Showing 27001 words to 30000 words out of 88290 words
Chapter 10 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
jin kunya ta fa, yanzu ke ko a jikinki ki tsaya haka a gabana”
“dan mi zanji kunyarki,ni bana jin kunyar kowa”
“dama taya za kiji kunya bayan wannan tsinannun na maki wanka har yanzu” ta faɗa yayin da take zame hannunta daga saman idanunta
ƴar dariya Nailar ta saki “Aunty sopi wai har yanzu baki daina jin haushin Lara da Lolah ba”
“taya zan daina jin haushin su,wasu ƙatti da su kamar ƴan dambe kullum suna gane man jikin baby” ta faɗa tana tsuke fuska
tsawan shekaru abun na cimata tuwo a ƙwarya dan dai kawai bata da yanda za tayi,da tana iya hana Nailar wankan da aike mata da tuni ta hana hatta masu aikinta haushin yanda Nailar ta sakar masu komai na rayuwarta take ji ,ace comon sutura su za su cire su sa mata.
“zaki fara ƴan tunane tunanen naki ko,su fa basa da laifi,nice mai laifi sai dai idan ni zaki hukunta”
“zan hukuntaki ne mana idan har baki daina wannan san jikin hanzarce ba”
“shikenan yanzu tunda kin korar mansu sai ki ƙarasa aikin na su”
dungure mata kai Aunty Sophia tayi tana ɗaukar rigar da zata sa,ɗan sosa in da ta dungureta tayi “ karfa garin wannan fushin naki ki ɓata man gyaran kai na”
zura mata rigar Aunty Sophia tayi,ta zage mata zip,kallon yanda rigar tayi mata tayi a mirror
“yanzu haka zaki je maza suyi ta kallon jikin ki”
“iya kar su kallon,kuma ma Ni da nake zaune a office ina ruwana da su”
“kafin ki shiga office ɗin maza nawa zasu kalle ki musamman wannan ƴan iskan security guard ɗin naki masu fuskar sheɗanu”
“to yanzu wane kaya ki ke so na sa?”
Na jikinta ta nuna mata dariya Nailar ta saki “ kina so ajina ya zuba ko,ace na zama tsohuwa”
“zaki zama tsohuwar ne mara kunya” murmushi kawai Nailar ta saki,idan har kaji dariyar Nailar to tana tare da Aunty Sophia ko momyn ta,Aunty Sophia baturiya ce amma ɗabi'unta sun banbanta dana turawa.
sun ɗan ɗauki tsawan lokacin wajen shiryawa,ba ƙaramin kyau Nailar tayi ba kamar ka saceta ka guda,sosai rigar tabi shape ɗin jikinta,ƴar pose Aunty Sophia ta ɗauko mata tare da sunglasses mai shegen kyau pose ɗin taji adon stones multicolors sai ɗaukar ido take,wata ƴar locker Nailar ta nufa,ɗan duƙawa tayi saitin wata ƴar na'ura dake jikin locker ɗin,idanunta ta saita a jikin na'urar da alama Eye ID ne a jikin ƙofar,nan take ƙofar ta buɗe,ƙananan bindigu ne a ciki nau'i daban daban tare da bullet ɗin su,watama idan ka ganta zaka ɗauka lipstick ne,ɗaya daga cikin su ta ciro.
bullet ta ɗauka guda biyar ta zuba a ciki kafin ta ɗaga rigar dake jikinta,wani ɗan belt dake jikin boyshorts ɗin dake jikinta ta saka bindigar da alama anyi shi ne saboda haka.
maida locker tayi ta rufe,juyowa tayi tana kallon Aunty Sophia da tunda ta buɗe locker ta kauda kai,bata ma san ganin abunda ke ciki, murmushi Nailar ta saki tana ƙarasowa inda take.
A tare su ka fice daga ɗakin Aunty Sophia na faɗin ji take kamar kar Nailar ta fita Ita kuwa sai sakar mata murmushi take.
A parlor su ka samu masu aikinta su biyu na jiran su kowacce su ta ɗauki wankan suit black color,tunda su ka fito Aunty Sophia ke banka masu harara sai kace sune za fita da Nailar ba ita bace zata fita da su ba.
Elevator su ka shiga ta kai su a salin main parlor gidan wanda in ka shigo dashi zaka fara cin karo.
main entrance ɗin gidan su ka nufa,yanzu ma sai da ƙofar tayi scanning fuskar Nailar kafin su ka fice harda Aunty Sophia.
Harabar gidan ƙwanyar take da haske kamar da rana,motocin ne guda biyar a bakin ƙofar fitowa,huɗu baƙaƙe ne ƙirar HYUNDAI yayin da ɗayar ta kasance fara ƙirar Mercedes benz s class a tsakiyar su.
rissinawa security guard da masu aikin dake yawo jefi jefi su kayi suna gaishe da Nailar da Aunty Sophia,cikin kulawa Aunty Sophia ke amsa masu.
har gaban Mercedes benz ɗin Aunty Sophia ta raka Nailar,da kanta ta buɗe mata door ɗin ta shiga tana mata fatan dawowa lafiya,kissing hannunta Nailar tayi tana faɗin saina dawo,a dawo lafiya Aunty Sophia ta faɗa tana rufe mata marfin motar.
Motocin security guard ɗin su ka shiga tare da masu Aikin Nailar,Aunty Sophia na nan tsaye har su ka nufi gate ɗin gidan,sai da taga bata ganinsu tukunna ta koma ciki,ranta duk a jagule, ji take inama zata iya hana Nailar fita.
_*HEART OF VEGAS CLUB AND CASINO*_
Tun daga nesa zaka fara hangen hasken sparkling bulbs na haska saman building ɗin in da aka rubuta _* heart of Vegas club and casino*_ da wani irin style.
Tsarin ginin building ɗin ma kawai abun kallo ne,
A katafaren parking lot na club ɗin da ya ciki da tarin rides masu shegen kyau da tsada su kayi parking a wajen parking ɗin motocinta wanda ya kasance nata ne ita kaɗai su ka nufa.
Dai dai ta parking ɗin su su kayi, security guard ɗinta ne su ka fara fitowa tare da masu aikinta,ɗaya daga cikin su ne yazo ya buɗe mata marfin motar.
A hankali ta zuro ƙafafunta,kafin ta ƙarasa fitowa,gaba tayi suna biye da ita a baya,da wasu jibga jibgan security guard dake sanye cikin baƙaƙen kaya ƙugunsu soke da bindigu su ka ci karo a bakin entrance ɗin shiga,tun kafin ta ƙaraso su ka bata hanya suna ɗan rissanar da kansu Alamar gaisuwa,ko kallon in da suke ba tayi ba ta nufi security door ɗin shiga.
Wata irin katafariyar ƙofa ce wacce kai daga ganinta kasan ba ƙaramin waje bane,ƙofarce ta fara magana cikin harshen turanci
“welcome to Heart of Vegas,ur Access card please” da sauri ɗaya daga cikin masu aikin ta ciro wani ɗan card a pose ɗin Nailar dake hannunta ta mannashi a jikin ƙofar.
dan da nan ƙofar tayi acknowledging card ɗin tana faɗin“welcome miss Nailar”
nan take ƙofar ta shiga zugewa,ciki ta kunna kai suna biye da ita.
wani irin katafaren club ne su ka shigo,yaji kayan alatu kamar baza'a mutu ba,yana yin tsarinshi yasha ban ban da sauran clubs.
mata ne a tsaye a stage strippers cikin wata irin shaiɗaniyar sutura suna poll dance sauti na tashi,ga mata ga maza wasu a zaune wasu a tsaye suna taka rawa ana spraying dollars,wasu na shan giya,wasu na shaƙar cocaine,ga customize azul na yawo ta ko’ina ana kaiwa wayanda sukai order, gawasu kalan shisha da a irin wannan club ɗin kaɗai ake samun su, ga vape anasha suma,idan kashigo club din nan kai kanka kasan ana barin kuɗi, ga wasu irin security guards dake a different corner tsaitsaye da communicative devices a kunnensu kai kace gumaka ne yanda suka tsaya kiƙam ko alamar breath babu.
Kiɗan dake tashi ne ya tsaya,Dj ne ya shiga sanar da zuwan Nailar hakan yasa mutanen dake ciki kai duban su gareta,ihu da sowa ne ya fara tashi wasu na ambatar Queen wasu President,ƙayataccen murmushi ta saki tana ɗaga masu hannu,gun gun wasu maza ne su ka nufo in da take sai tangaɗi suke alamar sun sha sun sha sunyi tatul,da sauri security guard ɗinta su ka dakatar da su, murmushi gefen fuska ta saki tana yarfa masu ƴan yatsunta haɗi da ɗan cizon ƙasan lips ɗinta so sexy,ba ƙaramin jan hankalin mazan dake wurin tayi ba harda ma mata,ca su ka yi mata da idanu kamar tsaffin mayu ga nama suna kallo amma ba halin tunkara.
fly kiss ta sakar masu tana nufar glass elevator dake cikin wurin, security guard ɗin ta na biye da ita.
Wani irin ƙato casino su ka shigo,yaji kayan alatu a cikin uwar dukiya a ka narkar wajen gidana shi ba kaɗan ba ,da kaɗan ne bai ƙarasa girman club ɗin da su ka fara shigowa ba.
Wani irin casino Aesthetic ne mai matuƙar ɗaukar ido,ga wasu matsiyatan poker tables and gaming table haɗe da chairs ɗin su,casino cards ne a kowane table,a ƙalla ko wane table na ɗauke da chairs guda biyar.
Mata da maza ne zazzaune saman chairs ɗin, casino cards ne a gabansu suna buga caca ga tarin dollers da kowane a cikin ya ajiye a matsayin kuɗin wasan shi, nau'in beers ne masu tsadar gaske haɗe cigarettes wanda tsadar su ta kai mutum ya sayi gida da mota na mutunci a gaban su,wasu na shan giya wasu na zuƙar taba ana buga wasa kiɗa na tashi ƙasa ƙasa.
nan ma security guard ne a kowane corner tsaye ƙiƙam.
murmushi Nailar ta saki ganin yanda ake buga wasan,fito tayi wanda ya jawo hankalin mutanen dake wurin,ihu mazan dake wurin su ka saka suna faɗin QUEEN!!!!
dariya Nailar ta saki tana ɗaga masu hannu,wani ɗan corridor ta nufa,shuffle machines ne haɗe da slot machines, video poker and video lottery terminals a wajen, ma'aikata ne zaune saman poker chairs suna opreting ɗin su.
cikin girmamawa su ka shiga gaishe da ita kamar za su russuna mata,jin jina masu kai ta shiga yi, office ɗin ta ta nufa dake can floor ɗin ƙarshe,a bakin ƙofar shiga office ɗin security guard ɗinta suka tsaya masu aikin su ka bi bayanta.
wasu numbobi ta danna a jikin ƙofar nan take ƙofar ta buɗe,kutsa kai tayi ciki jelarta na biye da ita,wani irin katafaren office su ka shigo kamar na shugaban ƙasa,ga sanyin AC dake busowa kamar ƙanƙara,ƙaton transparent glass office table ne a ciki haɗe leather chair mai shegen kyau,laptop ce ajiye saman table ɗin haɗe office lamp,daga gefe 50gm ne na cocaine anyi packaging ɗin su sai Cuba Aliados cigarettes dake a cikin ƙana nan kwalayenta itama anyi packaging ɗinta sai kwalaben shisha nau'i daban daban masu tsadar gaske,ga ɗan madaidaicin bottle keeper wanda aka jera kwalabanan beers kala daban daban.
daga can gefe poker table ne wanda ke ɗauke da casino cards,sai faskekiyar glass computer dake ajiye anyi connecting ɗin ta da gaba ɗaya CCTV CAMERAS dake heart of Vegas.
Cikin office ɗin su ka ƙarasa,chair ɗinta ta nufa ta zauna yayin da masu aikin suka nufi wasu sofas guda biyu su ka zauna, laptop ɗin dake ajiye saman table ɗin ta buɗe,opreting ɗinta ta shiga yi a hankali.
Muryar na'urace ta karaɗe office ɗin tana sanar da zuwan MDs na gaba ɗaya club da casino ɗin, izinin shigowa ta ba da ta hanyar danna wani maddani a jikin table ɗin,a hankali ƙofar ta shiga zugewa,wasu murɗa murɗan ƙatti ne majiya ƙarfi su ka shigo cikin shigar baƙaƙen suit,gaban table ɗin Nailar su ka ƙara so.
gaishe da ita su kayi suna russunawa,amsa masu tayi tana nuna masu kujerun dake facing ɗinta,zama su kayi saman kujerun.
“is there any problem?”
“no ma,but kayan da Boss ta turo suna hanya,muna sa ran isowar su next tommorow around 2:00Am”
jinjina kai Nailair tayi“good,bayan nan babu komai?”
“yes”
“ok,take this” ta faɗa tana nuna masu packeg ɗin cocaine da cigarettes,miƙewa tsaye su kayi,ɗaukar kayan su kayi suna mata sallama haɗi da ficewa.
tura kujeran da take zaune tayi,ƙafafunta ta ɗaura saman table ɗin tana jinginar da kanta saman head ɗin kujerar,ɗaya daga cikin masu aikin ce ta miƙe,can cikin office ɗin ta nufa,bata jima a sai gata ta fito hannunta ɗauke da ƙatuwar kwalbar champagne haɗe da champagne tulip glass sai ice a cikin bowl,har gaban table ɗin Nailar ta ƙaraso,ajiyewa tayi,ice ɗin ta fara zubawa a cikin cup kafin ta buɗe kwalbar, tsiyaya mata tayi cikin cup ɗin ta miƙa mata,amsa tayi tana wani lumshe ido.
barin wajen tayi,komawa tayi ta ɗauko masu milkshakes guda biyu,duk yanda su ke son shan kayan shaye shaye Nailar ta hana sai dai su sha lemu ko milkshake.
wayarta ce ta fara ringing,kallon screen ɗin tayi love shine sunan daya bayyana, murmushi ne ya bayyana a fuskarta, picking call ɗin tayi tana kara wayar a kunne.
“sweetheart” shine sunan da Nailar ta furta,on the other hand murmushi ta cikin wayar ta saki
“baby nah ya ki ke,ya gidan” ɓata fuska Nailar tayi “babu daɗi,yaushe zaki dawo?"
“kinyi kewata ne?”
“i really miss u, please come back home” Nailar ta faɗa kamar zata sa kuka
murmushi ta saki
“i think next week,fatan kina office?”
“momy mai makon ki tambayi lafiyata amma ta office ki ke,wai tsaya dani da wannan business ɗin ma wa ki ka fi so ne?”
“nafi sonki sama da komai, sorry fatan kina lafiya”
“lafiya lau,fatan kema haka”
“ina lafiya kamar yanda ki ke,kina office ɗin?”
ɓata fuska Nailar tayi
“yes,su Joseph sun sanar dani kayan da ki kayi order suna hanya?”
“yes, Please my baby ki kasance a wurin lokacin da shipment ɗin zai ƙaraso bana son any problem ya faru, kaya ne masu tsadar gaske, munada tarin customers a ƙasa wanda zuwan kayan kawai su ke jira”
“please momy,su Joseph za su iya ji da komai ba sai naje ba”
“no kije dai zaifi,zan turo maki komai ta email,ki tabbatar ba wani kuskure”
turo baki Nailar tayi ba tare da tace komai ba da alama ba taji daɗi ba,sallama su kayi, ajiye wayar tayi saman desk tana lumshe ido haɗe da sakin ɗan ƙaramin tsaki.
Sai Around 5:00Am ta koma gida a gajiye,ko kayan dake
jikinta bata cire ba ta faɗa saman bed,ficewa masu aikin su kayi bayan sun ajiye mata bag ɗin ta haɗe da wayarta.
Aunty Sophia da saurinta ta zo amma sai ta tarar tana bacci, murmushi kawai tayi taja mata blanket,kissing forehead ɗinta tayi ta fice daga ɗakin...
_Ep 13_14_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘
______________________________
*ABUJA NIGERIA*
Turus ta tsaya ganin ko kallon dinner ɗin da aka kawo mata ba tayi ba, kallonta ta kai zuwa bed ɗin dake ɗakin, a zaune take ta jingina da head bord ɗin gadon,photon mahaifiyarta tare da mahaifinta ne riƙe a hannunta sai aikin shafawa take yayin da hawaye ke sintiri a fuskarta.
girgiza kai Yumnah tayi yayin da take ƙarasawa bakin bed ɗin, zama tayi kusa da ita tana dafa kafaɗarta,cikin sigar lallashi ta fara magana.
“sister Nainarh na san abun da ciwo, nasan zai ɗauki lokaci kafin zuciyarki ta dake, sai dai ki sani yawan ku ka da sa damuwa a rai bashi ke maganin matsala ba Adu'a itace maganin duk wata matsala, a halin yanzu Adu'arki su ke buƙata sama da komai, in sha Allah komai daran daɗewa gaskiya za tayi halinta, in dai da rai wata rana a gabanki duk wani mai sa hannu a al'amarin zai zo a ƙasƙance dan neman yafiyarki,dan haka ina so ki daina yawan kukan nan da sa damuwa a ranki”
shiru Nainarh tayi tana sauraron Yumnah, hannu Yumnah tasa ta shiga goge mata hawayen dake zuba daga fuskarta tana sake kwantar mata da zuciya.
“kiyi haƙuri kinji,komai zai wuce in sha Allah”
“na kasa mantawa da irin kisan wulaƙancin da a kayi ma mahaifana,a gaban su ka kashe shi amma Court ta ɗaura laifin a kan mahaifiyata ba tare da tausayin halin rasa mijinta da take ciki ba”
“Allah ya fisu Nainarh,duk wani mai sa hannu asirin shi zai tonu,ki kwantar da hankalinki komai zai wuce mahaifiyarki zata dawo gare da izinin Ubangiji,ki daina kuka kinji” jinjina mata kai Nainarh tayi,sosai Yumnah ta shiga kwantar mata da hankali,har ta samu ta ɗan saki jikinta.
*ASO VILLA*
Kyakkyawar matashiyar matace kwance saman makeken gadon ta,daga yanayin yanda numfashinta ke fita zaka fahimci ba ta cikin kwanciyar hankali.
Wani mahaukacin Nocking a kayi ma ƙofar ɗakin wanda yayi sanadiyyar farkawar ta,a firgice ta farka tana ambaton Innalillahi wa Inna Ilaihi rajiun,sake nocking ɗin a kayi kamar za'a ɓalla ƙofar.
Waro kyawawan idonta tayi tana kallon ƙofar gabanta na wani irin lugudan duka, Adu'a ta shiga yi Allah yasa ba shi bane duk da ta san babu wanda zaiyi mata wannan Nocking ɗin a irin wannan lokacin bayan shi.
Wata irin kakkausar murya wacce kenuna mamallakinta a buge yake taji daga bakin ƙofar ɗakin
“KAINART wai uwar mi kike a ciki ne da bazaki zo ki buɗe man ba, wallahi ki ka bari na shigo da kaina sai kin yaba ma aya zaƙinta” ya faɗa yana sake kaima ƙofar wani mahaukacin duka.
hawaye ne su ka wanke fuskarta dama ta san zaiyi wuya ace ba shi bane,ita kam yau ta shiga uku dan daga yanayin muryar shi baya a cikin hayyacinshi,banko ƙofar yayi kamar zai karyata, da gudu ta duro daga saman gado jiki na rawa ta kama handle ɗin ƙofar ta buɗe mashi.
matashin magidanci da aƙalla zai kai kimanin shekaru 32 zuwa da 3 a duniya,baƙaƙen suit ne a jikinshi yayinda hannunshi ke riƙe da ƙatuwar Whiskey , kyakyawane sai dai munanan ɗabi'un shi sun boye kyawun fuskarshi.
cikin ɗakin ya ƙaraso yana huci kamar wani mawuyacin zaki, jifa yayi da kwalbar dake hannunshi ƙasa ta tarwatse sauran ruwan dake ciki ya malale a ƙasa,ja da baya tayi ganin irin kallon ƙasƙancin da yake mata, cikin rawa murya tace
“dan Allah ya Zaabith kayi....” bata ƙarasa ba ya wanketa da lafiyayyun maruka har sau biyu,dan da nan jinta da ganinta su ka ɗauke na wucin gadi taurari ta fara gani suna mata shawagi a cikin idanunta, bata dawo daga hutun marin da yayi mata ba taji saukar belt, dukanta ya shiga yi kamar ya samu jaka.
kuka take tana ambaton “dan Allah ya zaabith kayi haƙuri, na tuba bazan sake ba” ko saurarenta baya yi dukanta kawai yake kamar an aiko shi,bai ƙyaleta ba sai da ya tabbar ya sauya mata kammani tukun ya jefar da belta ɗin ƙasa,wuyan rigarta ya cakumo yana manne bakinshi da nata,kamar zai cire mata baki haka ya shiga kissing ɗinta,cikin rashin imani ya shiga yayyaga suturar dake jikinta, doguwar sumar kanta ya jawo kamar zai cire mata ita yayi jefa da ita saman gadon babu tausayi ko imani ya shiga biyan buƙatar shi da ita, sai da ya tabbar ya kusa kasheta tukun ya ƙyaleta ya miƙe,yana tangaɗi ya nufi wata ƙofa wacce nake kyautata zaton toilet ne.
wani sabon kuka ta saki ta rasa wannan wace irin rayuwa take, ko baiwar da aka siyo ba'a wulaƙantata kamar yanda Zaabith ke mata kuma a haka wai ita ɗin matarshi ce ta sunnah