Showing 147001 words to 147628 words out of 147628 words

Chapter 50 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

fada yana qoqarin daidaita numfashinsa,don bayason tace komai,hannunsa ya sanya a gadon bayanta ya matseta cikin jikinsa gami da rabata da qasa kaman yadda zaka rungumi yaro a haka suka fita a toilet din.



Batasan da gangan yayi ba?,oho.....amma gaba daya suka zube a gadon yana fadawa samanta. Ya aje mata nauyinsa sosai har sai da numfashinta ya fara nauyi



"Oh....sorry" Ya furta yana dagata gami da bar mata towel din a tare da ita. Rintse ido tayi tana qin dubansa,bai damu ba ya jawo boxer dinsa dake yashe a gefe tun dazun ya saka,ya sanya hannu ya sauketa zuwa sofa bed ya fara tattare comforter da bedsheets din harma da pillow case din,don bayason anni ta sake dawowa idanunta su gani. Toilet ya koma ya shiga sheqa musu ruwa,jikinsa yayi wani irin sanyi ganin yadda ruwan ke wanko jinin. Da gaske ya shigeta ne da tabbaci da yaqinin ta riga ta saba......ya kuma samu qofar a kulle gam....dole taji ciwo koma wanne iri akace masa taji. A yadda yakejin cikakkiyar lafiya a jikinsa ya sani,koda bazawara ce yaje mata da irin yanayin jiya lallai saita yabawa aya zaqinta ballantana ita din da take sabon hannu.



Luggage dinta ya bude,ya fidda mata kaya bayan ya saka wata sassauqar riga a jikinsa over sized shirt da wandonta. Fara ce qal data dace da black trouser dinsa. Sama sama yake jinsa shima,saidai abinda ke gabansa ya shafe komai.



Da rinannun idanunta ta dubeshi sanda ya aje mata kayan,tana so ne ya matsa ya bata waje ta shirya amma bataga alamun xai matsa din ba,hasalima tsaye yake a kanta ya zube duka hannayensa a aljihun wandonsa kaman zai lasheta,ya zube mata nauyayan idanunsan nan yana jin kamar ya buda qirjinsa ya fiddo mata mahaukaciyar soyayyar data sakar masa.



"Ka fita zan shirya" Ta fada a taqaice ba tare data kalleshi ba,hannayensa ya fidda daga aljihunsa ya juya a hankali ya fita.



Duk yadda taso ta miqe sosai don ta shirya amma hakan ya gagareta,ba zata iya tsaiwa normal kaman kowa ba,abinda ya sanya hawaye yaci gaba da zuba a idanunta,saita dinga jin data sani ta barshi ya taimaka mata,amma kuma batason komai da zai dinga hadata dashi. Da qyar ta lallaba ta saka underwears dinta ta maida rigar,sannan ta lallaba hannun damanta ta kwanta tana ci gaba da fitar da ruwan hawaye.



A nutse anni ta murda qofar tana shigowa da sallama,wata kunya ta taso ta lullubeta,saita rufe idanunta tamkar me bacci,tana fata annin taji kaman baccin takeyi ta juya ta barta.



"Sannu....." Anni ta fada a hankali da alama ta fahimci ba baccin takeyi ba.



"Zaki iya tashi?,doctor zata shigo ta dubaki". Kai kawai ta gyadawa anni ba tare data iya furta komai ba,ta motsa a hankali tana tunanin yadda zata tashi din. Matsawa annin tayi ta kamata a nutse tana cewa



"Yi a hankali" Tausayinta yana kama annin. Yanayin yanayine bame dadi ba,iya yau kawai ta fahimci yaron nata yadda jikinsa ke agine hakama komai nasa



"Allah ya baki ikon jurewa" Annin ta fada cikin ranta. Sai a yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake kaucewa abubuwa da dama,azumin litinin da alhamis akai akai,harma wani lokaci yakanyi azumin annabi dawud,yau yayi gobe ya huta. Wani lokaci takance



"Ka dinga hutawa mana me babban suna......ga azumi ga aiki,shi kansa aikin busy din da kake sakawa kanka pressure din tana yawa". Sau tari murmushi kawai yakeyi ko ya kafa mata hujja da







*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*

08187255862



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login