Showing 114001 words to 117000 words out of 161316 words

Chapter 39 - Ahalinmu Daya Book Two Complete Hausa Novel

04 Nov 2025

306

_Typing馃摬_

*_AHALINMU 茒AYA_*

馃挆馃挆馃挆

*_Fatima Y zakariyya馃憣_*

_Tymer's henna_馃拝

*Nazari writer's ass......馃摎*





_Sarauniyar馃懜 Nazari writer's鉁嶏笍_

*_(THE QUEEN馃憫)_*

________Dedicated to anty salma馃拵

*_Part 2_*

(Littafi na biyu馃摌)

_Godiya ta musamman gareku 蓷aukacin masoya na ina matu茩ar yaba muku, alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke.馃馃槝馃槝_

*Da sunan Allah mai rahma mai jin kai*

*_in the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful_*

鉃★笍馃吙锔 2锔忊儯5鈨b灃2鈨6鈨p煋

Khaltum wadda ke sauri sosai tanata faman ha蓷a hanya, ko nisan gurin a ranar bata gani, gaba 蓷aya tabi taru蓷e, wanda da gani take zata da蓷e bata je, inda Suhaiman take ba Saboda nisan dake tsakanin su, Amma yanzu ina bata ko ganin hakan,

Ras" Gabanta yafa蓷i jinta yi karo da mutum, take ta rufe fuskantar da tafukan hannayen ta, taruntse ido hankalin ta tashe ta furta wayyo Allah na shiga uku, jikin ta yahau 蓳ari dama ga tsoron abunda kunnuwan ta suka jiyo mata,

"Ke Tsawa Barrister Sulaiman ya daka mata, _Are you Nonsense_? Ke wace irin shashasha ce da bakya kallon gabanki,"

"Sai a lokacin ta janye hannun ta daga fuskar tata, jin Mutum ne ba aljani ba Don ita gaba 蓷aya tagama tsorata tayi tunanin aljani ne tayi karo dashi, saboda tsabar ru蓷u da tashin hankali ko gaban ta bata kallo sauri kawai take,"

Kanta a 茩asa ta furta, Ayya kayi ha茩uri, wallah bangan ka bane,"

"Mtss yaja tsaki tare da wucewa da hanzari,

"Wata irin ajiyar zuciya Khaltum ta sauke, tare da dafe 茩irjin ta, Wai Allah Nagode, Bataji haushin abunda ya mata ba saboda tasan laifin tane, amma duk da haka taji haushin ce mata Mahaukaciya da yayi,

Da sauri Barrister Sulaiman yajiyo, tunawa dayiyi, da maganar mahaifin sa, Na yarinyar da yace ya gani ankawo sannan kuma barazana acikin Rayuwar Su, Toko dai itace? ya tambayi kansa Gashi baigan ta da Uniform 蓷in ma aikatan Estate 蓷in ba,"

Ke" ke

Sauri Khaltum ta 茩ara jin ana Magana,

Ke tsaya Dake nake shine kike 茩ara Sauri,

Jin hakanne yasa ta tsayawa Cak tajiyo a hankali, kanta na a 茩asa,"

"Dai dai 茩arasuwar sa ya Furta, Wacece ke?"

"Aiki aka kawo ni,

" Aiki Anan kuma? Sannan ina uniform 蓷inki na ma aikata, kunawa ne aka kawo?,

Tunawa tayi Suhaima tace duk wanda ya tambaye ta tace ita ka蓷ai ce,

"Nika蓷ai ce, Sannan ba abani uniform Ba ni ba茩uwa ce anan,"

茒an Jim yayi kamar mai Nazarin ta gani yayi kamar bata da gaskiya gashi jikin ta na rawa, 茒ago da kanki inason ganin fuskar ki,"

A hankali ta 茒ago ta kalle shi, Barka da Safiya tafa蓷a a hankali,

Zuba mata ido yayi batare da yace komai ba sosai yake kallon ta har saida taji ta tsargu ta茩arayin 茩asa da kai,

Batare da ya 茩ara cewa komai ba yajuya ya cigaba da tafiya abunsa, ganin hakanne yasa ta cigaba da tafiya itama cikin ranta kuma haushin sa ne fal, Idan ba rainin hankali ba kawai ka tsaidani ka hau kallo na aikin banza, masifa ta shiga yi ita ka蓷ai,"

"Ni banga abun da zangyara acikin parlour nan ba, Idan ba masifa ba, kalli ko ina tsaf yake, cikin ranta tayi maganar tare da kai duban ta zuwa, upstairs 蓷in dake parlourn, ko dai na hau saman nan nagani, Batare da wani dogon tunani ba Suhaima ta haura upstairs 蓷in sa sassarfa,

Dr. Sulaim Hameed Arab Taga an rubuta jikin wani tangameman hoton sa dake ma茩ale jikin Bangon parlourn Upstairs 蓷in, wanda kana hawa dashi zaka fara tozali sanye cikin shigar sa ta Doctor ga sirrin farin glass manne a idon sa, hakan ba茩aramin kyau ya 茩ara masa ba fuskar nan tashi kamar kullum a 蓷aure Tamau, kallon hoton tayi wannan shine ganin ta dashi na biyu 蓷aya a zahiri sai wannan hoton, Mutum sai kace aljani, Suhaima ta fa蓷a afili ta 蓷ora da Fa蓷in kuma wallahi sai na rama abunda kayimin,"

Sosai tsarin parlourn ya burgeta kasan cewar akwai banbanci da na 茩asan, shi wannan komai na ciki, black and white ne hakan ba茩aramin burgeta yayi ba, tana son abu fari da ba茩i sosai,"

Ganin shima a gyare yake ko ina tsaf tsaf, hakan yasa ta 蓷an zage parlourn kamar me neman wani abu, saida ta 蓷an jima kafin ta nufi downstairs da niyar anjima zata dawo,?

Kai tsaye ta nufi waje bayan ta sakko,"

Suhaima, Suhaima, Khaltum takwala mata kira ganin tana shirin bin wata hanya cikin Far fajiyar Part 蓷in,

Da sauri Suhaima ta juya jin muryar Khaltum, tafiya ta farayi tana nufar inda Khaltum 蓷in take, itama ta taho suka ha蓷e, da hanzari Suhaima ta kama Hannun ta,

" Khaltum lafiya kuwa?,

茒aga mata kai Khaltum tayi alamar eh saboda wahala tama kasa magana,"

"Kinga Khaltum ki nutsu ki sanar min Meye ya faru me ke damun ki? Gaba 蓷aya bakya cikin hayyacinki, Talk Khaltum Menene?

Ganin gaba 蓷aya hankalin Suhaima ya tashi ne yasa, Khaltum 茩a茩alo Murmushi ya茩e, wanda yafi kuka ciwo, Ba wani abubane bafa kawai nagaji shiyasa kinsan tafiyar akwai 蓷an tsayi,

Oky ga can muzauna saiki sanar min sannu, Suhaima tayi gaba ru茩e da hannun Khaltum kamar wata 茩aramar yarinya haka takebin bayan Suhaima Sororo,"

"Bayan sun zauna Khaltum ta dawo hayyacin ta, Ta kwashe komai na abunda kunnuwan ta suka jiyo mata a cikin parlourn Mai Girma Hasheem, sai ta 蓳oye mata ha蓷uwar ta da Barrister Sulaiman, don tasan halin Suhaima sarai idan taji baza a wanye lafiya ba,"

"Shiru Suhaima tayi na wasu 拼an da茩i茩u kafin ta nisa ka蓷an, Dakyau Khaltum naji da蓷in jin wannan sosai kada kidamu kedai kawai ki kula sannan kicigaba da sa ido sosai, Dama nasan akwai, Manya Manyan 茦ulli a cikin wannan Kurman Estate 蓷in Amma Da sannu zangane komai"

"Ni dai wlh abun harya fara bani tsoro anya baza mu ha茩ura mu koma gida.....

Kallon da Suhaima ta watsama ta ne ya hanata 茩arasa maganar da ta 蓷akko,"

Take kwayar cikin idon Suhaima tajuye ta riki蓷e zuwa Rainbow colour, Khaltum Babu abunda zai hanani 茒aukar fansa Sai iKon Allah, Allah baya son zalinci baya son meyin sa saboda haka wlh ba gudu ba ja da baya, inason kicire wannan tsoron naki idan ba hakaba, saidai keki koma gida, Fansa ta cikar buri na, Tana kai wa nan tami茩e,"

Kamo hannun ta Khaltum tayi cikin sanyin jiki, shikenan, Allah yabamu nasara akan su,

Ameen, Suhaima ta fa蓷a har lokacin kwayar idon ta, bata koma dai dai ba,"

"Nibari Nakoma kada a nemeni khaltum tafa蓷a dai dai tana mi茩ewa,"

"Suhaima tace Harkin Huta kenan,

Em kawai Khaltum tace, Bata jira cewar Suhaima ba ta wuce kai tsaye,"

"Bayan Khaltum, Suhaima tabi da kallo, Ajikinta Tana jin kamar wani Babban Al'amari na shirin Faruwa tsakanin ta da 拼ar Uwar tata, Da sauri ta kauda tunanin, jiki babu kwari tanufi Part 蓷in Hajiya Umma saboda a can komai nata yake,"

Bayan La'asar, gaba 蓷aya Aka hallara A Parlourn Baffa, 瞥a 拼an sane maza kusan dukan su Kamar yadda suka saba Hutun 茩arshan makon Su a gida Ranar Lahadi da yamma sai su ziyar ci mahaifin nasu,

Alhaji Hameed, uncle Mansur, Daddyn Canada, Uncle Yusuf, Mai Girma Hasheem, Uncle Shaddad, wanda shi gaba 蓷aya baya magana iya kacin sa ido ne kawai, yanzuma uncle Yusuf ne yaje part 蓷in Sa ya taho dashi,"



He Excellency Sambo, yabada uzirin bazai samu halar taba yana da Meeting, uncle A, da CONOLET Aliyu, basa 茩asar su ka蓷ai ne babu a cikin 拼a拼an Baffa maza a parlour ,

Ga ba 蓷aya suka gaisa da mahaifin nasu,

Kafin kowa ya茩ara cewa wani abu Sulaim yame茩e tsam,

Kallon shi Baffa yayi, Ina zakaje?

Baffa zamu koma Part 蓷i nane, Yarima Nason Hutawa,

Koma kazauna ai shima 蓷an gida ne inaso na fa蓷i wani sa茩o idan nagama, zaku iya tafiya,

Bamusu Sulaim Yakoma ya zauna kusa da, Aminin Nasa sai Saleem dake gefe,"

"Alhamdulillah Naji da蓷in Ganin ku Kamar kowane 茩arshan Sati, Gashi a wannan Satin mun samu 茩arin Babban Ba茩o kuma 蓷an gida, 茒a ga Adalin Sarkin Gabas, Yarima Sultan Amadadin Iyalan gidana Muna maka Barka Da zuwa Tare da Fatan Zakaji da蓷in zama Acikin mu, Baffa yakai 茩arshan Maganar tare da Duban Sultan,"

Murmushin Girma Yarima Sultan Yayi, Take Mulkin Ya motsa A nutse ya tashi yaje gaban Baffa, Cikin Girmamawa Ya russuna tare da cire hular kansa kamar yadda yake wa Mahaifin sa Alama ce ta Girmamawa Kuma iya sarakai suke yiwa haka amma gashi yayiwa Baffa,

"Allah ya 茩arawa Baffa lafiya, Ina godiya bisa karramawar Dana samu, Bisa Haka Ina ro茩on Allah ya ja Kwanan Ku, Mai Martaba yace Agaya Maka yana Mi茩o Gaisuwa ga Abokin sa Dattijon Arzi茩i,"

Shima Murmushin Baffa yayi, Tashi ka zauna 茒ana, Na gode kwarai, Ina amsa gaisuwar gwarzon Sarki,"

Saida Yarima Sultan ya maida hular kansa Tare da dai dai ta mata zama, sannan ya tashi ya nufi Gurin Alhaji Hameed Mahaifin Sulaim Wanda suke kira da Abiiy, Cikin tsananin Girmamawa ya gaidashi Tamkar wani Sirikin sa, Bayan yayi masa barka da zuwa, Yarima Sultan yayi jam'i wajan gaida sauran mutanan Parlourn sannan Yakoma ya zauna,"

"Sosai Uncle Mansur yaji haushi, Akan me Su bai girmama su kamar yadda yayiwa Abiiy ba, Uncle Mansur Akwai son Girma ga Hassada Da Ba茩in ciki, ba bar komai daga cikin halin mahaifiyar suba,

Bayan Yarima Sultan Ya zauna, Baffa ya cigaba da Magana,

"Duk Da ba a Meeting Room muke ba ina so insanar muku da Cewar muncan za tsare tsaran Company's 茒in mu, Sannan zamu Canza gaba 蓷aya, Managers and Directors NA Kowane Community Of Companies, Mun Tattauna da 蓷an uwanku Hameed Game da hakan Saboda Wasu dalilai Kasan cewar Akwai wata Matsala da Aka gano Amma anakan Bincike haryanzu,"

Dim Dim, DiDim 茩irjin Uncle Mansur Yabada 茦ara, Barrister Sulaiman wanda Har ya sako kai cikin Parlourn, Kunnuwan sa sun jeye masa komai, saboda tsabar tashin Hankalin da ya ziyar ce shi Mutuwar Tsaye Yayi, ya kasa gaba ya kasa baya,

Sannan akwai Jirin Sunayen Sabbin Directors and Managers, A hannun Hameed, Duk wanda yake da magana Akan hakan ko yana da sunan wanda yaga yadace abawa dama to zai iya yin magana da Shi Hameed 蓷in bayan mun tashi,"

"Wanka Suhaima tayi ta zura doguwar rigar Abayar da Dr.Muhibba tasa aka basu lokacin da suke asibiti, Haka Kawai take jin nisha蓷i a cikin ranta, Bayan ta kammala shirin ta tare da 茒aure Fuskar ta da mayafi kamar yadda tasaba kullum Idon ta kawai ake iya Gani a fuskar ta,

"Fitowa tayi, a Parlourn ta tarar da Hajiya Umma na zaune tana kallon, Sunna TV, kasan cewar Baffa yace baza Su zauna a Sashen ma'aikata ba shiyasa aka bawa Suhaima 蓷aki a acikin 蓷akunan dake Parlourn 茩asa, 茩arasawa tayi gabanta, Barka da Gida,"

" Duban ta Hajiya Umma tayi, Barka dai kina lafiya?"

Lafiya alhamdulillah, Akwai Abunda za'ayi ne yanzu?"

A'a Babu, "

"A huta lafiya Suhaima na kai wa nan ta tashi tanufi waje cikin ranta tana adda'ar Allah yasa kada hajiya umma ta da kayar da ita kamar yadda tayi mata jiya da yamma ta hana ta fita, Ita kuma Bazama ne yakawo taba, da wannan tunani Suhaima ta fice daga Cikin Parlourn salin alin batare da ta dakatar da ita 蓷in ba",

"Kai tsaye ta nufi Sashen Sulaim Yadda tafita 蓷azu tabar shi bahaka ta tarar dashi ba, an茩ara gyara komai, ko ina sai 茩alle yake, ba tayi wani mamaki ba, take zuciyar ta ta ayya na mata, Abokin aikin tane yayi gyaran saboda dama kullum shi yake aikin gyaran Parlourn da yamma, kasan cewar sa Christian ne kuma bayajin Hausa shiya basu ta蓳a gaisawa da Suhaima ba duk da suna yawan ha蓷uwa, koda sun ha蓷u saidai kowa yayi abunda ya kawo sa ya fice,

"Kai Tsaye ta nufi kitchen dake Ma茩ale cikin Parlourn akaro na farko tun zuwan ta saidai taga wannan Christian 蓷in dabatasan Sunan saba yana shiga yana fita amma ita bata ta蓳a shiga ba, Babu ko 蓷ar cikin ranta, Kallon kitchen 蓷in take komai a tsare ya burgeta sosai, cikin ranta ta furta, wai ahaka kitchen Ne nan, yakai girman gidan wani saboda tsabar al'mubazzaran ci, ehm Allah yasa dai ku蓷in halal ne ake facakar nan dasu, tafa蓷a lokacin da take 茩arasa shiga cikin kitchen 蓷in,"

"Gurin cooker gas tanufa kallon shi ta shiga yi ganin irin na Kichen 蓷in Hajiya Umma ne yasa ta 蓷an sakin murmushi saboda ta iya kunnashi hajiya umma ta koya mata dama shi ka蓷ai ne matsalar ta, Jitayi tana sha'awar yin Girki, Take tanufi wata 茩ofa dake cikin Kichen 蓷in bisa mamakin ta tana tura 茩ofar ta tafi tabu蓷e, kayan abinci ne aciki kala kala, STORE NE dan茩are da nau'i nau'i na kayan abinci, sosai Suhaima tayi Mamakin to ko dai yana da Aure ne?" amma ai da yana da Aure da zanga matar Anan, ganin bata da amsar tambayar tane hakan yasa tabar gurin ta nufi freezer, key 蓷in dake Ma茩ale jikin freezer 蓷in ta mur蓷a, kayan miya ne aciki da nama kala kala, hadda ni茩a茩茩en naman kaza 蓷an ye, Kasa 蓳oye mamakin ta tayi, Suhaima sai magana take ita ka蓷ai, ganin tana 蓳atawa kanta lokaci ne yasa ta, fara shirya ha蓷a蓷蓷an girkin gargajiya,"

Bayan ta ha蓷a komai na girkin ta 蓷ora, sai tafita, takoma Parlourn SHOWGLASS tanufa ta 蓷akko turaren wuta mai 茩amshin gaskiya tasa acikin Borner tare da jonawa acikin Socket take parlourn ya kara蓷e da 茩amshi, ta 蓷auki Room freshener ta茩ara fisawa sa茩o da lungu na parlourn,"

"Wasu ha蓷a蓷蓷un Food flasks, Suhaima ta 蓷aukko da aka jerasu daga 蓷an saman kanter, irin Flasks 蓷in nan ne da ake kira da CI BARI KALLO iya kallon suma sai yasa ka茩oshi, jikin su black ne sai 蓷an ratsin golden, DASHISHI DA MIYAR GANYE Ne Suhaima tayi wanda miyar taji Nama da ganda, sai chicken and salad, da fish perpp soup, 茩amshi NE Mai da蓷i Kawai ke tashi, Suhaima ba baya ba wajan girki gwana ce, Mother ta horasu akan girke girke kala kala, Suhaima ce kawai ta tsaya ta koya Amma Khaltum saidai a gama abata kawai tasani bata son aiki kwata kwata,

"Saida ta kammala zuba komai, sannan tayi amfani da kayan iyatatuwa wajan ha蓷a lemon na'a na'a da lemongrass, tasa a friegh ta nufi dinning Area Tajira Komai a dinning Table, takoma Kichen 蓷in ta gyara komai tsaf dama tanayi tana gyara gurin da ta 蓳ata, saida ta maida komai ma hallin sa, sannan ta 蓷akko, lemon da ta ha蓷a, yayi sanyi sosai ta zuba acikin jog wanda yake maha蓷in, flasks 蓷in ne, da 拼an cups 蓷in sa ta 蓷ora saman tire shima takai saman dining table 蓷in,

"Sosai Suhaima ke hidima ta kaca me sai zirga zirga take daga parlour zuwa kitchen ,"

Jin anfara kiran sallar magrib yasa ta fita takoma part 蓷in Hajiya Umma don gabatar da salla, gashi tanaso ta yau da daddare ta koma dajin nan don cigaba da binciken ta,"

_____________________

"Kasa shiga parlourn Baffa Barrister Sulaiman yayi, cikin tashin hankali Yakoma ya shiga mota yanufi house 蓷in su, Shikenan tamu ta茩are A fili ya Fa蓷in hakan tare da dannawa Uncle Mansur Call akaro na biyar baya 蓷agawa,"

Sulaim kai tsaye daga masallaci bayan sun gabatar da sallar magrib suka wuce Part 蓷in sa a mota 蓷aya su ukun, gaba 蓷aya sun gaji so suke su huta, gashi yayi waya da Ummeetha tace masa sunanan tafe Zasu biyu jirgin dare, To yasan dole zasuje suyi musu barka da zuwa,"

"Sosai ya 茩ara ware manyan idanuwan sa don son tabbatarwa shin Part 蓷in nasa ne ko ko, don shi a tunanin sa Part 蓷i Hajiya Umma ne suke tunkara, saboda tsabar dadda蓷an 茩amshin dake dukan hancin sa,"

Saleem ne ya kasa ha茩uri yace, gaskiya inajin wani irin dadda蓷an 茩amshi kuma na abinci, ko dai tsohuwar nance ke girki, amma kuma daga wannan part 蓷in ne",

Kodai yunwa kake ji ne cewar Yarima Sultan,

"A'a amma dai wlh yanzu har nafarajin ta Saleem yafa蓷a dai dai suna tura kai cikin Parlourn 蓷auke da sallama,"

Masha Allah nima naji gaskiya Yarima Sultan ya fa蓷a, tare da kallon Sulaim Aminina Kodai Baffa yayi maka aure ne Bamu saniba don wannan 茩amshin abincin irin na matar gida ne..!!

_F pen_

[01/04, 3:10鈥痯m] Zarah Tymre's Henna: https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group馃憞

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_Typing馃摬_

*_AHALINMU 茒AYA_*

馃挆馃挆馃挆

*_Fatima Y zakariyya馃憣_*

_Tymer's henna_馃拝

*鉁═AURARIN MARUBUTA WRITER'S ASS...鉁煋*

*_T.M.W_鉁嶏笍*





_Sarauniyar馃懜 Taurarin Marubuta writer's鉁嶏笍鉁╛

*_(THE QUEEN馃憫)_*

________Dedicated to anty salma馃拵

*_Part 2_*

(Littafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login