Showing 78001 words to 81000 words out of 147628 words

Chapter 27 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

da matsala ko damuwar komai". Kai kawai sabreen ke jinjinawa tana sake girmama kaidin maamah din. Ta tabbatar ita zata kawo tsaiko a samun fasfunansu,wataqila ma kuwa an samu ta riqe ne taqi gayawa momma din. Tanason ta yiwa momma bayanin da zata fahimceta,amma kuma bataso ta daga mata hankali. Tana ji a jikinta zata iya komai,kuma wannan lokacin kamar wata dama ce da Allah ya ara mata akan maamah din



"Momma"



"Na'am sabreen"



"Komai da kike kallonsa a haka yanzu a zahiri ba'a haka yake ba........abinda zance rayuwarsu tana cikin hadari babba........basa hannunta yanzun suna wani hannun na daban,saidai bana son ki gayawa kowa,don Allah mommma......koda ta kiraki kiyi kaman bakisan abinda yake faruwa ba.......in sha Allah nan da kwanaki kadan zan turosu su biyoki". Shuru momma din tayi tanaji a jikinta ba lafiya



"Amma sabreen me yake faruwa?".



"Ba wani mummunan abu bane momma,kada ki tashi hankalinki.....kawai dai komai kiyishi kamar bakisan anayi ba" Kai ta jinjina bawai don hankalinta ya kwanta ba sukayi sallama.



Tana ajiye wayar ta sabule zobunan hannunta guda biyu na gold,ta kama hannun titi ta zubasu tana kallon idanunta.



"Yanzu bani da contact na kowa.....inaso ki saida wannan,ki nema mutumin da ya muku visa na fita india ya yiwa su huda duka su ukun komai,inaso kada su wuce sati biyu a nan don Allah titi". Zobunan ta kalla sannan ta maida dubanta ga sabreen



"In sha Allah.....zanyi duk yadda zanyi na miki abinda kikeso". Kai ta jinjina tana jin wata nutsuwa tana saukar mata. Murya ta daga ta kira huda,ta shigo ita daya,abinda ya sanya titi miqewa don basu guri.



"Ina wayar hannunki?" Ba musu ta dauki wayar daga kan cinyarta ta miqawa sabreen din. Saita karbeta tana juyata a hannunta. Waya ce me asalin tsada da kyau wanda kusan sai wane da wane. Idanunta ta maida fuskarta tana kallonta



"Huda baki dago komai ba?,bakiji komai ba game da matar da aka kira da sunan uwar mijina?" Tayi mata tambayar kai tsaye tanason samun wani abu daya danganci maamah. Shuru hudan tayi,tana qoqarin recalling komai,tun daga ranar farkonsu cikin gidan kawo yau.



Siririyar ajiyar zuciya ta sauke,a hankali ta maida dubanta ga sabreen



"Inajin kawai batamin ba.....duk kirkin da take gwadana mana sai nakeji jini na da nata kaman bai hadu ba.......sannan yadda take mana kirki kaman ba haka dabi'arta take ga masu aiki qarqashinta ba" Hudan ta fadi abinda da gaske haka takeji a zuciyarta take kuma hasashe.



Wani siririn murmushi sabreen ta saki tana saukar da kanta qasa gami da juya wayar hannunta. Anzo daidai gabar da tafiso.....anzo daidai wajen da zata gwadawa maamah shege......anzo daidai gurin da zatayi wasa da hankali da kuma tunaninta kamar yadda mage kanyi da qadangare ko bera a duk sa'ilin da yayi gigi ko kakambar shiga hannunta.



Daukewa murmushin fuskarta yayi lokaci guda,ta maida kallonta kan hudan



"Ina fata ba wani abu na cutarwa data taba muku......idan kuma akwaishi ko da da mugun kallo ne ina saurarenki". Kai ta girgiza tana kallon addar tata,tanason kuma fahimtar dalilin da yasa taketa mata tambayoyi haka



"Babu kwata kwata adda......saidai kawai nidai hankalina ya kasa nutsuwa da ita... Musamman da ya zamana kusan ko yaushe tana mana alqwarin zata kawomu wajenki sai kuma ta gaza cikawa.....har sai da mijinki yazo.....shi yace ta barmu muje". Jinjina kai take tana duban huda dake bayani,fuad ne kenan.......me yasa yace suzo din?,shima akwai yiwuwar yana da nashi boyayyen manufar?.



"Kinsan garkuwa tayi daku?,kidnapping a fakaice?" Tambayar ta zowa huda a bazata,ta zaro idanunta waje tana dafe hannunta saman qirjinta.



"Kidnapping fa adda?" Kai ya gyada mata gami da lumshe idanunta,sai kuma tace



"You are free in sha Allah.....zaku bi momma mali soon......abu daya nakeson na gaya miki ko bayan kun tafi......be smart as much as you can.......ki dinga amfani da kwanyarki da basirarki.....ki kula da nadra da Haneefa,ki zame musu garkuwa kamar yadda na zame muku.....sannan......ki zama mara saurin yarda da mutune,walau maza ko mata,a family yake ko a wajen family......saurin yarda tushen kowacce rushewa ce" Ta qarasa maganar tana nunata da yatsa.



Iska ta zuqa sosai sanda take cikin napep din sannan ta furzar da ita waje,tana jinta kamar mutumin daya dauki dutsen dala da gauron dutse yau Allah ya 'yan tashi ya samu saukeshi daga saman kansa. Sakayau take jinta,wani farinciki yana ratsata gami da iskar abun hawa wadda ta manta rabon data ratsata. Ta ware idanu sosai tana kallon titi.....Don yaushe rabonta data fito?,ko fitarta ta qarshe cikin rufaffar mota ne qarqashin kulawar jami'an tsaro.



"Sabreena Ahmad AKA MUHSEENA" Sunan da taji an ambata kenan saitin kunnenta. Ko daga bacci ta tashi tasan waye?......wannan wata shaidace kuma stamp ne daya kasance nasa shi kadai. Mashkur....ta gayawa kanta da kanta,don haka ta tattara dukka nutsuwarta da qarfin halinta ta maida sashen da sautin ya fito.



Shi dinne,zaune a seat din driver,ya dafe dukka hannuwansa saman steering din motar yana jifanta da wani zazzafan kallo. Duk da yadda haushinta da wutar son daukar fansa ke ruruwa a ruhinsa.......amma hakan bai hana shaidan harbawa zuciyarsa wutar matsananciyar sha'awarta ba. A yadda yake hangen wani lafiyayyen kyau a tattare da skin dinta......wani irin kyau da abaya fatarta bata sameshi ba,sai yakejin burinsa ya ninku zuwa gida biyu,YA DAUKI FANSA sannan kuma YA KASHE QISHIRWAR SHA'AWARTA A RANSA. Dadaddiyar qishirwar data maidashi sakarai kuma shashasha a kanta duk da tarin tsananin wayonsa.



"Damn it!" Ya furta da qarfi yana dukan steering din motar tasa gami da cije lips dinsa gami da kashe mata idanu guda daya. Salin alin ta dauke dubanta daga kansa,tana jin wani matsanancin faduwar gaba yana saukar mata. Faduwar gaban da bata taba ji ba a kansa ko akan wani d'a namiji ba idan ka dauke fu'ad din



"To ko wannan shine haqqin aure da kowacce mace kejin nauyinsa a kanta?" Ta tambayi kanta da kanta tana jinjina girman abun. Kafin ya sake cewa komai traffic light ya sakesu,motarsu ta riga tasa yin gaba. Cikin mamaki sai ta samu kanta da addu'ar kada ubangiji ya bashi ikon ganinsu har ya biyosu yaga gidan da take,duk da ta sani......gidan su zai wahala ya zama wani boyayyen gida da zai wahalar da za'a iya ganoshi.





*MUHAMMAD FU'AD*



Basuyi nisa can can ba ya tuna yabar file dinsa a gida,wanda file ne dake da muhimmanci ya dubashi a yau ya tura da bayanan cikinsa ga company din da suka nema sanya hannun jarinsu a kamfanin. Ba kasafai ya fiya son yin alqawari ba tare daya cikashi ba,idan har hakan ta kasance ta tabbas baida yadda zaiyi ne,don haka ya sanya su saddiq sukayi gaba,shi kuma suka juya da wasu motocin suna dawowa gidan.



Wuri wuri zuwaira tayi ta shiga raba idanu sanda taji dirin shigowar motocin nasa harabar gidan. Raba idanu ta shiga yi sannan ta furta kalmar



"Na shiga uku!" Bayan ta tuna gargadin da yayi mata a ranar daya fara ganinta. Yadda tasan halinsa ta kuma haddaceshi bata haddace fuskarsa haka ba,ta tabbatar yazo ya sameta a sassan kamar yadda ya gargadeta shan ruwanta a gidan ya qare. Wani abu guda daya da bata qaunar ya faru......zaman gidan yafi mata zaman ko ina......zaman gidan cike kuma yake da 'yanci,ba kyara ba tsangwama,hakanan ba nauyayen aikace aikace a cikinsa,sabanin gidan maamah din da yake cike da tsarabe tsarabe kala kala.



Wuf tayi ta miqe tana dosar qofar da zata sadata da sassansu kamar zata ci da baka,cikin ranta cike fal da Allah ya qarawa laila tare da fatan ubangiji ya hadata dashi yaci zarafinta har fiye da tunaninta taga yadda abun zai kaya.



Da nutsuwar nan tasa ya shigo cikin falon,idanunsa suna kan inda ta tsaya a dazun sannan ta waiwaya tana komawa ciki. Ya janye lumsassun idanunsa yana wucewa parlor na biyu,daga nan ya doshi qofar da zata sadashi da hallway da kuma stairs dinsa.



Saurin ja yayi da baya kaman yadda itama taja da baya da sauri. Ya zuba mata idanu yayin da ita kuma kwarjininsa yaso bugar da ita. Bata shirya ba amma sai gata tana rusunawa gami da gaidashi



"Barka da safiya hamma.....ya aiki?"



"Kece laila?" Ya tambayeta yana dinke girarsa tsaf saboda yadda yaga abun ya masa wani iri. Ta yaya zata ratsa privacy dinsu ta shigo har nan wajen?,wani irin rashin hankali ne da ita matar gidan zata bari haka ya faru?. Shi din wani irin mutum ne me tsananin son privacy,kamar yadda yake da iyakoki akan komai daya shafi rayuwarsa.....kuma kowanne mutum da nashi iyakar.



Murmushi ta saki tana wani karyar da wuya gami da rolling idanunta a kansa



"Eh hamma.....nice.....baka gane ni ba?,nazo ne duba.....ammm.....ammm sabreen,maamah nason magana da ita da gaggawa,so kuma unfortunately sai na duba ko ina na gidan amma babu ita.....infact ma ta fita.....".



Banbarakwai yaji maganar kamar da wani yare daban take magana. Ta fita?,zuwa ina kenan?,sannan da izinin waye ta fita?. Ajiye duka maganganun yayi gefe guda yana dubanta



"What I have told you tun ranar farko?.....so ki hada kayanki kibar gidan nan" Yayi maganar da murya me kaushi dake cike da zallar umarni.



Hukuncin ya daketa so sai hakanan ya mata tsanani,iya ganinsa data sakeyi yanzu ya sake tada tsimin soyayyarsa a zuciyarta,saita dubeshi a rikice



"Amma hamma....maamah ce....."



"Arguing won't help the situation" Ya fada da wani irin yanayi maras hargagi saidai kuma me ban tsoro ne a idanuwanta. Sum sum da wani irin sagaggiyar gwiwa tsoro da bacin rai ta miqe tana fita daga wajen. Ya bita da wani irin matsiyacin kallo,sannan yaja tsaki kamar zai tsinke harshensa.



Har ya taka stair case din sai kuma ya dakata. Ta fita bata gidan?,maganar ta dawo masa fes cikin kansa. Juyawa yayi don tabbatar da abinda lailan ta fada,ya fara bincike gidan guri guri.



Kaf ya gama duba ko ina a gidan,ya kuma tabbatar bata nan din. Wani wutar fushi yaji tana ruruwa cikin ransa,yana so yaje ya saukewa duka Securities na gidan,amna kuma wata zuciyar na gaya masa MARTABAR AURE koda sunanta MATARKA KADAI A FATAR BAKI.



Samun kansa yayi da bin lafiyar daya daga cikin kujerun parlor din farko,yayi relaxing kawai a ciki yana jin yadda jijiyoyin kansa suke harbawa,ba abinda zuciya bata raya masa ba,ina ta tafi?,wajen su waye taje?.



"Da igiyar aure na?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin yadda zuciyarsa yadda take tafasa. Bai taba tunanin akwai wata diya mace da zai bari tayi masa wasa da igiyoyin aurensa da ya biya sadakin daya nemo da guminsa ya bayar ba,kai koda sadakarta aka bashi muddin da sunan muhammadu fu'ad jikan jadda aka daura bazai taba bari wani abu ya gilmawa mutuncin igiyarsa ba......idan shi ya warwareta tofa wannan daya.



Ba kasafai ake barin napep shiga unguwar ba,wannan ya sanyata dole ta sauka daga baya ta sallameshi,sannan ta fara takawa cikin nutsatsen takunta zuwa street din nasu.



Duk gidan dake da security a wajen suna ganinta sai taga suna miqo gaisuwa da wani irin respect,abun sai ya shiga bata mamaki ita kanta. Wai har girma da matsayinsa yakai wannan?,sannu sannu sai taga alamun mamaki bisa fuskar duk wanda ya ganta tana takowa da qafafunta.



A hankali taji alamun tafiyar tayar mota daga bayanta. Bata waiwaya ba,don tun can dama ita bame damuwa da abinda bai shafeta bane



47



_Daga abdullahi dan abbas R.A yace,Lokacin da aliyyu R.A ya auri nana fadima,sai manzon Allah S A W yace"ka bata wani abu(a matsayin sadakinta),sai sayyadina Aliyyu yace "ba komai a wajena" Sai manzan Allah S A W yace "ina sulkenka?"_









"Ameenatu" Taji muryar nan dai ta dazu tayi kiranta. Sai da taja numfashi sosai tana son danne bugun da zuciyarta keyi sannan ta waiwaya inda ya daidaita motarsa saitinta,yana zaune kusa da window yana murxa steering hankali kwance fuskarsa shimfide da wani shu'umin murmushi.



"Na rantse wannan karon ba zaki sha ba......na miki wannan alqawarin muddin na haifu cikin uwata da ubana......lallai saina maida sha'awata a kanki......sai kuma na bankadawa duniya wacece ke bayan na maido kudadena cikin dukiyata......ki rubuta ki ajiye" Daga haka yayi saluting nata,sannan ya taka motar da gudu yana wuceta.



Bata fasa takawa tana nufar gida ba,kamar yadda bata fasa bin bayan motarsa da kallo ba har ya qurewa street din nasu. Wata mahaukaciyar fargaba tana ratsa zuciyarta,sunan mashkur tare da cikakken sanin wayeshi yana gewa tunaninta,a haka ta isa qofar gidan,ta kuma yi tsaye tana duban dogayen katangun gidan kamar me karantar ilimin zanen gidaje.



Tana wassafa yadda zai iya tsallake wadannan dogayen katangun mansion House din......tana qiyasta ta yaya zai iya wuce wadannan securities din da samudawan dake tsaron kowacce kusurwa ta gidan?. Tsaron gidan kadai ya dan sanyawa zuciyarta nutsuwa.....saidai kuma bai kore fargaba ko kuma ya mantar da ita wanene ASALIN MASHKUR BA.



Gangar hankalinta bata dawo jikinta ba sai data sanya qafafunta cikin gidan,idanuwanta kuma sukayi mata arba luxury cars dinsa dinnan dake ajiye a parking lot na gidan.



Sai yanzu ta tuna bata nema izinin kowa ba sanda zata fita,don sam ta manta hakan yana cikin wata doka dake kan kowacce macen aure.....baya ga haka.....a lokacin ba abinda take iya tunawa illa hanyoyin da zata nesanta rayuwarsu da maamah din.



Da confidence din ba lallai su hadu ba har ta wuce daki.....ba lallai ma yasan bata a cikin gidan ba ta tura glass door din parlor din tana sanya qafafunta.



Da bude qofar da haduwar idanuwansu lokaci guda ya faru. Iya kallon data gani cikin rusunannun idanuwansa sun bata wata fargaba da bata taba jinta akan kowa da komai ba.



Dakiya ta aro ta azawa ranta,tana jin a ranta a yanzu daidai take da kowa a cikinsu.....ko shi ko mamarsa. Tana jin lokaci bijirewa dukka wani sharuda nasu yazo,tana jin abinda ya rage mata biyu ne......ta samu tabbacin fitarsu zuwa mali a sannan takejin zaman wannan qallagaggen gidan dama me gidan gaba daya ya qare mata.



Cikin dakiya da basarwa taci gaba da takowa kaman bataga kowa zaune a parlor din. Tsaf ya gama karanta da kuma fahimtar abinda take shirin aikatawa. Ba za'a fishi sanin miskilanci take taken miskili da kowacce dabi'a tasa ba,sai ya dauke kai kaman bai damu da takunta ba,zuciyarsa na sake matsewa,ransa kuma yana qara baci har zuwa sanda ta raba tsakiyar falon.



Ba zato ba tsammani ta tsinceshi a gabanta. Tsaiwarsa yayi mugun dab da ita,hucin fitar numfashinsa da wani irin dumi da yake bayyanar da bacin rai da zuciyarsa ke ciki yana sauka saman goshinta. Motsawa tayi da nufin ja baya don bata tazara a tsakaninsu qirjinta na wani irin bugawa,saidai da tsananin zafin naman nan nasa ya cafki hannunta yana matsawa da kyau



"Daga ina kike?!,ina kika fita?,gurin waye kika je?" Ya tambaya a jere cikin tsawar data ratsa dodon kunnenta har sai data runtse idanunta.



Tattara dukka qarfinta tayi ta sabule hannunta daga nasa,wanda ta samu sauqin hakanne saboda banguls din hannunta ya riqe saita zame ta barshi dasu,saidai ko taku biyu batayi ba ya rufo mata baya,sai ya zamana tana tafiya da baya da baya,shi kuma yana maida qafarsa kowanne gurbi data cira qafartata.



Kowanne taku guda daya sai qwayar idanunta sun gauraya da nashi. Abinda take gani cikin idonsa batasan wanne iri bane......wani yanayi ne da bazata iya fasaltashi ba. Yana sake kunsatota yana sake maimaita mata tambayoyin da suke sake razanata,bata ankara ba taji ta bugi bango,tabbacin kowanne space ya qare mata kenan,sai tayi cak sanda ya iso dab da ita,cikken motsi idan tayi yana iya sata ta kasance cikin jikinsa.



"Gurin wa kika je?,me kuma kikaje yi nace!"



"Ban sani ba" Ta fada da rawar murya tana qoqarin daidata mode dinta. Ko kusa ko alama bata tanadi amsar da zata bashi ba.....shi kuma ya matsa mata da tambaya.....tambayar da ba abinda take mata sai qara fusatata......GURIN WA KIKA JE?,ME KIKAYI?,idan ya fada din sai taji kamar ha debo garwashin wuta ya watsawa sassan jikinta ne. Ba abinda yake tuna mata sai mummunar kalmar yawan mutane musamman na cikin gidansu suke jifanta da ita.....kalmar da koda ta nuna ta shanyeta tana iya hana idanunta bacci da wani matsanancin fushi da bacin rai.....shima irinta yakeso ya ara ya yafa yayi aiki da ita a kanta?,batajin kunnuwanta zasu iya jurar ci gaba da jin ana jifanta da kalmar da bata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login