Showing 108001 words to 111000 words out of 147628 words

Chapter 37 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

ta fada cikin dattakon nata tana juyawa da nuna alamu na surukuta



"Da kun qaraso din dai anni" Sabreen ta fada adan kunyace da nufin tsaida annin



"A'ah qaraso nan din sabreen.....ki fito a hankali karki gaggawa" Anni ta fadi tana qara yin gaba,amna da abun yaketa burgeta takeson tayi tsokana nata binsu da dariya.



Dukka hannayensa ya zube a aljihun wandonsa yana qare musu kallo cikin quntataccen qaramin store din ajiyar kayan aikin sola dana engine din gidan idan ya samu matsala. Daga daren jiya zuwa yau idan ka kalli fuskokinsu sai kace basu bane,kada ma mashkur daya kwana a daure yaji labari.



A duk sanda ya kalli mashkur din shi kadai yasan abinda yakeji......har yanzu maganganunsa sunqi daina amsa kuwwa a kuwwa a kunnensa.......har yanzu ya gaza daina tuna sunyi gamayya a daki guda qarqashin abun shaye shaye guda.



Taku biyu yayi y is gaban qofar yana duban mashkur din



"Waye ya aikoka?,ko kaine ka aiko kanka da kanka makasarka?" Kai ya mirgina alamun eh.....koda meye zai faru bayajin zai iya buda baki ya fallasa wannan sirrin.......sirrin da idan har ya bari ya fita to tabbas shima ya gama jin dadin rayuwarsa har gaba da abada koda yayi escape. Abu ne bisa sharadi da yarjejeniyar da aka qullata bisa masaniya da kuma abinda zai faru a qarshe.



Sosai fu'ad ya zuba masa idanu yana karantarsa,yanayinsa ya tabbatar masa bai shirya fadin gaskiya ba duk da baqar wahalar da ta nuna kanta a tattare dashi. Bayajin zai iya wahalar da kansa tsaiwa yana batawa kansa lokacin tambayarsu,yana da wadanda zasu tafi masa dasu har su gane kuskuren da suka tafka na shiga gonar da ba nasu ba. Hannu kawai ya daga ya yiwa Jordan alama,Jordan din ya jinjina kai sannan ya juya yana fita hanyar waje da sassarfa irin ta majiyin qarfi,cikin qasa da minti biyar sai gashi sun shigo da wani.



Kakkauran mutum ne,me qiba da madaidaicin tsaho,yana da baqar fata data haska sosai cikin color din uniform din 'yan sandan dake jikinsa. Maqale da jikin rigar rubutun sunansa ne S.nuhu,wanda iya rank dinsa zai nuna maka cewa shine commissioner of police na jahar gaba daya.



Salute na juna sukayi shi da fu'ad din,sannan yace



"Yallabai yace idan da damuwa ayi gaba dasu" Kai fu'ad ya jinjina yana baro jikin qofar yana takowa a hankali gami da dubansa



"A wuce dasu a ajjiyemin su,har sai zuwa sanda na buqacesu". Kai s nuhu ya gyada cikin girmamawa,daga yanda fu'ad yayi maganar ya gama fahimtar komai. Suna girmamashi kaman yadda yake girmamasu,tun daga can copral har zuwa matakin qarshe na samansu,wannan ya sanya basuyi qasa a gwiwa ba suka bashi kyautar jami'an tsaro cikin mutanensu,mutum ne me qoqarin kiyayewa da mutunta doka. Yana da qarfin mulki dana dukiyar da zai iya komai da yaga dama musamman a yanayi irin na qasarnan da zaka iya komai ba komai bane,amma baya yin hakan,komai din yana qoqarin ganin ya azashi akan mizanin daya dace.



"Don girman Allah ka taimakeni.....kayimin sutura.....yallabai ni na fadi gaskiya,na fadi gaskiyata......iyakar gaskiyata kenan". Hanzari ya fada yana hade Hannayensa waje guda yana kallon fu'ad da tuni ya soma wucewa xuwa cikin gida.



Ko muryarsu bayason ji bare yakai ga kallon fuskokinsu,don haka baiko waiwayo ba bare ya saurareshi. CP s.nuhu ya daka masa tsawa



"Miqe muje......ku daukeshi ku samin a mota,mutanen banza kawai......banda ma me jadda din kuka samu waye kamanshi da zaku keta masa haddin gida ku shiga ku wayi gari haka da sauran lafiyarku?,ba a nan zamu gane gaskiyar taka ba......muje don ubanka" Cp ya fada shi kansa abun yana masa takaici.



Sam baisan da zuwan annin gidan da safen ba,don haka kanshi tsaye ya shiga falon hankalinsa yana ga samanshi. So yake ya isa ya kulle kansa don baya buqatar ganin kowa kaman yadda bai buqatar hayaniya ko dogon magana sam sam. Saidai yana sanya qafarsa a falon yaji muryar annin sanda take fadin.



"Allah ya qara lafiya......yasa kaffara,saiki dinga kula da jikinki da kyau,Allah ya inganta". Murna ta kama amna,duk yadda taso cinye maganar amma sai data fito



" Anni......wai.....wai hamma shima ya kusa zama daddy?".



"Ungo nan" Anni ta fada tana watsa mata yatsunta biyar,saita saka hannu ta qunshe bakinta tana dariya.



Shikam daga shi har sabreen dake zaune daga gefe maganar tazo musu a wani irin ba zata.



"Allah ya inganta?....zama daddy?,wata qaryar ta gilla musu kenan?" Ya fada qasan ranshi yana yamutsa fuska gami da watsa mata wani irin kallo duk kuwa da cewa yana nesa kadan dasu,sannan dukkansu ba wanda yasan ma ya shigo parlor din. Kai ya jinjina wani abu yana tsaye masa a wuya



"To yaushe tayi cikin?" Yaji tambayar ta taso daga ransa,take yaji kansa ya qara masa wani nauyi saboda wani tunani da yazo ransa.



Dukka juriyarsa da yakejin kamar tana sulalewa ya tattaro yana sake maimaita sallamarsa,suka daga kai dukansu suna amsawa banda sabreen da tayi qasa da nata idanun tana jin sam sam bata sha'awar dubanshi.



Gefan anni ya zauna kaman yadda ya saba a gida,duk sanda zai iso gabanta gefan ta nan ne wurin zamanshi. Tuni amna ta kama kanta tana gaidashi cikin tsoro,don tasan zai wahala baiji abinda ta fada ba.



"Ina kwana?" Sabreen ta samu kanta da fadi duk da bata dubeshi ba,haka kawai takejin wani irin nauyin anni.



"Lafiya qalau.....ya jikin?" Ya furta a dake yana dan duban fuskarta kadan wajen daya lura a jiya ya fashe,baiga komai ba don ta rufe wajen da dan kwali,sai ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa zafi.



Ba abinda ya hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a bakinta,zuciyarsa ta sake matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin bai samu cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun.



Hankalinsa ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da girmamawa. Yaji dadin yadda farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya faru a gidan ba jiya da daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya



"Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita sosai.....inajin idan zai yiwu ma nabar amna a gidan,don a yanayin mace irin haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai yakeyi". Dan satan kallon anni yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon me ciki take yiwa sabreen din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi tayita masa kuka.



Kwata kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule masa,yana jin kamar kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana jin ciwon yadda mahaifiyarsa ta xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da yarinyar da kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi.



"Ashsha......da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu ke da ba cikakkiyar lafiya gareki ba?" Anni ta fadi sanda Sabreen din ta fito daga kitchen ta ajiye mata tray dake dauke da spicy black tea soyayyen qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi tun shekaran jiya waccan amma ta kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta yayi ba. Zataci din amma gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya ita ko ma'u suka girka abu sai yayi musu yawa.



Sallamar da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can.



"Sannunku dai.....gafaranku" Zuwairan ke fadi tana rarraba idanu. Zuciyarta cike fal da fargaban kada shigowarta ya zama silar barinta aiki.....amma kuma tana jin relief na wani fannin idan ta tuna tana da assurance na bazaice komai ba muddin annin tazo gaidawa.



Zubewa ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara hankalinta ta maida kan annin tana zuba gaisuwa.



"Ya mukaji da wannan abu?" Zuwairan ta fada duk da a tsorace take.



"Ke!" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake saurin isar da saqo gun wanda aka kira saboda zurfin muryar da wani irin kaifi





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 62







62







"Eh......na'am" Ta fadi adan zabure



"Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?" Ya tambayeta kai tsaye da wani kallo da yaso rikita duk lissafinta. Kai ta fara girgizawa



"Ranka ya dade.....aah"



"Good" Ya jinjina kai



"Bacen a gun" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa qarshe tana miqewa da hanzari gami da cewa



"Tuba nake.....tuba nake". Daga shi anni har amna binta sukayi da kallo,a mamakance anni ta maido dubanta kansa bayan ta fice



"Allah me mutane.....ina ka samo wannan Muhammadu?"



"Maamah ce....." Ya fadi a taqaice yana jin wani abu game da matar tare da bin hanyar da ta wuce da kallo kaman tana wajen har a lokacin. Tun bai qarasa ba ta fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada tana fadin



"Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce.....diyata" Anni ta fadi tana murmushi. Qasa sabreen ta sakeyi da kanta tana dan qaramin murmushi. Karon farko idanunsa suka soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani abu me.kama da murmushi akan fuskarta......hakanan lokaci na farko da yaga wani alamu na wata aba wai ita KUNYA a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin wannan abun da takeyi har qasan ranta take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da kanta,abinda bai taba gani ba a tare da ita sai yau.



"Allah ya qara sauqi kinji.....ki kula da jikinki da kyau" Anni ta fadi tana jin yaqinin kamar abinda dai take hasashen ne yake tare da sabreen. Har cikin zuciyarta takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma kuma ta gaza tunawa.



"Ameen anni.....na gode" Siririyar muryarta da yau kadai tayi wani irin laushi ta fito tana furta hakan har yanzu kanta a qasa.



Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take jiranta da masu tsaro lafiyarta mutum biyu



"Zamu tafi tare da amna din.....amma anjima da dare in sha Allah zata dawo,sai kinfi jin dadin xaman......nasan halin Muhammadu....indai kin ganshi gida zaune to saidai annual leave dinshi yazo ko kuma baida lafiya da gasken gaske". Haka kawai ta samu kanta da kallonshi ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran zama ne maras dadi da ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci dabi'u masu yawa tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi kowa sanin muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba.....sannan zaman kadaici baya damunsa sam sam.



Suna a tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din gidan. Idanunta akan bayan motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna din,dan wanzuwarsu na qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi da takeji a zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da magani har xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin asarar daya tafka da ba zata fadu ba.



Sai da motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da kuma wajen waye take?. Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a hankali tana komawa ciki.



Da kallo ya bita ranshi yana sake masa susa......idanunsa suka sauka kan hips dinta da suka bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma bane,take zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe kansa,sai kawai yabi bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome.



Tana dab da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya cimmata. Bata zaceshi ba ta tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa junansu,wani irin kallo na tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na dauke da wani irin nauyi da baisan yadda zai rageshi ba.



Ta dauka zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma sai taji ta sare nan da nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye sila ba. Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali ba hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa qoqarin hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel din jikinta daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi babban aikin rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin rai amma kuma yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk da cewa ta kowacce fuska.....duk kuma inda ya juya.....kowacce hujja idan ya daga,ya tattaro ta nan data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin WACECE ITA.



"Wancan lokacin.......na taba ganinsa cikin hotel a abuja yana cigiyar karuwarshi da suka kama daki,ta kwashe masa kudade masu yawa kwatankwacin yadda ya faru da kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki sai KE!......Wanene shi?,ya akayi ya shigomin cikin gidana?,cikin dakin da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halak?".



Wani irin duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin da batasan ya faru ba......eh ta taba binsa abuja.....kuma aikin mashkur kusan shine aiki na qarshe da tayi har yau kuma bata sake sha'awar maimaita wani abu makamancinsa ba.......amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a matsayin karuwa yana cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a kunnuwanta......duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan a gaban fuskarta......to takan iya manta ya kuke da ita?.



"Am asking you......" Ya fada yana jin ya soma hasala ganin shurun da tayi kamar ba da ita yake magana ba.



"Ban sani ba......." Ta bashi amsa muryarta tana so ta fara rawa. Me zata gaya masa wanda zai sanya ya fahimceta?.



"Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an fasa kowanne gini na gidan nan ba......ya shigo dakinki ba tare da kinyi yunqurin kiran koda security daya na gidan nan ba......ya shigo dakinki daidai lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike daure da towel kadai da hijabi?" Ya qarasa maganar yana qarasawa dab da ita,yana kuma kaiwa qarshe a tsawace har sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu.



Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a namiji.....wanda tuni ta karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci.....izgili da toxarci na da namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya daukesu.



"Ban sani ba nima" Ta sake maimaita masa don da gasken batasan yadda akayi mashkur ya shigo ba.



"Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo kanta?!.....nace ita ta kawo kanta?!!!" Ya fadi da qarfi kaman yana shirin fasa mata kunnuwa.



"Stop it!.....wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma kakeso na baka amsarta?!" Itama ta maida masa muryarta na rawa,oily eyes dinta suna qara walainiya cikin hasken ranar daya fara dagawa.



"Ni kikewa shouting?" Ya tambayeta da tsananin mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta janye magana ta gaba da yaso fadi. Bai fiya daga waya a cikin irin wannan yanayin da yake cikin tsananin fushi ba......amma yana expecting kira me muhimmanci daga gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar ivory Coast,dole ya ciro wayar.



Shi da ita dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta fara janye idanunta tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa.



Ya sanyata a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin karuwarshi ko yarinyarsa.....batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?.



Ta nashi bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas ba abinda zai hanashi tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba.



"Sorry sir" Yaji an fada da sauri,abinda yakai hankalinsu kenan wajen. Me sunan malam ne,da sassarfa yake barin wajen saboda kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da bai biyo ta wajen ba.



"Zo nan" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa dake dauke da newspaper daya saba ajiye masa duk safiya daga kamfanin jaridu daban daban.



Sunkuyawa tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka kawai taji bama zata iya zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi ba Shima.....wacece faridan?,meye alaqarsu da koda yaushe layinsa cikin karbar kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan me sunan malam.



"Good morning sir" Ya sake gaidashi cikin girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa masa newspaper din ba kaman yadda ya saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne a daura da dining suna jiran fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai kuma fitowar gobe.



"Morning.....how

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login