Showing 30001 words to 33000 words out of 147628 words

Chapter 11 - A Duniyata Boon 2 Complete Hausa Novel

shaqa tare da qamshin nasa yake zuwar mata hunhunta. Tsaki ta saki a boye yadda bazai ji ba,ta maida kanta daya window din da take zaune daura dashi. Batasan sun fara tafiya ba sai da taga motar ta fara sulalawa tana nufar makeken gate din gidan suna gilma shukokin da aka qawata wajen dasu.



Basuyi nisa ba kira ya shigo masa,wanda shi ya zame masa abokin tafiya. Duka maganganun cikin harshen turanci yake yinsu da wani irin accent dake nuna zallar qwarewa gami da gogewa a yaren. Kusan fin rabin maganganun nasa ba wani fahimtarsu takeyi ba,don zuciyarta tayi nisa da wani tunani na daban. Ta wani bangaren kuma yadda yake lanqwasa harshensa ba kowanne word take ganewa ba a matsayin karatunta na wadda ya dakata daga aji biyar biyu na babbar secondary wato senior secondary school.



Sanda motarsu ke qoqarin cusa kai ta cikin babbar gate din dake da wani irin girma da kuma jan hankali,a sannan ne ya katse wayar ba kuma don ya gama ba. Ya kashe wayar gaba daya tana kallonsa ta gefen idanu,ya zurata cikin wani dan abu daya matsa ya fito ya saka wayar ya koma ciki. Adan qaramin zamansu na mintuna ta karanci abubuwa daban daban tattare dashi,kusan kaman komai nasa na dabanne kuma daban yake,saita tabe baki sanda suka isa babban parking lot na alfarma da gidan ya mallaka.



Qasa tayi da kanta tana jan mayafin data lullube kanta dashi sanda take hangar wasu mata suna bullowa daga wata qofa da tafi kusa da parking lot din,kafin takai gayin komai amna ta bayyana ta kama murfin tana budewa,abinda ya bata daman jin maganganunsu. Muryar amna ta fara ji



"Inna uwaisha......ga addan namu.......ku fito mana da ita a hankali" Ta qarasa fada tana qaramar dariyar dake nuna zallar farincikinta



"Kinyi qoqari auta sannu.......kin gama naki" Wadda aka kira da uwaisha ta fadi tana matsowa gaban motar



"Kamar gaske" Sautin muryarsa ta fita a hankali ya furta sanda kan sabreen ke qasa tana jin wani fargaba haka kawai na haduwa da mutanen da batasan su kuma meye nasu kalar halin ba,sunan auta da taji an ambata sai ya sanya duka tsigar jikinta ya tashi,haneefa da tun da safe take kokawa da tunaninta ta fado mata.....ko yaya ta wuni?.



"Zallar karamci da girmamawa da mutuntawa muke gabatar miki" Abinda inna uwaisha ta fada kenan kamar tasan abinda sabreen ke wassafawa qasan zuciyarta. Miqa mata hannu inna uwaishan tayi tana fadin



"Sauko a hankali nayi miki jagora zuwa ciki,ki shirya don kowa na dokin jiranki". Bata musa ba ta sakawa inna uwaishan hannunta



"Fatabarakallahu ahsanul kaliqeeen......da iya lallen nan ma kawai an tashi kaina yallabai". Inna uwaishan ta fada tana dariya dariya idanunta akan muhammad fu'ad dake qoqarin ficewa a motar sannan ta maida dubanta ga amna data dage mata gira alamun Yes.



Inna uwaisha na daya daga cikin makusantan anni da suka daukeshi tamkar d'a,duk da cewa tana da jika qwaya daya amma idan kaga suna raha da amna saika dauka yaya ce da qanwarta,hakanan suma ta daukesu duka mazan gidan. Bai iya cewa komai ba,sai dan motsawa da labbansa sukayi alamun murmushin dole kawai ya sanya qafafunsa ya fice daga motar.



Kunnuwanta kawai ke iya jin surutansu amma idanunta suna a rufe. Batasan ina suke nufa ba saidai idanunta na iya kallon lullubabban luxury marbles din dake shimfide a wasu sassan na gidan,a haka taji sun isa wani daki da a nan inna uwaisha tace da ita



"Fell free sabreen.....ki shirya amna zata tsaya dake,idan kun kammala zan dawo mu wuce wajen taron,kowa ke yake jira". Kai ta gyada a hankali,cikin ranta kuma tana zancan zucin wanne shirin kuma zata sakeyi bayan na jikinta.



Sanda amna ta gabatar mata da komai na shirin shuru kawai tayi tana bin kayan da kallo......shin da saninsu wanne irin aure ne akayi suke wahal da kansu haka da kashe kudade da hidima?,ko kuwa kallo kawai sukewa abun irin duban bangon littafi ga idanuwan da basusan meye a cikinsa ba. Wata lafiyayyar Moroccan gown dake da wani irin ado na daukan hankali......saidai kuma duk da adonnan nata sam bata da nauyi ko kadan. Hade take da wani irin hijab dan qarami da yafi mata kama da na Indonesia ko Malaysia.....a ciki batasan wanne ne ba. Komai na kayan fari ne qal da wani irin haske me daukan hankali. Ita kanta bayan ta gama shiryawa batasan lokacin data dauka tana kallon kanta ba,sai take ganin kamar ba ita ba.....duk da kusan komai ma yana zuwa mata ne da wani irin ba zata da bata taba zato ko kawowa cikin rayuwarta ba.



Amna ce ta fara shigowa wadda fiye da dazun a yanzunma ta susuce wajen yabawa sabreen din.



"Inna Allah kwanan nan hamma zai manta da wani gold da Diamond"



"Maza dai ya jiki" Inna uwaisha ta fada tana riqe hannun sabreen suna nufar qofar fita.



Suna shiga wajen tasan sun iso,duk da kusan kowa na zaune a nutse ana sauraren jawabi daga bakin malamai.



"Muna yiwa amarya barka da shigowa". Maganar data dauki amsa kuwa cikin hall din,ta kuma bawa maamah damar fara gyarawa tsaf don bayyanar da kanta a wajen.



Ringing biyu wayar tayi ya daga yana sakata a kunnensa



"Ya kamata ka qaraso wajen walimar fa.....akwai mutanen da zaku gaisa dasu"



"Bana kusa"



"Kaman yaya?" Farouq ya tambayeshi a mamakance



"Eh.....kaman yadda kaji bana kusa,uzuri ya kamani nadan fita"



"Why.....you know......"



"Anni zata fahimceni idanma kai baka fahimta ba.....sai na dawo" Ya amsa masa yana katse wayar ya maidata ya ajiye. Shi a yanzun kasuwancinsa shine abinda yafi damunsa shine kuma gaba da komai,bai takurawa kowa ya matsawa kowa ba,don hatta da saddiq daya Kamata ace a yanxun suna tare suna duba al'amuran da suka taso musu bai masa magana ba,bai kuma ce komai dashi ba saboda yaga ya sanya kanshi cikin hidimar bikin sosai,ya bashi lokaci ya qare ya dawo hayyacinsa.....tafiya ce dai dasu tsakanin jibi da gata,kuma bazai dage masa qafa ba dole ya shirya su wuce. Girgiza kai kawai farouq din yayi,halin fu'ad saishi,baisan ma yaushe ya fita din ba bayan sun shigo cikin gidan tare. Ya sanshi sarai ya kuma sani,wani irin mutum ne shi da kasuwancinsa ke gaba da komai idan ka dauke shi anni abba da su saddiq,amma koma meye yana ji a jikinsa,yana Kuma fatan duk yadda yakai ga gujewa auren da bashi wani rashin muhimmanci ya zame masa silar shiryuwa da saituwa kaman kowanne magidanci.



A nutse farouq ya ratso cikin mutane ya yiwa anni rada. Kai kawai ta gyada sanda idanunta suke kan sabreen dake zaune waje daya bata ko qwaqwaqwaran motsi. A iya haka tana iya hangen nutsuwa a tare da ita,sannan haka kawai takejin qaunar yarinyar cikin ranta.



Tana iya hangen wasu abubuwan ta cikin mayafin dake lullube saman kanta,a sanda walima tayi nisa..... Kai kawo na mutane ya qara yawa tata zuciyar cike take da lissafe lissafe kala kala. Lumshe idonta tayi sanda aka fara gabatar da miqa gudunmawa ga amarya,wato kowa zaizo ya zube mata tasa gudunmawar adan wani babban qwarya dake ajiye a gabanta maimakon yin liqi,wanda daga nan za'a fara gabatar da lectures akan zaman aure. Numfashi ta sauke daga can cikin hunhunta,duk cika da batsewar mutanen dake a wajen bata hangi wani nata ko mutum daya ba. Sai takejinta bare a wajen da wani irin rashin sukuni da takura.



*DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK)*

08187255862



5�� 5�� 5�
� 5�� 5�� 5�� 5�� 5��

_ZAFAFABIYAR_



6B6O6O6K 62



g,D� D� �



5�K�5�<�5�B�5�@� 21





21





A nutse aka fara zuwa daya bayan daya ana zube sabbin 'yan dubu dubun fil a miqe cikin bundles dinsu a gabanta. Ta rasa tsakanin burgewa da rashinsa wanne takeji cikin zuciyarta?,duk da ta hangi tarin nutsuwa da kamala a komai na taron.



Idanunta ta sake dagawa a hankali ta cikin mayafin tana kallon bakin qofar shigowa gurin dake facing dinta......tamkar abinda ake jira kenan saita hangi huda na shigowa. Da farko ta dauka kaman gizo idanuwanta sukeyi mata ko kuma me kama da ita ne,saidai shigowar nadra da haneefa ya qarasa kore mata dukka shakkun data soma ji cikin ranta. Wannan bai saketa ba taga abinda ya kusa doka zuciyarta saboda firgici.....maamah ce.......tana biye dasu da dukkan alamun da zasu gwada maka tare suke......tare suka shigo,don waiwayawa haneefa tayi da alama kiran sunanta tayi,sai taga ta riqe hannunta haneefa na mata murmushi tana maida mata sukaci gaba da takowa wajen tare.



"A ina ta gansu?,a ina ta daukosu?,ya akayi taje ko sukazo wajenta?,tun yaushe?,me kuma take gaya musu?" Tayi tambayar sanda taga ta tsaidasu duka su ukun kuma kowacce ta tattara mata hankalinta.



Sanye take cikin wata 'yar ubansun super embellished me asalin tsadar da jikinta ke bada wani irin santsi tamkar ba atamfa ba. Tun daga yanayin shigar zaka tabbatar da gaske ta dauki duniyarta dama rayuwarta gaba daya.....hakanan da gaske komanta yana mata dadi yana kuma tafi mata yadda takeso. Daga bayanta hajja harira ce data shirya kanta itama cikin applique lace ruwan sararin samaniya. Ita dinma duba daya zakayi mata ka tabbatar da halin yazo daya kamar yadda abotar tazo daya.



Kai tsaye ta daga yatsa tayi musu nuni da kujerar da sabreen ke zaune a kai,sai dukkaninsu suka maida idanuwansu kanta. Fuskokinsu suka cika da farinciki duk da basa iya ganin fuskarta sosai,suka motsa kamar zasu taho zuwa wajenta,amma sai taga ta sunkuya tana magana dasu. Cikin qasa da second talatin taga sun maida hankalinsu gareta.......sun kuma juya suna binta a baya zuwa hanyar data nufa,daidai lokacin da me gabatarwa ke bada sanarwar



"Mahaifiyar ango ta shigo......uwarsa kuma zata marabceta" Maganar data finciko hankalin sabreen daga shingen tunanin data afka sanda take binsu da kallo suna biye da maamah sau da qafa.....kai kace ummeensu ce ta dawo duniya.



"Uwa?.....mahaifiya?,wacece?" Ta samu kanta da shiga wannan rudanin tare da fatar a yau ta samu warwarewarsa,don haka ta buda dukka idanunta tana bin kowanne kusurwa da kallo tanason samun warwarar rudaninta.



Cikin nutsuwa da girmamawa anni ta miqe tana dosar inda maamah ke a tsaye,fuskar annin shimfide da fara'ar data ratsa har qasan zuciyarta. Har yanzu gangar jikinta da ruhinta basu daina jin farinciki da alfaharin aurar da fu'ad ba......wani abu guda daya daya zamewa maamah tamkar dafi tsakiyar tsokar zuciyarta



"Ameenatu ce ta aurar dashi" Kalmar da inda tana da ikon gogeta tsaf saita gogeta daga dukkan wata ma'adana ta kalamai.



"Barka da zuwa......sannunku da zuwa......"



"Uwa kuma mahaifiyar muhammad fu'ad jadda ba,ai haka ya kamata ne gabatarwarki ta fadi" Hajja harira dake tsaye gefan hannun hagun maamah ta furta da wata irin izza.



Kallo daya anni tayi mata ta watsar da ita gami da bawa banza ajiyarta,idanunta suna sauka akan fuskar 'yammatan su uku da take ganin tamkar ta taba ganin fuskar a wani waje. Kallonsu kawai tayi suka fara gaidata daya bayan daya,ta amsa musu tana dafa kan kowaccensu da madaukakiyar fara'a da kuma kulawa,kulawar da ta sauka har cikin idanun sabreen wadda ruhinta gaba daya yana a wajen,saidai babban qalubalenta bata iya jin me aka tattaunawa akai.



Tun daga tashin anni har tsaiwarta a wajen sabreen na tuna guraren data taba ganin fuskar matar ne. Indai da gaske itace anni......itace uwa ga fu'ad ba shakka ta santa......amma ta yaya haka ta kasance?,ya akayi yake da uwaye biyu?,me yasa anni data taba sani duk da alkhairi ya hadasu ba ita ta nema masa ita ba?,sai waccar baquwar fuskar da bata taba ganinta ba kafin faruwar wannan abun kaf tsahon rayuwarta?.



"Barkanki kade Ameenatu.......sannunki da hidima" Maamah ta maida mata da wani irin salon murmushin da ya sanya anni tajishi har cikin jinin jikinta.



"Ina tayaki murnar aurar da fu'ad da kika samu damar yi......wannan babbar dama ce da zata zame miki tarihi kuma abun tunawa watan watarana.......ina aka tanadarwa mahaifiyar fu'ad domin ta zauna ita da qannen matarsa?" Tayi tambayar kai tsaye cikin isa......



"Ai albarkacin kaza qadangare kansha ruwan kasko mariya....muhalli har sai kin baiwa wani" Anni ta fadi duk da rabin hankalinta yana kan yaran abubuwa masu yawa suna yawo a ranta. Waiwaya tayi ta yafito muhsina inna uwaisha dake shirin wucewa



"Itace mariya.......a cikata da irin karamcin nan da aka gada,koda zata cika hall dinnan da jama'arta.....a tabbatar an gamsar da buqatarsu,a nuna mata dattako da dattijantaka" Dukka anni tayi maganganun da kai da bakasan komai ba zaka dauka zallar magana ce kai tsaye,saidai gasu hajja da maamah din dukkaninsu sunsan magana ce akayi musu me harshen damo. Juyawa abinta anni tayi tana komawa cikin jama'arta,maamah tabi bayanta da kallo tana jin zafin jirwayen datayi musu me kama da wanka. Zafafan baqaqen maganganun data fahimci kowaccensu,amma kuma saiga murmushi yana subucewa daga saman fuskarta



"Kwanaki kadan suka ragewa izzarki ameenatu.....na rantse koda pant din dake jikinki da kudin muhammadu aka siyeshi saikin zareshi kin miqomin.......na rantse sai na sanya fu'ad ya gaya miki maganganun da zasuyi silar ajalinki......maganganun da zasu zame miki dafin da zuciyarki zata buga ta tarwatse pieces " Tayi dukka maganganun ita da zuciyarta tana me cike da alwashi.



Duk da wadannan abubuwan data samu ta kuma aiwatar zuciyarta ta kasa samun nutsuwa ko qanqani.......sam farincikinta har yanzu rabi ne......daga sanda ta iso bakin qofar mansion House din Alhaji hamza kibiya duka sai taji ta raina nata gidan kwata kwata. Batajin akwai wani gida ko gini da fu'ad zaiyi mata komai kyau da dukiyar da aka narkar ya zauna mata a rai muddin zai zamana muhallin Alhaji hamza kibiya yafi nata......indai zai zamana matsugunnin ameenatu zai d'ara nata.



Daina fahimtar komai tayi......daina fuskantar duk abinda ake gudanarwa tayi,dukka idanunta dama hankalinta suna kan 'yan uwanta,suna kan kowanne motsi da kai kawo nasu. Hankalinta taji yana tashi,bata qaunar kowacce mu'amala ko alaqa kome qanqantarta tsakanin maamah dasu,saidai yadda taga tana jansu a jiki,ta wani.mugun sake musu ko ita batajin ta sake musu haka. Haneefa duk girmanta tana saman cinyarta tana wani lallabata,irin lelen da haneefa din keso a matsayinta na auta take kuma qishirwarsa.



Cafko hannun amna tayi wadda ta zuge tata jakar ta fara fiddo sabbin 'yan dubu dubu kaman ba'asan ciwo da zafinsu ba.....kamar ba wasu abu masu muhimmanci ba tana zubewa sabreen din.



"Kiramin su nadra.....kice suzo yanzu yanzu injini". Dubanta amna tayi duk da bata iya ganin fuskarta sosai.



"Su waye?" Ta tambayeta don bata gane ba. Ajiyar zuciya ta sauke tana qoqarin saita kanta,sai sannan ta tuna amna din bata sansu ba



"Sun shigo yanzu su da......." Ta dakata tanason tuna sunan da ake kiranta dashi



"Su da maamah" Kai amna ta daga tana hangensu daga nan inda take,kwata kwata bata qaunar abinda zai hadata da matar,bata qaunar kallon da take binta dashi irin kallon dake fita daga idanuwanta zuwa kanta,amma zuwa aiken sabreen ya zame mata dole



"Okay" Tace da ita



"Na gode" Sabreen ta fadi da sauri saboda jin dadin zatayi mata abinda takeso a sanda bata da damar tashi.



Da ido take bin amna sanda take nufarsu,duk wani taku dake qara kusancin ama dasu bugun zuciyarta qaruwa yakeyi,ta kasa dauke idonta daga kansu daidai da second guda har zuwa sanda ta qarasa gabansu. Taga amna ta mata magana,ita kuma ta waiwaya tayi magana dasu kafin ta sake dubanta still ta gaya mata wani abu daya sanya amna din juyowa ta dawo mata.



"Me suka ce?" Ta fara da tambayar amna din tun bata gaya mata komai ba



"Zasu zo.....zasu taho tare da maamah din wai". Idanunta ta maida ta lumshe tana girgizawa amna kai kawai. Wani irin rikitaccen yanayi yana sauko mata,kada dai ace suna jin wani sauyi na daban akan maamah kamar yadda takejin wajabcin bin umarninta tako ina yana ratsata?.



Tun daga wannan sa'ar nutsuwa tayi mata qaura,ta kasa debe idanunta daga kan 'yan uwan nata,duk wani motsi murmushi da kuma fara'ar fuskarsu ya tabbatar mata suna jinsu ne cikin sukuni da farinciki,har zuwa lokacin da aka bada sanarwar isowar mahaifiyar ango zuwa inda surukarta take.



Tamkar mejin tsoron wani abu haka zuciyarta taci gaba da bugawa sanda maamah ke kusantota tana takowa wajenta dasu nadra gaba daya. Idonta ta lumshe da sake budesu akansu gaba dayansu tana me kyautata zaton saisun iso gareta ne kai tsaye kafin aiwatar da komai......saidai kuma akasin haka ne ya faru. Kamar kowa suma wajen zuba kudin suka nufa,kowacce ta dire rafas na dubu dubu sabbi guda uku dake hannunsu huda kuma ta zuba biyar. Bin kudin tayi da kallo,suka kuma tsaye mata a rai.



"Wai ina momma bahijja?" Tambayar da bata da amsarta batasan kuma wanda zai gaya mata amsar ba. Ta tabbatar daga kansu har zuwa momma ba wanda zai basu wannan kudaden son suzo su zuba a wajen.....amsarta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login