Showing 93001 words to 96000 words out of 147628 words

Chapter 32 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

zaki iya to bismilla,ga fili ga me doki,kinsan dakin dana sanya aka sauketa ai" Ta furta tana nuna mata hanya,sannan ta juya hankalinta kwance tana fita daga dakin.





&k'arfe biyar da rabi yammacin ranar jerin luxury cars dinsa sukayi matsugunni a babban sashen ajiyar motoci na mansion House din nasa. Wani baqon abu daya kwana biyu baiyi ba,wato dawowa gida a lokaci irin wannan. Dawowarsa da wuri shine qarfe takwas zuwa tara na dare,wanda ita kanta matar gidan batasan lokutan dawowarsa ba.



Kaman ko yaushe daga farfajiyar gidan ya tsaida kowa ya kuma sallami kowa,wanda kusan quarters ne guda daga can wani sashe daban na gidan da yawancinsu suke da nasu apartment din,ba lallai ma ka fahimci da wasu dake rayuwa cikin gidan bayan ainihin masu gidan saboda nisan tazarar dake a tsakaninsu.



A hankali yake takawa zuwa ciki suna magana da farouq qasa qasa.



"Na fita daga company,kuma ina tunanin sai gobe zan sak shiga......wani irin headache ne yake matsamin tun jiya......but daga dazun zuwa yanzu kaman ya qaru"



"Dude.....kana over work fa?,Allow your self downtime......kana da aure amma a suna kawai......kasan benefit na aure kuwa da ba zasu qirgu ba?....Emotional support and mental health duka zaka samesu if ka bawa matarka damar shiga rayuwarka"....





" Hey.....zaka fara ko?,waye ya gaya maka kowacce mace ake bawa dama ta shiga rayuwarka?,wasu matan poison ne fiye da yadda kake kimantawa,they are wicked" Ya fadi yana hadiye wani yawu lokacin da madaurin tunaninsa ya warware yana koma masa can shekarun baya.....sanda maamah ta zama silar rasa lafiyar mahaifinsu duk da kasancewarsa mutum ke kazar kazar,ta kuma zama silar barinsa sararin da suke kai yanxu suke rayuwa akai wato DUNIYA. Daidai sanda ta sauka daga saman high chair din data zauna a akai cikin kitchen din suna taba hira da ma'u,wadda take hada qullin wainar shinkafa zata soya musu



"Bari na dauko na dawo" Tace da ma'u din tana gyara yafen qaramin Chantilly veil din data lullube sassalkan gashinta. Furucin nasa ya sanyata tsaiwa cak sanda muryarsa ta kaiwa kunnuwanta saqon da yake isarwa farouq,sai taja da baya tayi tsaye jikin qofar yana jiran wucewarsa don ta wuce itama zuwa dakin.



"Let's try not to judge people and instead understand their perspectives".



"Am not judging fa......dude ba zaka gane bane,na iso gida.....i need to rest.....call you later"



"Okay byee" Farouq ya fada yana sauke wayar iska ya furzar daga bakinsa yana duban file din dake gabansa cikin katafaren kamfanin sarrafa kayan abincinsu dake sharada industrial area. Yanaji a ransa zai sake rage kwanakin tafiyar nan tasu ko wataqila hakan zai kawo kasuncin da yake fata tsakaninsa da ita. Yasha attempting saka amna cikin abun,yasan zatayi aiki sosai.....saidai kuma amna din quruciya tayi mata yawa,baisan ya zata dauki abun ba,uwa uba yana buqatar yayi komai cikin sirri.



Shurun da taji cikin parlor din ya sanyata tunanin ya wuce,ta sauke siririyar ajiyar zuciya,kunnuwanta na maimaita mata da meye da meye ya fada akan mata?. Siririn tsaki ta saki zuciyarta na siffantashi da jerantashi cikin sahun mazan da sam bausan mutuncin diya mace ba....suke mata kallon kuma wata halitta da bata da wata daraja kwata kwata.



Siririn tsakin daya sanyashi daga kansa a hankali daga rufe bottle na ruwan da ya tsaya ya bude yasha saboda yadda maqoshinsa ya bushe,yana ji kamar bazai iya qarasawa saman ba.



Guri daya idanunsu suka hadu,ya kafeta da qwayar idanunsa da sukayi wani laushi tubus saboda yadda ciwon kan ke sara masa lungu da saqo na cikin kansa. A hankali ta zare nata idanun daga kanshi,sannan ta koma da baya zuwa kitchen din ba tare data qara koda second uku a wajen ba.



Kansa shima ya dauke yana ajiye robar,sannan ya soma takawa a nutse yana wucewa ciki kafin ya haura zuwa saman. Tun daga wancan ranar bai qara ganin gilmawarta ba cikin gidan,wasu lokutan ma sai yaje gaida anni ta tambayeshi iyali take fado masa a rai. Wani irin mummuna fito na fito yayi da kansa akan damuwa da abinda tayi masa a ranar din,yana ganin bai cancanci ya sanya damuwarta a ransa har haka ba.....sai ya sake qarawa kansa wani busy din akan wanda yake ciki,yana saka ran wannan ya zama silar mancewarsa da komai,wanda yawan ayyukan da suka zarta qa'ida din daya azawa kansa yake kyautata zaton shine silar wannan ciwon kan da ya fara fama dashi.



A gajiye da wani irin bacin rai da baisan meye dalilin faruwarsa ba daga shigowarsa gidan ya dinga zare suit din jikinsa yana zubarwa,duk da cewa ba al'adarsa bace hakan.



Bathroom ya wuce kai tsaye,ya hada ruwa me dumi da zai dace da yanayin sassanyar iskar dake kadawa,wanda asalinta hadarine daya hado,bai saukar da ruwan ba,amma ya canza kala zuwa ruwan toka,ya kuma bada iska me sanyin dadi dake busawa da qamshin qasa,yanayin da yake bada tabbacin anyi ruwa a wani gurin kusa da kano.



Mintuna kusan arbain ya fito daure da towel,gargasar jikinsa dama sumar kansa duka sun jiqe da ruwa. Faffadan qirjinsa dake lullube da gargasa ya fara gogewa da towel din yana isa gaban madubi,daidai sanda yaga wayarsa na haske. Kaman ya share saboda bayason doguwar magana,amma koda ya duba yaga maamah ce sai ya zamana bashi da wani zabi daya wuce ya daga kiran.



Sai daya zauna saman bean bag chair din dake ajiye a gefe sannna ya daga hade da sallama.



"Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe idanunsa saboda yadda kansa yake sarawa.



"Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan kun tashi,akwai muhimmiyar magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson ganinka" Ta fada kanta tsaye. Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero buqatunta kai tsaye ba tare da neman jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta itace kadai damuwa zata sauya ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba ta aje tata damuwar da son kan a gefe ba.



"Bana company na dawo gida....."



"Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason ganinka lallai lallai a yau din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni" Ta sake fadi da dukka sautin da zai gaya masa da gaske take.



Jaririyar ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa



"Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya fada da raunanniyar murya,yana jin har qasan ransa ya rasa wani part me girma a rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana da anni,yana da farouq,yana da saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin kamar shi kadai ne.....yanajin kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin maraici da kadaici yana mamayarsa.



"Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya sawwaqe" Ta hade maganar duka lokaci guda.



Ya jima idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa abubuwa da dama ciki harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci idan dayansu baida lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame damuwa da lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi.



Sai daya bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet dinsa,boxer kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe jikinsa da turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na saukar da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen dakin dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki.



Cikin duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke nannauyan numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce.



Ana kiraye kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya daukeshi,yaji dadi sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala. Masallaci ya wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya shirya cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar royal blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan wandon da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa ruwan gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala ka kalleshi sau daya ka kauda idanu

(Niko nace uhmmmm,kaman kuwa yasan zance akazo yi gurinsa=��).



Clogs ya sanya gold color,ya feshe jikinsa da mayen turarensan nan dake saurin kama zuciya.



Key ya laluba a ma'ajiyarsu ya dauki spare key din daya daga cikin motocinsa. Yau din da kansa yake sha'awar yin driving,abinda ya jima rabonsa da yayi. Yanason ya shaqi fresh air dinnan shi kadai ba tare da wani a gefensa ba wai da sunan yana kare lafiyarsa ba.



Ta kammale komai a daki kaman yadda ta saba duk dare,wanda idan ta shiga kuma ita da fitowa koda hallway ne sai kuma da safe. Tun wancan ranar ta sake jin ta tsani dukka wani abu da zai sake hadasu ko ya hada alaqarta dashi. Idan ta tuna tambayarsa din kuma takanji wani mugun haushinsa na sake mamayarta,tana jin a sannan me yasa bata amsa masa da eh wajen wani naje ba?.



Sai data zauna tsaf sannan ta duba night stand fridge dinta babu ruwa ko qwaya daya a ciki. Baida girma fridge din,don haka kadan kadan take saka ruwan saboda gorar zata cika waje. Miqewa tayi tana yamutsa fuska,ta dauki Indonesian hijab dinta navy blue ta zura wanda ya haskata matuqa,ya kuma fidda lallausar sumar dake kwance gaban goshinta. Harta miqe ta dauki wayar huda da zuwa yanzun tayi nisa da amfani da ita,tayi playing drama din da take kalla daga inda take,a haka ta fita rabin hankalinta yana kan wayar.



Wannan dalilin ya sanya bataji saukowarsa ba daga stairs din saboda lallausan clogs din dake qafarsa baya bada sauti ko kadan,duk kuwa da cewa da dan sassarfa yake saukowar yana gaggawar isa ga mota,so yake yaje ya dawo da wuri akwai ayyukan da bai samu daman yi ba dazu,yanaso ko cikin daki ya ragesu.



Stairs din ya danyi kwana kadan wanda sai kazo rabi sannan zaka hangi wanda ke fitowa daga farkon hallway din,kaman shima......sai daya zo rabi sannan ya ganta. Idanunsa suka sauka saman fuskarta data fita fes cikin tsakiyar hijabin kalar luxury Morocco din jikinsa. Hasken dake fitowa daga cikin wayar ya haske fararen idanunta dake sheqi kamar an diga mai. Bai fasa saukowa ba kaman yadda taci gaba da takawa idanunta kafe akan wayar,har sai da cikin jikinta taji kamar ta iso qofar da zata sadata da parlor din.



Daga kan da zatayi ta tsinceta dab dashi sanda yake stair din qarshe. Sai ta juya a hankali da zummar yi masa yadda ta saba wato komawa don ta kubcewa hada numfashi dashi.



55





_Daga abu hurairah RA yace,manzan Allah S A W yace: "ku kashe baqaqe guda biyu koda kuna cikin sallah; MACIJI DA KUNAMA_









Taku biyu kacal tayi ya cimmata,ya kuma sanya hannunsa ya dawo da ita baya,sai gata tsaye cak a gabansa kaman ba inda ta matsa. Idanunta tsakiyar nasa idanun da suka qaa girma kadan saboda ciwon kan dazu,yayin da hucin numfashinsa ya dinga fita cakude da qamshin turaren jikinsa yana kaiwa ga hancinsa.



"Wanne kalan dodo ne ko abun tsoro a jikina da kike gani?" Ya jefa mata tambayar a zafafe yana ware mata idanunsa. Ja baya tayi niyyar yi da sauri saboda yadda ta dan tsorata kadan da yadda idanun nasa suka qara girma,ga wani shimfidadden kwarjini dake fita daga cikinsu ya daki zuciyarta lokaci guda ya kuma ninka gudu da bugun zuciyartata.



Hannunsa qwaya daya ya sanya yasake dawo da ita gabansa yana sake bude mata girman dukkanin idanunsa.



"Ki nunan abinda ke baki tsoro a jikina nace!" Ya fada da dan tsawar takaicin abinda takeyi masan. Shi tun farko mutum me dan kai tsaye,koda laifi kayi masa yafison ka fuskanceshi kai tsaye.....haka koda matsala kake dashi yafiso ka tunkareshi kai tsaye ku warwareta.



So take ta maida masa me zafi ko zata fanshe abinda ya gaya mata ranar nan,amma sai ta lalubi kwanyarta da bakinta tsaf ta rasa komai kamar an mata sata.



Ringing din wayarsa ne ya sanyashi maida dubansa ga wayar. Kusan a tare idanunsu suka kai kai,kuma daga shi din har ita sunga sunan da yake rubuce a kai FAREEDA KHALED MUSTPHA.



Maida dubanta tayi ga fuskarsa ba tare da tasan dalilin hakan ba,sai kawai ta zabi ta zille ta tsakanin qofar ragon da yayi mata,saidai kuma tana motsawa kamar hankalinsa yana maqale ne a jikinta ya daga kai ya watsa mata idanunsa bayan ya maida wayar aljihu ya sakeyin kicin kicin da fuska.



"Daga yau duk ranar da kika qara ganina kika koma kaman kinga dodo saina biki har cikin dakin na zaneki tas ciki da baya". Maganar tayi mata banbarakwai,kamar wata nadra ko haneefa?,wannan mamakin ya bayyanata tsakiyar qwayar idanunta da baisan me yasa yake yawan sanya nasa idanun a cikinsu ba duk sanda magana irin haka ta hadasu.



"Kina mamaki ne?,ko kina ganin kin wuce duka?,ki gwada koda gobe ne ki gani.....and,daga yau kada ki sake ganina baki gaidani ba......tunda ko banza ana ci dake ai ko?,koda ban baki abinda wadancan suke bakin ba" Ya qarashe maganar yana sakar mata hanya.



Cikin qasa da second uku ruwan hawaye ya tararwa idanunta,ya za'ayi ya qara mata ciwo akan wancan ciwon,tana jin lallai yau ta barshi ya tafi haka yaci bulus din da ba'a taba cinta a kanta ba



"Ka daina burga kaman kana da abun bayarwar.......ni bana buqatar ragowar su fareeda tunda akwai masu fresh......." Cak maganar ta tsaye mata a maqoshi sanda yayi wani irin waiwayowa daidai sanda yake dab da zarcewa falon. Batasan ta juya ba har ta soma tafiya zuwa dakinta ba sai da taji tana taka lallausan carpet din dake shimfide daga tsakiyar wajen.



Dif wuta ta dauke masa,zuciyarsa ta shiga raya masa nau'ikan hukunci mafi tsauri daya dace yayi mata. Saidai kiran wayarsa ya sake katse masa duk wani hanzari,ya duba kiran a fusace yana tunanin fareeda ce,amma ganin maamah ya sanyashi tattare duk wani bala'i daya taso masa ya hadiyeshi,sannan ya daga wayar yace da ita a taqaice



"On my way"



"To ka hanzarta" Maamah ta fadi tana jin dadin yana hanya bawai yaqi amsa kiran nata bane.



Kai ya jijjiga yana takawa a hankali yana ficewa,saidai a ransa yaci alwashin dole ya ajiye mata abun tunawar da bazai sake fadin magana ta maida masa ba. Duka duka shekarunta nawa amma sanadin aure raini yana neman shiga tsakani?". Ya fada qasan ranshi sanda yake tayar da motar.



Da wani irin speed yake jan motar,wanda dama sabonshi ne gudu a mota,ba tun yau ba ba kowa ke iya shiga mota ba indai shine zai tuqa. Idonsa ya lumshe yana tuna abinda tace masan,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa.....zai wahala cikakkiyar budurwa me kunya ta iya fadin hakan.....ita kuwa bata cikin kowanne sahu,dom haka idan ta fadi sama da haka ma fuad kada kayi mamaki.....kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa.



Har ya isa gidan maamah wannan kalmar ta kasa fita a ranshi



"Ragowar su farida....kamar ma kana da abun bayarwar" Har cikin ransa ya gamsu ta rainashi,sai ya samu Kansa da kallon Kansa a side mirror,yana tuna dararen da yake kashewa a tsaye ba tare daya isa ya kwanta ba bare ya samu cikakken bacci saboda tsananin yadda ya kame kanshi. Da wannan bacin ran,da kuma tunanin hukunci mafi tsananin daya kamata ya dauka ya isa parlor din maamah.



Mamaki na gasken gaske ya cikashi lokacin da yayi sallama ya tsinci fareeda cikin masu amsa masa sallamar tasa. Tana zaune hankali kwance saman sofa din parlor din. Sanye take da riga da wandon Palazzo daya bude sosai daga qasa. Rigar me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login