Showing 105001 words to 108000 words out of 147628 words

Chapter 36 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

wani abun mamaki yadda suketa haushi ya ninku,yana ganin sanda me kula dasu ya dubasu,ya kuma yiwa security na gidan magana suna sake bincike sassannin gidan amma basu ga komai ba saboda sun shigo ne ta hanya mafi sirri da samun tabbaci,kuma sun samu mafakar da binciken me bincike bazai taba kaiwa nan ba.



"What are you waiting for?!!!" Fu'ad da dama dukkaninsu suma a cike yake dasu ya fada a tsawace,ba shiri suka durfafesu,hanzari yayi wuf ya kama qafarsa yana sake roqonsa.



Wani wawan duka yakai masa da qafar daya sanya hanzari zubewa warwas,basu saurara masa ba suka sungumeshi suka hada da mashkur da tsabar razana ya kasa magana,sai yakejin kamar qiyama ce zata tashi. Yasan illar karnukan,don sanda yake sharafinsa ya ajesu a gidansa sun kusa guda biyar,hakanan baisan adadin mutanen da ya sanya suka yagalgala ba.



"Karku sakasu a cikin cage din.....ku ajiyesu dakin kusa dashi" Ya basu umarni sanda suke kicin kicin fita dashi.



"Okay sir" Suka amsa masa sanin wayeye farouq wajen boss din nasu. Shi daya ne duk duniya yake tada hukuncin da fu'ad yayi kuma ta zauna ba tare da haufi ko kankare ba,shi yasa suka karba umarnin nasa kaman yadda ya basu.



Yadda yaga komai yasan ba lafiya ba.......yadda kuma yaga yanayin hannunsa da gidan ya tabbatar akwai gagarumin wani abu daya faru.....uwa uba wani kwantaccen fushi d yake gani a fuskar Fu'ad ya sanar masa akwai matsala ko a yadda ya fita a fusace.









*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 60







60





Tun bai qarasa inda yake hangen security na gidan daya tara ba yakejin muryarsa dauke da fushi me nauyi. Fada yake da duka zuciyarsa da jikinsa ma,sam kaman ya manta dare ne a yanzun......daren ma kuma irin daren da akayi ruwan sama ya dauke wanda ke ninka kowanne dare a shuru da daukewar sawu.



"Your services are no longer required......you were fired!"



"Ya salam" Farouq ya fadi,abinda yaketa sauri ya dakatar dashi kenan. Fushinsa na yau yanata bashi mamaki,sau tari shike daukan abu da sauqi......yawancin lokuta shike jan qafa da jan lokaci akan abubuwa irin wadannan......yana bin komai da lura a kuma tsare,har sai ya tabbatar dashi a inda ya dace.



Kasa cewa komai yayi,don su kansu ma'aikatan da security din dake on duty a daren kowa cikin matuqar tashin hankali yake. Yadda suke roqonsa da mabanbantan harsunansu dukka sai suka bawa farouq din tausayi. Kowanne a cikinsu idan ka dubi fuskarsa ya kadu da hukuncin ba zata na me gidan nasu.



"Calm down.....ya isa" Farouq ya isa gabansu yana fadi bayan komawar fu'ad din ciki. Hankulansu kuwa suka bashi cikin mutuwar jiki hankali a tashe.



"Ku kwantar da hankalinku.....kowa ya koma bakin aikinsa kafin wayewar gari......but,ku sake tsaurara kula kafin muga abinda hali zaiyi.



Duk da bawai tabbaci ya basu na cewa ya dawo dasu bakin aiki ba amma hakan ya faranta musu. Sun sani babu wani guri da zasu samu walwalar rayuwa da 'yanci da albashi me tsananin azabar tsoka kaman gidan jadda.....salary yake musu na kece raini......irin salary din da sunyi imani ko a villa suke aiki babu me biyansu irinsa. Uwa uba ga ihsani da alkhairi da suke samu kowanne lokaci,wanda ya kusan kamo abinda ake biyansu albashin aikinsu. Da yawansu suna jin idan ba gidan Muhammad jadda ba babu a inda zasu iya aiki,shi yasa suke riqe da aikinsu fiye da yadda ma yake tsammanin zasuyi.



A parlor ya sameshi a tsaye kaman wanda zama ya gagareshi. Baice masa komai ba ya taka inda yake tsayen ya riqe hannunsa sannan ya wuce dashi,suka ratsa hallway din suka saura samansa.



Saman monotti sofa ya zaunar dashi,ya taka da kansa zuwa shiyyar da aka tanada don ajjiye first aid box,don kusan yasan komai na gidan tunda shine ma tsara yadda zai kasance din.



A gabansa ya zauna,ya bude box din ya ciro cotton wool da spirit ya tsiyaya ya fara goge masa ciwon. Sai a yanzu yake danjin radadin da hannun ke masa amma kadan kadan,saidai har yanzu abinda yakeji a zuciyarsa ya dara wanda ke a hannunsa.



"Ko meye da sauqi ake daukarsa......da irin wannan temper din da kake ji a ranka komai fa bazai warware ba" Farouq ya fada yana qarasa goge masan,har yanzu kuma yana mamakin abinda ya birkita nutsatsen mutum irin fu'ad din. Duk da ya sani,ba abu bane me sauqi a keta alfarmar gidanka a shigo maka ba......to amma kuma yadda yasan fu'ad zai iya cewa tun wani zamani can daya shude rabon da yaga wannan attitude din a tattare dashi.



Wayar tafi da gidanka din dake falon,wadda ke ajiye kusa da console mirror din parlor din ce ta dauki tsuwwa. Saddiq dake zaune daga gefe dukka jikinsa a mace ne ya dauka



"Daga hallway bedroom ne"



"Ka daga ko Dr rubayya ce" Farouq ya fadi sanda yake tattare ragowa ragowan audugan da yayi amfani dashi. Maganan second goma sukayi kwata kwata,ya sauke wayar yana duban farouq



"Dr ce ke magana.....tace ta kammala......amma wai tanason ganin hamma".



"Ka gaya mata tayi abinda ya dace kawai basai nazo ba" Ya fada yana jin ciwon kan daya tashi da jin dadin ya sauka yana son dawowa. Kai farouq ya girgiza yana dubansa,muryarsa a qasa qasa yadda saddiq bazaijishi ba yace



"Dole kaje tunda tace kaje din.....dole saika gwadawa duniya halinka?" Idanunsa da har yanzu basu koma fararensu ba ya watsawa farouq,kaman zai magana sai kuma ya fasa ya tsuke bakinsa. Kamar bazai tashi ba kafin ya miqe yana kiran sunan Allah,wanda motsawar bakinsa ne kadai zaisa gane hakan.



A hankali yake sauka zuwa qasan,saidai duk sanda ya kusanci dakin sai abun daya faru mintunan baya yayita dawo masa. Bama irin idan ya tuna ba komai a jikinta......daga ita sai towel sai hijab,sai yaji tamkar iskar da yake shaqa tayi masa kadan. Su biyu a daki tana daga ita sai shi.....su biyu a dakin da babu cikakkiyar sutura a jikinta......gaban hijabinta yasha cukuikuiya?.....duk sanda ya kawo nan sai ya lumshe idonsa saboda ji yake kaman an dauka adda an kafta masa sara a tsakiyar kansa.



Handle din ya murza ya tura ya shiga da sallama saman labbansa. Ma'u dake gyara dakin ta dago daga kwashe sharar data gama,ta rusuna tana gaidashi duk da dare ne,sannan ta kwashe dustpan da vacuum cleaner din tayi waje dasu.



Haka kawai ya samu kansa da bayason kallon fuskarta,don ba abinda yake tuna masa sai a yanayin data fado jikinsa.



"Numfashinta ya koma normal,kuma yanzun haka bacci take me kyau.....ko da wanne lokaci ma zata farka abinta........amma please sir......koda asthma dinta baiyi tsanani ba at least ya kamata ace an ajjiye mata in healer.....and ya kamata ta dinga kula da gujewa ta'ammali da abubuwa masu hayaqi da yawa". Kai kawai ya jinjina ma Dr rubayya



"Allah ya qara afuwa yasa kaffara.......idan kuma ana buqatar wani abun.....am ready in sha Allah,koda yaushe kuka kirani am available for your needs".



"Thank you" Ya fada can qasa da kalar miskilancin nan nasa da ba wani baqon abu bane a wajenta.



Already kafin ta fita ya kira saddiq ya gaya masa gata nan su maidata gida,yana kuma sauke wayar kiran farouq ya shigo masa



"Mu duka mun wuce gida,but.....na kira wasu daga cikin guards dinka an qara akan na cikin gidan......in sha Allah kome zaiyi daidai......but please please.....karka dauki doka a hannunka akan mutanen nan". Farouq ya fada cikin narke murya. Ya dade da sanin halinsa,muddin ranshi yakai qololuwar baci irin wannan bai iya hukunci ba.



"Kaji?" Farouq ya sake maimaitawa jin yayi shuru baice komai ba.



"Alright" Ya fadi a hankali kamar wanda maqoronsa ke masa ciwo yana gintse kiran.



Iska ya sake furzarwa daga bakinsa,daga jikinsa har zuciyarsa babu wani abu dake masa dadi,sai ciwo kawai.....wani irin ciwo me radadi a gangar jiki da zuciyar.



Karon farko ya maida dubansa saman fuskarta,wanda daidai nan idanunsa suka hangar masa wayar dake gefan pillow dinta. Wani abu ya tsarga masa har yatsun qafarsa,sai ya miqa hannu ya dauko wayar.



Tabbas itace wayar daya gani a hannunta shekaran jiya.....wayar da baisan yadda akayi taxo gidan ba ta kuma zama mallakinta har take amfani da ita.



Jujjuya wayar yayi sosai yana qare mata kallo,sai ya latsa malatsin gefe haske ya kawo,ya sanya dan yatsa ya shafi fuskarta take ta bude.



Bangaren kira ya shiga ya soma dubawa,kirane da numbers barkatai wanda kusan dukansu babu suna. Ci gaba yayi da dubawa har zuwa kan date din shekaran jiya wanda wata number data qare da 01 itace number qarshe da aka amsa kira da ita.



Kai ya jinjina a hankali yana komawa bangaren saqonnin karta kwana wato sms. Dunqule hannunsa yayi da kyau yana ci gaba da duba saqonnin da suka shigo da mabanbantan numbers suma,wanda dukkaninsu suna dauke ne da nau'ikan kalaman soyayya iri iri,saidai kowanne saqo ba wata amsa guda daya da ta maida masa.



Kasa ci gaba yayi da dubawa saboda yadda dukka jikinsa ya dauki tsuma,sai ya kashe wayar ya jefata aljihunsa sannan ya miqe yana dubanta da wani zafin zuciya. Takawa ya soma yi a hankali,har cikin jiki da zuciyarsa yana jin bazai iya zama da ita na daren gaba daya ba a daki daya,sai daya hau saman sannan ya kira sashen ma'u yace taje ta kula da ita,baima aje wayar daidai ba ya dora kansa a hankali saman sofa din yana fidda numfashi kansa kaman zai fado.



Tunani ne iri daban daban suke barazanar tarwatsa masa kai,ya rasa da wanne zaiji?,da wanne zai fara?,meye daidai cikin hasashensa meye ba daidai ba?,ganin yana neman rasa nutsuwarsa cikin qasa da minti talatin,sai ya miqe a gaggauce ya jawo earpiece ya toshe kunnuwansa da karatun qur'ani,abinda ya sanya duk abinda yakeji ya soma sauka a hankali,nutsuwarsa ta soma daidaita,nauyin da yakeji a qirjinsa da zuciyarsa suka soma raguwa,sannu a hankali ya maida idanunsa ya lumshe wani bacci yana yin awon gaba dashi a cikin falon.



*_TO ASUBA TA GARI......SAIDAI KUMA KO DAME SAFIYAR RANAR ZATA WAYE MUSU DASHI?_*









*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_Zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 61







61





Tun daga sanda ta farka bata samu wata nutsuwa ko kwanciyar hankali ba sai bayan data tabbatar ba wani abu a jikinta da mshkur din ya samu kaiwa gareshi



"Allah na gode maka.....Allah na gode maka" Ta dinga maimaitawa cikin bandaki hawaye na layi bisa kuncinta.



Wanka ta sakeyi dab da asuba da ruwa me dumi sosai,koda ta fito ma'u ta ajiye mata wasu kayan da zata saka. Har zata fita ta bata waje ta canza kayan tace ta zauna,tana jin ma'u kamar jininta,tana jin gamsuwa da dabi'un ma'un. Mutum ce me kamun kai sosai,kawaici gami da kauda kai daga kan komai da bai shafeta ba ko kuma ba'a sanya da ita ba,wannan yana daya daga cikin dabi'un da suka sake sanyawa hankalinta ya kwanta da ma'un.



Ko data shirya hijabi da abun sallah ta buqata,ma'un ta bata ta koma ta zauna. Ta shimfida ta tada sallar. Isha'in da bata samu yi ba a dazu ta bayar,sannan ta dora da shafa'i ta kuma zarce da nafilfilun da ita kanta batasan adadin guda nawa tayi ba. Sam sam bata jin koda digon bacci a idanunta,samun kanta tayi da tsananta addu'o'i masu yawan gaske cikin sallarta. Idanunta sun zubda hawaye masu yawan da adazu bata zubda su ba,jikinta yayi wani mugun sanyi zuwa bayan wani lokaci,qafafunta sunsha tsaiwar da zama kawai take da buqata,saita zauna din tana irga tashihi da yatsun hannunta.



Tuna abinda ya faru da ita dazun kawai razani yake haifar mata,yayin da kwanyarta tayi nisan zango wajen tunanin waye yake da alhakin zamewa mashkur jagoran daya risketa har cikin dakinta.



Tayita qoqarin tuna abinda ya faru bayan zubewarta amma ta kasa tuna komi......abinda kawai take iya tunawa sanda ya shigo dakin da fadawa jikinsa da tayi tana neman tallafi cikin kubcewar numfashi.



Kiran farko dana biyu duka akan kunnenta akayi shi,bayan sauran masallatai sun tada tasu sallar sai itama ta miqe ta bada nata faralin.



Ci gaba tayi da zama still a wajen......tana tsammanin wai ko zataji bacci amma babu shi ba alamarsa. Wani firgici takeji har tsakiyar zuciyarta wanda bada taimakon hailala da takeyi zuwa yazu batajin zata iya zaman dakin ma gaba daya.



Sanda gari yayi haske ta kalli ma'u dake gefe a zaune,qaunar ma'un da darajarta yana qaruwa cikin idanunta. Sam tana lura da ita batayi bacci ma itama



"Kije ki huta ma'u.....baki samu bacci ba kema" Sabreen ta fada muryarta a karye da wani irin sanyi da bata taba yi ba. Dan murmushi ta saka tana gyara zamanta



"Ba wani damuwa.....bai kamata ai na barki ke kadai ba......saidai ko idan kina buqatar cin wani abu?" Kai sabreen ta girgiza mata



"Bana buqatar komai.....kije kidan rage baccin ma'u ki kintsa......kya dawo daga baya,bana buqatar komai". Kai ta jinjina sannan ta miqe tana mata sallama ta fice.



Qarasa shafa addu'o'inta tayi ta miqe tana son jin qara watsa wani ruwan dumin ko jikinta zai qara yi mata dadi. Wannan karon saita taka zuwa bakin qofa ta murza lock dake jikin qofar kamar me tsoron maimaituwar abinda ya faru daren jiya ya sake faruwa,sannan ta juya a hankali tana wucewa toilet din.



Tare dasu Jordan da farouq ya kawo suka wuce sallar asuba,wadda duk da qarancin baccinsa hakan bai hanashi samun sallar asuba ba. Tun daga fitarsu zuwa dawowarsu su kansu sun fahimci sam yau ba'a mode dinsa yake ba. Idan kai baqo ne a rayuwarsa ba lallai ka fahimci lokutan walwalarsa dana bacin ransa ba......kawai zai zame maka kaman daya ne saboda rashin fara'a da bai da ita......amma gasu da suke tare dashi tsahon shekaru,suna iya fahimtar walwalarsa da akasinta dukka qarqashin dabi'arsa me kamanceceniya da juna.



"Mu qarasa ciki jordan" Yace da jordan din bayan sun shigo ainihin farfajiyar gidan. Ba musu ya takewa uban gidan nasa baya suna takawa zuwa dakin da ya bada umarni a ajjiye masa su.



Duk da kusan dabi'ar gidan shuru ce,amma a yau tana jin gidan ya sake zama shuru gaba daya. Hakan yake don tun daga gate din farko na gidan zakaji gidan yayi wani mugun shurun da ko tarin wani babu. Zaka rantse da Allah mutuwa akayi cikin gidan saboda yadda kowa ya sake shiga nutsuwarsa. A mugun kasalance da wani irin rashin kuzari ta shirya cikin atamfa dinkin plain zani da riga,wanda babu wani ado da akayi mata ko guda daya face qwarewa da gwanancewar dinki daga telan nasu.



Dare daya amma gaba daya ta fada,tayi wani rama da ta bayyana har a qasusuwan wuyanta,fuskarta tayi fayau,inda ya fashe a jiya sai yanxu ya fito sosai ta ganshi. Tsaga ce 'yar siririya bame yawa ba,fuskarta tayi wani fayau kaman wadda tayi zazzabin dare. Koda ta kalli fuskarta gaba daya sai taji zuciyarta ta karye,ta koma da baya a hankali tana sake tuna yadda mashkur ya fado mata daki.



Duk wanda wani bala'i ya sameshi kalleshi kawai......ashe fiye da haka matan da ibtila'in fyade ya fadawa suke ji?. Raurau idanunta sukayi,can qasan ranta sai ta samu kanta da godewa Allah da ya bata ikon tsame mata da yawa da suka fuskanci ibtila'i irin wannan zuwa sauyin rayuwa daya kawo musu sassauci da rangwame.



Qasa tayi da kanta,daidai lokacin da taji ana mata knocking. A nata zaton ma'u ce......wannan ya sanyata kanta tsaye ta nufi qofar ta kuma bude tana bada hanya,saidai a maimakon ma'u anni ta gani,gefanta kuma amna ce tsaye tana riqe da purse din annin.



Wani irin nauyi da bata taba jin irinsa ba ya saukar mata,tayi qasa da kanta tana basu hanya.



"Ai jikinma yayi kyau.....basai mun shigo har uwar daki ba,mu koma falo mu gaisa a can" Anni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login