Showing 114001 words to 117000 words out of 147628 words

Chapter 39 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

furfura koda qwaya daya dake tsakiyar kanki ba......muddin naxo na sameki kin koma gifan gidan maamah........ki tabbatar daga ranar kin tashi daga aiki......kiyi nesa da ita da komai da kowa daya danganceta.....and hakan bawai xai sakaki kin tsira ba,duk mutumin da yake gidan nan daga kwana uku baya zuwa jiya da abin ya faru baxai tsira ba a waje na......wanda kawai zai tsira shine MAI GASKIYA ". Duburbucewa tayi har akwatin kayan asirin maamah na shirin tarwatsewa daga hannunta. Gab gab gab haka hannuwanta da qafafunta suka dinga haduwa waje daya,wannan wanne irin kalar tashin hankali ne?,wanne irin yaro ne wannan maras imani.... Lallai dole mallakarsa ta yiwa mariya wahala,zuwaira ta furta hakan a ranta sanda take ta qoqarin kai kanta ga sassansu don ta samu ta sulale kaman yadda ya shawarceta. Ayadda ta sanshi tana ganin ko cinye namanka yace zaiyi zai iya......musamman shi daya mallaki masu gidan ranar da babu me tuhumarsa ko bin ba'asin abinda yayin.



Gaba daya wunin yau duka hankalinta yana kan wayoyinta,bama ita ba.....hatta da fareeda kowanne motsi nata yake kan social media's tana hasashen watsuwar abun a kowacce kafan sada zumunta. Sanda taga ankai azahar shuru sai duk wata nutsuwa ta soma barin gangar jikinta,hankalinta ya gaza kwanciya kwata kwata,ta kuma shirya kai tsaye ta kira driver ya dauketa zuwa gidan maamah.



A sannan ita dinma duban wayar take tayi.......tanaso ta samu wani haske ko yaya yake.......tunda ta zauna take saqa yadda komai zai kasance.......take qiyasta irin tozarcin da zata yiwa sabreen. Lallai sai ta sanyata ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa.......ita kanta batasan adadin yawan tozarci da qasqancin da zata sanyata ta fuskanta ba.



Mamakinta ya tsananta ainun da rashin samun kai,sai taji ta kasa jira,kai tsaye ta daga waya don kiran fareeda,amma sai fareedan ta hutashe da ita saboda turo qofan setting room din da tayi ta shigo tana taunar chewing gum kaman yadda ya zame mata al'ada,duk kuwa da cewa yau din bata cikin wannan mode din,amma cin chewing gum din ya zame mata dabi'a.



"Ke nake shirin kira yanzun.......banga tasirin aikinki ko wani motsi na daban ba" Maamah din ta furta kanta tsaye tana duban idanun fareeda. Idanu tadan xubawa maamah din,mamakin dabi'arta tana dan kamata. Kanta tsaye take magana akan duk wani abu daya shafi buqatarta,ba ruwanta da wata matsalarka ko fuskantar yanayin da kake ciki.



Kanta ta dauke tana qarasowa ciki,sannan ta yiwa kanta mazauni saman hannun sofa din tana harde hannuwanta a qirjinta



"Wannan shine aiki mafi kashe kudi da nayi......sannan shine aiki mafi jinkirin samun nasara" Tayi maganar tana duban maamah din.



"Masu aiki sun kammala.......naki aikin da nawa duka ba wanda ya kawo result me kyau........abu daya ya rage shine,ki kira d'anki ki tuntubi sakamako daga gareshi". Gyara zamanta maamah tayi tana duban fareeda,ta soma fahimtar wasu halayenta da inda dabi'unta suka sanya gaba,bata gayawa fareeda tayi failing a nata agenda din ba.....ya akayi amma ta sani?.



"Na yarda har abada yaro yaro ne.......kina tunanin samun galaba akan duk wani lamari daya shafi fu'ad abune me sauqi?,inda kuwa hakanne da bakizo gabana ba......da babu ke cikin babin qaddararmu sam sam" Maamah ta fadi tana duban fareeda.



"Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba..........a naki lisssafin kiran fu'ad kai tsaye na jefeshi da salon tambayoyinki abune me sauqi da zai sanya mu wanye lafiya?" Ta qarasa maganar tana duban fareeda data zubawa maamah nata idanun.



"Kina iya kiransa ta wata siga daban ki kuma zaqulo bayanan da kikeso......amma zai zama babban kuskuren rayuwarki ki biyo masa ta waccan hanyar taki....."



"Amma bisa alqawari da yarjejeniya.......xaki zama tsanina na mallakar fu'ad haka ne?"



"Har yanxu ina kan wannan bakan.......amma fidda sabreen daga gidansa aikinki ne......zai iya zama nawa aikin,amma kuma salon aikin nan da yake zamowa ba waji bi". Sun jima suna kallon kallo tsakaninsu,kowanne da kalar saqar dake cikin zuciyarsa game da dan uwansa,kafin fareeda ta fiddo wayar da musamman saboda kiran fuad din ta tanadeta. Da kowacce waya da kuma kowanne layi ta kirashi ba zata sameshi ba saida wannan wayar kadai.







*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862





5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 65





65





_Manzon Allah S A W bai taba aibata abinci ba,idan ya burgeshi sai yaci,idan kuma baiyi masa ba sai ya qyaleshi(ba tare daya aibatashi ba)_







Tsaf ya shirya cikin trouser dark blue na yadin vicuna,yayin da sanya black shirt data fidda ainihin kan sassalkar fatar nan tasa me tsananin haske,wadda ta cakuda da hutu da jin dadin dake bayyana kansa cikin kowanne hali yake. Kyakkyawar qasumbar fuskarsa da bata da cika irin ta cukus ta sake qawata fuskarsa da sanya masa kwarjini,tana da santsi kwatankwacin sumar dake lullube saman kansa. Baqa ce sidik kaman gashin girarsa dana idanunsa,hakanan kaman sauran gargasar dake lullube da sassan jikinsa. Agogo fata ya daura a tsintsiyar hannunsa me tsananin tsada daya dace da shigarsa dama tsadar kayan jikinsa,yabi ko ina na jikinsa ya feshe da lallausan turaren nan nasa me taushin qamshi.



Tsananin dauriya kawai ta sanyawa ruhinta,tun bayan dawowar amna da batakai magarib ba kaman yadda anni tace taketa qoqarin shimfida walwala akan fuskarta,duk da cewa abun ba haka yake ba daga qasan zuciyartata. Amna din ta dabance,tana da barkwanci da sakin jiki ga duk wanda ta yarda dashi,wannan ya sanya cikin qasa da awa guda taji nauyin dake qirjinta yana raguwa,lokaci lokaci labarun amnan suna sake dauke hankalinta daga yanayin da take ji.



Ita ta tilastata da yammacin kan su fito daga daki zuwa kitchen



"Wainan fulawa nake sha'awa.......yakumbo ce take mana,ta tafi ganin gida tun wancan satin,muje na gwada ko zan iya please adda" Ba zata iya qin tankwabar da tayinta ba,haka ta maqala hijab saman doguwar rigarta ta bita kitchen din,wanda a qarshe sabreen dince ta hada Mata wainar ta soya mata ta kuma tara mata a warmers. Ta cika da mamakin yadda akayi amnan ta iya girki kala kala amma bata iya wainar fulawa ba. Qwarewar amnan a girki yana bata sha'awa,harma takanji tana sha'awa itama iya kalolin abinciccika.



Suna a saman dining tana kallon yadda amnan ke santin wainar fulawan,time to time tana murmushi kawai. Ta sake yarda da gaske rayuwa mataki mataki ce,kowanne da kuma kalar muhalli da hurbin data ajeshi.



Duk da fiye da rabin hankalinta bashi a wajen,amma hakan ba hanata jin saukowarsa ba a jikinta. Qamshin turarensa ne ya fara isa ga hancinta,kafin daga bisani qamshin ya fara mamaye parlor din.



Cikin dabara ta dauke duban ta daga wajen da yake takowa,tanason nuna sam sam ma bata ganshi ba. Duk sanda fuskarsa zai bayyana a gareta,ba abinda yake tuna mata sai tambayoyinsan nan data tsana,tambayoyin dake matuqar qona masa rai ba kadan ba.



"Hamma......barka da yamma" Amna ta furta da murmushi saman fuskarta sanda ta waiwaya ta ganshi,sai ta aje wayar hannunta tana bashi hankalinta gaba daya



"Barks lovey dovey" Yayi maganar da wani kwantaccen sauti daya sanya sabreen taji tsigar jikinta ya zuba,take kuma ta daga kanta a hankali kaman me tsoron ganin wani abun tsoro,duk yadda taso ta yiwa idanunta shamaki amma sai da suka fada kan fuskarsa,ta kuma ci karo da wani yanayi dake shimfide saman fuskarsa din. Shi ba murmushi ba sannan kuma ba'a daure fuskar take ba......saidai yana yin ya nuna ya zama very calm ba kaman yadda take ganinsa kwanakin da duka wadannan abubuwan suka faru ba.



Zamewa amna tayi tana sake gaidashi bayan gaisuwar daxu,ya amsa yana motsawa alamun xai wuce. Wayarsa dake riqe a hannunsa ta fara bada wani sassanyan sautin sarewa maras hayaniya da yawa,kafin daga bisani sunan FAREEDA KHALED MUSTAPHA ya fita tarwai ta cikin speaker din. Duk yadda taso watsar da sunan daga cikin kunnuwanta amma hakan ya gagara. Sunane data jima tana jinsa akai akai,har kuma ya soma zama a kwanyartata. Maida hankalinta tayi ga amna amma saita gaza ci gaba da hakan,batasan yadda akayi idanunta suka dauketa zuwa fuskarsa ba. Wayar ya daga zuwa fuskarshi yana duban me kiran,sosai ya zubawa numbers din nata idanu,manhajar daya dora kan wayar tasa ke harbawa daga gefan hagu na wayar tana nuna masa abinda fareeda din ke aiki dashi wanda ke fasa duk wani shinge da zai saka number dinta,duk sanda ta jira kiran ya samu damar isowar gareshi kai tsaye. Dan qaramin murmushi ya subuce masa wanda iyakacinsa labbansa,saidai a nata idanun qaruwar murmushin ta gani. Idanunta taja ta lumshe daga kallon dark pink lips dinsa. Batasan me yasa gabanta yayi wata wawiyar faduwa ba,sai kawai taji bata da sha'awar ci gaba da zama a wajen. Tsam ta miqe sanda amna ke ce masa



"A dawo lafiya hamma...." Ta fara saukowa daga steps din,a cikin jikinta taji amna din na satar kallonta,wani nauyi ta sakar mata da bisa dole ta motsa labbanta tana fadin



"Adawo lafiya" Sosai yaji kalmomin sun zama baqi a kunnensa,har ya motsa kaman zai waiwaya sai kuma baiyi hakan ba ya amsa



"Allah yasa" Yana takawa gami da ficewa da takun nan nasa da ta dade da haddaceshi. Wani irin taku yakeyi tamkar namijin toro,zakayi tunanin wani saraki ne,ko kuma yana qawata takun nasa daidai da yadda zaija hankalin masu kallonshi.



Ficewarsa daga falon ya bata wani qaramin sukuni,sai ta fasa komawa dakin ta sauka saman sofas din dake falon ta zauna tana maida numfashi. Idanunta ta maida hanyar daya wuce din



"Fareeda KHALED MUSTAPHA" Sunan ya dawo mata radam a kunne,murmushinsa kuma ya sake giftawa ta idanunta,ta sake lumshe idonta ta kuma budesu lokaci daya



"Waya sani ma ko ita ta kirashi?,wa yasan inda zasuje?" Ta furta can qasan zuciyarta tana tuna irin tuhumomin da take gani a kanta cikin idanunsa.



"Waye yasan abinda shi yake aikatawa ma?" Ta sake samun kanta da fada qasan zuciyarta. Ko daya ba zata taba aminta da cewa shi din a tsare yake ba......taga matasa masu tarin yawa da ni'ima da baiwar dukiyar da yake da ita yasu bata taka rabinsa bama......amma qazantar dake cikinsu sai Allah. Kamar dai shi......a haka kamilallen mutum....amma badininsu wata irin danqararriyar qazantace maras dadin gani ko tabawa.



"Adda......." Taji muryar amna daga gefanta. Fararen idanunta ta daga tana duban amna gami da katse tunanin dake kai kawo a ranta



"Amna" Ta amsa mata murya qasa qasa tana nazartar fuskarta. Fuska ta narke sosai tana zagayowa gabanta ta zauna.



"Nace wani abu adda bazai zama shishshigi ba?" Tayi maganar da alamun son ta furta abinda ke bakinta. Qaramin murmushi ta sakar mata don ta bata nutsuwa da gamsuwa akan duk maganar da zatayi



"Fadi amna mana" Sai data gyara zamanta tana maida mata murmushin sannan tace



"Yaaa saddiq yana bani labarin hamma......duk da na fisu sanin hamma ta wasu abubuwan.......amma ya saddiq kuma zai iya fina saboda shi din PA dinsa ne.....duk inda zai saka qafa a gida ko a office suna tare.......kinsan waye hamma kuwa?,ya yake?" Tayi tambayar da murmushin daya kusa zama dariya akan fuskarta.



Numfashi taja a boye tana jin sunansa kawai da amna ta kira yana qara yawaita bugun zuciyarta,inda zata iya zata dakatar da amna daga yi mata duk wata hira data shafeshi......kwanaki kaddan suka rage masa cikin rayuwarta.......tana jiran kawai ranar da zata samu tabbacin su huda sun isa mali lafiya hannun momma bahijja.......a wannan lokacin komai zai tarwatse.



"Saikin fada amna" Ta fadi bawai don ranta yana so ba,sake gyara zama sosai tayi ta riqo hannun sabreen



"He's a loving and caring partner.he wants a deeply romantic connection with his wife" Ta fada murya can qasa,kaman tana tunanin yana kusa dasu kuma tana tsoron kada ya jiyota. Dukka idanunta sabreen ta fiddo waje tana kallon amna,yadda amna din tayi maganar da wani confidence da qwarin gwiwa ya bawa sabreen mamaki.....can qasan zuciyarta kuma sai taji kaman tanason taja hira kadan da amna din. Abu daya dai tayi amanna fuskar fuad ta gida daban......fuskarta ta gidansa daban.....kamar yadda fuskarsa ta mu'amalarsa ta waje daban,banda haka mutum kaman fuad dinne zata siffanta haka?.



"Kina da ja ko adda?......" Ta tambayi sabreen kai tsaye,tana jin tanason tayi hira da ita.......tanaso ta fadi mata abinda ta fuskanta ko ita ta fahimci ba daidai ba



"I swear adda........He envisions a future where he and his wife grow old together,hand in hand......ko a gabana wannan yasha fadinsa......musamman idan suna hira na sako da sako shi da BB farouq.......hamma na yana son soyayya,ya kuma cancanceta......hammana yana son kulawa......that's why yakeji dani,komai na hammana daban yake a wajena.....tausayin hamma nakeji coz....He suffered a lot in his life

He had a rough past" Ta fada dukka a jere tana riqe da hannun sabreen kaman hakan shine zai saka ta fahimta abinda takeji a zuciyarta na tausayin hamman nata. Baki da idanu kawai sabreen ta sake tana kallon amna,tana sake gasgatawa da imanin cewa eh lallai da gaske wannan mugun yana da muhalli me girma da fadi a rayuwarta......amma wanne irin hardness ne haka ya fuskanta?,mutumin da ya rayu tsakanin iyaye biyu 'yan uwa hudu?,mutumin dake cikin daula da dukiya?.



"Believe me adda......please,ki qara akan kulawan da kike bawa hamma,He's passionate about building a strong loving relationship with his wife.......na dade da sanin duk wadda ta samu hamma fuad.....She's the luckiest woman alive and she's incredible fortunate" Murmushi ta samu kanta da subucewa dashi,saita miqa hannu ta riqe amna din sosai bawai don maganganu da yabo a kansa sun burgeta ba,aah......sai don ita din mutum ce me girmama 'yan uwantaka,saboda tasan girman soyayya da qaunar dake tsakanin 'yan uwa me girma ce......itace babbar shaida ta farko akan hakan akan kanta ma.



"Duka wannan yabon amna......anya baki fiya son kanki da yawa ba kuwa da wannan birkitaccen hamman naki?" . Murmushi amnan ta saki itama,har qasan ranta taji dadin yadda sabreen ta karba maganganunta,amma har ga Allah tana son matar hammanta ta zama dream wife nashi kaman yadda dukkaninsu suka fahimta



"Ki budewa hammana zuciyarki da kyau.....zaki sha mamaki adda.......inajin tukuicin zuwa dubai zakimin duk sati.....nayita zuwa ina ganin burj" Murmushi ta sakeyi kawai batace komai ba......abinda ya bawa amna daman sake cewa



"Adda.......na baki kadan daga tarihin hammana dana samu tun kafin a haifeni.....wannan ne kadai zai zame miki jagora wajen sake fahimtar waye.....ya kuma.baki qwarin gwiwan tallafarsa" Zame hannuwanta tayi daga cikin na amna tana girgiza kai



"Zaki bani.....amma ba yanzu ba amna.....kinga bana jin dadi sosai" Itama tayi maganar tana narkewa amna kaman yadda amnan keyi. Murmushi ta saki tana tuna warning nata da anni tayi akan ta kula da ita,kuma kada ta matsa mata da yawa,don haka sai tace



"Mu barshi pending......har sai kin samu lafiya" Kai ta gyada tana lumshe ido kadan



"Na gode" Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda amna ta fahimceta ta qyaleta. Sam bata son jin komai daya shafeshi,saboda tasan zasu fadi kirkinsa ne kawai bawai don haka yake ba,zasu fadi kirkinsa ne don haka yake nuna musu a fuska da mu'amalarsa da su,amma a waje kuwa.....babban azzalumi ne a wajenta mugu kuma.



Maida dubanta tayi kan maamah



"Ban taba kiran wani d'a namiji da adadi me yawa ba irin wannan sai d'anki......na masa kiran qarshe......inaso naga naki qoqarin" Abinda fareeda ta fada kenan ranta yana motsuwa hadi da qara baci akan lamarin. Bata taba daukan plan dinta bazaiyi wani aiki ba,kudade ta kashe masu nauyi don a buga ninkin adadin news paper din da aka saba bugawa a kowacce rana......sannan a fiddata tituna a kuma rabata kyauta ga kowa basai kowa ya siya news paper ba a ranar.



Guri daya maamah ta zubawa idanu tana murza tafin hannunta,tana ji a jikinta lokaci yayi da zata koma wajen boka ta zube masa komai.......ta gaya masa buqatarta ta gaba,ta zube masa ruwan kudin da ko bai shirya ba dole yayi aikin nan......daga can wani loko na zuciyarta tana fargaba.......tana fargabar kalamansa na can watannin baya......kalamansa na qarshe a haduwarsu ta qarshe dashi.





_taurarinta nada tsananin haske da wahalar cusa kai a cikinsu.......tabata abune da zai iya zuwa da nasara da kuma akasinta.........KINYI KUSKUREN ZABINTA......amma itace mahadin masarrafin b'arin nasa tauraron..........taurarinta sune abokan tafiyar nasa taurarin.........kusan komai nasu suna kamanceceniya da juna.......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMU GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA_



Gumi ne taji yana tsatsatsafo mata......a take sai taji ai kaman ta fara shiga matsalar daya ambata mata. Sai yanzu kwanyarta ta fara aikin da a wancan lokacin bata yishi ba wato na fahimtar ma'anonin maganganunsa. Kenan aikin banza takeyi?,kenan ba wadda zata iya cika mata burinta akan faud sai sabreen din da take kokawar fitarwa a gidan?,wannan wanne AKASI NE da boka ke magana a kai wanda yace muddin ya gushe ita zata iya cika mata burinta......wanne akasi ne?.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862





5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 66







66





_ko kisan manzan Allah S A W da kansa ya kasance yana neman tsari daga sharrin abinda ya aikata da wanda bai aikata ba? Yakan ce"Allahumma inni a'uzu bika min sharri ma amiltu wamin sharri ma lam a'amal"_



_shi daya kasance Allah ya gafarta masa duk wani abu da zaiyi da wanda ma yayi,ina gake?_







Dukka jikinta sai ya dauki wani irin dumi,tamkar ma ta manta da fareeda dake zaune gefanta,wani yalwataccen tashin hankali ya duro mata......cikin qasa da minti guda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login