Showing 3001 words to 6000 words out of 147628 words

Chapter 2 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

zata koma tamkar bawa da ubangidansa a hannuna........bansan me yasa yarinyar ke yimin kwarjini ba,bansan me yasa nakeji wani abu daban ba idan ta kalleni......inason dukka wadannan abubuwan su shafe daga idanuna".



Wani murmushi dake dauke da tarin boyayyun ma'anoni da rufaffun qudurori dake amsa kuwwa da amon nawa burin yana sama da naki hajja tayi,sannan ta harde qafarta tana cewa.



"Dukka wannan qanqanin aiki ne a wajensa,kuma ko iya haka aka tsaya zaki bawa wani labarin zafin aikinsa......isassun mata kawai ke iya aiki dashi,matan manya da iyayen manyan mutane irinki,saboda daga sadakin aikinsa kawai zaki fahimci ba gama garin boka bane.....don haka ki rubuta ki ajjiye.....dukkanin wadannan burirrika naki tamkar sun gama cika ne......saidai banji share dita a wannan kasafin naki ba".



Rausayar da kai maamah tayi tana sakin murmushin jin dadi. A qasan ranta tana mamakin son kudi tsantsa irin na hajja din,duk kuwa da cewa lullube take cikin wadata me tarin yawa.......saidai wadatar yaranta idan kaf idan aka hadesu batakai kaso daya cikin ukun abinda fuad ya mallaka ba shi kadai......amman duk da hakan bata raina kudi komai qanqantarsu(tabbacin zuciya ta zarme da yawa dason abun duniya,Allah ka kiyashemu).



"Baki da dukkan wata damuwa hajja,kina da million uku a ciki,kafin alqalami ne kawai......kuma somin tabi,nan gaba kadan ke zaki dinga bada wannan adadin a matsayin taki kyautar"



"Qwarai da gaske kuwa mariya" Hajjan ta fada kanta tsaye tana duban idanun maamah da wani irin confidence daya sanya maida hankalin maama duka a kanta. Wannan ya sanya ta sassauta kaifafa harshenta da nuna dukkanin qwarin gwiwar dake kan fuskarta.



"Yaronki ai yarona ne mariya...ni nasan bani da haufi....ba zaki taba butulcemin ba" Ta sake yiwa kalamanta ado da wasu kalmomin



"In sha Allahu" Maamah ta amsa tana rausayar dakai har yanzu murmushin na saman fuskarta,ta kuma jawo wayarta tana fadin



"Bari na nemi musaddiq ya nemo yaron can,don da zafi zafi ake dukan qarfe......gobe nakeso muyi sammakon tafiya hado dukka ayyukan dama sauran bayanai......bikin nan da gaske tahowa yakeyi,kwana shida kacal ya rage......inason tasan da zaman kowacce doka qa'ida dama sharadi kafin ta samu lasisin karbar igiyoyin auren d'ana a kanta". Da wani kallo hajja ta bita kawai ba tare da tace komai ba.....saidai kuma can cikin wani saqo na zuciyar magana ce me yawa nauyi da kuma dogon xangon da bazai yiwu baki ya furtata ba.



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

5�!�5�"�5�'�5�"�5�'�5�"�5�#�5�*�5�:�5�"�5�3�





6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 4





A nutse ta daga kai tana kallon hajjan



"Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba.



********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES.



Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske.



Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta.



Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa.



A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa.....wadanda sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi mutuwar murus akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka kashesu dashi.......sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar.



Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har amaryar ba ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da lallai yake da buqatar hawa yayi a can din.



Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan......don komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar privacy.



A daren da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar. Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa.



Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din.



"Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu.



Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call.



Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro.



Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa.



"Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad



"Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa



"Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan.



Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu



"Am asking you seriously fa.....where are you?"



"Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......."



"Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?.



Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi.



Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar.



Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar.



"Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace



"Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?"



"Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa.



"Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?.



"Jibi din zan shigo in sha Allah anni"



"Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa.



Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?.



"Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji.



"Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya.



"Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka"



"Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah.



Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta.



Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren.



"Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya



"Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe.



"Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata.



"Tana bangaren beauty spa"





5�?�5�j�5�c�5�^�5�n�5�V� 5�i�5�V� 5�c�5�V� 5�`�5�j�5�Y�5�^� 5�c�5�Z�.

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

5�!�5�"�5�'�5�"�5�'�5�"�5�#�5�*�5�:�5�"�5�3�

6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 5





"Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka.



******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu.



Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima cikin gidan.



Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba.



Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace.



Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a.



"A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude.



"Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi fata>�z�=�
�).



Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login