Showing 126001 words to 129000 words out of 147628 words

Chapter 43 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

farouq da idan ya motsa tsaf xai iya cewa ma bai sanka ba.



"3bedroom?,why not a siya me 4bedrooms farouq?"



"Akwai baquwar halitta ne a cikinmu da bata samu waje ba?". Kai fu'ad ya girgiza yanason gajarce maganar,don ciki yakeso ya shiga yayi bacci ko na awa daya ne



"Babu.....amma dakunan sunyi kadan.....kafi kowa sanin bana iya hada daki da kowa ba ko tun ba yau ba?"



"To dawa na hadaka.....kajimin mutum zaimin sharri" Rainin hankalin farouq yakai masa ko ina,yana dab da bashi naushi idan baiyi wasa ba,sai ya ware hannunsa daga qirji yana dubansa



"Ka canza plan dinnan,ta koma dakinsu anni tayi squatting tare dasu,saddiq su kwana da musaddiq.....kai kuma muje mu kwana tare". Baya yaja da sauri yana zare ido kaman yaga abun tsoro.



"Mu kwana da kai?,alfanun uban me zanyi maka fu'ad?,me zakaji da kwana da namiji gardi dan uwanka bayan ga halalinka a gefe?" Maganar ta fara girmar kunnuwan fu'ad,tun ba yau ba yasan farouq idan baiso ba tantirin kansa ne,baisan sanda hannunsa yakai kan cup din da saddiq yasha ruwa ba ya jefeshi dashi,Allah yasa yana da zafin nama ya cafe



"Na rantse da Allah xan ruguza maka kai......kai wanne irin dan iska ne?,maganan da nake maka daban yadda zaka juyan zance daban?,ta yaya zan kwana da wata alhalin muna muhalli daya da anni?". Dariya tana cin farouq amma ya maze



"To ba dole nace haka ba?,ga mace me namiji zai maka?,nima bazan kwana da gardi ba,ka cire riga wannan qattin muscles din naka suyita bawa mutum tsoro.....in fact ma ni na fara rehearsal na yadda zan fara kwanciya daga ni sai fannah ta....anni kuma da kake magana akwai wanda zai kaita son ganinku tare....ko turmusheta kayi a gabanta ai saidai tabar muku gurin da gudu.....banson gulma banson k......" Bai qarasa ba yaji saukar abu a qeyarsa,agogon hannunsa ya kwance ya sake jifansa dashi don ya rasa dame zai jefeshi wannan karon.



Dafe wajen yayi ya waiwayo yana dubansa fuska a hade



"Amma dai kasan wannan zallar cin zali ne ko?,ni nakar xomon?,kaje ka yiwa anni bayanin abinda yasa zaka aikota kwana da ita daki daya mana da kanka".



"Ya isheka farouq" Ya fada yana nunashi da yatsa,alamun ya fara qureshi.



"Oho" Ya fada yana sungumar ruwansa yayi dakinsu baiko sake waiwayoshi ba.



Shuru ne ya ratsa falon bayan wucewar farouq din,sai motsinsu kadan kadan da yake jiyowa daga dakunansu. Maganar gaskiya farouq ya cuceshi,inda kuma yasan da wannan da tuni ya sanya an canza musu gida da yafi haka yawan dakuna kafin su qaraso. Miqewa yayi abisa dole yana soma dosar dakin,abu daya ya sani shi bayason takura,yana son bajewa sosai ya sake a duk inda ya zabi rayuwa,so wanzuwarta cikin dakin kuwa bazai bari ya zama silar hanashi sakewa ba.





*Maamah*





Sake juya tickets din hannunta tayi guda biyu tana sake qare masa kallo. Mamaki da wani irin dunqulallen baqinciki yana yayyanka zuciyarta. Ta rasa wanne hamshaqinne ya juya tafiyar daga farkonta ta koma qarshe?. Maldevis shine waje na farko da zasu je a qa'ida kaman yadda ta samu tabbacin dukka iyalin gidan alhj hamza kibiya can suka wuce.....saudiyya kuma shine waje na qarshe da zasu ziyarta daga nan kuma sai gida Nigeria,amma wanne hamshaqinne ya karkatar da tata akalar tafiya daga saudiyya kafin ta sauka maldevis sannan su rankaya su wuce turkey tare?.



"Hajiya ameena.....tabbas wannan aikin ameena ne" Ta fadi tana jin wutar qiyayyar matar tana sake ninkuwa a ranta. Zazzafar iska ta furzar tana fitar da idanunta waje irin na zallar takaici da kuma tunani. Ita kuwa ta yaya zata dagawa ameena qafa?,ta yaya zata bar ameena taci gaba da shaqar iska cikin aminci?,ba ragi tsakaninta da ameena har abada......yadda bata barta ta samu cikakken iko da mulki da 'ya'yanta ba.....tabbas haka zata zama silar tarwatsa nata ahalin gaba daya,duk wanda ya gaya mata cuta ba shakka ita mutuwa zata gwada masa,sai kawai taja wayarta tana laluben fareeda,tana jin wannan karon a gaban idanun ameenatun zata gwada mata nata izzar da qarfin mulkin kasancewar uwar data dauki cikin fu'ad tayi naqudarsa ta kuma haifeshi.......a gaban idanun kowa zata gwadawa sabreen ta isa da danta......zata nuna mata kuma tana da ikon sanya yaronta ya auri mata d'ai d'ai har guda uku rigis bayan ita.



Shuru fareeda tayi tana sauraren bayanan maamah,saidai kuma zuciyarta cike fal da bacin rai da baqin kishin sabreen. Wata zazzafar iska ta furzar tana ajiye bututun shisha dinta ta gyara zamanta



"Maldives ai gida ne......ina da sauran visa din qasar da ban gama cinyeta ba,muddin na samu ticket jibi warhaka ina can......ko ba ticket zan sanya daddy yamin hiring private jet......kya sameni a can" Daga haka ta yanke wayar tana latsa wayarta ba bata lokaci tana neman number wayar daddy din nata.



Tafasa kawai zuciyarta takeyi,wannan karon da zafi zafinta zata shiga,zata budewa sabreen aiki sosai kaman yadda zata budewa fu'ad,tana jin komai mai sauqi ne......amma zata bari ta tabbatar da samun private jet ko ticket to Maldives.



Bugu daya rak ya daga,ba kasafai ta fiya masa sallama ba,kusan sallamarta kiran sunansa ne



"Daddyyyy.....maldevis" Ta fada da wata irin shagwaba kamar yarinyar da aka Haifa jiya jiya



"Mamana......maldevis a daren nan?"



"Daddy gobe......ina da sauran visa na da kamin last two months.......ticket kawai daddy nakeso......please daddy,it's an urgent need daddy". Murmushi ya saki yana juya kai kafin yace



"Wani irin emergency issue ne haka ya taso mamana.....nifa mamana yanzun duk hankalina yana kan aure,kiyi aure haka mamana.....ki zabi duk kalar mijin da kk so zan tsaya miki" Maganar sai taji kaman tazo akan gaba,ta saki dariya tana cewa



"Nayi maka alqawari daddy.....indai na samu wucewa Maldives gobe ko jibi,ina dawowa zan gabatar maka da mijin da zan aura"



"Really mama na?!" Ya tambaya da excitement cikin muryarsa



"Yes dad.....na taba maka qarya ne?" Ta sake fada cikin narke murya



"No mamana......bani minti goma.....i will get back to you"



"Thank youuuuuuu" Ta fada da sautin dariya tana sauke wayar.



Lips nata ta cinje tana duban wayar gami da saqa abubuwa iri daban daban akan fu'ad. Zuwa sannan ta gama karance halayensa na girman kai da izza,yana da tsananin taurin kan data tabbatar ita din kanta shaida ce,taso koda bata aureshi ba ya bata hadin kai su mori quruciyarsu tare,amma martanin da yayi mata ya mata ciwon data jima tana riritashi a zuciyarta.



"Tabbas saina biyo masa ta bayan gida,idan baiyi wasa ba sunansa ne zai fito a next newspapers da magazine ba na waccan karuwar matar tasa ba......tunda shine garkuwarta.......shi din ya kamata na taba qarfinsa" Ta fada da murmushin mugunta tana murza yatsunta bayan ta tabbatar da hukuncin daya fado ranta shine abinda ya kamata ta zartar.



Qarar wayarta ya dawo da hankalinta,ta daga da sauri ganin me kiran. Wani ihun murna ta saki sosai tana jin dadi



"I love you daddy......thank you so so much......bansan ma ya zan gode maka ba" Ta fada duk a rude saboda jin dadin samun ticket na tafiya Maldives jibi. Tana Lagos don haka ba ita babu bin jirgi zuwa Lagos din,kawai kanta tsaye jibi zata bi qatar Airways zuwa can



"Ki kawomin miji kawai bayan kin dawo"



"Baka da matsala dad....." Ta fada tana yanke kiran.



Tun a daren ta gama komai,ta gama hada komai ta kuma tanadi komai gudun samun matsala goben kada ta tashi da uzurin da zata tashi ba'a daidai ba har ya jawo ta hada kayanta ba daidai ba.



*_hmmmmmm,uhmmmmmmmmm_*





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �







5�K�5�<�5�B�5�@� 70





70





Sam sam bata fahimci daki daya farouq ya hadesu ba sai da ya murda handle din ya shigo cikin sallama. Daidai lokacin da taketa qoqarin kauda luggage din zuwa kyakkyawan gurin ajiyar kaya dake a dakin bayan ta ware scarfs din kanta ta daure sumarta dashi.



Kallon juna sukayi,sai kowa yayi qoqarin dauke idonsa daga kan dan uwansa. Haka kawai ta samu gabanta da faduwa,tunaninta kuma ya koma baya na yadda aka kasafta dakunan



"Tashin hankali!.....shine part na na?" Ta fadawa kanta da kanta. Sam sam bata taba hango yiwuwar wanzuwarsu a daki daya ba......ita da mutumin da basa ga maciji sam sam,ta yaya zata iya hada numfashi dashi qarqashin rufin daki guda daya?,lallai inda tasan da yiwuwar faruwar hakan wannan kadai a wajenta ya isa dalilin da zai hanata yin tafiyar ma gaba daya.



Sakin abinda takeyi tayi ta kuma ware veil dinta ta lullube kanta dashi dukka tana satar kallonsa. Baiko nuna yasan da tsaiwarta a wajen ba,hasalima yanata daddaga labulayen dakin yana laluba sauran gurare irinsu socket na dakin,switch da sauran gurare saboda tsaro,gudun samun wata boyayyar camera da basusan da ita ba.



Baisan ta fice ba sai da yaji alamun jan qofar,ya bi qofar da kallo kafin daga bisani ya dauke dubansa daga wajen yana ci gaba da abinda yakeyi.



Wannan dukka ba take taken raini bane ba?,amma ba wanda ya jawo masa illa farouq,kuma tabbas zaija kunnensa,bazai yiwu cikin qasashe biyu da xasu sake zuwa a gaba ya qara hada musu guri ba,duk da kusan duka qasashen ba inda baida gida mallakin kansa uku ko hudu,da kansa zai zabi gidan da yakeso saboda gudun faruwar hakan.



Sai daya tabbatar da lafiyar dakin sannan ya soma rage kayan jikinsa,don bazai iya bacci haka ba,ko wankan ma bayajin zaiyishi sai idan ya tashi,duk da farouq nason rage masa jin dadinsa.....don da gaske hutu yazoyi,yazo.ya huta inda ba zaa sashi magana bs ko ciwon kai.



Turus tayi sanda ta fito parlor din,wayam ba kowa sai dan motsinsu daga dakunansu. Bin duka qofofin dakunan dake kulle tayi da kallo,saita rasa meye abunyi.



Da kunya dai ta jewa dakinsu anni wanda ta tabbatar a yanzun suma hutawa sukeyi,idan ma taje tace mata me?. Ba zata zauna daki daya da d'anta ba wanda mijinta ne a qa'ida duk duniya kuma haka suke kallonsu?,wanda sukasan sahihin zamansu mutanene daidaiku.......hatta da amna bata sanya ran ta gama fahimtar komai da komai. Rasa madafa tayi,dole a qarshe kwanyarta ta gaya mata bata da sauran wani abunyi illa ta koma dakin ta rungumi haquri na yau,zuwa gobe saita nemawa kanta dalili da mafitar da zata sanya a raba dakin.



Daidai sanda ya isa bakin qofa da zummar kashe switch na qwan ita kuma ta murza qofar ta shigo. Baikai ga kashewa ba,don haka tsaf ta ganshi.



Murdadde kuma qaqqarfan muhammad fu'ad jadda,ma'abocin daga qarfe da dukka surar jikinsa ta koma ta qarfafan maza,saidai surar batayi muni ba,ta dace da zatinsa ta kuma shekarunsa.



Babu komai a jikinsa sai gajeran wando iyakar cinyoyinsa,gaba daya faffadan qirjinsa dake lullube da ni'imtaccen tattausan gashi ya tare kusan rabin qofar dashi,abinda ya sanyata saura kadan ta fada qirjin nasa,abinda kuma ya saka tsoro ya kusan sanyata shidewa,ta daburce duka cikin qanqanin lokaci,saita juya da hanzari da zummar ficewa a dakin don ba zata juri ganinsa haka ba.



Sosai ya raina sanya hannu qwaya daya ya jawota zuwa gabansa,yanzun hakan ma yayi mata,ya kuma ajeta a gefe,ya saka hannu ya murza key din qofar ya rufe dakin,ya cilla key din saman gado sannan ya juya yana kashe switch din. Dakin yayi duhu,saidai duhun bazai hanaka ganin komai dake dakin ba amma bada fitacciyar suffarsa ba. Takawa yakeyi hankalinsa kwance zuwa gadon kaman ba'a tube yake ba



"Sannu a hankali wataran zan baki mamaki tunda na hanaki wannan rainin hankalin da kikemin kaman dodo......sai kace a kaina kika taba ganin namiji a t......" Sai kuma bai qarasa ba yaja tsaki sanda yake dora kansa saman pillow hadi da lumshe idanunsa ya sauke numfashi.



Komai ta kasa cewa saboda tsoro daya cakude da takaici. Ta zuba ma fuskarsa idanu duk da bata iya ganinta sosai tana jin bacin rai yana taso mata. Ta tsani koda kalma daya ta hadasu shi yasa take kauce masa,don kowacce magana zai gaya mata bame dadi bace a zuciyarta da kunnuwanta.



Don kanta ta samu waje ta nade tana curewa guri daya bayan ta gaji da tsaiwa,don tuni yaja duvet ya rufe jikinsa dukka gaba daya har saman kansa.



Tsakiyar baccinsa ya dinga ganinta tana nufoshi cikin swimsuit sanda yake zaune daga gaban swimming pool din yana kallonta. Kanta tsaye ta yiwa kanta mazauni saman cinyarsa,yayin da albarkatun qirjinta yake tokare masa fuska da wani irin salo na tsokana,baisan ya akayi ba ya samu kansa da goga fuskarsa a jikinsu,abinda ya tashi kowacce tsiga ta jikinsa kenan,kowacce kafar jikinsa ta soma fidda zufa,ya kuma jawota ya qanqameta da kyau yana cusa fuskarsa tsakiyarsu kaman me neman taimako.



Wani birkitaccen salo takeyi masa,wanda ya taimaka wajen fitarsa a hayyacinsa,ya kuma juyeta saman sun lounger din da yake kai,take al'amura suka fara kankama tsakaninsa da ita.



Karar fadawar wani abu ruwan dake gabansu shi ya farkar dashi har a zahiri. Idanunsa ya runtse da qarfi yana jin wani abu yana yawo a sassan jikinsa. Yana jin tamkar a yanzun idanu biyu komai yake faruwa,wani irin zazzafan yanayi da ya jima bai tsinci kanshi a ciki ba saboda yadda yake yawaita yin takatsantsan.



"Why?,why?" Ya tambayi kansa da kansa muryarsa can cikin maqogoronsa. Me yasa zata biyo shi har baccinsa?,ba zata qyaleshi ya huta ba kenan?. Ko a baya da yake fuskantar irin mafarke mafarken nan......babu guda daya daya taba ganin ainihin fuskar ko gangar jiki,wannan shine na farko da komanta ya bayyanar masa a zahiri.



Fitowarta daga toilet shi ya sanya ya ware rinannun idanunsa a kanta. Duk da bata iya ganinsa sosai amma taga alamun ya farka daga baccin. Dama ya kamata ace ya farka din,tunda agogo ya nuna mata lokacin magariba yayi,amma kuma batasan yadda zata tayar dashi ba,to ya samawa kansa lafiya daya farka din. Dakin ya mata duhu saboda yadda duhu ya soma mamaye garin,saita laluba har ta dace da makunnin ta kunna qwan dakin,take haske ya gauraye ko ina tarwai. Idanunsa ya lumshe yana cusa shi cikin pillow



"Oh shit" Ya fada qasa qasa. Qoqarin tashi yake kafin hakan takai ga faruwa sai gashi ta rigashi kunna hasken dakin. Ta yaya zai iya tashi ya miqe ya wuce zuwa bandaki a yanayin da yake ciki?,tambayar dashi kansa baisan amsarta ba.



A nata bangaren ta gama gajiya da zaman dakin,burinta kawai ya budeta ta fita,bataga wani alfanun zamansu suna musayar numfashi ba idan ba tsabar muguntar nashi bane ya motsa. Ta duba luggage dinta ma sam bata ga hijab ba,sai mayafai ta hada kusan uku dasu zatayi sallar. Ba ita ta hada kayan ba,zata iya cewa batasan ma meye a ciki ba,anni ce ta musu siyayyar duk da uban lodin kayan da suke da wanda ita kanta batasan adadi ba,amna kuma ta shirya mata tace basai ta buda ba ta saka mata komai,ta kuma biye matan bata duba ba.



Bashi da wani sauran abinda ya rage illa dole ya tashi din,don haka ya tattara uban duvet din ya nadeshi a jikinsa ya sauka yana wucewa toilet din a gurguje. Ta danyi mamakin shigarsa toilet fa duvet,amma sai kuma sai ta kauda abun daga ranta ta shimfida abun sallah tana jiran lokaci ya qarasa cika.



Ya jima a toilet din yana qoqarin ganin yanayinsa ya daidaita,yasha azaba qwarai har ya dinga tunanin anya yau zai tsallake kuwa?. Kowanne jijiya ta jikinsa aikawa take da saqo,sai bayan kusan minti talatin ya samu yanayinsa ya dawo daidai,amma abinda yakeji a jikinsa bai sauya ba tunda jikin bai samu abinda yakeso ba. Dukka jikinsa ya wani mutu qwarai da wata irin kasala data sakar masa da nauyin jiki,haka yayi wanka ya daura alwala ya fito. Sauqinta daya data samu tana sallah sanda ya fito din,don da alama a yanzun ma gaba gadi ya fito abinsa,ya buda kayansa ya shirya cikin Moroccan jallabiyya black me adon golden din zare,ya saka qaramae gold din hula ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki key ya bude qofan ya fice don zuwa su hada jam'i dasu saddiq kaman yadda suka saba duk sanda sukayi tafiya a qasashen daba masallaci a kusa da masaukinsu.



Fitarsa sai taji kaman ta samu 'yanci ne,ta kammala sallarta ta fada wanka. Koda ta fito lokacin isha'i yayi,tasan qwarai tana da nauyin wanka,amma na yau ya haura na kullum

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login