Showing 117001 words to 120000 words out of 147628 words

Chapter 40 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

taji tana tsananin buqatar ganinsa.



"Ke nake sauraro" Muryar fareeda ta yanke mata tunaninta. Idanu ta zubawa fareedan na wasu daqiqu kafin ta kammala tunani a kanta dukka cikin sakanni,murmushi ta sakar mata.



"Mu da kikaga muna cimma nasara a rayuwarmu......ba da gaggawa muke tafi da komai ba......kibarmin komai a hannuna......indai kinga baki samu fu'ad ba.....to tabbas bani na haifeshi ba". Maganar ta faranta ran fareeda duk da ta xuba mata kokwanto me yawan gaske. Amma itama ta yarda da kanta......tasan kuma nata kalar takun,don haka ta miqe da nata murmushin tana ajiye mata bundle na dollars.



"Ki qara da wannan......amma buqatata yazo ya ganni koda na minti talatinne kacal" Ta furta tana zuge zip din Jakarta,a qasan ranta kuma tana samun tabbacin da gaske ne fu'ad baya sakar mata zallar ruwan kudi.......abu na farko daya fara jefa mata shakka a zuciyarta akan matar.



Matashin billionaire irin muhammad jadda......wanda tsananin yawan dukiya da arziqin daya mallaka a gefe guda quruciya da kyau su suka saka mata kwadayin mallakarsa......kudaden data bata din ya kamata ace a kullum a arziqinsa basufi kudin siyan wasu qananun abubuwa ba....amma ya zamana ita ke fara'a da samunsu?. A arziqin mahaifinta idan aka kasa arziqin fu'ad hamsin qwaya daya ne.....amma ace ita karan kanta tana da qarfin halin yin kyauta irin wannan?. TABBAS AKWAI MAGANA.....MAGANGANU MA,ta furta a sarari qasa qasa.



Kudin kawai take juyawa a hannunta farinciki yana kamata. Ta samu kudin da zata tunkari aikinta,duk da tana baqincikin yadda kudin xasu salwanta,amma kuma idan ta tuna da ribanya ribarsu da zatayi sai taji koda ta salwantar da finsu ma ba komai bane. Saidai tana buqatar magana da yarinyar.......maganar da zata sake bata haske akan mataki na gaba da zata tabbatarwa boka shi take da buqata. Wa zara kira?zuwaira.....



Kira daya biyu uku hudu har goma wayar zuwaira a kashe take. Tayi tsaki har batasan adadinsu ba,da waye zatayi magana ya hadata da yarinyar?. Tsam ta miqe data tuna daxun maganarsu ta qarshe zuwaira ta gaya mata yarinyar taje gidan ita da mamarta,saidai batasan ko tana can ko sun dawo ba. Ta qwalawa badawiyya kira



"Ki tafi gidan hamza ki karbomin number wannan yarinyar"



"To hajiya" Ta amsa mata a ladabce sannan ta juya tana ficewa ba tare data tsaya jiran komai ba.



Hannunsa ya sanya saman labbansa kawai yana sauraren bayanin manager na gidan jarida na qarshe da yakeyi,wanda banbancinsa dana sauran qalilanne



"Amma wallahi wallahi ranka ya dade kaman yadda 'yan uwana suka fada ne......wallahi bansan sadda aka buga labarin ba......ni dinma kamarsu gayyata na samu na taron 'yan jarida unexpected.......amma sanda na iso na samu jaridar ta fara fita hannun dealers na dakatar da saidata......waye zaiyi wasa da mutum kamar kai?,wanne gangancinne zai debi mutum......ko baya ga haka kana da mutunci da martabar da bai kamata mu bari a bata sunanka dana iyalinka ta wannan hanyar ba" Mutumin da aqalla ya kusa shekara sittin a duniya ya fada cikin matsanancin takaicin yadda duk karamci irin na jadda jaridarsa ta shiga sahun wadanda suka ci masa mutunci....duk da Allah ya taqaita an daqile fitar jaridar.



Iska me zafi ya furzar daga bakinsa yana sauke qafafunsa qasa,kanshi yana sake daukan zafi da lamarin.



"Inason list na dukka mutanen dake da aiki a ranar a dakin buga labarai.......da full details na kowa" Ya fadi a ransa yana jin zaiyi aikin daya jima baiyi ba.



"Sir.......ai mun kammala wannan.....muna jira ne kawai ka gama ji daga bakinsu......dukkanin dealers din mun karbi copy na newspapers din daga hannunsu,yanzu haka ba wanda keda sample nata.....Allah yasa munyi abun da sauri basukai ga rarrabawa qananun 'yan kasuwa ba,mun samu dukkanin jerin mutane hamsin da uku dake da aiki ranar a gidajen jaridu ukun......saidai mun rasa mutane uku a ciki,mutum daya daga gidan kowacce jarida......abinda ya qarfafa zarginmu akan suke da hannu.......na tura ma'aikata don binciken inda suke,kuma ina saka ran koda wanne lokaci zasu bani information,amma sauran mun tabbatar basu da masaniya akan komai" Wani abune daya tsaya masa tun jiya ya dinga sulalewa yana narke masa,ya gyada kai yana jin sassaucin dunqulallen abun daya tare masa wuya. Kafin yayi magana aka nemi izinin shigowa dakin. Ma'aikacin ya duba ya kuma bada izinin shigowa.



Salute nasa sukayi mutum biyun da suka shigo,suka kuma miqa masa wani takardu.



"Auwal sadi.....nura mahadi......labaran isyaku.....gaba dayansu mun samu tabbacin sun fita daga qasar nan kusan awanni biyu da suka shude,saidai kowannensu mun samu tabbacin qasar daya sauka.....auwal ya sauka a uk.......nura South Korea......shi kuma labaran ya sauka a china".



"South korea.....UK.....china" Fu'ad ya furta sunayen a fili yana irgawa da yatsunsa,sai ya fesar da iska a bakinsa yana maida dubansa kan CP.



"Well done sir......i really appreciate your effort,thank you for your hard work.......a sallamesu inason muyi magana privately"



"Okay sir" Ya amsa masa cikin girmamawa.



Cikin qasa da mintuna ya sallami kowa,ya kuma riski fu'ad din cikin motarsa qirar Mercedes sprinter. Duk yadda yaso mazewa da ganin alatun dake cikin motar tamkar kana cikin wani hamshaqin parlor din bawai mota ba amma ya gaza,sai daya daga kanshi ya kalli saman roofing din da yafi kama da lafiyayyen roofing din dakin sanda fu'ad ke qara hasken cikin motar daga galaxy blue stars zuwa brighter light.



"Ina expecting tafiya nan da kwanaki uku......inason kayi gaba da kula da komai har zuwa sanda zan dawo......saidai banason binciken ya dakata......zanyi qoqarin ganin an kawosu daga dukka qasashen da suka tsallaka din don su fadi wanda ya basu contract din......wadancan mutum biyun kuma,ko tambayarsu bana fata kuyi.....ajiya na baku......irin ajiyar nan ta ma'anan ajiya" Yakai qarshen maganar yana tura cheque na kudi daya rubuta masa masu yawan gaske. Kai ya girgiza



"Nop sir.....bazan amshi komai ba,aikina ne nakeyi kuma dole mutum irinka a masa aikin daya dace saboda alfanunsa ga al'umma". Wani abu dake gefansa ya dannan wata qaramar ma'ajiya ta fito,ya jefa cheque din yana cewa



"Ba bribing naka nakeyi ba.......wannan din kyauta ne na baka,na jima da sanin wanene kai......inda baka cancanata ba ko qwandalata ba zata shiga hannunka ba.....kana daya daga cikin mutane masu aiki tuquru da qoqarin kamanta gaskiya duk da yadda qasarmu ta lalace.....so you deserve it,xan baka koda bakamin aikin komai ba"



"Thank you sir.....thank you so much" S.nuhu ya fada yana jin dadin gwaggwabar kyautar da me jadda din ya bashi.



Tunda wuri taqi zaman parlor din don batason ma ya dawo shi ya gansu ko ita ta ganshi,ta zame tayi zamanta a daki dole amna ma ta biyo ta can.



Tana saman sofa din dake gefe daya a dakin,amna na zaune saman tattausan carpet din tana assignment. Idanunta kan takardun tana jin sha'awar amna din,tana jin inama ace itace ta samu dama irinta amna?,inama ace ta samu daman zuzzurfan karatu kaman amna?,wadda gata ya sanya tace bazatayi karatu wata qasar ba tsabar samun dama.



Maida bangon littafin tayi tana duban sabreen cikin murmushi



"Done......sai yanzu hankalina ya kwanta...lecturer dinnan mugu ne adda.....any mistake game over" Murmushi ta tayata dashi,ta jawo jakarta tana qoqarin maida litattafan



"Adda......kin taba jin labarin labarin uwar data watsar da yaranta tun suna qananu ba tare data damu da waye zai kula dasu ba?,waye zai zama gatansu?" Takai qarshen maganar tana zuba idonta akan fuskar sabreen. Maganar sai tayi ma sabreen wani iri,a hankali ta girgiza kanta



"Aah amna"



"Kin taba jin labari,bayan wasu shekaru ta dawo garesu,amma kinsan me yasanya ta dawo garesu?" Kai sabreen ta sake girgizawa



"Kudi......arziqi da rufin asirin da suka samu tazo ci,ba yadda suka rayu bane damuwarta......ba lafiyarsu ko akasinta ba". Idanu sabreen ta zubawa amna tana jin labarin ya kasa kama hankalinta,tsahon wasu mintina ba wanda yace da kowa komai,har sai da sabreen ta fara magana



"Wanne irin cukurkudadden labari ne wannan amna?,a ina kika jiyoshi." Qaramar dariya amna ta saki tana janye jakarta gefe



"Labarin mijinki kenan.....hamma na....." Bata qarasa ba shigowar saqo wayarta ya katse sauran maganar dake bakinta. Wani irin shuru sabreen tayi lokacin da hankalin amna yayi kan wayarta



"Maamah?,mariya?....." Abinda kawai sabreen ke iya juyawa cikin ranta kenan



"Bai rayu da ita ba?......batasan komai nasu ba?......batasan wahalarsu ba?,dukiyarsu tasa ta dawo??,dukiya???" Tarin tambayoyin da suka jujjuyawa cikin kwanyarta kenan. Maganganun amna gaba daya sai suka kasance mata kamar ta jefeta da wata cukurkudaddiyar sarqa,ta kasa hada daya da daya ya bata biyu.



"Unbleavable!......oh my god!" Amna ta furta da wani irin qaraji,abinda ya yanke zaren tunanin sabreen kenan,ko kafin ta farga har amna ta fado jikinta ta cukuikuyeta



"From nigeria to Maldives........wedding bells adda.......wedding bells" Ta fada tana dariyar dake cakude da farinciki zalla a muryarta. Qoqarin dagata sabreen takeyi cikin murmushi da mamakin abinda ya sanyata tsananin farinciki irin haka



"Zaki karyani auta" Ta fada a dan shagwabe tana riqe amna din. Da sauri ta dagata tana fadin



"Am sorry adda.....wani irin mamaki uncle BB ya bani......yayi surprising dina irin wanda ya jima baimin ba......adda hutunmu na wannan shekarar zai fara daga Maldives......kinsan mafarkaina akan wajen kuwa?,kowanne year idan anzo zaben wanne qasa za'a je idan na kawo sai BB da saddiq sun kushemin.......yaa musaddiq kawai ke goyon baya na" Ta qarasa maganar muryarta a narke,da alama tana jin haushin yadda abun yake kasancewa. Dan murmushi sabreen ta saki,don ita inda take maganar ma batasan ina bane ballantana tasan muhimmancin da yake dashi ba da za'a dokanta aje.



"Your dream have come true"



"Really adda.......adda wannan shine tafiyan da zatafimin kowacce dadi da alama......ina da sister like you nima wannan karan.......ha saddiq ya daina yimin gori idan za'a fita......i don't know yadda zan miki bayanin Maldives......but gani ya kori ji" Dan qaramin murmushi ta aje mata kawai don ita bataga wani abun doki ba a nan.



"Labari na biyu adda.....muna da biki,borno zatayi kira......bikin BB farouq date din yayi daidai da dawowarmu da sati biyu kacal".



"Ma sha Allah.....Allah ya sanya alkhairi"



"Wannan qarshen shekaran bame sauqi bace adda......can't wait......bari na bawa besty labari" Ta fadi tana laluben number wayar aminiyarta guda daya da take da ita.



"Adda......anya ba honeymoon BB farouq ya hada muku keda hamma ba?" Amna ta dakata daga qoqarin kiran besty din nata da take tana duban sabreen. Bata jira ma sabreen ta bata amsa ba ta saki dan qaramin ihu tana tsalle gefe



"It makes sense=�L�.....that's my big bro farouq" Amna ta fada tana dariya nishadi kaman zai kasheta. Baki kawai sabreen ta kama tana kallon amna



"Amna......nace miki binku zanyi?". Tana dariya ta bata amsa



" It's for the whole family adda........kowa ma yana tafiya hutu a wannan lokacin,indai kai under jadda family kake......hatta ma'aikatan dake aiki cikin gida lokacin hutunsu ne.....kawai dai,nayi mamakin rage date din da aka saba tafiyan" Ta fada tana duba wayarta.



Rasa abinda sabreen zata fada tayi,maganan gaskiya ita sam bata shirya zuwa ko ina dasu ba,don bata jin tana cikin family dinsu,hasalima tazara take son bayarwa tsakaninsu.



Duk sanda amna ke waya da qawarta ita tayi nisa wajen juya maganganun amnan. Wani irin mamaki ke tsarga mata,wai dama haka matar take tun usul?,ta yaya zata samu gaskiyan abinda amna ta gaya mata?,tun tale tale gurbataccen hali gareta?,indai haka ne mene yaran sukayi me muni da zata cutar dasu?. Kwanyarta ta sake harbawa,da qarfi da yaji ta soma qoqarin hada daya da biyu ko zata bata daidai









*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862





67





_Manzan Allah S A W yace "idan dayanku zaiyi fada/zai daki dan uwansa,to ya guji fuska/kada ya mari fuskarsa_



>���<��� _sai a kiyaye,mari ko dukan fuska haramunne a musulunci_







"Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta



" Adda......maamah keson magana dake" Amna da sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana.



Hannu kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta.



"Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?"



"Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?". Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani qudundunanniyar ma'ana.



"Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba



"Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta



"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta.



Ko da amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra data zame musu dole duk lokaci irin wannan.



Dukka maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya furucinta ne ke mata kai kawo a rai.



Tanaso jin rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da shedaninta dake gefe suna gaya mata



_karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine

'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da rashin nasara haka ba.



Tunda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da take da muradin qarasawa ba.



Wayarta ta fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice.



Dab da zata bar falon taji laila na kiranta



"Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa.



"Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci



"Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba" . Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata



"Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki"



"In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya"



"Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa da dama.



Tafiyar awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun tsirrai tana wucewa ciki.



Gurine da zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli yaumin neman duniya,tamkar sun manta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login