Showing 54001 words to 57000 words out of 88290 words
Chapter 19 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
shiga ƙirar ACURA RDX black color Aunty Sophia ta rakata,da kanta ta buɗe mata back seat ɗin motar ta shiga ta rufe,ɗaga mata hannu tayi tana juyawa ta koma ciki.
A jere motocin su ka fice daga gidan,babban titin da zai fitar da su gaba ɗaya street ɗin su ka hau,suna karya wata kwana motocin su Joseph suka kunno kai,haɗewa su kayi da nata motocin su ka ɗauki babbar hanyar da zata sada su da ƙaton PORT dake RENO.
Tafiya su kayi mai ɗan nisa tukun su ka iso PORT,ƙaton port ne iya ganinka,ga manya manyan truck dake kai kawo ɗauke da containers,a parking lot ɗin dake port ɗin su kayi parking.
kusan a tare su ka buɗe cars door ɗin su ka fito,motar Nailarh securitys ɗin su ka nufa tare da Joseph,car door su ka buɗe mata ta fito,ya mutse fuska tayi tana kallon port ɗin kafin ta kai dubanta ga Joseph.
“ina containers ɗin su ke ne?” ta faɗa ganin tarin containers dake wurin ga wanda trucks ke ɗawainiyar ɗauka.
“sai mun fara zuwa office ɗin C G tukun”
“ok mi kake jira”
“sorry boss” ya faɗa yana ɗan rissinar da kai haɗi da nufar office ɗin CG ɗin dake cikin port ɗin,tsaki taja tana komawa cikin motar ta zauna,bata rufe door ɗin ba ƙafarta ɗaya a ciki ɗaya a waje.
Bayan kamar 5 minutes Joseph ya dawo tare da wani mutumin dake sanye da uniform white color hannunshi ɗauke da wasu takardu, bayansu matasan samari ne har su shidda suna sanye da overall orange color.
har gaban motar su ka ƙaraso, ƙarasawa Joseph yayi bakin door ɗin motar
“boss ga CBP nan,shine in charge na cargos ɗin”
zame shade ɗin dake fuskarta tayi tana kallon mutumin da tunda Joseph yayi magana yake washe baki
“ƙarasa” Joseph ya faɗa yana nuna mashi bakin door ɗin motar,ƙarasawa mutumin yayi,fuskarshi ɗauke da fara'a ya gaishe da ita cikin girmamawa.
glass ɗinta dake hannunta ta ɗaga mashi alamar amsawa, murmushi ya saki yana jin jina kai, takardun dake hannunshi haɗe pen ya miƙa mata
“CG ya sa hannu sai naki kawai ya rage”
yamutse fuska tayi tana karɓar takardun da yake miƙo mata, sign ta shiga yi a takardun ba tare da ta ko karanta abun da su ka ƙunsa ba.
miƙa mashi tayi tana faɗin “what next?”
“za muje ne kiga kayan”
“ba sai naje ba kawai su ɗauko” ta faɗa
“please madam ganin yanada amfani,kuma zaki shaida adadin containers nawa ne su ka iso”
yamutse fuska tayi tana zuro ƙafarta da nufin fitowa ringing ɗin wayarta ne ya dakatar da ita,jawo wayar tayi tana duba sunan mai kiran nata Sweetheart shine sunan daya bayyana a screen ɗin.
picking call ɗin tayi haɗi da kara wayar a kunnenta,fitowa ta yi su ka nufi cikin inda containers su ke,cike da shagwaɓa take waya da mahaifiyar ta ta data kira dan taji ya abun yake tafiya.
a gaban wani ƙaton container ship dake bakin ruwa, trucks na jidar containers su ka tsaya, Nailarh na can bayan su tana waya,nuna ma Joseph containers ɗin su da trucks su ka ɗauka har guda biyar yayi.
jinjina kai Joseph ɗin yayi
“aikin ka yayi kyau,fatan kayi waya da Madam?”
“eh tun kafin ma ku ƙaraso ta kira ni”
“ok good,muje ko” Joseph ya faɗa yana nufar Nailarh harta kammala wayar.
Juyawa tayi ta koma inda su kayi parking,motar ta shiga security daya buɗe mata ya rufe door ɗin,sallama Joseph yayi ma in charge ɗin ya shige motar shi, a jere su ka fice daga port ɗin trucks ɗin containers ɗin su na biye da su...
A jere su ka fice daga port ɗin trucks ɗin containers ɗin su na biye da su, wata hanya su ka ɗauka daban, tafiya su kayi mai ɗan nisa kafin su ka iso wani ƙaton orphanage, daga yana yin ginin zaka san cewa bana ƙana nan mutane bane,yanada girma sosai.
horn su kayi a bakin gate ɗin, can cikin bacci masu gadin orphanage ɗin su ka ji ƙarar horn ɗin, ba suyi mamakin jin horn da tsohun dare nan ba saboda mamallakan orphanage ɗin sun saba yi masu shigar dare irin haka.
ɗaya daga cikin securitys ɗin ne ya leƙo ta ƴar ƙofar dake jikin gate ɗin,kallo ɗaya yayi ma motocin ya fahimci ko su waye, a hanzarce ya koma ciki, gate ɗin ne ya shiga zugewa zuwa gefe guda, da gudu motocin su ka danna kai zuwa cikin orphanage ɗin,da sauri securitys ɗin su ka shiga motocin dake bakin gate ɗin su ka bi bayan motocin.
wasu irin gine gine na zamani su ka shiga wucewa ba laifi Orphanage ɗin yanada girma sosai, a bakin wasu manya manyan store har guda biyar su ka yi parking,fitowa su ka shiga yi daga cikin motocin su, wani matashin saurayi ne ya fito daga motar Joseph tun ɗazu sai yanzu ya fito,black American ne, neck ɗin shi yasha zanen tattoo kallo ɗaya zaka mashi ka gane riƙaƙen ɗan duniya ne.
motar da Nailarh ke ciki Joseph ya nufo, back seat ya buɗe mata, fitowa tayi a dai dai lokacin da securitys ɗin ke ƙarasowa, da sauri su ka nufeta, gaishe da ita su ka shigayi cikin girmamawa, ko arziƙin kallo basu samu daga gareta ba, trucks ɗin ta nufa umarnin a buɗe su ta bada,fitowa drivers ɗin su ka shigayi,kowace truk mutum uku ne su ka fito daga cikinta, babu ɓata lokaci su ka shiga buɗe bayan truck ɗin, wasu irin tarin kwalaye ne a bayan truck ɗin, da hannu tayima Joseph alama da ya zo, da sauri ya nufo in da take, wayarta ta miƙa mashi,da sauri yasa hannu ya amsa,video ya shiga ɗaukar kayan.
truck ɗayace ba'a buɗe ba kallon drivers ɗin tayi “wannan fa?” ta tambaya tana nuna masu truck ɗin, Joseph ne yayi saurin faɗin
“ina tunanin itace wacce madam tace kar a shiga da ita”
cike da bada umarni ta furta “ku buɗeta” da sauri Joseph yace “ba kuji ana magana” a hanzarce su ka shiga buɗe truck ɗin, wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi a lokacin da tayi arba da abunda batayi tunanin gani ba, da tsantsar mamaki take kallon matasan ƴan mata da samari dake bayan truck ɗin an rufe masu bakunansu yayinda hannayen su ke a ɗaure.
da sauri Joseph ya sauke wayar ƙasa, da mugum mamaki tashiga kallon drivers ɗin kafinta sauke idanunta akan Joseph, cike da tuhuma ta furta“miye wannan?”babu wanda ya iya buɗe baki a cikin su ya bata amsa, suma sun shiga ruɗan, sunyi matuƙar mamakin ganin yaran, wata irin gigitacciyar tsawa ta daka masu kamar ba Nailarh ba.
“tambayar ku nake miye wannan, ina aka samu wannan yaran??”
ɗaya daga cikin drivers ɗin ne yayi ƙarfin halin bata amsa “mu ma bamu sani ba kawai dai mun samu truk ɗin a cikin jadawalin da miss m...“ kasa ƙarasawa yayi saboda tsawar data daka mashi, bashi da tayima tsawar ba hatta Joseph sai da ƴan hanjin cikinsa su ka kaɗa.
gaba ɗaya fuskarta ta rikiɗe da tsantsar ɓacin rai, a fusace ta buɗe baki da nufin magana amma sai ringing ɗin wayarta ya dakatar da ita, da saurin Joseph ya miƙa mata wayar, picking call ɗin tayi ba tare da ta ko duba sunan mai kiran nata ba.
muryar mahaifiyarta ce ta daki dodon kunnenta daga cikin wayar “hello baby har kun kammala” saurin maida kiran tayi zuwa video call, back camera ta kunna ta saita wayar dai dai inda truck ɗin take.
“momy wannan container ta waye?” ta faɗa ranta a matuƙar ɓace, a kwance take saman hammock chair a bakin beach daga Ita sai bra da wani matsiyacin pant mai igiya gefe da gefe kusan rabin mazaunanta a waje,ta rufe idonta da baƙin shade hannunta a riƙe da coconut drink tana sha.
cike da bariki irin bata fahimci mi Nailarh take nufi ba tace “wace container baby?”
“wacce idanunki su ka nuna maki” ta bata amsa dai dai da tambayarta dan ba ƙaramin ɓaci ranta yayi da ganin yaran ba.
“sorry baby na manta banyi maki bayani ba,marayu ne basu da gata, gashi suna fama da wata lalura na turo su nan ne saboda suna buƙatar emergency treatment”
maida front camera tayi tana jifar mahaifiyarta ta da wani kallon rainin wayao
“amma momy kwata kwata yaran nan basuyi kama da patient ba kama suke da wanda a kayi kidnapping, momy ina ki ka samo yaran nan?” ta kai ƙarshen maganar babu alamun wasa
“baby kin fi kowa sanin mahaifiyarki ko dabba bazata iya sacewa ba bare mutum, ki yarda da ni yaran nan taimakonsu kawai nake son yi”
“idan taimakonsu ki ke son yi mi yasa baki turosu a Flight ba amma ki ka turo su a container bakunan su a rufe,mi hakan yake nufi?”
“ki yarda da ni baby taimakonsu nayi” ta faɗa cike da shagwaɓa kamar bada ƴarta take magana ba
“gaskiya banji daɗin yanda ki ka sa aka ɗaure su ba,kamar wasu dabbobi”
“sorry baby na amshi laifin hakan bazai sake faruwa ba, sorry” ta faɗa tana ɗan kama kunnenta, tsaki Nailarh taja tana rejecting kiran.
umarni ta bada akan su fito da yaran bayan ta tura securitys ɗin orphanage ɗin sun kira doctors ɗin dake hospital ɗin orphanage ɗin, ɗaya bayan ɗaya su ka shiga fito da yaran sai layi su ke kamar za su kifa ƙasa da alama wani abun aka basu wanda ya gusar masu da hankalin su.
doctors da nurses dake ɗauke da stretcher ( gadon ɗaukar marasa lafiya) su ka ƙaraso wasu sun su sai hamma suke da alama daga bacci su ke, cike da girmamawa su ka shiga gaishe da Nailarh bata wani amsa masu ba ta bada umarnin a ɗauki yaran, babu ɓata lokaci su ka shiga ɗaukar yaran a gadon ɗaukar marasa lafiya suna nufar hospital ɗin, bayan su Nailarh tabi, ganin haka ne yasa Joseph bin bayan su.
cikin gaggawa likitocin su ka shiga ba yaran emergency treatment dan ganin sun dawo cikin hayyacin su, sun shafe awanni da yawa suna abu ɗaya sai da ƙyar su ka samu yaran suka farfaɗo amma sun gagara gane taƙamaimai abunda ke damun yaran.
kallon Nailar dake zaune saman waiting chair Joseph yayi, idanunta a lumshe bacci ne sosai a idonta amma saboda san ta san mike damun yaran taƙi tafiya gida, cike da tausasa murya joseph yace “boss ya kamata ki tafi gida ki huta”
“bazan tafi ba sai na san abunda ke damun yaran nan”
“am sorry boss, da dai kin tafi har yanzu bincike doctors ke yi kuma na san idan suka gama bincike har gida za su kawo maki result ɗin”
“kana ba kanka wahala Joseph babu in da zan tafi bansan abunda ke damunsu ba”
lallashinta ya shiga yi shida securitys ɗin amma babu wanda ta saurara a cikin su sai ma cewa tayi idan ba so suke suyi ta aikin su ba to karsu sake mata magana.
ganin dai da gaske ba amincewa za tayi ba ne yasa Joseph yanke shawarar kiran mahaifiyarta, number mahaifiyarta ya shiga dannanama kira amma ba tayi picking ba, canza akalar kiran yayi ga Aunty sophia, baiwar Allah tunda Nailarh ta fita bata rintsa ba, ta kasa zaune ta kasa tsaye hankalinta duk a tashe yake saboda inda Nailarh ta tafi, kiran Joseph na shiga wayarta har sai da gabanta ya faɗin, jiki na rawa tayi picking ko da ya sanar da ita dalilin kira ba ƙaramin kwanciya hankalin ta yayi ba.
“please bata wayar” ta faɗa, da sauri ya miƙa mata wayar“boss miss sophia na son magana dake” a hankali ta buɗe ido tana jifanshi da harara, saurin sadda kanshi yayi ƙasa, kauda fuska tayi gefe ba tare da ta amshi wayar ba, kara wayar yayi a kunnenshi “taƙi karɓar wayar” ya faɗa
“sata a speaker” shine kawai abunda Aunty sophia ta faɗa,ok ya furta yana sa wayar a speaker
“hello baby kina jina?” Aunty sophia ta faɗa
da wata kalar kasalalliyar muryar ta wanda bacci ke neman fin ƙarfinshi ta furata “Aunty sopei ”
“baby mi yasa baki son ki dawo gidan, kin san yanda hankali na ya tashi da fitar da ki ka yi, tunda ki ka fita ko bacci na kasa yi please ki dawo gida”
“zan dawo Aunty sopei kawai ina son na san abunda ke damun yaran”
“karki damu har gida doctor zai kawo maki result ɗin su kuma nayi maki alƙawarin tare da ni zamu zo duba su idan doctors sun kallama bin cike amma yanzu ki dawo gida”
“shikenan sai na dawo”
“yawwa ko ke fa keda na sanki babu ruwanki da shiga abunda bai shafeki ba?”
“ke ki ka fara koyaman damuwa da damuwar mutane” murmushi Aunty sophia ta saki da alama taji daɗin maganar Nailarh.
“sai kin dawo” da ok ta amsa mata, rejecting kiran Joseph yayi yana sauke ajiyar zuciya, harara Nailarh ta watsa mashi murmushi kawai ya saki, tashi tayi ta leƙa ɗakin da yaran suke kafin ta nufi ƙofar fita,har inda motocin su suke doctors ɗin suka rakata kafin sukayi mata sallama.
a guje motocin su ka fice daga orphanage ɗin, tun a hanya su ka rabu da su Joseph su kuma suka kama hanyar gida, Nailarh bata san sun iso gida ba saboda tun a moto bacci yayi awana gaba da ita, sai da Aunty sophia tasheta tukun ta san sun ƙaraso,fitowa tayi su ka nufi cikin gidan, direct bedroom ɗinta Aunty sophia ta nufa da ita, suna shiga ta faɗa kan bed ko takalman dake ƙafarta bata cire ba.
murmushi kawai Aunty sophia ta saki, da kanta ta shiga rage mata kayana jikinta, rigar suit ɗinta ta zame mata haɗe da earring ɗinta da wristwatch tukun ta zame mata takalman ƙafarta, idanunta ta sauke akan gun ɗin dake suke a ƙugunta har zata wuce sai kuma tasa gefen suit ɗinta ta zame gun ɗin, a cikin rigar ta naɗeta,dressing room ɗinta ta nufa, maida komai tayi a mazauninshi, a saman locker ta ajiye mata gun ɗin saboda bata san password ɗin locker ba kuma Nailar tafi amfani da eye I D, ficewa tayi daga dressing room ɗin ta koma bedroom ɗin, gyara mata kwanciya tayi kafin ta fice daga ɗaki baki ɗaya.
*ABUJA NIGERIA*
Nainarh da yumnah ne suka fito daga bedroom ɗin mom,less ne a jikin yumnah ɗinkin bubu ta yafa mayafi saman kanta yayinda Nainarh ke sanye da riga da skirt na atamfa hijab ne a jikinta saɓanin yumnah dake da gyale, hannunsu riƙe da na su Ammar, Aman da jamala da alama fita za suyi.
Part ɗin dady su ka nufa,da sallama a bakin suka shiga a parlor su ka sameshi shida mamy,ciki suka ƙarasa, kallo ɗaya mamy tayi masu ta ɗauke kai dady kuwa da fara'a sa yake kallon su, a saman rug carpet su ka zauna cike da girmamawa su ka gaishe da su dady kawai ya amsa masu amma mamy yi tayi kamar ma bata san da zaman su a parlorn ba.
“my friends sai ina haka?” dady ya faɗa yana kallon su Ammar, Aman ne ya bashi amsa da
“gidan papah” ɗaure fuska dady yayi “shine za ku fita ba tare da ni ba, kodai mun dai abotar ne ban sani ba?” jamal ne yayi saurin cewa “A'a ka tambayi Aunty Nainarh idan tace aje da kai shikenan” gaba ɗayan su suka kai duban su ga Nainarh da
kwata kwata hankalinta baya kansu tunda su ka shigo idanunta suka sauka akan wani ƙaton photo dake manne a bango,sosai ta shagala da kallon photon, tayi mamakin ranar da su ka shigo bata ganshi ba tunanin ta fara yi to kodai ba'a jima da sashi ba.
ɗan taɓo ta yumnah tayi “dady na magana” da sauri ta kai dubanta ga dady “Aunty Nainarh jamal yace sai kin amince za'a tafi dani, za kuje dani kuwa?” saurin sadda kai ƙasa tayi tana sakin murmushi, murmushi shima dadyn ya saki yana leƙa fuskarta “idan na fahimta wannan shirun alamace ta ba'a zuwa dani” da sauri ta ɗago tana faɗin “A'a dady zamuje da kai”
“wasa nake maku sai kun dawo ina gaishe da mutanen gidan”
tashi yumnah tayi tana kama hannun Nainarh
“za su ji in sha Allah, ku tashi mu tafi”sallama su kayi masu suka fice, taɓe baki mamy tayi tana kallon dady “wai ni kam Janar da sanenka wannan yarinyar take zaune a gidan nan?”
“wace yarinya kenan” dady ya faɗa yana kai duban shi gareta dan bai fahimci akan wa take magana ba
“wacce su ka fita yanzu da yumnah”
“wai kina magana ne akan Nainarh”
“ni ban ma san sunanta ba amma ita nake nufi”
“da sani na take zaune gidan akwai matsala ne?”
“ni gaskiya bana son zamanta a gidan nan”
“miye matsalar ki da zamanta a gidan yarinyar da ba'a kanki take ba”
“kamarya miye matsalata, gidan mijina ne fa,kawai sai mu zuba ma zulaihart ido tayi ta yin abunda taga dama, hakanan zata kwaso mana yarinya idan ta cutar damu fa??” tunda ta fara magana dady ya kafeta da ido tsantsar mamaki ne akan fuskarshi ko miye abun masifa kamar wacce ke jiran mutane
“ni gaskiya bana son zamanta gidan”
“ta kawo duk wanda zata kawo gidan mijinta ne kuma gidan ƴaƴan tanada ƴancin ajiye duk wanda ta so”
“haba Janar wai miyasa kullum kake fifita zulaihart a kaina ne, komai tayi dai dai ne a wajenka amma ni kuskure ɗaya zanyi ka ɗau mataki a kaina” ta faɗa rai a ɓace,mamaki yaƙi ɗaukewa akan fuskar dady lamarin mamy har tsoro yake bashi
“ni gaskiya bana son zamanta a gidan”
“to sai mi dan baki son zamanta a gidan, naga ba'a kanki take ba kuma gida gidana ne kuma ni na amince da zamanta dan haka bana son na sake jin kinyi tari akan Nainarh, idan ba haka ba ranki ne zai ɓaci”
“hakama za kace,kenan Zulaihart tafini?”
rai a ɓace dady yace
“Zulaihart tafiki komai mabaruka, ko ƙafarta baki kama ba, dan Zulaihart ban taɓa bata umarni ta saɓa man ba, Zulaihart bata man rashin kunya kamar yanda ki ke man,Zulaihart bata sa'insa dani,nayi mata cin mutuncin mafi muni a rayuwa amma haka nan tayi haƙuri dani take zaune da ni har kawo yanzu duk da a ƙasarta da Al'adarta bata saba ganin