Showing 90001 words to 93000 words out of 147628 words

Chapter 31 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

ta girgiza tana fadin



"Bakice ba ai". Fuska kadan maamah ta bata



"Haba ke kuwa auta.....yarinyar kirki,zo ku gaisa mana....wataqila sanda zata tafi ai baki fito ba". Dawowa tayi ta rusuna har qasa tana gaida hajjan abinda bai taba faruwa ba kenan tsahon rayuwarta. Da fari idanuwa kawai hajjan ta saki tana kallon lailan,har sai da taji lailan ta maimaita gaisuwar sannan ta duqa tana dagota daga tsugunnon da tayi



"Ki dauko mayafinki kizo mu tafi gida" Ta fada muryarta na rawa amma tana qoqarin danne rauninta don bata fatan maamah din ta gani.



Kai ta girgiza tana duban maamah wadda tayi kaman batasan abinda ke faruwa ba,tana laluben wajen zama hankalinta akan fuskar wayarta



"Nafison nan hajja.....ni ki barni a nan" Ta fada tana zamewa daga jikin maamah din ta wuce abinta hankalinta kwance zuwa hanyar dakin da aka bata.



"Bismillah.......zauna mana surukata" Maamah ta fada fuskarta a sake. Kalmar suruka din da maamah ta fadi shine ya sanya hajja jin wani abu tamkar wutar lantarki ta fusgeta. Cikin qasa da minti guda gumi ya fara tsatsatsafo mata ta kowacce kafar gashi ta jikinta.



"Atika!" Maamah ta qwalawa me aikinta kira,wanda cikin qasa da minti daya ta bayyana,sanin da sukayi mata batason ta kiraka ka samu jinkirin zuwa.



"Dauki remote ki kunnawa surukata A.c,karki saka da yawa kada kuma ta saukar mata da zazzabi"



"To hajiya" Atika ta fada da rawar jiki tana me aiwatar da abinda maamah ta umarceta.



Zagayawa kawai kalmar takeyi cikin kunnuwan hajja.....indai har kalmar surukuta zata fita daga bakin maamah a wannan yanayin,lallai ne ba abinda bata sani ba kenan.



"Ki maida hankalinki jikinki hajja......har mariya ce zata firgitaki har haka?". Wani sashe na zuciyarta ya bata qwarin gwiwa har ta samu qarfin halin tattara 'yar nutsuwar jikinta tana neman wajen zama gami da fuskantar maamah.



"Mariya......zuwa nayi na duba lafiyar laila.....ya kuka tashi?". Murmushin nan dai ta kuma saki,sannan ta ajiye wayarta a gefe tana bada hankalinta gaba daya a kan hajja



"Laila tana lafiya......kuma zata ci gaba da kasancewa lafiya sumul a hannuna......kinsan na iya riqon 'ya'yan jama'a" Ta fada hankalinta kwance.



Murmushin qarfin hali hajja ta saki,sannan ta jinjina kai



"Ai na sani mariya......mun tashi lafiya?"



"Lafiyarmu sumul qalau hajja....." Daga nan ta fada nazarin da wacce kalma zata tunkareta. Idanunta ta daga tana duban maamah.



"Muna magana jiya sai kuma Kira ya yanke....."



"Eh wannan case din na gama solving nasa,saura fitar result"



"Zancanmu fa kan laila da fu'ad?" Hajja ta jefa mata tambayar kai tsaye,duk kuwa da cewa ita kanta me bawa wani amsa ce.....saidai tanaso takai mariya inda take buqatar aje.



Buda baki maamah tayi da nufin cewa wani abu......amma sallamar jarma daya daga cikin masu gadin gidan yayi sallama daga can bakin qofar falon.



"Malam jarma ya akayi?" Maamah ta buqata sani sanda yake duqewa a wajen



"Baqi gareki hajiya......ban sani ba zasu iya qarasowa ko a maidasu?". Fuskarta da dan mamaki take dubansa



"Baqi kuma?,daga ina?"



"Diyar ambassador Khaled mustapha ce,haka tace a gaya miki". Wani madaukakin mamaki ya cika maamah din,ba ita kadai ba,hatta da hajja sunan yaja hankalinta qwarai da gaske.



Miqewa maamah din tayi tsaye tana dubansa



"Maza ayi mata izini ta shigo......na tabbatar koma meye ya kawota nan,silar haihuwar ALKHAIRI ne fu'ad" Ta furta tana jin wani irin alfahari da haihuwarsa fiye da kowanne lokaci. Uwa uba tana yine da biyu,don ta tabbatar gaba daya hankalin hajja yana kan abinda yake faruwa.



Sanye take da wani matsiyacin yadi da aka narkar da kudade masu nauyi kafin siyansa da yagalgalashi,aka kuma yi masa dinkin fitted gown data zauna a jikin laila......kai kace a jikinta aka dinkashi.



Yadda dinkin ya zauna mata a jikinta.....hatta da dagawar numfashi daga cikinta da qirjinta kana ganin gudanarsa. Ba mayafi a jikinta,sai dankwalin material din da aka mata wani dauri dashi saika rantse hula ce ta kafata. Wasu nau'ikan dan kunne manya ne a kunnenta,wanda suke tafe da.manyan banguls da suka dace sak kalar material din jikinta kamar a company daya aka qerasu. Highhill ta sanya masu tsananin tsini sarqafe da igiyoyi,kaman yadda qwayar idanunta ke saye da tafkeken glass daya kusa cinye rabin fuskarta. Labbanta kwance reras da lip gloss,iya wannan kadai zai gaya maka tafiya akayi irin ta masu abun,ba wahalar hanya tunda sararin samaniya ne yayi aikin.



Yadda take taku daya bayan daya tana takowa ciki,idanunta kan kowanne sashe na parlor din tana yaba alatun da aka zuba.....haka bakinta ke bada satin qas qas na chewing gum din da take taunawa cikin bakinta.



Tana daga tsakiya,gefe da gefanta kuma fitattu kuma manyan qawayenta ne,lubna da jalilah,daga bayanta kuma masu aikinta ne data taho dasu suma guda biyun.



Fuskar fareeda ba boyayyar fuska bace musamman idan kaidin ma'abocin kallon news ko dabdala a social media ne. Kusan duk wani motsi na mahaifinta ko na siyasarsa zaka ganta a ciki zaka kuma tsinceta a ciki dumu dumu.



Lafiyayyen murmushi ya kubcewa maamah,ta taka a hankali tana marabtarsu. Doso sun da maamah tayi shi ya sanya laila cire glass din fuskarta dukka a qoqarin ta na nunawa girmamawa ga maamah din.



Cikin qasa da minti biyar suka yiwa kansu mazauni a parlor din,sannan kuma gabansu ya cika da nau'in kayan ciye ciye daban daban na alfarma.



"Nasan zakiyi mamakin zuwana wajenki maamah?" Ta fada tana qoqarin karyar da muryarta.



Kai maamah ta jinjina,tako ta ina tanajin wani girma yana hawa kanta



53





_Daga abu hurairah Allah ya qara yarda dashi yace:mazan Allah S A W ya ambaci ranar juma'a,yana cewa "A CIKINTA KAWAI WANI LOKACI,BA WANI BAWA MUSULMI DA ZAI RUSKETA YANA ME TSAIWA YANA SALLAH YANA ROQON ALLAH WANI ABU FACE SAI ALLAH YA BASHI ABINDA YA ROQA DIN". sai manzon Allah yayi nuni da hannunsa na qanqantar lokacin (ma'ana baida tsaho,Allah yasa muna cikin wadanda zamu yita ruskarshi)_







"Eh to.....zai iya kasancewa abun mamakin ta wani fuskar,ta wata fuskar kuma ba abun mamaki bane,musamman idan kikayi duba da irin kalar zuri'ar da Allah ya bani" Tayi maganar da nufin jifa ga ma'anoni guda biyu tana gyara zamanta.



Kai laila ta jinjina tana tsare maamah da ido,tun kafin tazo ta hadu da ita tasan wacece ita,don haka ko sau daya bataji d'ar ba na samun nasara ta hannunta ba.



"Ko zamu iya kebewa muyi magana?" Laila ta fada tana duban maamah.



"Me zai hana?,bismillah" Maamah ta fada tana miqewa,sannan ta fara takawa,sai kuma ta tsaya tana duban hajja,wadda keta kokawa da zuciyarta akan tayi abinda ya kamata



"Yi haquri hajja.....zamu gana,yanzu zamu fito" Ta fadi mata tana sakin wani murmushi dake dauke da ma'anoni da dama. Sabon mariya ne......jifan maqiyi da murmushi ko kuma abokin adawa,wannan shine kusan makami na farko da take fara yaqar zuciyar abokin burminta,yayi tsammanin ita din wawiya ce.....itadin ba wani abu da zata iya,saidai kuma daga qarshe reshe ne yake juyewa da mujiya,sai taje maka da wani irin kalar farmakin da zaya kaika qasa koda baka shirya hakan ba. Bata da cikin mutanen da mariyan zata iya farmaka ta haka har kuma ta samu galaba,saboda sanayya ce ta kar da kar,ba wani abu ko hali nata da zata layance mata dashi.



Dan madaidaicin parlor din shima sai daya ja hankalin laila,duk da ba wani baqon abu a ciki wanda bata sani ba.....amma yanayin tsarin da yadda aka zuba komai luxury ya bala'in shiga ranta. Wannan karon maamah ta fahimci haka,saita jefeta da murmushi sanda take zama tace



"Hala kema ya burgeki?,aikin muhammaduna kenan.....komai nasa me tsari ne". Lumshe idanu laila tayi tana sake ji yana kuma shiga ranta,jini da jijiya harma da b'argonta qaunarsa tana sake ratsata



"Inama zaki lamuncemin na zama matarsa.......bisa farashin dala dubu d'ari" Ta furta qasa qasa tana kallon maamah.



Zubawa laila idanu tayi sosai tana jin sautin muryarta yana zagaya dakin,duk kuwa da cewa ta kammala taqaitaccen bayanin nata dake qunshe da saqo me tsananin nauyi.....ci gaba tayi da kallon laila tana son tantance Gaskiyar abinda ta fada ko kuma akasin hakan.....magana ake ta kusan million dari da hamsin ko da sittin fa......kawai don tanason fu'ad?,kawai don tanason ta aureshi?.



Wane sashe na zuciyarta da kwanyarta da yake da kaso mafi girma wajen tsara mata komai ya harba,wannan ya sanya duk wani abu data shirya ambatawa ya wargaje,take ta sauya yanayin fuskarta daga me yalwar fara'a zuwa tsukakkiya



"Wane irin magana ne wannan?,ance miki neman kai nakeyi da yaro na?" Tayi maganar a dake cikin qoqarin nuna bacin rai,da kuma tankwabar da tayin gwaggwabar garabasa da ribar da zata iya samu.



Ga mamakinta murmushi laila ta saki,hankalinta kuma a kwance ta koma tayi relaxing jikin kujerar tana duban maamah,sannan a nutse ta daga qafarta ta dora daya saman daya tana ci gaba da dubanta.



"Karki wahalar da kanki.....kada kuma ki wahalar da shari'a,kada kiyi kaman bakison kudi hajjiya......idan sun miki kadan kawai kice na qara miki,sai na qara mikin a wuce gurin.....fu'ad kawai nakeso,kudi ba matsalata bace sam sam". Sake tsare laila tayi da ido a karo na biyu tana karantar gaskiyar abinda take fada har zuciyarta. Qwaqwalwarta ta lula zuwa duniyar tunani duk da bata barta tayi nisan zango ba.



Akan me zata bari tayi asarar kudin da take gani a gabanta yanxu haka?,bayan tana da damar mallakarsu?. Tabbas akawai manufar turo laila da ubangiji yayi cikisu a daidai wannan lokacin da take neman dukka hanyar da zata cisge sabreen daga gidan fu'ad.....babu ko shakka laila itace macen daya dace ta maye mata gurbinta.



Duka ma a ture ta batun kudaden da zata mallaka......babban abun alfahari ne a yadda ubangiji ya yiwa yaronta kudi yabi sahun manyan masu kudin africa ma gaba daya......ace kuma yau shine yake auren diyar mutum kaman ambassador khaleed mustapha,wanda a muqamai dai na duniya tana jin ba wanda bai riqe ba,saidai kuma a lahira idan ana riqewa.



Lallai ne ita mariya sunanta yana dab da sake fantsama cikin bakunan al'umma.....qawaye dangi da 'yan uwa,tana dab da sake taka wani matsayi na zama cikin manyan matan da fu'ad har yanzu yaqi sakar mata jelar macijin tayi wasa da ita da kyau,....wannan shine mafarin da tauraruwarta ta gaza yin haske kaman yadda takeso. Sunanta takeso ya zama cikin jerin sahun sunayen mata masu aji da sukafi kowanne mata a africa da duniya ma wasa da kudi.....cikin jerin sunayen iyayen attajiran 'ya'ya da kowanne taro ake kwadayi da rububin gayyatarsu,saboda sun zama bangon sugar ko na zuma,masu yayyafin kudi in dollars not in naira......don tana jin zuwa yanzu a arxiqinsa ita kanta tafi qarfin yin kyauta da naira.



"Ki rubuta dukka adadin da kikeso" Ta tsinci muryar laila tana fadi,saita sauke idanunta akan abun rubutun da laila ta aje a tsakaninsu tana rutsata da idanu. Maida dubanta tayi kan fuskar laila,duk da alamu sun nuna tasan wani abu a kanta......amma ba zatayi saurin bada kai bori yahau ba haka da wuri gudun raini.



"Ba ta wannan nake ba.....kawai ina duba cewa mahaifinki babban mutum ne da yakai kowacce uwa taso hada jini dashi.....ko don saboda shi zan shige miki gaba har ki samu fu'ad.......amma samun muhammad ba abu bane me sauqi......da gareshi akwai wasu tsauraran matakai,kamar yadda nima daga wajena akwai wani mixani da nakeso duk matar da zai aura lallai saita cikemin su cif da cif......yanzu haka rashin cike wancan mizanin daga matarsa ta yanzu ya sanya take fuskantar barazanar gutsirewar aurenta daga yanxu zuwa kowanne lokaci"



"Daga yanzu zuwa kowanne lokaci?,ashe ma baki da guarantee......ashe baki da tabbas?" Laila ta fada da narkakkun idanunta dake nuna yadda suke da kyakkyawar alaqa da kayan maye





"Ai kawai kiban wannan kwangilar.......nan da jibi ko gata.....kwanaki uku idan sunyi yawa zata zama tarihi a rayuwarsa......shiga cikin mutane xai gagareta......bama ita kadsi ba,haka dukka wani dake da nasaba ko alaqa da ita" Tayi maganar da cikakken qwarin gwiwar daya sanya maamah tsayawa ta xubawa laila ido.



Daga jin alwashin dake fita daga bakin laila kadai ya isa ya gaya maka ita dinma wata akwai wani magana ta daban a kanta......itadin ma a shirye take



"Dole kema nayi takatsantsan dake.....aminta dake haka lokaci guda babban kuskure ne......amma dole na fara miki da karin maganar nan da hausawa ke fadin DUK WANDA YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGAKA TASHI.



Murmushi ta sake mata tana dubanta,ta sake yalwata fara'ar dake saman fuskarta tana kallonta.



"Wannan ba wani abu bane da zai zama matsala......na baki wuqa da nama.....idan akwai wani information da kike buqata dukka a shirye nake na baki shi". Kai laila ta jinjina tana sakin murmushi



" Zan iya gaya miki har fiye da abinda kika sani......ina da labarin abinda na tabbatar ke baki sanshi ba". Ta qarashe maganar tana bude handbag dinta qirar kamfanin Hermes ta zaro cheque.



Rubutu tayi samansa hankali kwance tayi kuma sign dinta,sannan ta miqawa maamah. Kudi ne a rubuce kamar yadda ta furta zata bayar da farko,maamah din bata gama wannan tunanin ba muryarta ta sake fargar da ita



"Wannan din somin tabi ne.....muddin kikayi nasarar zama surukata,zaki mallaki wata power ta fada a ji a manyan gurare da dama ta hannun mahaifina".



Komai ganinsa maaamah ta dinga yi kaman cikin mafarki,duk da ta tattara dukka mamakinta ta hadiye don ba buqatar laila ta karanci komai.



"Zamu iya ganawa dashi a yau?" Laila ta tambaya maamah tana jin kwadayin ganinsa a daren yau.



"Baki da matsala da wannan"



"Zamu wuce masauki yanzu haka don mu huta sosai,bayan magrib sai na dawo,hakan yayi?"



"Yayi" Maamah ta fada tana daga zaune har yanzu,don mamakin da taketa boyewa yaqi barin zuciyarta. A gabanta Laila ta miqe tana fita daga parlor din,maamah kuma ta rakata da idanu.



Tana fita daman jira takeyi,ta miqa hannu ta jawo cheque din tana dubawa



"Da gaske adadin ta rubuta,akwai genuine din signature nata da komai?" Sake jujjuyashi tayi a hannunta,sai kuma wani murmushi ya qwace mata.



"Lallai ni mariye me sa'a ce,ko rashin samun fu'ad a hannu akan lokaci na yarda lokaci kawai ne baiyi ba" Ta gayawa kanta da kanta tana gyara zamanta sosai tana jin kamar kanta zai fashe saboda wata izza da take saukar mata har tsakiyar ruhinta. Ta zubawa guri daya idanu murmushi na fita daga fuskarta lokaci bayan lokaci. Yau da wacce irin sa'a ta tashi?,wacce addu'a tayi yau?,babu....shine amsar data bawa kanta da kanta,don ko basmala cikakkiya bata jin tayi tun daga safe kawo yanzu.



A dan fusace ta juyo jin an murda qofar ana shigowa,saboda ita din bata sakarwa kowa da kowa shigo mata guri kai tsaye ba....ko waye kai saika nema izini ta kuma baka.



Idanu suka zubawa juna ita da hajja,saita janye cheque dinta tana lanqwasheshi ta daga pillow din kujerar gefanta ta saka a qasansa. Idanun hajja yana kai,abun kuma ya sake haifar mata da wani matsanancin bacin rai. Iya wannan abun da mariya takeyi kawai ya isa gaya mata komai daya faru ya faru ne bisa son ranta da kuma zabinta. Tunda suke da mariyan ba rufa rufa irin wannan tsakaninsu......tayi baqi ta kasa ganawa dasu a gabanta?,taga takarda duk da batasan ta mece ba amma mariyan ta jata ta boye?.



"Kinga surukarki ko?,diyar ambassador khaleed mustapha" . Maamah ta sake maimaita abinda tasan already hajjan ta jishi.



"Musaddiq ne kenan shima????". Kai da maamah kr girgizawa ya hana hajja qarasawa.



" Fu'ad dai,d'ana fu'ad ". Da wani mahaukacin mamaki hajja ke bin maamah dake doka murmushi da kallo



"Kinga Kalar surukan da ake fatan samu......wadanda za'a ciccibi juna....ba wadanda suke hangen turmusheka kai da mafarkinka ba.....maciya amana masu fatan kayi gyangadi su kafta maka sara.......zan shiga ciki in huta,ina da baqi anjima......idan kin gama ki rufe gurin.....karki damu kanki da lamarin laila......dama haka rayuwa take.....ka riqe dan wasu kaima a riqe naka,duniyar juyawa take haka da sauri........su madeena sun isheki zama.....ni kuma laila kadai ta isheni" Tana qarasa maganarta ta fara takawa zata fice



54





_Daga nana aisha RA tace,manzan Allah S A W yace: "anayin wanka akan abubuwa guda biyar,janaba....da wankan juma'a...da idan anyi qaho,da wankan mamaci(mutum ya yiwa gawa wanka)_









"Mariya!" Hajja da zuwa lokacin ta kasa riqe kanta ta kirata a hautsine



"Koda wasa......koda tsautsayi kada kiyi tunanin cutar da laila......karki manta dukka sirrikanki a nan suke" Tayi maganar tana nuna mata tafin hannunta.



Murmushi ta kuma sakar mata sannan ta juyo sosai tana amsata.



"Wadannan sirrikan da kike da ganin sun isa abun tunqaho.....nabar miki su halak malak kiyi yadda kikeso dasu.....laila kuwa a yanzu mallakina ce,baki da hurumi a kanta,idan kuma kina ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login