzu gidan akwai sauran baqi don haka yafi kyautata zaton uzurin daya sakata kashe wayar kenan.



Yayi zaton zai samu saqon farouq amma sai ba tarar ba. Ya danji ba dadi,don haka kai tsaye ya fara kiransa.



Bugu daya ya daga kamar dai dama wayar tana hannunsa yana jiran kiran nasa ne. A nutse ya masa sallama,daga can background yana dan jin muryar mutane.



"Kaji muryar ango......so fresh" Farouq din ya fada kansa tsaye.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*

08187255862





5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 16













"Sai yanzu aka tashi kenan?" Farouq din ya sake fada ba tare daya damu da abinda zaice da farko ba a lallai sai ya tsokalo shi



"Eh.....ka nemeni ne?"



"Wa?,ni?,ya za'a yi na batawa kaina lokacin nemanka?,waya gaya maka ana kiran ango a irin wannan time din?"



"To hell with you farouq a'ahhhhh" Ya fada sounding bored kadan kadan.



Murmushi me kama da dariya ya saki wanda har sautinsa ya bayyana sosai.



"An maka uziri kome zaka fada you're forgiven" Hannunsa ya dora saman sumarsa yana shafawa,ya fuskanci farouq so yake kawai ya haukatashi



"Where's anni?"



"Na barta a gida tana preparing na walima....."



"Ya salam" Fuad ya fada yana lumshe idonsa. Sam ya mance da batun walimar kwata kwata.



"Su haajj na yiwa rakiya airport......they're leaving".



"My regards to them please.....idan na sake nutsuwa zuwa anjima in sha Allah i will give them a call"



"Ance maka daga yau har wani satin an maka uzuri fa.......ka samu nutsuwa yadda ya dace dudu" Ya rigashi katse wayar wannan ya hana fuad gaya masa abinda yayi niyyar fada din,sai kawai ya zame wayar daga kunnensa,qasan ransa yana fassara maganar farouq da kuma sakata a inda farouq din ke nufi



"God forbid" Ya fada qasa qasa. Hasashen gaba days banbarakwai yayi masa sanda ya dora tunanin a muhallin da farouq ke nufi,tattara tunanin yayi ya azashi a mizanin shirme gaba daya,ya fara lalubar number amna.



Sai data kusa yankewa sannan ta daga



"Hamma" Ta fada a shagwabe.



"Hamma ka manta dani.....adda tayi taking dinka away.....as far as yadda zata iya" Ta qarasa fadi da qaramar dariya a muryarta da ba sosai ta bayyana ba



"You amna.....lovey dovey will never be forgotten........hayaniya yayi yawa amna.......bansan haka ake abun ba"



"Hamma yafi haka fa.....don kaqi bada hadin kai ayi komai" Hannunsa ya dora a goshinsa yana furzar da qaramar iska. Shikam ko zancan bayaso,abinda yake gabansa kawai yanzun shine damuwarsa.



"Ya gidan?" Ya tambayeta.



"Full with 'yan biki dake jiran walimar anni......ina yini hamma" Ta hade amsa tambayar tasa da gaisuwa.



"Alhamdulillah.....how about anni da abba?"



"Abba dai ya fita tun dazun.....kuma ina jin sai dare zai dawo........anni tana daga baya da mutane"



"Okay.....bata wayar"



"Okay hamma" Ta amsa shi tana miqewa gami da ficewa.



Bai yanke kiran ba saita maida kunnenta,tana tafiya wajen annin tana ta bashi labarai kala kala. Bai yanketa ba yayi shuru yana saurarenta. Yasan halin amna sarai,bata gajiya sam sam da hira.



"Kice ameh ya kirani....."



"Okay hamma.....ga anni" Saita miqawa anni wayar,ta samu plastic chair daya daga cikin kujerun dake wajen ta zauna tana kallon yadda aka qawata wajen walimar da wani irin tsari me kyau,tamkar wani hamshaqin event center.



"Barka da warhaka anni......ya hidima ya rana?" Murmushi ta sauke,har cikin ranta farinciki yana mamayarta idan ta tuna a yau muhammad dinta ya zama cikakken magidanci



"Barka kade me babban suna.....mun tashi lafiya zance ko mun yammata lafiya?". Tambayar tata tadan sakashi yaji nauyi,kada itama fa ta dauka wani abune ya boyeshi,kada ta fassara wani abu na daban akan yarinyar ma da bai samu daman ganinta ba



"Lafiya anni alhamdulillah"



"Haka akeson ji.....na aika baraka takai muku breakfast da lunch.......nayita so nace idan ta isa ta hadani da d'iyata mu gaisa saina sha'afa......in tana kusa bani ita" Rasa abinda zaice yayi,yadan diririce kadan har hakan yaso ya nun alamu a muryarsa,yayin da annin ta dauka wani abunne na daban ya kawo hakan,kodai baiso aji muryarta a fahimci wani abu,don haka ta katseshi



"Kaga rabu da ita.....anjima idan kun iso wajen walima ma gaisa.....za'a fara immediately after asr prayer"



"Allah ya kaimu anni.....Allah ya qara girma da lafiya"



"Ameen ya hayyu ya qayyumu" Ta fada tana jin dadin yadda sam baya gajiya da mata addu'a.



Ita ta fara katse wayar,sai shima ya sauke yana kallon fuskar wayar. Inda anni ta sani data qyale walimar nan,duk da ita walima duk inda take albarka ce. Agogo ya kalla har daya na rana yayi,sai ya aje wayar yana jin zuwa yanzu ya kamata ya laluba kitchen ya samu koda tea ne ya sanyawa cikinsa. Duka wani abu daya saba sha da safe irinsu goji berries water da turmeric tea,cinnamon tea da sauransu,wannan ya sanya yake da wani irin cikakkiyar lafiya da kuzarin da idan ya shiga cikin maza kuzarinsa yake fita daban,kaman yadda yake da cikakkiyar lafiya irin ta d'a namiji,wanda yayi imanin banda busy da business daya saka a gabansa suka fatali da komai da yakeji......tabbas da bai isa yakai har wannan lokacin haka ba,dalilin da yasa ya janyewa amfani da wasu abubuwan irinsu ginseng tea,sai time to time idan yana da buqatar hakan,ko ya kwana biyu bai sha ba.



Fararen loopers slipper ya sakawa qafafunshi,wadanda suke mahadi ne na fararen pyjamas din jikinsa da suka fidda siga da surarsa. Yanayin fatarsa kadai ya isa ya fadi maka irin wadata da nutsuwa da yake ciki,skin dinsa so fresh da ba lallai ta wata macen ta samu irin wannan kyan da glowing din ba.



Sai daya shiga toilet ya daura alwala,ya dauki qaramin towel ya tsane ruwan jikinsa sannan ya maida takalmin ya nufi qofa yana gyara hannun pyjamas dinsa daya tattare.



A nutse ta idar da sallara azahar tana maida idanunta wajen sujjadarta. Tana jin idanun a jikinta sunyi mata nauyi,nauyin da bata raba dayan biyu yunwa ce da kuma bacci. Baccin kam tana da tsananin buqatarsa,ita kanta ta sani,saboda ita kanta tasan cewa taci bashin baccin yadda ya kamata,abincinne bata jin akwai muhallin da zata sakashi a cikinta,saidai jikinta na sake gaya mata ya zama dole ta nemeshi.



Dole ce ta sanyata miqewa,a nutse ta nade abun sallar,ta gyara yafen dan madaidaicin hijab din data dauko daga closet din nata ta daure igiyar sannan ta juya tana lalubar qofa bayan shawarar da zuciyarta ta bata nata duba cikin kayan da aka kawo ko zata samu abinda zata saka a cikinta.



A nutse ya sauko daga saman yana sake jin nutsuwa da gidan da tsarin gidan. Ya dauke idanunsa daga hallway din da yake kyautata zaton shiyyarta ne. Qofan dake damansa ya karya zai bude sai kuma ya fasa,ya koma ya kama handle din wooden door din ya bude yana isa ga falon.



Ko ina da komai yana nan kamar yadda ya barshi a jiya,da alamu ba'ayi amfani da parlor din ba kwata kwata. Zarcewa yayi parlor din farko wanda keda kitchen din,ya sauka daga kan step din a nutse sannan ya zarce zuwa dining da hake hango basket akai,da alama saqon da anni tace ta aiko ne.



Yana daga tsaye ya miqa hannu a mamakance ya jawo basket din,yadda aka kawoshi haka aka ajiyeshi,da alama ba'a ko budeshi ba ballantana a taba komai a ciki.



Waye to ya karba saqon ya shigo dashi?. Ba kowa sai ita wannan shine amsar daya bawa kansa,don ya sani ba wanda zaiyi gigin shigowa cikin gidan saboda sunsan doka da kuma tsarinsa. Duk wani ma'aikaci dake aiki a qarqashinsa,daga cikin company har zuwa cikin gida kowa yana tsayawa iya limit dinsa ne,ba wanda yake wuce qa'idar aikinsa ko kuma limit dinsa.



Komai anni ta zuba na duka irin abinda tasan yafiso yaci da safe ya kuma ci da rana,ya sauke qaramar ajiyar zuciya yana sake jin qaunar matar da martabarta suna hauhawa a zuciyarsa. Baiga wani abu da zai taba annin ya bari ba ko wayeshi,take sai yaji ransa yadan baci,ganin kamar ta wofantar da kayan da aka kawo din. Daidai abinda cikinsa yake buqata ya zuba,kafin ya gama duka ya bata wajen saboda rashin sabo,ya manta when last yayi serving kanshi,duk wani motsinsa akwai masi hidimta masa.



Tsaki kadan yaja ganin bacin da wajen yayi,ya soma wassafa yadda zai aje masu masa hidima cikin gidan kaman yadda ya saba,don bayajin zai bari ya takura har haka,ya dauko komai cikin qaramin serving tray ya dawo ainihin parlor din,sai ya azashi saman side table. Har zai zauna sai ya fasa,ya dauko remote yana lalubar channel din dake haska rate na dollar pounds da rate na diamond da sauran harkokin kasuwanci. Har yanzu yana cike da mamakin yadda abun ya kasance,duk da iya bincikensa har yanzu ba wanda yasan daga ina faduwar gold din haka rugu rugu ya samo asali.



Ya soma sipping pomegranate juice kenan idanunshi suka sauka akan basket din. Tun basket din jiya da farouq ya hadoshi dashi,wanda shi kansa baisan anihin meye da meye a ciki ba. Bacin ran da yaketa qoqarin boyeshi dole a wannan karon ya bayyana kanshi.



"What's all these nonsense?" Ya fada can qasa labbansa suna motsawa.



Kamar jira akeyi yayi tambayar yaji alamun motsin mutum. Fararen idanunshi ya daga still cup din yana saitin bakinsa,baikai bakinsa ba bai kuma dire ba,ya zube manyan idanunshi a kanta. Karon farko da ya fara mata kallon kai tsaye a rayuwarsa,karon farko da yayi mata kallon da zai iya gane face dinta.....don kuwa a baya zai wahala ya iya cireta cikin mata goma ko biyar idan aka zube masa su.



Kwata kwata bata lura da mutum ba sanda take sauka daga steps din zuwa qasa don nufar kitchen,amma da yake cikin dabi'arta akwai sanya idanu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login