Showing 159001 words to 161316 words out of 161316 words

Chapter 54 - Ahalinmu Daya Book Two Complete Hausa Novel

04 Nov 2025

274

Doesn't say she's cancelling this Marriage, then Surely, she will Regret marrying me_"

"Dafa 茩afa蓷ar shi Sulaim yayi, Yace kayi ha茩uri Saraki Bayayya ga iyaye Dole Na Tabbata Baza suyi komai don su cutar damu ba, ina so kada kayi wani yun茩uri, kami茩a komai ga Allah, zanso kasaki Ranka kayi Farin ciki, Sultana zata iya zama yadda kake so bayan Auren ko, Emm"

"Murmushin ya茩e Sultan yayi, tare da fa蓷i komai Ya wuce Amma dole sai na fara jamata kunne, ta janye maganar auren Da kanta idan ba haka ba zata ga abunda bata so, Yanzu kai ya maganar naka Aure, Har yanzu banga Saleeman ba,

"茒aure Fuska Sulaim yayi Tamau, Nifa ban tsara Wani aure yanzu ba, Inada plan da yawa sai na fara gyara aiki na Sannan komai zaimin dai dai, Ita fa wannan Yarin yar Tanada Damuwa, Ga hayaniya tana son takura min, Ban masan ta yadda zan iya zama da ita ba,

"Idan ka nuna baka so Zata bari, Yarima Sultan yafa蓷a yana kallon sa,

"Oh Matsalar ta ne, Ni ba ruwa na Idan suka ajiye ta ta gaji da zama Dole zata tafi, Saboda bazan ta蓳a iya Cutar da jinin Uncle Bello ba, kuma 茩anwa ga, Saleem 蓷ina" Kawai bana son wani Aure gaba 蓷aya yanzu, ba da ita ba koma da wace,

A haka Suka Cigaba da Hirar su Cikin nuna Kulawa da damuwar Juna, Daga yadda Suke Maganganun zaka fahimci Gaba 蓷ayan su basa Son auren, Sai da Dare ya raba sosai har lokacin, Samrat da Sajad basu dawo ba,

Tunda ga Wannan rana Kullum Sulaim da Suhaima sai sun ha蓷u a wannan Garden 蓷in, Dama Sulaim, Yana Son ka蓷ai cewa shi ka蓷ai Duk lokacin da yake ba茩atar hakan wannan Garden 蓷in ne wajan zuwan sa, Sai Allah yasa wa Son Gurin Itama Kullum idan bata jeba Sai taji duk babu da蓷i,

Wata rana ya riga ta zuwa wata rana ta riga shi zuwa, Basa kula juna wata rana kuma sukan yi magana jefe jefe, Har sai ran kowa ya 蓳aci acikin su, Sulaim yarasa dalilin 茒aya sa ta shike son shiga rayuwar sa, ita kuma ta rasa dalilin daya Kullum yake Bibiyar ta,

***Niko Nace Lallai Suhaima Sannu da 茩o茩ari kizo har part 蓷in Mutum Kuma ki ringa tunanin ya na bibiyar ki馃槀***

~ Barrister Sulaiman ~

"Haba Beb dan Allah kiyi ha茩uri yanzu idan kika tafi ina zakije Nace miki fa, Ana 蓷aura aure na da Sabrina zan mai dake gida Sannan babu wanda ya isa ya hana ni zama dake Tunda a yanzu kin zama mallaki na,"

Cikin Zafin rai, khaltum ta Fizge hannun ta, cikin Kuka ta furta, Gaskiya Nidai ka mai dani ko kabar ni natafi yau kusan Tsawon Wata guda Ina cikin wannan 茩aton gidan ni ka蓷ai wata rana Ka kwana wata rana kabar ni ni ka蓷ai, ina kake so na tsoma raina Karaba ni da 拼ar uwa ta yanzu nasan kullum cikin ne mana take don baza ta ta蓳a gajiya ba, Tunda mun riga munyi Aure kawai mu koma, cikin Kuka Mai sauti takai 茩arshan maganar,

"Oh my god, Beb Kiyi shiru kukan ki na tadamin hankali kinsan ina son ki, Zama mu koma Soon Bawani long time NE ba, ko two weeks bazai kai ba, kuma ina tare dake, yanzu idan muka je ke a matsayin mata ta, akwai damuwa ne,

Yanzu kin ha茩ura ko? Zan siya miki duk abunda kike so ko Meye shi matu茩ar da ku蓷i ake siya,

Da sauri Khaltum ta goge hawayen idon ta tare da washe baki, To Shikenan na ha茩ura amma yanzu ka kaini inda mukaje ran nan 蓷in nan,

Murmushi Barrister Sulaiman yayi don ya gane inda take nufi, Gaba 蓷aya yagama gano Khaltum Indai da abun duniya to tabbas mantawa take da komai, amma shi son gaskiya yake yi mata,

"Yauwa yanzu naji kince na Rabaki da 拼ar uwar ki, Dama kina da 拼ar uwa a cikin Estate 蓷in mu?

"Cikin dabir dabir tace, A'a Kawai ba ru蓷e ne shiya Amma bani da kowa, Maganar Suhaima ce ta dawo mata cikin kai, wanda tace mata katta sake ta bari wani yasan su biyu ne,

"茒aga 茩afa 蓷aya yayi tare da ta蓳a baki, OK yanzu ki shirya sai mu tafi ko?

Tun kafin yagama rufe baki Khaltum ta Nufi bedroom 蓷in ta da gudu, ta fa蓷a toilet, Shikam Murmushi kawai yayi,

~ Suhaima ~

A yau kiran da tayiwa wayar Mother yafi 茒ari, Take tausayin kanta ya kamata, tafara tunanin ta yadda zataje Garin su can Bichi Don Duba halin da mother 蓷in take ciki, Abun ya fara bata tsoro, a iya sanin ta Mother bata kashe wayar ta, Kuma Ta tabbata ba rashin Caji bane, Don Basuda matsalar wuta, Koda matsala ta samu A iya Tsawon Kwanakin nan sana da wata 茒aya ai yaci ace ko gurin masu caji take,

Tuni jikin Suhaima ya bata ba lafiya ba, Khaltum ce ta fa蓷o mata a rai Kasa daure wa tayi Wasu siraran hawaye suka zubo nata, Yanzu Shi kenan na zama ni ka蓷ai, Khaltum ina kika shiga Me yasa zakimin haka Why khaltum, kar kibari Arabamu ina tare dake, Sosai Suhaima tashiga sun bato ita ka蓷ai, daga 茩arshe ta yanke Shawarar Duk yadda zatayi wajan Zuwa Bichi sai tayi don Dubu mother ko zuciyar ta Ta samu salama,

A yanzu ji take komai yazo 茩arshe tagama gano komai da kowa acikin Estate 蓷in jira kawai take lokacin fara gabatar da hukunci yayi, kuma bata son fara ai wayar da komai Sai ta fara fa蓷a wa mother,"

*BARNO STATE*

_Masarautar Gabas_

Gaba 蓷aya hankalin kowa dake cikin Masarautar, Ya koma Gurin shirye shiryen biki Sosai kowa ne 蓳angare an kaca me da hidima, ko wane sashe da irin shirye shiryen da Suke,

Gaba 蓷aya hankalin kowa ya koma gurin shagalin Bikin Yarima Sultan da gimbiya Sultana, Yarima Safwan da Gimbiya Shaheeda,

Mai Martaba yabada umarnin A fa蓷awa Ummu Mu'azzam Mahaifiyar Su Gimbiya shaheedah, An bata izinin halartar bikin 拼ar ta, Amma baza ta wuce kwana uku ba, lokacin da sa茩on ya risketa Ba laifi taji da蓷in hakan, Tunda batasa rai da wannan alfarmar ba, Itako Gimbiya Shaheeda sosai tayi ba茩in ciki Ace wai Mahaifiyar ta Sai an bata izinin Zuwa shagalin Auran ta kuma shima sai an 茩a'ide mata kwanankin da zata yi,

Ji tayi ai kodan wannan wula茩ancin sai tasan yadda tayi Mulki ya dawo hannu yayan ta mu'azzam kodan jin da蓷in Mahaifiyar ta,

Yanzu kowa ya ajiye baton duk wani 茩ulli da makirci da wani da maganar mulki, bawai don abun baya ransu ba, kowa da abunda yake shiryawa, Sai zuwa bayan biki a 蓷ora sabon lale daga inda aka tsaya, ko wane mugu ya adana muguntar sa har zuwa a gama gaba 蓷aya hidimar,

Yarima Sultan ne, Zaune a Babban Parlourn Galadima Murtala na sau茩ar ba茩i, Ancika gaban shi da nau'i Nau'in abinci kala kala, da kwandon kayan Mar'mari, Wanda aka lullu蓳e shi da Lallausan yadin karan miski,

Daga ni kasan hankalin sa na wani gurin, Fuskar shi, Babu alamar wasa Ya ha蓷e cikin Shigar Sarakai ba 茩aramin kyau yayi ba, A gogon dake 蓷aure a wrist 蓷in sa yaduba, tare da sakin siririn tsaki,

Cikin Taku izza da isa Gimbiya Sultana ke taka wa taci ado Sosai Tayi kyau sai dai sai dai Tufafin da tasa Sam bai hau da Kwalliyar taba, Bayan ta kuyan gine guda biyu, A dai dai 茩ofar shiga Parlourn suka ja suka tsaya, ita kuma ta tura kai ciki, Bakin ta 蓷auke da Sallama, Fuskar ta 蓷auke da Annurin ganin Abun 茩aunar ta,

Ciki Ciki Sultan ya Amsa Sallamar, Wanda badon, Bakin shi da taga ya motsaba da sai tace bai Amsa ba,

"Barka da Warhaka Yarima na Allah yasa kana cikin Aminci"

"Lokacin da na 茒ibar miki ya 茩are, Sai kuma wani lokacin Yarima Sultan ya fa蓷a yana mi茩ewa tsaye,

"Da sauri Sultana ta Mi茩e itama, Haba Yarima Na kofa magana baka bani damar yi ba,

"Kin za蓳i Aure na ko? To ki蓷au mata kan zama dani, Amma a yanzu lokacin ki ya茩are, yana kaiwa nan ya fara taka wa A hankali, sai kuma ya tsaya cak, ba tare da ya juya ba yace,"Haryan zu kina da za蓳i, da Sauran Dama, ki janye Aure na ko, ki Barshi wannan ba matsala ta bace, da hanzari ya 茩ara sa fita daga Parlourn, Fadawan sa suka rufa masa baya,

Har ya 蓷au tsawon lokaci da fita, Sultana bata daina kallon 茩ofar ba, Can kuma ta Du茩ushe Saman Gwaiwar ta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,

Ummul Bait Kallon Sultan tayi, Tace Yarima Kafara bujerewa magana ta ko?

"Cikin Sauri Yarima Sultan yace, tuba nake Amin Afuwa, Bana fatan Allah yanuna min Ranar da zan koda 茩in sauraron ku bare na bujerewa maganar ku,

"Ameen, Amma ai nace kaje Gurin Sultana ku tattauna, Kaji ko tana da bu茩atar wani abu ko?

"Allah ya temaki ke daga can nake, na baro ta cikin Aminci,

"Masha Allah Amma kayi Sauri, Akwai wani Sa茩o da ya iso Bayan Fitar ka,

"Allah ya 茩ara miki Lafiya, Yarima zai so sanin daga ina sa茩on yake,

"Sulaim ne Ya aiko, Zuwa ga Amaryar Yarima Zaka iya zuwa ka duba,

Shiru Yarima Sultan yayi yana mamakin Jin sa茩o daga Aminin sa kuma Ta hannun Ummul Bait Sannan zuwa ga Amaryar ta, Me hakan ke nufi? Take yayi wa kansa Tambayar, Yaushe Aminina yazama Mara kirki yanzu goyan bayan Auren nan yake kenan!? Wallahi sai na rama,

"Allah yasa Yarima yana lafiya, Tunanin Meye kake?

"Murmushi ya 茩ir茩iro tare da Fa蓷in, Alhamdulillah Ummee, ina lafiya,

"To zaka iya tafiya, sai ka duba sa茩on Meye, Da'alama kaya ne,

"To na barku lafiya ya fa蓷a tare da fice wa yanufi Part 蓷in sa yana tunanin, irin Rashin mutumcin da zai wa Sulaim tun a waya kafin su ha蓷u, saboda dama sun tsara A Kano za suyi Walima,

~ Suhaima ~

Zaune take inda tasa ba zama, a kowa ne dare, Sulaim na tsaye daga gefe kamar dole hannun sa ru茩e da Cup mai 蓷auke da Black Tea aciki, Kallon gefan ido Sulaim yayi mata Ganin ta zubawa Guri 蓷aya ido ne yasa shi kai nashi idon gurin,

"Suhaima ce tace, Bana son a tsaya min akai, Naji da蓷i zaka zama Ango jibi, ka daina zuwa inda nake,

Duban ta Sulaim yayi sosai, Amma dai kamar kinada Ta蓳in Hankali, ko kin manta nan 蓷in Mallaki nane, kin takuramin kin shiga rayuwa ta, ina so dama in sanar miki, Da zarar angama Wannan Bikin Zanyi maganin ki,

"Suhaima tace, Wani lokacin kamar ba kai ba, Saboda kana da abun dariya, Ba mamaki inada Ta蓳in hankali, Amma koda nan 蓷in yake mallakin ka, tunda kaga ina zuwa sai ka hu茩ura saboda akwai abunda nake yi anan 蓷in, Amma kada kadamu kan ka dan baza ka ta蓳a sanin ko Meye ba, Sannan kamar yadda kake jira agama biki kayi magani na, nima hakan kawai nake jira"

"kamar yadda kike zuwa nan saboda wani abu nima Ina da nawa dalilin, Wanda bazai sa saboda ke na bari ba, idan kina bu茩atar ka蓷ai cewa to ki canza guri, Dama irin ku marasa gaskiya ai dole su runga zama su ka蓷ai, Bansan dalilin daya sa baffa ya yadda dake ba, Yakai 茩arshan maganar yana kai cup 蓷in Black tea 蓷in bakin Sa,

"A 蓷an zabure Suhaima ta furta, Inna lillahi wa inna ilaihi raji un, wanda yayi dai dai da Shima Sulaim ya furta, Ya rabb me wannan yana kallon sama,

"Wannan shi ne karo na biyu da Suhaima ta kalli Sulaim sosai, Cikin yanayin mamaki ta Furta, Shin Dama kaima kana ganin abunda nake gani anan,?

"Kema kina gani?Shima da mamaki ya tambaye ta,

茒aga masa kai tayi alamar eh, Harcikin zuciyar ta tana 茩ara tsinkewa da Al'amarin, Ta ta蓳a tambayar Princess ko tana ganin abunda take gani a gurin Tace mata, A'a Suhaiman ta 茩ara nuna mata Amma tace ba abunda taganin, har mata so mai da Suhaiman mahaukaci ya,

Shima Sulaim mamaki yake taya akai Suhaima ke ganin abunda Ya tabbatarwa kansa shi ka蓷ai ke ganin sa, Tun yana 茩arami acikin Estate 蓷in, A kwai lokacin da ya ta蓳a fa蓷a wa baffa, Suka zo tare Baffa baiga komai ba, Sai sukai tunanin wai aljanune suka bu蓷e masa ido, Ya茩ara tambayar Sultan still amsar 蓷aya ce babu abunda shima ya gani, Tunda ga lokacin ya tabbatar wa kansa shi ka蓷ai ke ganin Abun,

Tabbas akwai wani abu a 茩asa, Suhaima tafa蓷a tana kallon Sulaim shima ita yake kallo..!!!

ALHAMDULILLAH!

ALHAMDULILLAHI!!

ALHAMDULILLAHI!!!

*_Anan ne nakawo 茩arshen Littafin AHALINMU 茒AYA BOOK 2 sai mun ha蓷u acikin AHALIN MU 茒AYA Takun 茦arshe Insha Allah, ina ro茩on Allah S.W.T Yasa damu da Alkhairan sa, Allah ka ha蓷a mu aladan, kuskuran dana aikata acikin wannan littafi Allah kaya femin_*,

*Kuci gaba da bibiyar, Al茩alamin Fatima Y zakariyya (Tymer's Henna)鉁嶏笍 don samun da 蓷a蓷an littattafan Hausa novels馃摎*

_茦ir茩irarran labari ne, idan wani ko wata yaji yayi dai dai da rayuwar sa ko wani labarin to, Arashi akasamun, Kuskurana da zaku tsinta aciki kuyi watsi dashi saboda nima 拼ar Adam ce kamar kowa zanyi kuskure zan aikata dai dai,_

*_Godiya ta musamman gare ku Masoya na Alkhaerin Allah yakaimu ku a duk inda kuke a Fa蓷in duniya, Allah ya faran tamuku ya albarkaci rayuwar mu baki 蓷aya, Allah ya sakawa iyayen mu da Mafificin alkhaeri, Ka gafar ta musu, kabiya su da aljannah ma 蓷aukakiya馃げ馃げ馃げ_*

*NOTE! NOTE!! NOTE!!!*

_Gamasu 茦orafi ko shawara, 茩ofa a bo蓷e take, zaku iya nemana ta wannan number 蓷in 08141825210 WhatsApp only,_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login