Showing 96001 words to 99000 words out of 147628 words

Chapter 33 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

gajeran hanny ta lafe a jikinta ta kamar yadda Palazzo din ya fidda shape din hips din ta zuwa qugunta. Bandana ce kawai saman kanta,hannunta riqe da wayarta.



Kallo daya tak ya mata ya dauke kansa kai kace bai taba sanin wata halitta a duniya me ire iren kama da ita ba. Qasan maqoshinsa kuwa kawai kaiwa da kawowa maqogoronsa yakeyi,adams apple dinsa yana motsi daga sama zuwa qasa,ya taka a nutse kuma kai tsaye ya wuce gaban maamah din a ladabce.



Tunda yayi sallamar ya shigo taji gaba daya an tsinke duk wata jijiya daka iya baiwa dan adam kuzari daga jikinta. Tunda take haukan son fuad bata taba tunanin haduwarsa da kyansa ya zarta yadda ta gagganshi bama sai yanzu data ganshi cikin shigar mutanen Morocco,wanda nan Nigeria zaka ga suna kama da tufafin da sarakuna ke sanyawa musamman idan suna ganawa da baqi cikin gida. Numfashinta cak yaso tsayawa,muhammad fuad ya wuce yadda take hangensa a nesa,a take taji tabbas zata iya sadaukar da komai data mallaka don ta samu fuad din a matsayin mijin aure

(Anya....fuad din fa me tsada ne......amma muje zuwa,tunda kin kama maamah wataqila kina da rabo).



Kusan duka gaisuwar da sukayi shida maamah da gajeriyar gabatarwar da maamah tayi masa bata ji ba



"Baquwar taka ce muhammadu.......ina me umartarka ka saurareta ka kuma fahimceta.....duk wanda yayo tattaki qafa da qafa ya taho gareka saboda yana sonka ba qaramin masoyi bane,idan Allah yaso kuma matarka ce" Ta fadi maganan qarshe tana yunqurawa ta miqe.



Daga kai yayi yana duban maamah sanda take jifan fareeda da murmushi,da salo kuma na bada goyon baya take cewa



"Gashinan fareeda,bari na shiga na fito kafin ku gama"



_idan Allah yaso kuma matarka ce_ yaji amsa kuwwar maganarta ta qarshe tana nanata kanta cikin kunnuwansa. Maganar sai taso ta masa kama da maganar data masa daidai sanda ta tilastashi auren waccar yarinyar.......me yake shirin faruwa?.ya tambayi kansa.



"It will never happened" Ya fada yana qaryata komai da zuciyarsa ke qiyasta masa zai iya faruwa.



"Hi......ka ganni har gida?,yanzu ka yarda garin masoyi baya nisa ko?" Ta fada tana sakar masa murmushi,murmushin nata dake daidai da diban garwashin wuta ta watsa masa.



Wannan bai dameta ba,yanayin fuskarsa duka bata sakashi a mizanin damuwa ba.......zai gata ta zame tana saukowa qasa. Ta qaraso dab dashi tayi Zaman raquma tana dubansa



"Please Muhammed kada kayi rejecting dina.....na maka alqawarin zame maka duk kalar matar da kakeso kake buri" Ta furta da tsananin narkewa.



"Stop it please......ke me yasa baki nemawa kanki martaba mutunci da kima?". Ya fada bayan ya daga mata hannu ya dakatar da ita daga maganan farko launin idanunsa sun fara sauyawa saboda bacin rai.



A rikice ta girgiza kai ganin yana juye mata zuw wannan fuad din me wahalar samu.....wannan fu'ad din me tsananin tsauri



"Mutunci martaba da kima duka susha zamansu muddin zan samu muhammad fuad". Shuru ya ratsa qarshen maganarta,ya xuba mata ido yana sansano alamu alamun hauka tattare da ita,sai ya matsar da fuskarsa kusa da tata kadan,da wani sauti can qasa wanda tsanantar bacin rai da kuma sarawar da kansa yayi ya dawo da ciwonsa sabo fil ya tilas masa maganar a haka yace



"Gashi shi kuma muhammad fu'ad din saida wadannan abubuwan ake samunsa......." Daga haka ya miqe tsam da zafin nama,sai gata ta miqe tare dashi cikin tsoro da fargabar kada yaqi tsayawa ya saurareta duk da kuwa ta dangana da mahaifiyarsa.



"Umarni nake baki......ki tattara kayanki kibar gidan nan,kada na dawo jibi na sameki,don gobe ma tayimin kadan,bazan iya shaqar iska a wajen da kika dade a cikinsa ba". Yana kaiwa qarshe ya juya da zafin nama me gauraye da fushi ya soma fita.



Ta dauka zata jure saita kasa,ta bishi a baya da gudu gudu tana kiran sunanss,saidai ko ta kanta baibi ba,ya bude motarsa ya shige ya kunna ya tasheta da wani irin qarfi ya fusgeta yana fita a gidan,don ko sanda ta qaraso sawayen motar kawai ta samu,saita zube a wajen tana qwala kiran sunansa,abinda kunnuwan maamah suka jiye mata kenan,ta fara saukowa da sassarfa daga sama.



Baisan yadda yakai kanshi gida ba saboda tashin hankali da tsananin ciwon kan daya saukar masa,shidai yaji daya daga cikin security nasa na cewa yabar motar daga nan zai qarasa shigo da ita ya gyara parking din.



"Sai yaushe maamah zata canza?,sai yaushe zata zama cikakkiyar uwa?,sai yaushe zata zabi girma da mutunci sama da kudi?,sai yaushe?,sai yaushe?".



Kusan wannan shine abinda ya sanyashi kwana ya kuma tashi da ciwon kan daya hanashi fita,ya kuma kashe dukka wayoyinsa don baya qaunar ya nemi wani ko shi a nemeshi.









*_WASHEGARI__*



*_BAQIN DARE_*



*_MUHAMMAD JADDA RESIDENT_*





*10:45 NA DARE*



Tunda ta fara kallon film din hankalinta bai kwanta ba sai yau da taga qarshensa. Duk da cewa ya bata mata lokaci sosai,don sai a yanzun sha daya saura na dare ta kammala......amma kuma ya haifar mata da wani irin nishadi a zuciyarta,nishadin da duk idan ta tuna yadda rayuwar stars din ta kasance a ciki sai taji ta saki dan murmushi kadan. Sam ita din ba ma'abociyar kallo bace......wannan shine film na farko data fara kara full kuma wai korean series.



Idanunta ta lumshe tana shaqar iskar dake kadawa sosai take kuma yiwa kanta hanya ta windows din dakin da yawanci yakan barshi a bude saboda samun fresh air da tafi iskar ac artificial air dadi a wajenta.



Gabanta yadan buga kadan,tayi kuma hanzarin bude idanunta sanda taji kaman motsin taba window din. Ta tsaya cak daga qoqarin fidda rigar jikinta da takeyi,tsahon mintuna biyar bata sake jin komai ba,saita matsa gaban windows din dukansu,ta bisu daya bayan daya ta zugesu,ta kuma sanya musu lock.



"Sabreena kin zama matsoraciya" Ta tsokani kanta da kanta,ta kuma sakarwa kanta da kanta din murmushi. Ita kanta batasan yaushe ta koma hakan ba,saidai girman gidan koda rana ce ta take tsoro yake bata,duk da tassn cike yake da security musamman idan ma'u ta gama kai kawonta ita da ameh kowa ya wuce gefansa.



Towel ta daura babba,har zata wuce toilet din taji kaman yau garin da iska,don haka ta miqa hannu ta dauki hijab din da tayi salla dashi ta zura a jikinta ta wuce bandakin.



Tana wankan amma kadan kadan takejin gabanta yana faduwa wanda ita kanta batasan dalili ba. Yau din sai ta samu kanta da rage tsahon lokacin da takan dauka a bandakin,cikin qasa da mintuna goma ta kammala,tayi brush ta busar da kanta,sannan ta daura towel din ta maida hijabinta ta fara takowa tana fitowa.



Sanda ta dora hannunta akan handle din gabanta ya sake yankewa ya fadi.



"Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel" Ta furta a hankali kaman yadda yanzu yadan fara zama a jikinta,don cikin jadawalin karatunsu da rumaisa akwai azkar sosai da addu'o'i masu yawan gaske.



Jiki a sanyaye ta murda handle din ta jawo qofar ta bude sannan ta fito,kai tsaye ta soma nufar madubi. Abun mamakin yadda takejin baqon qamshi cikin dakin,tadan tsaya kadan tana buda hancinta still qamshin takeji,sai kuma tunanin iskar dake ratsowa ta cikin rufaffun windows din qilan ke debo qamshin daga waje zuwa dakin,don haka hankalinta kwance ta qarasa gaban mirror din tana duba fuskarta da jiya taqi wani qurji qwaya daya ya fito mata.



Wutace tsaf ta dauke mata kafin wata mahaukaciyar faduwar gaba ta rufto mata,tun daga saman kanta har zuwa yatsun qafafunta da ganin fuskar dake tsaye a bayanta.



Dagawa qirjinta ya shiga yi daga sama zuwa qasa cikin wata irin razana da takejin kamar tana shirin dimaucewa ne......sake matsota yakeyi idanunsa cikin nata,kaman yadda fuskarsa ke shimfide da shu'umin murmushin nan data saba gani a fuskarsa a shekarun baya.



"Mmmm........." Ta dinga yunqurin fadin sunansa,amma sai taji kaman an sanya gum an manne labbanta na sama da qasa guri guda.





*_TOFA!_*



*_WAYE WANNAN?_*



*_NACE WAYE WANNAN?_*



*_MUHAMMAD FU'AD NE DA KANSA?_*



*_KO KUMA WANI MUTUMIN NE NA DABAN?_*



*_TURQASHI_*



*_Allah yasa muna cikin masu rabon ganin ranar litinin lafiya_*



*_karku yadda karki yarda aci gaba da sukuwa da zamiya cikin labarin nan ba tare dake ba_*



*DA SAURAN KALLO!!!*



Tofa nayi qarqaf=��=��

Allah ya bani ikon baku na ranar monday=�O�<���=�O�<���=�O�<���=��



56





_Daga ummu habiba uwar muminai Allah ya qara yarda a gareta tace,naji manzon Allah S A W yana cewa "duk wanda ya sallaci raka'a sha biyu daga rana zuwa dare(bayan sallar farillai guda biyar),Allah zai gina masa gida dasu a aljanna_



_muslmin ne ya rawaito_



_raka'o'in nan sha biyu sune,biyu kafin asuba,hudu kafin azahar da biyu bayan azahar,biyu bayan magariba,biyu bayan isha'i saiki qara da wuturi_



_Sannan akwai hidisi me zaman kansa abdullahi bin umar ya rawaito,manzan Allah S A W yace ALLAH KA YIWA BAYAN DAKE SALLAH RAKA'A HUDU KAFIN SALLAR LA'ASAR RAHAMA_



*_IBADA DUK IBADA CE,AMMA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJEN ALLAH DUK QANQANTARSA SHINE WANDA ZAKA DAWWAMA KANA YI,SAIKA DAUKI WANDA KASAN ZAKA IYA DOREWA_*







Tana kallonsa ta cikin madubin yana ci gaba da kusanto inda take,saidai gaba daya ta kasa motsa koda yatsanta ne ballantana tayi tunanin abu na gaba daya kamata ace ta aiwatar.



Shu'umin murmushinsa da kallon da yake dubanta dashi duka ba wanda ya fasa,yaci gaba da kusantota kowacce gaba ta jikinsa tana jin wani shauqi tare da dokanta ta sadar da kanshi gareta. Irin yadda ya fitinu da ita ba abu bane me sauqin fassarawa ba......sai kuma gashi a bagas zaice ko a banza wata hanya ta samun isa gareta ta riskeshi cikin sauqi,wanda zai iya kiran hakan da qatotuwar sa'a cikin rayuwarsa.





"Mashkur!" Ta fusgi sunan da hanzari ta kirashi a tsawace bayan ta maimaita la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen har batasan adadi ba.



Tsaiwar da yayi ita ta bata damar waiwayowa da wani irin hanzari kamar wadda aka fusga. Idanu ta zuba masa kaman yadda shima idanun ya zuba mata yake kallonta da dukka iyakacin kallonsa.



"Me ya kawoka gidan mutane?......har dakin matar aure?" Ta fadi da wata irin birkitacciyar murya data cika da razani da tsoro.



Wata irin dariya ya qyaqyace da ita,harda komawa ya fada saman gadon nata,sannan ya tashi ya miqe yana fuskantarta. Ya bude baki zaiyi magana a hankali sautin saukar ruwan saman farko ya baqunci kunnensu,shatin ruwan ya fara sauka ta glass din windown dakin sai ya saki murmushi yana dawo da dubansa kanta.



"Kin gani ko?,.....ko Allah ma yana sona......ko Allah ma yasan kin cuceni....kuma ko Allah yasan kedin azzaluma ce,wannan zubar ruwan shi zai sake toshe kunnen duk wani da kike tunanin zai ceceki ko zai kawo miki dauki,duk da kuwa wannan ginin gidan naku dama kaman anyishi ne domin ni,yana riqe sirrin kowanne motsi yadda ya kamata". Ya fada yana kallon yanayin roofing na dakin yana sakin murmushi.



"Nayi mamaki wai da kike tambayata abinda ya kawoni,bayan akwai basussuka na da yawa a kanki?".



"Mashkur ka haukacene?,kasan gidan waye ka shigo?,gidan matar aure har tsakiyar dakin aurenta..... " Fara takowa yayi yana sake nufota yana dariya



"Ina cikin gidan muhammad fu'ad jadda,the owner of jadda diamondchore resources.......sannan ke din sabreena ce,mata a wajensa.....bayanin yayi daidai?" Ya jefa mata tambayar yana dage mata dukka girarsa biyun bayan ya tsaya daga takowar da yakeyi.



"Ko kina buqatar wani qarin bayanin?......kinaso ne na gaya miki da license dina na shigo gidan nan?,da license daga hannun wata mace mafi kusanci da me gidan?". Daukan tunaninta yayi ya luluqa wajen lalubar ma'anar abinda yake fada,da license daga hannun wata mace mafi kusa da me gidan?,wace kenan?.



Kaman yasan abinda take tunani a kai yace



"No dear......kada ki wahal da kanki wajen tunanin wace..... Ki bari na gama kashe qishirwata sosai sannan mu zauna mu tattauna..... I need you.....na azabtu da yadda asara biyu ta fadamin......babu ke ba kudina......come please" Ya furta yana kawo mata cafka.



Batasan tana da tsananin zafin nama har haka ba sai data kufce masa ya kama iska. Sukabi hannunsa da kallo dukka su biyun shi da ita. Shi dariya ya saki yana jijjiga kai



"Kada ki dauka kedin me sa'a ce ko da yaushe.......idan a wancan karon kin kubcemin...... Na rantse wannan karon baki isa ki kubuta ba,koda kuwa a gaban mijinki ne a yau sai na kashe qishirwar dake raina" Ya furta yana daga rigarsa,take ta hangi hancin bindiga daga aljihun trouser dinsa. Kaman an debo bulo an jibga mata haka taji wani matsanancin tashin hankali ya keto mata,bata gama sauke abinda ya taso mata ba ta ganshi ya taso mata yayo kanta gadan gadan. Wani irin qarfi ne yazo mata,ta tattara hijabin jikinta da batakai ga cireshi ba da kyau ta haura sofa bed din dake gabanta ta wuce tsakiyar gadon



"Ka fita min a gida.... Ka fita tun ban tada security din gidan nan ba" Ta fada tana duban sashen da wayar girke take a dakin wadda zata baka daman kiran kowanne sashe na gidan. Ta shiga shock sosai sanda ta lura ya gutsire wayar gaba daya ya fasa kan,duka yaushe yayi hakan da ko alama bataji ba.



Dariya ya saki yana cewa



"Kinga abinda ya samu telephone din ko?....." Bata bari ya qarasa ba ta tattara dukkanin qarfinta ta kwarara ihu tana fadin



"Wani ya taimakeni" Abinda ta dinga maimaitawa kenan har sai da taji maqoshinta yana wani suya da radadi. Dakatawa tayi hawaye suna cika idanunta,tana duban mashkur dake qyaqyata dariya.



"Zan iya qara miki lokaci kici gaba da ihu......kiyita ihu har iya yadda kikeso".



"Fuad!. ....fuad!!!!" Ta sake qwalawa kiran sunansa. Karo na farko da ta fara ambatar sunan nasa kenan.



"Yana can yana bacci" Ya fada yana juyi kaman zai taka rawa



"Na sakashi bacci,kuma bazai tashi yanzu ba,sai na gama hutawa da matarsa" Ya sake maimaitawa cikin yanayin nishadin da kana kallonsa zakayi imani yakai masa har qasan zuciyarsa nishadin da yake ciki.



"Mashkur,........ka saurara haka,ya kamata kasan kuskure kake tafkawa ba qarami ba.......ketawa matar aure haddi mashkur?!" Ta furta a tsawace. Dariyar nishadi ya saki yana kallonta,ya kama button din rigarsa ta saman ya fara ballewa yana zareta ya yar.



"Kada kiyi kaman bakisan komai ba.......kina tunanin yaune na farko dana fara kwanciya da matan aure?,na kwanta dasu har bansan adadi ba......kawai ke dince ta daban,kin kasa fita a raina......bazan miki qarya ba,koda na dandana yadda kike banajin zan iya ci gaba da rayuwa ba tare da ke ba......shawara daya kawai zan baki,kada kiyimin gaddama.......ki bani kawai salin alin don na tabbatar kinsan komai,ba wani abu baqo a wajenki"



Sasai kalamansa sukayi mata nauyi a qirji,ta tabbatar inda za'a tsaga jikinta ba za'a taras da jini ko digo ba saboda tsananin tsoro da fargici. Ranta yakai maqurar baci sanda taga yana yunqurin haurowa gadon



"Har ka mutu mashkur ba zaka taba samun komai daga gareni ba.... Ko gawata tafi qarfinka mashkur bare gangar jikina a sanda numfashi yake busawa".



"Well.....tunda kin zabi muje ta haka dake!" Da furucin da haurowarsa saman gadon duka lokaci guda suka faru. Wani tsalle tayi da zummar barin gadon,saidai kuma ya samu nasarar take qasan hijabinta da qafarsa ganin zata kufce masa,abinda ya sanyata data dira din bata sauka a daidai ba,hannunta ya daki side bed ya bada wani irin qum.



Qara ta saki cikin tsananin azaba......azabar da bata hanata ci gaba da qoqarin qwatar kanta ba,cikin sa'a santsin bedsheets din dana hijabinta suka sanyashi ya zame zaman lallausar katifar,saita miqe itama,amma ta kuma zamewa take fuskarta ta bugi gefan bedside din still.



Bata damu da radadin daya sake ratsata ba.....sake miqewa tayi tana harin qofa,abinda ya lura dashi kenan shima ya miqe da azama,tana isa qofar shima yana qarasawa sanda take kici kicin bude key din,ta finciketa ya watsar ya saka key ya kulle qofar. A zafafe yabar bakin qofar yana nufar qofar toilet yana cewa.



"Yau zaki gane waye mashkur.....tunda baki zabi komai ya kasance ta hanyar maslaha ba" Key din jikin qofar toilet din shima ya murza ya kulle,tana kallonsa sanda take qoqarin sake tashi saboda buguwar da tayi a hannu da fuska,yadan bude window din waje ya watsa Keys din sannan ya sake waiwayota.



"Kaji tsoron Allah mashkur......kada ka keta haddin aure.......da auren wani a kaina.......ba bazawara ko budurwa bace!"



"Allah yasa tattabara ce ke" Ya fada cikin rashin damuwa yana durfafota da sassarfa kaman me wasan motsa jiki.



Cafka ya sake kawo.mata ta sake samun nasarar gocewa abinda ya sake qona masa rai,sai kawai ya zabi ya galabaitar da ita.....don duka alamu sun nuna masa cewa gwana ce wajen iya zilliya,kada ta bata masa time ta kuma bata masa plan,don haka yakai mata naushi.



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login