Showing 33001 words to 36000 words out of 88290 words

Chapter 12 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

413

main entrance ɗin shiga gidan ya Naeem ya nuna ma sojan

“ka sashi frog jump ko sau ɗaya ya tsaya ka kirani”
“ok sir” sojan ya faɗan yana sakin murmushi dama rana irin wanann yake jira saboda yaron ya raina su kwata kwata baya ganin su da ƙima ya raina su.

barin wurin ya Naeem yayi ya nufi motar shi,shiga yayi,key yayi ma motar ya bar wurin.


“amma wallahi second father ya gama dakai FA'IZ,ya rasa wa zai sa ya hukunta ka sai waɗannan ƴan iskan sojojin, tir wallahi” yazdan ya faɗa yana buɗe marfin motar ya fito


“oya start,ko yanzu na kira shi” sojan ya faɗa yana kallon Fa'iz ɗin dake tsaye yana binshi da kallon ƙasƙanci
“an gaya maka tsoron shi nake ji ne?”
“wannan kuma matsalar kace,zaka fara ko sai na kira shi?” sojan ya faɗa yana zaro wayar shi daga Aljihu

“kai dallah malam dakata,ce maka a kayi bazan yi ba ne?”
“to fara idan ba so kake na kira shi ba”
tsaye Fa'iz yayi sai ƴan kalle kalle yake,yana tsoron ya Naeem amma bai son ajinshi ya zuba a gaban securitys ɗin gidan.


yazdan ne ya ƙaraso wajen shima sai layi yake kamar zai faɗi ƙasa,kayan jikinshi iri ɗaya ne dana Fa'iz sai dai shi kanshi kitso ne saɓanin Fa'iz dake da aski
“malam ai sai ka tafi ko” yazdan ɗin ya faɗa yana ma sojan kallon rainin wayau.



“na tafi saboda kai ka sani ko?”sojan ya faɗa ,kallon fa'iz yazdan yayi su ka kwashe da wata ƴar iskar dariya “cewa za kayi na shan fura kake so,ai da kayi magana”


Fa'iz ne ya zura hannu cikin Aljihu ya ciro bandir ɗin dollers ya watsama sojan yana jan hannun yazdan “zo mu tafi kaji”


ran sojan ne yayi matuƙar ɓaci hakan yasa ya fisgo rigar Fa'iz ɗin “kai har ni zaka wulaƙanta?” sojan ya faɗa
“an wulaƙanta ka,dama can kai ba wulaƙantaccen bane,maza ka sauke hannunka saman jiki na ko ranka yayi mummunan ɓaci yanzu” Fa'iz ya faɗa dai dai jiniyar motocin sojoji na tunkaro gidan,da sauri Yazdan ya duƙa ya kwashe kuɗin.


mota biyu ce ta security guard ta nufo parking space ɗin yayin da su ka sako wata baƙar Nissan a tsakiyar su, parking motocin su kayi,da gudu security guard ɗin su ka shiga fitowa suna nufar baƙar Nissan ɗin dake tsakiyar su, ɓack seat ɗin motar ɗaya daga cikin security ya buɗe.


Wata kaykyawar mata ce ta fito cikin shigar lafaya fara mai adon flowers ja,tasha adon zobba da sarƙa na gold, high hills ne a ƙafarta,cikin takun izza ta nufo in da su Fa'iz ɗin su ke ,sojan na ganinta ya saki Fa'iz ɗin yana ɗan rissanawa ya gaisheta,taɓe baki Fa'iz yayi yana faɗin matsiyaci kawai.



murmushi su saki shida yazdan suna ƙarasawa in da matar take, hugging ɗin su tayi itama fuskarta ɗauke da murmushi,raba jikinta tayi da nasu tana faɗin “ 5 and 6 lafiya na ganku tsaye nan,mike faruwa??”


kallon sojan dake tsaye yazdan yayi “wannan matsiycin ne ya Naeem wai yasa yasa Fa'iz tsallan kwaɗo” kallon sojan matar tayi “wai haka ne?”
“eh ranki ya daɗe” sojan ya bata amsa,dubanta ta kai ga Fa'iz


“laifin mi kayi mashi yasa a hukuntaka?”
“momy babu abunda nayi mashi,kawai kin san ya tsaneni ne” girgiza kai matar tayi

“babu yanda za'ayi Naeem yasa a hukuntaka haka nan Fa'iz dole a kwai abun da kayi mashi,jeka kawai wajen aikin ka” ta faɗa tana kallon sojan

“to ranki ya daɗe” sojan ya faɗa yana barin wajen,bai so Hajiya ta zo ba yaso yau ya koyama Fa'iz hankali amma idan ba yau ai akwai gobe.



cikin gidan su ka nufa ita da su Fa'iz ɗin securitys ɗin ta da PA ɗin ta har sun biyo su ta dakatar dasu,ciki su ka shiga su yazdan sai zuba mata ƙarya su ke wai sunyi broke gashi kwana biyu dady bai basu ko sisi ga motar su babu mai a ƙasa suke takawa zuwa school,murmushi kawai tayi tana girgiza kai ta san ƙarya su ke mata,hannu ta zura a jakar ta ciro bandir ɗin ƴan dubu dubu har guda shidda ta basu kowa uku uku,godiya su ka shiga zuba mata kamar tsaffin maroƙa.


A main Parlor su ka rabu ta nufi part ɗin mom su kuma su ka nufi part ɗin mamy.


tun daga first parlorn mamy Fa'iz ya shiga ƙwala mata kira

“mamy! mamy!! mamy!!!,wai ba kowa ne a gidan nake magana anyi man banza??” masu aikin gidan najin maganar shi su ka nemi wajen ɓuya dan sun san muddin ya gansu sun shiga uku baijin kunyar taɓa jikin su a gaban kowa ko da kuwa mahaifiyar shi ce .


kitchen ɗin part ɗin ya fara leƙawa ganin babu kowa ne yasa shi jinjina kai yana faɗin “ƙana nan ƴan iska basa nan kenan” ya faɗa yana nufar ƙofar bedroom ɗin mamy.


A bakin ƙofa yaci karo da mamy doguwar rigar less ce a jikinta kanta babu ɗan kwali gashin Attachment ɗin ta har gadon bayanta kamar dai kullum,daga sama har ƙasa ta shiga ƙare mashi kallon kafin ta sauke idonta kan fuskarshi da sawun hannun ya Naeem ya fito raɗau.


“mamy wai ina ki ka shige ne sai ƙwala maki kira nake?” ya faɗa yana layi kamar zai faɗo mata,saboda tsaɓar shaye shaye ko bai sha komai ba baya iya tsayuwa dai dai sai ka ganshi yana layi

“kai Ni da Allah karka faɗo man a ka,daga ina kake haka?”
“daga yawo”ya bata amsa a gadarance
“yawon iskanci ko, a can ma ka samu wani ya ɗauke ka da mari ko?,wallahi Fa'iz ka shiga hankalinka dani,kai kullum burinka kaja man abun zagi ko dan ubanka”

shafa kumatun shi yayi “nifa ba abun zagin da nake ja maki,kuma wannan sawun marin da ki ka gani Naeem ne ya mare ni dan kawai na bigeshi ban gani ba”

“mari fa kace, wai tsayama wane Naeem ɗin??”
“akwai wani Naeem ɗin ne banda wanda ki ka sani”
“ya mareka dan kawai ka buge shi?”
“eh” ya bata amsa
“yana cikin gidan ko ya fita”
“ya fita” ya bata amsa


“idan ya fita ai uwar shi na nan” mamy ta faɗa tana damƙar hannun Fa'iz ɗin ta ja shi zuwa part ɗin mom,dan suyi saurin isa ta corridor da zai sadaka da duk wani part dake second floor tabi,cikin ƙan ƙanin lokaci su ka iso part ɗin mom Fa'iz sai faɗi yake ta sake shi amma ina...
_*Ep 15_16*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘



______________________________




A saman sofa suka samu mom da matar data shigo,fizge hannunshi Fa'iz yayi, babu sallama babu Nocking mamy ta hau surfa masifa

“wallahi bazata saɓu ba bindiga a ruwa,bazai yiwu ko wane ɗan iska yariƙa dakar man yaro ba ehe” kusan a tare mom da matar data shigo su ka kai duban su ga mamy dake fama sirfa masifa, Yumnah da gudu ta fito daga ɗakin mom.


“naga dai iskanci babu wanda baiyin shi,Allah na tuba akwai wanda akafi sani da iskanci sama da soja,wane irin iskanci ne nasu Bama gani a gidanan, ko kuwa wanda ke matse ƴaƴan mutane a office da sunan aiki ne ba ɗan iska ba, ko wanda ya haiƙe ma tsarar haihuwar shi da ƙananun shekaru ya kuma wanke ƙafa ya koma can cikin nasara masu jan kunne dangi sheɗan ne ba ɗan iska ba, ko mai yawan mashaya duk daren Allah ne ba ɗan iska ba!!???”


daga mom har matar data shigo zuba mata ido su kayi kawai suna kallonta kamar wata mai taɓin hankali.

“to wallahi bazan yarda ba tunda ba wani yasha man wahalar haihuwa ba ehe” clapping hand taji anyi daga bayanta.


Da sauri gaba ɗayan su ka kai duban su ga dady dake tsaye can sama tun ɗazu ya dafa handrail,tunda mamy ta shigo yake tsaye yana kallonta,wani irin mummunan faɗuwa gaban mamy ya shiga yi duk a tunaninta baya gidan.


parlorn dady ya nufo yana faɗin “da kyau uwar ɗa,da kyau wacce ta iya haihuwar ɗan kirki” ya faɗa yana ƙarasowa in da suke.

Fa'iz shan jinin jikinshi yayi ganin irin kallon da dady ke mashi,yana ƙarasowa in da yake ya ɗauke shi da lafiyayyun maruka har sau biyu,da sauri ya dafe kuncin shi.



Mamy gabanta ne ya faɗi,nan ta shiga ƴan kame kame da nufin ba dadyn haƙuri,wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata wacce ba ita da yayi mawa ba hatta su mom sai da ƴan hanjin cikin su suka kaɗa “yanzu ni na mareshi ko zaki rama mashi??”


Ya faɗa yana sake saukema Fa'iz ɗin wani lafiyayyan marin “haba janar taya za kaita dukan yaron haka,ba fa shi yayi maka laifi ba”

“na sake marin shi dan na gwada maki iskancin soja kamar yanda ki ka faɗa”

dadyn ya faɗa a karo na uku yana sake ɗauke fa'iz ɗin da wani marin har sai da ya saki fitsari a wando, yumnah bata san sanda ta fashe da dariya ba, da sauri tasa hannu ta toshe bakinta gudun kar wani yajita.

“dan Allah janar kayi haƙuri, wallahi ba haka nake nufi ba”
“haka ki ke nufi mana,ai gwara na gwada maki iskancin sojan”

“dan Allah dady kayi haƙuri ba dan ni ba” fa'iz ɗin ya faɗa hawaye na zobo mashi shar

“yiman shiru ko nayi ƙasa ƙasa da kai a wurin nan shashasha” da sauri fa'iz ɗin yasa hannu yan kama bakin shi, kallo mamy dady yayi

“Mabaruka!!!” dady ya kira sunanta da kakkausar murya,jiki na ɓari tace
“Na'am”

“wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da ƙafarki zata sake takowa zuwa ɓangaren zulaihart da sunan tujara ko rashin mutunci, Naeem yaya yake ga Fa'iz ya isa ya hukuntashi akan kowane laifi da yayi,daga yau idan ki ka sake tada jijiyoyin wuya akan Naeem ko wani a cikin ƴaƴana ya hukunta ɗanki, ina mai tabbatar maki zaki gamu da fushina wanda hakan bazai taɓa maki daɗi ba kinji na faɗa maki”


“naji in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba” mamy ta faɗa kamar da gaske,hanyar fita dady ya nuna mata ita da Fa'iz ɗin

“maza kija ɗanki ki ba mutane wuri”

kama hannun fa'iz ɗin tayi sumi sumi su ka fice

kallon dady matar data shigo tayi “ina wuni ya Tahir, na sameku lafiya?”

“lafiya lau Salima ya mutanen gidan, ina ki ka baro man ƙanina” murmushi matar ta saki tana faɗin “ yana can yana fama da jama'a”

“ai dole ne, Allah dai yasa a gama lafiya” dady ya faɗa
“Ameen ya Allah”


“ki gaishe man da shi” dadyn ya faɗa yana nufar part ɗinshi

“zaiji in sha Allah” matar ta faɗa tana kai dubanta ga mom

“ba mu gisaba, na same ku lafiya?”
“lafiya lau hajiya salima, ya kuma fama da jama'a”
“lafiya lau Alhmdllh,ashe kuma abunda ya faru da Asma'u kenan, to Allah ya kyauta gaba”

“Ameen ya Allah” mom ta faɗa
“da tare zamu zo da Kainart bata jin daɗi ne shiyyasa bamu zo tare ba amma tana maki jaje”
“Ayya Allah sarki, ina amsawa Allah ya bata lafiya”
“Ameen summa Ameen”

ƙarasowa yumnah tayi cikin parlor
“momy shine baki zo man da su Ammar ba?”

“suna school ne yumnah”
“ke ki ka ma biye mata idan tana son ganin su ai ta san in da zata same su”
“ai kuwa dai, dan tunda yallaɓai yaci zaɓe ina jin zuwan yumnah Villa sau ɗaya shima bata wani jimaba ta dawo”


ɓata fuska yumnah tayi “school bata bari na saketa, kuma dokokin gidan gwamnatin ne momy sunyi yawa”

“kaji ja'ira banza lokacin da ku kuna gidan gwamnatin ai ba suyi maki yawa dokokin ba sai yanzu ko, kawai baki son zumunci”

“ba haka bane momy”
“to yaya ne?”
“ina nan zan zo kafin muyi resuming school”
“ina nan ina saurare Allah ya kawo ki lafiya”
“Ameen” tashi matar tayi tana faɗin


“bari na shiga ɓangaren mabaruka mu gaisa”
“to nagode Allah ya bar zumunci, a gaishe man da Kainart ɗin”
“za taji in sha Allah”
“momy sai na zo” yumnah ta faɗa

“Allah ya kawo ki lafiya” da Ameen ta amsa, har main parlor mom ta rakata, part ɗin mamy hajiya salima ta nufa.



Mamy a lokacin da su ka fito daga part ɗin mom, fiszge hannunshi yayi daga riƙon da tayi mashi

“mamy ai ga irinta nan sai da nace ki ƙyale ni gashi nan yanzu kin ja man shan maruka, na san yanzu hankalin ki ya kwanta?”

“wallahi Allah ne ya ceceta da ace janar baya gida yau data gane kurenta”

taɓe fa'iz yayi “ kullum haka ki ke cewa,kin taɓa ɗaukar mataki a kan mom ɗin ne ko da sau ɗaya, wallahi mamy ina guje maki randa dady zai shuka maki rashin mutunci saboda matarshi”


“wane shi, ya dai shuka mata rashin mutunci”
“ai yanzu naga faɗan da yayi maki ita yayi mawa,wallahi mamy ki rage shige mata wallahi ko ƴaƴanta ba raga maki za suyi ba, ki bar ganin kowa ya zuba maki ido a gidanan kamar ana tsoronki, wallahi lokacin biye maki ne basu dashi amma duk randa ki ka kaisu bango abun bazaiyi kyauba”



“faɗa mata gaskiya fa'iz kullum abunda nake so ta gane kenan amma taƙi, wallahi mamy wannan abun da ki ke ida sirema dady ki ke, dan zubarma kanki da mutunci ki ke a gaban kowa muma kina ja mana” Fa'iza ta faɗa wacce fitowarta kenan daga bedroom ɗin ta


baki mamy ta saki ta rasa har yaushe tayi lalacewar da Fa'iz da Fa'iza su ka rainata irin haka “ni ku ke faɗa ma haka dan uwarku?”


“gaskiya ce kuma daga ƙinta sai ɓata, kai yazdan zo mu tafi muje kawai restaurant muci abincin a can” Fa'iz ya faɗa yana jan hannun yazdan su ka fice, Fa'iza ma shigewa tayi ɗakin ta da kallo kawai mamy ta bisu.


duk wannan hargagin da take tana yi ne saboda su amma basa gani

“Allah ya wadaran naka ya lalace” ta faɗa tana nufar ɗaya daga cikin sofas ɗin parlorn ta zauna, masu Aiki dake laɓe suna sauraron abun da ke faruwa ban da Allah ya ƙara babu abun da su ke.


hajiya salima ta shigo parlorn bakinta ɗuke da sallama, da sauri mamy ta kai dubanta gareta,tashi tayi ta nufeta fuskarta ɗauke da murmushi, hugging ɗin juna su kayi.


“saukar yushe?” mamy ta faɗa tana jan hannunta su ka nufi sofa su ka zauna
“dama yaushe zaki ganni kinje kina tsula tsiyarki” mom salima ta faɗa


“wai da ke ce a parlorn, ni inama na lura da wacece ido a rufe suke ne raina ya ɓaci”

“ai naga alama, wai dama mabaruka har yanzu baki daina hargagi da zulaihart irin wannan ba?”

“yaushe kuwa zan daina, ai idan kinga na daina to na sake sender ta ƙasar su kamar shekarun baya” kallon baki da hankali matar ta shiga binta dashi.


“ke har yanzu kina tunanin zaki iya raba Tahir da zulaihart ne, to wallahi idan ma bacci ki ke tun wuri ki farka kar kije garin tsige igiyar Aurenta ke ki tsige taki a banza”


“ban gane ba, mi kike nufi”
“ko wannan matakin daya ɗauka yau akan fa'iz a gabanki saboda zagin ƴaƴanta da ki ka yi ya isa yasa kiyi hankali kisan cewa da da yanzu ba ɗaya bane”

“ni wallahi Hajiya salima kin barni a cikin duhu,dan ban gane inda maganar ki ta dosa ba”

“ kin manta bala'in da ki ka shiga lokacin baya?, da ba dan mama Ameena ba da yanzu kina wani gidan ba wannan ba, idan zaki canza salon kishin ki ki canza idan kuma haka ki ke ganin ya fiye maki tam, shi dai yaƙi ɗan zamba ne”


jinjina kai mamy ta shiga yi alamar gamsuwa da maganar hajiya salima “shikenan naji zanyi ƙoƙarin ganin na sauya”
“hakan dai shi ya fi, ni na shigo ko gaisawa ba muyi ba,kin wuni lafiya?”

“lafiya lau, ya yau ban ganki da tawagarki ba?”
“ki bari kawai ni na hana su biyo ni nace suyi zaman su jaje zanje ba ɗabbaka siyasa ba, ko security cewa nayi su jira ni a waje”


“kina sha'aninki ta wajen Ahmad, ai wallahi ni lokacin da janar na kan kujerar shugaban ƙasa duk in da zani da tawagata nake zuwa ai shine girman”


“ban manta ba” matar ta faɗa, mai aiki mamy ta ƙwalama kira dan ta kawo ma hajiya salima ruwa da lemu.

“ai barshi kawai mabaruka nasha a part ɗin zulaihart tafiya ma zanyi”

“nifa kinga abun da ke haɗani dake kenan,dan mi zaki sha ruwa a wajenta”

“ni dai yanzu idan na sake dawowa na sha, amma yanzu kam gaba nayi”
“shikenan Allah ya nu na man lokacin da zaki sake dawowar” da Ameen hajiya salima ta amsa, a tare su ka miƙe ita da mamy.



har parking space mamy ta rakata, sai da taga tashin motocin ta tukun ta koma ciki.


*ASO VILLA*


Kusan a tare motocinta da motar da aka ɗauko su Ammar daga school ta shigo.

A bakin main entrance ɗin shiga part ɗin su motocin su kayi parking, drivern da yayi driving ɗin su ne ya fito ya buɗe masu,da gudu su ka fito suna nufar motar kakar tasu,suna isowa security na buɗe mata ƙofa ta fito.


da gudu suka faɗa jikinta “oyoyo granny,shine ki ka fita bama nan ko” murmushi ta saki tana shafa fuskokin su
“ayi man afuwa gidan big daddy naje”

shagwaɓe fuska su kayi “amma granny kin san cewa muma muna son zuwa shine ki ka tafi bama nan”

“ayi man Afuwa,ai gobe za ku haɗu dashi a gidan Abbah” ta faɗa tana jan hannunsu suka nufi cikin gidan
“ai gidan Abbah ba gidan shi bane,mu gidan shi muke son zuwa”

“karku damu idan kuna son zuwa sai nasa dadyn ku ya kaiku gobe da kun dawo daga school,kunga sai kuyi ma Aunty Yumnah weekend ko” tsallan murna su kayi


“yeee har gidan papa ma sai muje”
“na san Aunty Yumnah zata kai ku ko ina,amma fa sai dady da momynku sun amince”

ɓata fuska su kayi “dady bazai amince ba mu dai kawai kice ya kaimu”

“to naji muje na duba jikin momyn ku” ɗan zaro ido su kayi suna kallonta

“mi ya samu momy?”
“bata jin daɗi ne” Hajiya Salima ta faɗa dai dai tana tura ƙofar ɗakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login