Showing 87001 words to 90000 words out of 147628 words

Chapter 30 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

jama'a,WANNAN ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_*







*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



51





_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_



_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_









Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana da ita sannan zuciyarta taci gaba da kwabar data fara mata.



"Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya amince da ita?,kada yaci abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika bashi tabbaci akan ingancinta da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin saman zargin dake kansa naki?".





Wannan tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da tazo kai,a gefe guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko tuntubarta akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA BA QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai



"Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a bayyane,daidai sanda taji an murda qofar dakin an shigo laila ta bayyana.





Da kallo tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman gwiwoyinta wani abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar mahaifiyarta shekara da shekaru.



"Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi har bata iya hada idanunta da nata.



Kai ta daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata jiya sai ya shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani bacin rai da radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga waya kawai tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana jin kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa mata gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a rayuwa bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin maamah.....ko kuma tayi wani abu da zai saba umarninta.



"Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya sanyata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu tayi daya bata mata rai ba.



"Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara miki,saiki duba idan akwai abinda baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A nutse take qarewa laila kallo,ji take a ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu da batasan wanne irin farinciki take ciki ba.....lallai da zata kasance wata halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa wannan tunanin tana runtse idanunta gami da budesu.



"Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki sake"



"To ba matsala.....waida so nake naje wajen hajja.....jiya muna magana bamu gama ba kika kirani" Kai ta girgiza,duk da tanason sake samun information,don tayi imanin duk abinda zasu tattauna tamkar a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta kammala da aikin sabreen tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne.



"Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na gani idan ya dace kije goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon wayarta cikin jiran tsammanin shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci.



Sanda laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki bayan sun gama wayar tana jinjina kai



"Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da gogewarsa sai a cikin kabarinki,a sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta gauraye da qasa,kin bani qofofi masu yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan shiga ta kowacce qofa......na fita ta kowacce qofa.....na shiga kuma cikin rigarki na dimauta duniyarki......sannan na hana muradinki da mafarkinki su zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa wayarta idanu dake aje tana ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo.



Tun safen har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar kiransa take. Sai bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu aikinta suka shaida mata tana da baqo me suna hanzari.



"Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a waje" Ta fada cikin doki da zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta maida kanta,har ranta tana jin mafita tana tunkaro ta.



Fitowarta ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman daya. Sanye cikin baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa kadan.



"Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata nannadaddun takardun dake hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba sannan ta zauna dasu ta soma budewa tana cewa



"Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari kamar yadda sunanka yake" Ta fadi a nutse tana bin list na sunayen da kallo da kuma hotunan.



Sai data gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana kallonsa



"Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada kai ranta yana yin fari.



"Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya dace mu dauka?" Ta fadi maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba yayi kadan ya miqa mata hannunsa yana cewa



"Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza takardar saman teburin dake tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya daidai fuskar mashkur,sai ya daga kai yana kallonta.



Duk da baiyi magana ba bai kuma ce komai ba amma maamah ta fuskanci abinda yasa gaba da abinda yake nufi. Sai ta zuba masa idanu tana sauraron qarin bayaninsa.



"Wannan shine mashkur......dan tsuntsu me wayo kenan..." Yayi maganar yana sake xuba yatsunsa saman fuskar mashkur. Sake jan hoton gabanta tayi,tunda ya aje din dama kusan fuskarsa tafi jan hankalinta. Yana da kyau daidai misali,wanda zaiyi daidai da plan dinsu,ta jinjina kai tana duban hanzari



"Yayi......a tsara komai.....amma karka manta,secretly" Ta fada tana nuna hanzari da yatsa.



"An gama" Ya furta yana murmushi.





*FAREEDA*



Ci gaba tayi da duba bayanan,murmushi yana sake wanzuwa saman fuskarta. Murmushin da takejin yana gauraya da farinciki da take da yaqinin zai zame mata tabbatacce ta hanyar samarwa da zuciya da ruhi abinda sukesu ta sassauqar hanya.



Sake bude shafin qarshe na takardun tayi,take hotonta ya mamaye screen din tab din nata gaba daya,shafin qarshen daya zama shine na qarshe data bude cikin dukka bayanan data samu. Ta barshi a qarshe ne saboda dukka sauran shafukan na dauke da full details da bayanan da suka faranta mata rai sosai,sukayi kuma daidai da muradinta.



Hoton sabreen din daya cika allon tab din ta zubawa idanu. Wani abu yana tsarga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafukan qafafunta. Wani mahaukacin wutar kishi ke ruruwa cikin zuciyarta. Ta kusa kwashe sakanni talatin a haka,kafin ta dafe dukka hannuwanta saman kujerar da take kai tayi zullo zuwa gaba har a sannan ta gaza dauke idanun nata. Labbanta suka motsa kadan rana son kiran ainihin sunan nata,saidai ya tsaya ne can qasan maqoshinta ba tare da sautin harafin ya fita ba. Adan hanzarce ta maida hannunta saman tab din tana komawa shafin da yake da alaqa da komai daya shafi sabreen din,ta sake karantawa sosai kamar me shirin haddace komai daya shafeta



"How comes?" Ta tambayi kanta tana yamutse fuska lokacin da takai qarshen bayanan



"Karuwa?......How did he get married to her?" Ta sake tambayar kanta da kanta



"She's karuwa officially fa?" Ta kuma nanatawa cikin zallar mamaki. Ba wata amsa data samu daga kowanne sashe na kwanyarta,saita dage kafadunta duka biyun sama tana sakin murmushi,lallai komai zai tafi da alama daidai



"Fu'ad isn't your type madam.....its over between you too" Tayi maganar tana nuna hoton sabreen da dan yatsa,saidai ba abinda ya canza zuciyarta daga mahaukacin kishinta da takeji.



Ta kowacce fuska,ta kowanne bangare sabreen din ta yaga mata indai ana batun kyau ne da sassanyan zubi da ta tabbatar yana daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin fu'ad din,banda hakan.....yadda ta samu full details dinsa zai wahala ya nuna interest akan karuwa har ya aureta.



"It's my turn......my time to shine has come" Ta fada da qwarin gwiwa,ta miqe tana nufar closet dinta ta sauke luxury luggage dinta guda daya ta fara selecting kaya tana shiryawa a ciki ba tare da jiran kowa cikin masu aikinta ba.



Cikin qasa da mituna sha biyar ta gama packing komai da komai nata,sannan ta dawo ta dauki wayarta ta kira number abbanta.



"Hello dad....." Ta fada a shagwabe. Ita din 'yar gaban goshinsa ce da dukka yaransa babu wanda ya kamo matsayinta a zuciyarsa. A kullum tana maida kanta tamkar 'yar shekara goma a gabansa,haka shima yake biye mata,saidai hatsabibancinta da girman izzarta ta dara tashi shi da yake da muqamin ambassador din gaba daya.



"Dad.....ayimin booking flight please......gobe nakeso if possible,it's an urgent dad..." Ta furta a shagwabe kamar yarinyar dake tsakanin shekara shida zuwa bakwai



"Thank you dad" Ta fada da murnarta jin ya bata tabbacin zaisa a mata booking private jet.



Da murmushi sosai a fuskarta ta soma turawa zababbun qawayenta da za'ayi tafiyar tare dasu request. Cikin qasa da minti goma ta gama komai,sai ta sauke wayar ta matsa gaban dan wani madaidaicin table dake dauke da tukunyar shi sha ta fara qoqarin hadata. Tanajin a yanayin da take ciki na farinciki ita daya zata tayata sarrafa murnarta,



Kyakkyawar zuqa tayi mata tana bulbular da iskar daga dukka qofofin hanci da bakinta,ta lumshe idonta fuskar sabreen na mata shawagi tsakanin tunaninta da qwayar idanunta



"Blast it!" Ta fada da qunan zuciya tana kaiwa iska naushi,tana jin kaman tayi using acid ta dauke wannan kyan da ya hanawa zuciyarta sukuni.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



52



_Daga dariq dan shihab RA,manzon Allah S A W yace "juma'a haqqi ce kuma wajibi akan kowanne musulmi yayita cikin jam'i,sai akan mutum hudu kawai(ta sauka),MACE,BAWA,YARO DA MARA LAFIYA"_



_Abu dawud ne ya rawaito_







&Shuru ne ya biyo baya duk da wayar tana riqe a kunnenta. Dukka bayanan zuwaira ta gama saurara wadanda suka gama bata tabbacin lallai da gaske yaran sunyi nisan da ba wanda zaice ga inda suke......uwa uba kuma yarinyar tana ci gaba da harkokin gabanta hankali kwance kamar ba wani qalubale a gabanta.



"Ni kaina yanzu komai na taba ko nace zanyi mata dakatar dani takeyi,waccar munafukar me aikin da ameena ta kawo mata yanzu da ita takeyi,munafuka me shegen iyayi da bariki,idan kikaga yadda takeyi mata zaki rantse da Allah sabreena ce babba ba ita ba". Wani tattauran yawu maamah ta hadiye,tsananin bacin rai yana sake cikata



"Ki saurara,ki sanya dukka kunnuwanki da hankalinki dama idanunki kan gidan......kada kice komai,kuma kada kiyi komai,akwai gagarumin al'amari da zai faru cikin gidan.....abu daya nakeso kiyimin,ki kasance me bibiyar diddiqi bayan faruwar lamarin" Abinda maamah ta gaya mata kenam ta kuma yanke kiran. Bin wayar tayi da kallo......har a sannan tanaji a ranta muddin tabar sabreen din taci galabar ci gaba da rayuwa tana shan inuwa da arziqin danta lalallai ba shakka bata cika mariya. Shekaru da gwagwarmar rayuwa da gogayya da tayi da kalar mata daban daban bai amfaneta da komai ba.....shekarun data kwashe ma a duniya basuyi mata amfanin komai ba,dole ta fiddota daga gidan......wannan shine zai bata damar yin walagigi da rayuwarta da kuma d'aid'aita rayuwarta kamar yadda ta d'ai d'aita mata burinta.



Qarfe daya da rabi na rana driver din hajja ya faka motarsu qarqashin muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci. Koda ya tsaida motar ya kuma kasheta amma hakan bai sanya hajja fitowa daga cikin motar ba. Da idanu take bin kowanne sashe na ginin gidan da kallo tamkar yanzu ta fara ganinsa. Saidai sam a badini ba wannan bane damuwarta ba......ba kuma shi take kallo ba.



Tana nazarin yadda ALKHAIRI ya juye izuwa SHARRI,ta gama tura mota tsaf tana shirin buleta da balbalin hayaqi maras dadin shaqa?,hayaqi mafi cutarwa cikin qofofin hanci da kwanyarta?..



Wata gauruwar ajiyar zuciya ta sauke,sannan ta balle murfin motar yau da kanta tana fitowa,sabanin a baya da sai driver ya fito da kansa ya bude mata sannan ta fito. Gyara yafen mayafinta tayi,kanta tsaye kuma take takawa zuwa hanyar da zata sadar da ita da ainihin cikin gidan.



Duk taku daya idan tayi la'anar maamah take cikin ranta,tana ji a jiki ta jefeta a wata kalar musiba da batasan ranar fitarsu ba. Zuciyarta tana mata wani qunci da ita kanta batasan iya adadinsa ba......amma wani sashen na zuciyartata yana sake jaddada mata



"Fushi ba naki bane.....nasara bata masu gaggawa ko saurin fushi bace!" Wannan shine abinda yaketa mata burki take hadiyewa da qyar. A jiya da qyar bacci barawo ya dauketa,cikin fargaba da tsoron fitar dukkanin sirrinsu daga bakin laila..... Yanayin aikin bokansu dabanne,a aikin da aka tanadarwa fu'ad harda na rariyar baki,wanda baida wani sirri na kansa sai abinda maamah ta buqaci ya sirranta,muddin maganin yayi tasiri a jikin laila kamar yadda aka tsara.....hakan yana nufin duk wani sirri nata yanzu a tafin hannun mariya yake?.



Wannan tunanin ya hana mata cikakken bacci da safe,ta dinga qididdiga da lissafin wucewar sa'o'i don ta samu ta fito zuwa gidan mariyan. Tanaso taga yanayin fuskarta,abinda zai nuna shine zai zame mata amsa na abinda take zato da zargi. Duk da cewa na tsuburi ya mata alqawarin ba abinda laila zata iya gayawa maamah.....to amma tasan aikin bokansu daban yake dana kowanne boka.



Sau daya tak! Yake maka aiki.....idan har yayi maka na biyu to tabbas ka taki sa'a,uwa uba yawan yawan ayyukansa basu da makari.....shi yasa ta jima tana murza zaren rayuwarta ta kowanne fanni.....a yanzu kuma bata fatan wata matsala tazo mata ta wannan fuskar.



Idanunta akan parlor din maamah.....falon da kullum maamah din ke kusheshi da ganin tsadar kayan adon ciki bai kama qafar na gidan alhaji hamza ba.....Parlor din da ita kuma hajja harira kullum kwanan duniya ta daga kai ta kalleshi sai kishin zamowarsa mallakar mariya ya baibaye zuciyarta da wata irin hassada me tsananin qarfi. Iya bariki da qwarewa wajen boyewa koma waye yanayin da kake ciki ya sanya maamah din bata taba fahimtar komai ba.



Takun da taji ana fitowa daga kitchen ya sanyata waiwayawa cikin tsammanin daya daga cikin masu aikin gidanne wadanda su zasu yiwa maamah maganar ta iso tana son ganawa da ita. Amma kuma sabanin hakan,laila ta gani a gaba,dauke da kwando cike da warmers kala kala,saman rigar jikinta kuma apron ce a daure.



"Laila?!" Ta kira sunanta cikin qaraji da wani kalar madaukakin mamaki tana takawa da hanzari don isa gabanta.



"Sannu da zuwa hajja" Lailan ta furta fuskarta shimfide da murmushi dake nuna ba wani abu da takejin ba daidai bane



"Bari na ajewa maamah abincinta nazo mu gaisa" Ta furta tana wucewa dining din. A nutse ta shirya komai.....kamar ba lailanta diyar gata ba,lailan da idan taci abinci ko kwanon da taci abincin batasan ta janyeshi ba......lailan da saidai tana mimmiqe saman sofa ko gado ta zabi abinda take da sha'awar ci.....wannan lailan itace yau a kitchen da rigar 'yan aiki?.



Sanda ta kammala shiryawar saita dago tana murmushi,suka hada idanu da hajjan tace



"Ina wuni?,na kira miki maamah din?,Allah yasa bata kwanta bacci ba don tace ko waye yazo kada a tasheta"



"Gani nan laila baccin baizo ba....kun gama ne?" Maamah dake saukowa daga stairs din ta fada.



Tare suka daga kai suna dubanta,sanye take da applique lace purple color da ya dan ciza kadan,dinkin doguwar riga da aka qawatata da wani irin dinki me daukan hankali. Shigar tabi jikinta....wadda ke bayyanar da zallar izzarta da isarta.



"Kun gama laila?" Kai ta shiga gyadawa kaman mara hankali da sauri



"Mun gama maamah ko akwai wani abun?". Ta fada a rusune. Murmushi maamah ta saki tana dafa kafadarta



"Amma dai yau kin koyi yadda ake dambun gargajiya da kuma liver salad ko?". Murmushi ta saki kaman wata shashasha



"Sosai ma maamah.....ai kin taimaken na gode sosai". Ta fada tana rusunawa a wajen.



"Shikenan,yanzun zaki iya yin wanka,idan kin gama kiyi zamanki a daki kada ka fito yanzu"



"To maamah" Ta amsa mata a ladabce tana juyawa ba tare data dubi ko bangaren da hajja take tsaye ba. Idanu suka hada da hajjan,wata tayi wata irin mutuwar tsaye. Gefe guda kuma taci gaba daya tamkar qwaqwalwarta ta daina aiki ne gaba daya. Wani qaramin shu'umin murmushi maamah ta saki,ta juya da hanzari bangare da laila ke tafiya



"Au.....nikam nace kin gaida mamanki kuwa?" Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login