Showing 18001 words to 21000 words out of 147628 words

Chapter 7 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

Tsaki hajja taja ta jawo wayarta tana mita ita daya



"Yarinyar nan inajin sai taje gidansu tayi kwana biyu sannan zata shiga hankalinta". Dab da kiran data mata zai shiga sai gata ta shigo. Niqi niqi dauke da kaya wanki a wanke a goge a hannunta. Mansura daya daga cikin surukan hajja da suke rayuwa gida daya,suke kuma karban duk wani mulki isa da izza tata hannu bibbiyu don ba yadda suka iya,an dauresu da duk wani zaren sihiri da zai bata damar mallakarsu kamar yadda ta mallaki mazajensu.



Ko sallamarta bata amsa ba sai harara data jefeta dashi



"Uban me kika tsaya yi?,na baki wanki tun bayan asuba da kadan amma sai yanzu zaki gama don bakisan muhimmancin kayan ba?" Bata amsa mata ba saboda nauyin kayan har sai data zubesu.



"Kiyi haquri hajja,sai dana sallami yara suka wuce makaranta,abbansu ya fita kasuwa sannan....."



"Sannu dadi 'ya'ya dadi miji,bakisan aikina gaba yake da nasu aikin ba su duka?,kada ki sakemin irin wannan?"



"Kiyi haquri" Ta fada kanta a qasa,saita janye kallonta daga kanta tana sake jan tsaki



"Laila tashi ki kwashe kayan nan ki zuban a wardrobe". Sai sannan ta cire kanta ta kalli kayan



"Kai.....gaskiya hajja sunyimin nauyi bazan iya ba.....saidai a barsu a nan,zuwa anjima idan na tashi na kwashesu daya bayan daya". Tsaki hajja din ta sake ja ta maida dubanta ga mansura din



"Kwashesu kikai min wardrobe,kuma bance ki zauna ba bare ayimin bincike a daki". Itadai batace komai ba ta tsugunna ta kwashe ta wuce dasu.



"Zaki ajiye wayar nan muyi magana ko sai na fasata?" Hajja tayi maganar da daga murya,abinda ya sanya laila kashe wayar ta ajiye agefe,sannan ta juyo wajen hajja



"Gani" Sai data dire cup din hannunta sannan tace



"Kaman yadda nasha gaya miki ina da plan ina da tanadi a kanki.....tanadina ba kowa bane face muhammad fu'ad jadda.....mamallakin jadda diamond chore resources.....dan qawata mariyah"



"Ahhhhhh" Laila ta fada tana fidda idanu cikin tsananin mamaki da kuma gigita. Wani abune da bata taba kawoshi cikin kanta ba,hasalima batasan akwai qawance har haka tsakanin momynta da mahaifiyarsa ba



"Wasa kikemin hajja?" Ta fada tana kallonta sosai gudun ganin samu da rashi



"Na taba wasa irin wannan dake?" Maimakon ta amsa mata saita daka wani irin tsalle tayi kanta ra ruqunqumeta.



"Wayyo Allah mamana......i love you so much mamana......you fulfill my dream"



"Kinga shashasha zata karyani......da Allah zauna muyi magana dake don gidansu zaki koma da zama na wani dan lokaci" Ido ta sake watsowa waje,tana jin komai kaman cikin shirin film ko labarun hikaya



"Serious?"



"Ubanki" Ta fada tana watsa mata zagi da yatsu biyar,saita saki dariya ta koma tana zama din kamar yadda hajja ta umarta. Baki ta daga zata watsawa mansura kira sai gata ta fito



"Yauwa saiki wuce ki tafi,ki rufen qofa.....ki gayawa madeena nan da minti talatin ta dafamin madara ta kawomin,wallahi kuma aka wuce haka sai ranta yayi mummunar baci". Kai a qasa ta amsa mata ta juya tana ficewa. Sai data fita din sannan ta maido hankalinta ga laila



"Kina jina ko?"





5�N�5�V�5�W�5�g�5�Z�5�Z�5�c�



Sake duban lokaci tayi,sha biyu saura na rana. Tunda ta farka tayi wanka da sallolinta bataji motsin kowa ba,don hatta securityn dake aikin kula da gidan bakajin motsin kowa,sanin da sukayi cewa hayaniya da motsi me qarfi na daya daga cikin abinda boss din nasu bayaso. Uwa uba ma su dake first gate bata yadda na ciki kamarta zai iya jiyosu. Bawai yunwa takeji ba,amma a jikinta takejin ya kamata ta sawa cikinta koda ruwan dumi ne. Kaman ba zata fito din ba amma ta miqe,ta lalubi mayafi ta lullube jikinta sannan ta sanya plate shoe dinta na jiya ta fara nufar qofa ba tare da tasan takan gidan ba ko kuma daga inda zata fara ba.



Rufaffen hallway din ta soma ratsawa,wanda aka qawatashi da wani irin wall led light na musamman,da wasu irin qananu masu haske da suka sake fidda ainihin kyan wajen. Tattausan runner carpet ne shimfide duka tsahon wajen tsakanin kowanne qofar daki zuwa na dan uwansa an qawatashi da wasu irin nature frames masu daukan hankali. Daga bangon dake facing naka kuma,babban console mirror ne da zai baka daman ganin kusan dukka jikinka har kusan cinyoyi. Akwai plants masu kyau data gani cikin flower vase masu wani irin daukan hankali,bata sani ba masu kyau ne ko ma decoration. Guri ne daya cika da hasken da koda allurarka idan ta fadi zaka iya tsugunawa ka dauka,ko ina fes da wani irin matsanancin tsaftar da babu qura ballantana ka saka ran samun wani abu waishi datti saman lafiyayyen marbles din dake lullube kuma shimfide a qasan wajen. Duk zuqar iska guda daya idan tayi da qamshi take kai mata har hanjinta,qamshin da sam bata da tabbacin daga ina yake fesowa ya karade kowacce iska dake kai kawo a wajen duk kuwa da a rufe hallway din yake.



Idanunta kafe akan staircase din dake gabanta. Batasan ina bane bata kuma fatan sani,nan din inda aka ajiyeta ma kawai tana jin ya isheta harta kammala abinda zatayi tabar cikin rayuwarsu,fatanta daya shine idan ta isa staircase din ta samu wata qofar tsakanin hagu da dama cikin dan lugu biyu da take ganin alamunsa.



Ajiyar zuciya ta sauke sanda take dab da bakin stair case din,akwai wasu qofofi hagu da dama,saidai ta daman tafi mata kama da qofar da zata sadaka da wani gurin.



Solid wood door ne me qofar biyu data dace da kalan gidan gaba daya dake bata kalan gold and off white,dayan pivot door ne wanda tafi kyautata zaton wani gurin na daban zai sadaka dashi,don haka ta nufi hannun damanta,ta sanya hannu ta murda handle din ta bude qofan a hankali kamar me tsoron wani abu.



Wani irin tsararren parlor ne da kana kallonsa zakasan ilimi hankali da dukiya duka sunyi amfani. Well designed parlor me wani irin sassanyan yanayi me jan hankali. Babban swarovski crystal chandelier din dake tsakiyar falon ce kawai a kunne,amma duka fitilun dake zagaye da falon a kashe suke,saidai duk da haka hakan bai hana fitar ainihin kyau da tsaruwar falon da aka qawata da kujerun qasar Italy.



Kutsa kai taci gaba dayi cikin falon kamar me tsoron sautin takunta,tako ta ina tsarin gidan yana dada kwance mata kai. Wani irin tsari dake da matuqar sha'awa da daukan hankali. Idanunta suka fada daya sashen falon.



Glass door ne da zai baka damar hangen wani guri da aka qawata da wani irin shuke shuke masu launika daban daban masu daukan hankali. Wajen yafi mata kama da qaramin lambun da zai taya mazaunin falon debe kewa. Ta sake wurga idonta.....ba wata qofar a nan data mata kama da qofar kitchen,sai wata qofar shigen qofar farko data bude.



Ita ta nufa kai tsaye,tana jin yadda qafafunta suke nutsewa cikin lallausa Italian Versace carpet daya dace ta kowacce fuska da kalar tsarin falon.



Steps hudu masu fadi ta soma cin karo dasu,wanda ta nan zata taka ta sauka cikin wani falon na daban da yasha banbam dana farko ta kowacce fuska. Furniture din ciki girma da tsari,saidai kusan komai nacan akwaishi anan,illa na wannan falon yafi na wancan yawa da girma. Rukunin kujeru biyu ya dauka saboda girmansa.



Sabanin wancan falon,wannan tafkekiyar tv plasma din da tafi qarfin Wall wooden TV stand din aka girketa samanta ce a kunne. Saudi qur'an ce kunne,saidai kuma sautin karatun sam baya fita. Lullube kowanne bango yake da tsadaddun curtain masu wani irin kwarjini da haiba,kowanne maqale jikin Drapery hardware,abinda zai baka daman ganin qifofin da sukayi saura ta wajen banda yalwataccen dining area da aka yiwa ado na musamman da roman shade curtain da zai baka daman kallon wani sashe na kitchen da glass door ya rabasu.



Qaramin tsaki taja tana janye kallonta daga kallon kowanne tsari na parlor din. Finally bayan ta gama duk bulayin ta samo kitchen din da qyar,don haka ta taka a nutse tana hawa steps din da zai sadata da dining din zuwa kitchen din.



Sak tayi canma tana kallon kitchen din,don wata aljannar duniyar ce da bata san ta ina zata fara ba. Komai a kitchen din baqonta ne,ba wani abu da zatace ta masa farin sani idan ka debe kayan amfani na yau da kullum da kowanne kitchen ake samu. Ya qawatu sosai da custom cabinets da aka sarrafa da wani irin gogaggen katako datayi imani badai daga qasar nan ba,yabi sauran kayan cikin gidan yazo ne daga wata qasar daban.



Tunaninta ya dawo da baya,shin yaushe duka suka samu wannan kudin?,a ina?,da har aka samu daman zuba mata wannan uwar dukiyar cikin gidan?. Anya kuwa bayan mutunci da kawun ya saida mata ba hada harda 'yancin jere ga kowacce diya budurwa ba?.



Iya wannan tunanin ya sake sanyawa taji komai na gidan ya fice mata a rai,baya kuma burgeta ballantana taba haskenshi. Taja qafafunta da sukayi mata nauyi tana nufan gas glass stove din tana fatan ta kunnashi daidai kama kowanne. Sai data bata lokaci shi kansa wajen gane kansa sannan ta saki ajiyar zuciya. Taja da baya tana baza ido don hango inda zata samu koda ganyan shayi ne,don dama cimar bata wuce haka. Daga can ta hango wata qofar,ta taka zuwa wajen tana addu'ar Allah yasa ta samu abinda takeso,don duka ta gwada duba cabinets din bata samu komai ba aciki,da alama shi kam banda kayan kitchen din da aka jera ba'a taba komai ba.



Cikin sa'a ta tadda yalwataccen guri da yafi mata kama da store saidai na musamnan. Don ba abinda yake zube a qasa hatta kuwa da buhunhuna da kwalaye,kusan duka wajen shima an masa kanta sosai kamar kanti ko shago,an saka komai a bangarensa daidai da kwalayen maggi kuwa. Daga gefe babbar freezer ce wadda batabi ta kanta ba,don ko sha'awar budewa bataji ba,to ta bude taga me?,ba wannan ne a gabanta ba.



Bangaran spices na tea ta nufa,ta bude ta debi kowanne daidai yadda zai isheta,daga wannan ba abinda ta qara ta dawo ainihin kitchen din,ta bare tukunya daya,ta nufi sink ta kunna famfo ta debi ruwa,sannan ta dawo ta kunna gas stove din ta dora bayan ta zuba komai.



Minti goma tsaf ya tafasa,ta soma duba mazubin da zata juye ta wuce dashi,don sam batason zamanta kitchen din.



Tea set ne kala kala,ta rasa ma wanda zata dauka. Taja qaramin tsaki still,komai na gidan ya fiya fi'ili da feleqe,tunda ta tashi komai ma sai tasha wahala take laluboshi,iya yau kawai.....neman kitchen da dafa tea ya zame mata alaqaqai?,ina ga sauran rayuwarta cikin gidan.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE_*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_zafafabiyar_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 15





16





Qarshe dai wani Wedgwood tea set din qasar chaina ta dauka ruwan sararin samaniya,ta juye duka ta zuba sugar a mazubin sugar din sannan ta dauka tray na set din cak tana wucewa ciki dashi.



A yanzun tafi fahimtar hanyar da take komawa ba kamar dazu ba. Tabbas duk yadda takai gason ta kushe komai ta kasa,duk.yadda takeso komai kada ya burgeta a gidan hakan ya gagara,dole ta sallama saidai still zuciyarta na gaya mata



"Allah yasa da kudin halal akayi komai"

(=�� yarinya tunda dai kin fara mora ai magana ta qare).



Bata tashi tunawa da personal wayan da ta bata ba sai data kusa kammala shan tea din. Qarar wayar ya Haifa mata da wata irin faduwar gaba. Wayace data jaddada mata cewa ta bata ita ne kadai saboda personal use dinta,bata bata ita don ta kira kowa ba sai ita kadai. Hannu ta tura qasan inda wayar ta fada tun a jiya da zazzabi ya kamata,ta duba fuskar wayar sunanta ya bayyana baro baro



5�H�5�V�5�g�5�^�5�n�5�V� 5�h�5�V�5�a�5�^�5�]�5�j� 5�V�5�Y�5�V�5�b� shine sunan data zabi ta sanya mata saman number. A zahiri tana qoqarin hana kanta daga wayar ne,don bata da buqatar jin muryarta kwata kwata.....amma a badini sai taji kamar ana tilastata daga wayar. Can qasan zuciyarta ta dinga jin bata da wani sauran sukuni saina daga wayar,a sanyaye ta latsa ta kuma kara wayartata a kunneta



"Amarya.....ina fatan kin tashi lafiya?" Sai da taja wani nannauyan numfashi tana qoqarin daidaita kanta kafin ta furzar da iskar a hankali a kuma sirrance



"Ina kwana?" Ta fada da sassanyan murya. Murmushi maamah ta saki,da gaske aikinta na jiya ya ratsata yadda takeso,ta tabbatar banda haka bataga alamun zata samu gaisuwa wajen yarinyar ba koda na minti daya ne



"Lafiya lau....ya baqunta?" Batasan wacce kalar amsa zata bata ba,don haka ta zabi tayi shuru. Itama shirunta ba shine damuwarta ba,isar saqonta zuwa ga kunnuwanta shine damuwarta don haka ta dora.



"Zuwa anjima kadan zan aike miki da me aiki da kuma 'yar 'yar uwata......zata zauna daku nadan wani lokaci ne.....me aiki zatayi aiki ne kadai da umarninki,da tayaki abinda kike da buqata......amma kula da muhammad da dukkan abinda zaici ban dorawa kowa ba yana wuyanki......kada ki damu da wanzuwarsu.....dukansu sunsan da tafiyar.....saboda haka ba buqatar boye boye wajen gudanar da aikinki,kiyi komai kawai gaba gadi. Abu na gaba muhammad bame sauqi bane.....kada ki sanya rai koki damu da rashin cin abincinki a zangon farko......kawai kici gaba da dafawar.....kici gaba da shiga lamarinsa.....kici gaba kuma da dukka qoqarin ki na ganin yaci yasha din.....yana da tsananin miskilanci......yana kuma da tsantsamin da sai kin zama me tsananin tsafta kafin ki samu abinda kikeso.....ina fata kin fahimta?". Can qasan ranta suya sosai zuciyarta takeyi. Tanajin maganganu na taso mata da ya kamata ta maidawa maamah.....amma sai takejin kamar biyayya wa umarninta ya zame mata tilas ne kawai,ba buqatar musu ballanta jayayya



"Kin jini?" Ta sake tambaya don tabbatar da taji komai din



"Eh naji"



"Yauwa.....saikin sake jina ko?,idan akwai tambaya ko wani abu daya shige miki duhu......qofa a bude take". Kasa cewa komai tayi,sai kawai ta sauke wayar daga kunnenta tana ajeta gefe tare da binta da kallo.



Shawarwari kala kala zuciyarta ke bata game da wayar,wata zuciyar na cewa ta zare layin ta karyashi ta yar,wata nace mata ta kashe wayar ta wurgar a dustbin,wata kuma na gaya mata ta sakata a silent tayita kira ba'a dagaba,amma daga qarshe ji tayi ko guda daya ba zata iyayi ba. Bawai don bata buqatar hakan ta faru ba....aah haka kawai taji aikata hakan bazaiyi ba,saita nutsa yatsunta cikin gashinta kawai tanajin kanta kamar ana yamutsashi......umarninta kadai take da muradin cikawa.



Kusan saman idanunsa hasken alfijir ya fara keta duhun sararin samaniya yana kore duhun daya mamayeta,duniya ta fara haskaka da siririn hasken nan dake juyewa izuwa hasken rana dake wadatar duniya da halittun cikinta.



Wayarsa ya kalla,a gida a lokuta irin wadannan ya kammala duka wasu addu'insa.....yana shiri ne ya fita gym da yake bawa awa daya.....so amma a yau din yadda yakejin jikinsa da sauran gajiya bazai iya komai ba,sai ya miqa hannunsa yana jawo wayarsa da yaga tana haske sanda qarfe bakwai da rabi na safe ya cika.



Joshua ne.....ma'aikacinsa dake kula da bangaren marketing da price na gold da Diamond a kamfaninnikansa. Yana cikin manyan ma'aikatan da baya iya tsallakema kiransu. Cike da mamakin kiran sassafe irin wannan ya sanya wayar a kunnensa



"Hello......" Fu'ad ya fadi da muryarsa maras hayaniya musamman daya kasance yanzun safiya ce



"Hello sir........good morning sir......ina expecting zuwa yanzu baka duba business side news paper da magazines ba ko?"



"Morning Joshua.......what's going on?"



"Sir......sun karya darajar gold da Diamond duka tsakanin tsakiyar daren jiya zuwa yau da safe".



"La'ilaha illlallah" Labbansa suka motsa ya furta a nutse idanunsa suna lumshewa. Daga yadda Joshua ke masa magana adan rude ya tabbatar abun ba qarami bane.



"Cool down Joshua......i will be online yanzu in sha Allah"



"Okay sir......but sir a irin wannan yanayin da sabon kamfani ke shirin fara aiki akwai hadari sosai a ciki.....akwai barazanar tsayawar abubuwa da yawa mo durqushewarsu......sir inaji a jikina an shirya wannan abunne kawai".



"Calm down Joshua,ba abinda zai faru in sha Allah.....let work together okay?".



"Okay sir....." Ya amsa da damuwa sosai a cikin muryarsa.



Kiran ya yanke yana sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da maida hankalinsa kan fuskar wayar tasa. Dole ya miqe a nutse ya fara bincika inda system dinsa suke da sauran kayan aikinsa.



Cup rabin qaramin cup tasha taji tea din ya isheta. A nutse ta maidashi ta ajiye tana bin cup din da kallo. Ya mata kyau sosai,amma kuma ba wannan tunanin bane a qasan ranta,ta janye idanunta tana lumshe. Ta ina rayuwa zata fara?,yaya rayuwar zata kasance?. Idanunta ta bude,sai suka sauka akan wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login