Showing 39001 words to 42000 words out of 88290 words
Chapter 14 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
hangen main entrance ɗin shigowa part ɗin daga compound ɗin gidan,armchairs ne guda biyu ajiye daga tsakiyar su ɗan madaidaicin glass table ne,idan ka kalli ƙasan parlorn zaka ɗauka mirror ne yanda yake ɗaukar ido dan kana iya kallon kanka tsab.
Daga cikin parlorn kana iya hangen katafaren dinning room, wanda aka ƙawatashi da haɗaɗen dinning table,ƙyataccen glass table ne mai mazaunin mutum shidda,wasu haɗaɗun chairs ne kewaye da table ɗin,daga saman ceilling ɗin dinning room ɗin ƙaton bulb ne ya haskaka ko ina na dinning room ɗin,ga wata irin zungureriyar floor lamp.
cikin parlorn su ka ƙarasa Yumnah na gaba yayinda Nainarh ke biye da ita tana ƙarema parlorn kallo,tayi mamakin wannan part ɗin wanene dan yafi ko wane part dake gidan haɗuwa da tsaruwa duk da ba ko ina na gidan ta sani ba,wayar landline dake ajiye cikin parlorn Yumnah ta nufa, number kitchen ta kira,daga can ɗaya ɓangaren a kayi picking call ɗin.
“na buɗe part ɗin ku nake jira” Yumnah ta faɗa tana rejecting ba tare da ta tsaya jin amsar da za'a bata ba,wata ƙofa Yumnah ta nufa ganin haka ne yasa Nainarh binta a baya,nan ma wani parlorn ne su ka shigo wanda yafi na farkon haɗuwa,komai na cikin shi blue White and gold color ne,glass door ne guda biyu a jere sai wasu corridor guda biyu dake hannu dama da hagu can ɗan nesa da ƙofafin,wanda na hannun hagu ya kasance gym room ne ɗayan kuma wani part ne mai zaman kanshi.
ɗaya daga cikin ƙofofin dake jere Yumnah ta nufa tun kafin ta ƙarasa ƙofar ta shiga zugewa da kanta,cikin ɗakin ta kunna kai Nainarh na biye da ita a baya,wani irin haɗaɗen bedroom ne su ka shigo komai na cikin shi black,white and gold color ne, bedroom ɗin yana ɗauke da Royal bed mai matuƙar ɗaukar hankali,bed ɗin a shimfiɗe yake da tausassan bedsheet ga ƙaton blanket mai gashi gashi a jikin shi,gefe da gefen gadon nightstand ne mai ɗauke da bedside lamp,daga gaban gadon Ottoman table ne color ɗaya da bed ɗin,ƙasan ɗakin shimfiɗe yake da rug carpet mai taushi,wani irin ƙayataccen dressing mirror ne a cikin ɗakin daga gaban shi stool ne mai taushin gaske.
cikin ɗakin su ka ƙarasa,dogayen curtains ɗin dake a sake Yumnah ta shiga zugewa,kafin ta nufi wata ƙofa wacce nake kyautata zaton dressing room ne mai haɗe da bathroom, buɗe ƙofar tayi,shiga ciki tayi ta bar Nainarh nan tsaye tana ƙarema bedroom ɗin kallo baƙaramin tafiya yayi da ita ba duk da babu wasu kaya a cikin shi.
fitowa Yumnah tayi “gyaran ma bazai ɗauki wani lokaci ba saboda babu datti da yawa” jinjina kai Nainarh tayi “eh gaskiya babu wani datti sosai”
“haka ne muje na duba sauran ɗakunan kafin su Ishrat ɗin su ƙaraso” da to Nainarh ta amsa mata,ficewa su kayi daga ɗakin,ƙofar dake kusa da wacce su ka fito su ka nufa itama ta glass ce kamar wacce su ka fito.
Nan ma wani bedroom ɗin ne su ka shigo kusan duk abun da ke cikin wacan a kwaishe a nan banbancin color ne kawai shi wannan red and white color ne saɓanin wacan,mamaki gaba ɗaya ya kashe Nainarh yanzu duk mutum ɗaya keda wanann part ɗin kuma ba zaune yake a ciki ba, zata so ganin wannan shalelen dady.
curtains ɗin shi kawai Yumnah ta zuge ta duba dressing room da toilet Kamar dai yanda tayi a wacan bedroom ɗin kafin su ka fice, corridor ɗin dake hannun damanƙofofin su ka nufa,ƙofofi ne guda biyu a wurin na glass daga in da su ke tsaye suna iya hangen komai dake ciki.
tura ƙofar su kayi su ka shiga ciki,wani irin azabebben parlorn ne su ka shigo wanda ya doke gaba ɗaya falukan dake part ɗin,yafi su komai nesa ba kusa furniture's ɗin dake ciki ma kwata kwata ba irin tsarin su ɗaya da waɗancan ba,komi na cikin parlorn white color ne da ratsin gold,daga cikin parlorn kana iya hangen bedroom da swimming pool ɗin dake part ɗin ta hanyar glass wall dake mamaye da part ɗin gaba ɗaya.
bedroom ɗin Yumnah ta nufa tana faɗin “gaskiya na fara kishi da shalelen dady” murmushin Nainarh ta saki tana biye da ita ba tare da tace mata ƙalla ba sai raba ido take a parlorn kamar ba'a niger ba,kusan suman tsaye Nainarh da Yumnah su kayi a yayin da su kayi arba da makeken bedroom ɗin da su ka shigo,riƙe ƙugu Yumnah tayi tana jinjina kai alamar mamaki tunda aka gina wannan sabon bata taɓa shigowa ba sai yau da dadyn yace su shiga a gyara,gaba ɗaya bedroom ɗin a mamaye yake da glass wall.
bedroom ɗin yana da girma sosai dan tsab za'a iya gidan parlorn, bedroom, kitchen da toilet wadatattu a cikin shi,
wani irin makeken king size bed ne daga can ɗan saman stape,a shimfiɗe yake da bedsheet mai taushi gaske da blanket kafi mage taushi,gefe da gefen shi nightstand ne,bed ɗin kusan rabi da kwatar shi a cike yake da pillows ƙasan bed ɗin na fitar da wani kalar haske,daga can gefen bed ɗin sofa ce mai masifar kyau color ɗaya da gadon itama ƙasanta na fitar da haske kalar na bed ɗin.
daga cikin ɗakin kana iya hangen haɗaɗen gym room dake can ɓangaren hagu na ɗakin,wasu irin expensive machines ne a cikin shi kamar a gym center,sai toilet da shima kana hangen komai dake cikin sa.
daga ɓangaren dama sliding door ne wacce idan aka buɗe ta ƴar baranda ce,cuddler chairs ne guda biyu ajiye a wurin daga tsakiyar su round glass table ne ajiye.
jinjina kai Yumnah ta shiga yi tsarin part ɗin ba ƙaramin tafiya yayi da ita ba,wayar dake hannunta ta dannan, video ta shiga ɗaukar part ɗin,tundaga parlor har zuwa wannan yar barandar,babu in da bata ɗauka ba har toilet tukun su ka fice daga part ɗin su ka koma parlorn na biyu da su ka shigo.
tsaf tsaf yake part ɗin saboda yawan gyarawa da ake duk da ba mai zama,ɗaya daga cikin sofas ɗin su ka nufa su ka zauna,daga cikin parlorn suna hange parlorn da su ka fara shigowa ta hanyar glass wall dake mamaye da parlorn.
basu jima da zama ba Ishrat ta shigo tare da wasu masu aiki su biyar haɗi da ita su shidda kenan hannunsu ɗauke da mop da tsintsiya da detergent,in da su Nainarh su ke suka ƙaraso,cikin girmamawa su ka gaishe da su,amsa masu su kayi Yumnah na faɗin “yawwa Ishrat sai kun mai da hankali,ki fara nuna masu in da za'a fara gyarawa,yau har sabon part ɗin dady yace a gyara”
gyaɗa mata kai Ishrat ɗin tayi,kasa masu aikin tayi gida biyu,biyu tace su gyara bedrooms da gym room,biyu kuma su gyara parlors ɗin da dinning room da kitchens,ita da ɗayar kuma su ka nufi part ɗin da su Yumnah su ka fito.
babu ɓata lokaci masu aikin su ka shiga gyaran ko ina a cikin gidan,main parlorn part ɗin Yumnah da Nainarh su ka nufa, sliding door dake wurin su ka buɗe suka fita ƴar barandar dake wajen,a saman chairs ɗin dake wurin su ka zauna,daga nan in da su ke suna hangen main entrance ɗin shigowa part ɗin da compound ɗin gidan,suna iya hangen katafaren parking space dake wajen,rides ne da yawa a ciki an lulluɓe su da alama an ajiye su ne kawai.
Kasa haƙuri Nainarh tayi har sai da ta tambayi Yumnah
“wai nan part ɗin waye?,naji kina faɗin shalelen dady dama ba ke bace Auta ba,dady na da wani ƙaramin ɗa bayan ke?”
kallon Nainarh da tayi maganar Yumnah tayi tana sakin dariya
“wai dan kinji ina faɗin shalelen dady?,dady baya da wani ƙaramin ɗa ko ƴa bayan ni,ni ce Autar sa”
“ok,amma nan part ɗin waye,mi yasa ki ke ce masa shalelen dady??”
“part ɗin ya SAM ne shi ne yaron dady na uku,daga ya Naeem sai ya Adnan sai ya SAM sai ya Irfan sai Aunty Fa'iza sai ya Fa'iz sai Yumnah Auta”
yumnah ta faɗa tana sakin murmushi, murmushi itama Nainarh tayi tana faɗin
“masha Allah,Allah ya Albarkace ku ya rayama dady ku” da Ameen Yumnah ta amsa tana faɗin
“tsawan shekara 18 kenan ya SAM baya ƙasar,tun ina ƴar shekara 2 da haihuwa ya koma US wajen granny da zama”
“ikon Allah,yanzu zuwa zaiyi ne yasa dady yace a gyara part ɗin?” girgiza mata kai Yumnah tayi
“babu wanda ya san ranar da zai zo,tunda ya tafi bai sake dawowa ba,kawai dai dady yana sa a gyara part ɗin ne duk ranar friday”
“sorry kar kice na cika shiga abun da ba ruwana,amma miyasa ya tafi tsawan wannan shekarun bai dawo ba??”
murmushi Yumnah ta saki “nima ban sani ba,kawai dai na taso naga baya gidan kuma bai taɓa zuwa ba”
jinjina kai kawai Nainarh tayi ba tare da ta sake cewa komai na,amma lamarin ya bata mamaki wane irin ɗa ne zaiyi nesa da iyayen shi tsawan waɗannan shekaru ba tare da ya waiwaye su ba,haka nan taji tana son sanin dalilin barin shi gida da rashin waiwayar iyayen shi tsawan wanann shekarun,wani ɓangare na zuciyarta na gargaɗarta da shiga abun da babu ruwanta, Yumnah ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗin
“next week fa muke komawa school,ni wallahi duk na ƙagara next week ɗin tayi dan na gaji da zaman gida”
yanayin fuskar Nainarh ne ya canza da alama ba tayi farin cikin da labarin komawar ta su makaranta ba
“ya dai,baki son komawa ne?” Yumnah ta faɗa tana tsareta da idanu, girgiza mata kai kawai Nainarh tayi ba tare da tace ƙala ba,itama Yumnah bata sake cemata komai ba dan ta san dalilinta naƙi son a koma,amma ya za tayi dole tayi haƙuri ta koma komi ƴan school ɗin su za su ce.
*ASO VILLA*
Gaba ɗaya a halin gidan sun hallara a katafaren dinning room dake villa ɗin domin breakfast, Zaabith na zaune saman chair dake kallon wacce su Ammar ke zaune,sai Irfan da Waseef dake zaune kusa da juna,sun duƙar da kai,magana su ke ƙasa ƙasa idan ba kana kusa da su sosai ba ba zaka iya jin mi su ke cewa ba.
kallo Zaabith dake cikin abinci hankali kwance hajiya salima tayi
“lafiya ka fito kai kaɗai,ina kainart ɗin take,ko har yanzu jikin ne??” da sauri ya ɗago yana kallon mahaifiyar tashi da tayi magana.
“zata fito,ta tsaya wani abun ne ciki” Zaabith ɗin ya faɗa yan maida kanshi ga abincin da yake ci,wani ɗan iskan kallo Ammar da Aman su ka watsa mashi ba tare da wani ya lura da su ba.
jinjina kai hajiya salima tayi tana kai dubanta ga sarah dake tsaye
“maza ki kira man ita sarah” da to sarah ta amsa tana juyawa tabar wajen zuwa part ɗin Zaabith.
bayan kamar minti biyar sarah ta dawo “lafiya, tana ina??” hajiya salima ta faɗa tana kallon bayan sarah ganinta ita kaɗai
“gata nan fitowa ranki ya daɗe”jinjina kai hajiya salima tayi
tunda ta tunkaro dinning room ɗin ya kafeta da ido,da yake chair ɗin da yake zaune tana fuskantar ƙofar shigowa dinning room ɗin,baƙar jallabiya ce a jikinta ta lulluɓa mayafinta ta rufe rabin fuskarta da har yanzu sawun hannunshi na nan raɗau kamar yanzu ne ya mareta.
wani irin kallo ya shiga jifanta dashi wanda ita kaɗai ta san ma'anar shi,saurin kauda kai tayi kamar bata ganshi ba, murmushi hajiya salima ta saki lokacin da kainart ɗin ta ƙaraso ciki.
da sauri Zaabith ɗin ya miƙe yana ja mata kujerar dake kusa da shi,alama yayi mata data zauna yana sakar mata wani soft smile,ɗauke kai tayi kamar bata ga abun da yake nufi ba ta nufi inda su Ammar suke,tashi Aman yayi ya koma kujerar dake kusa da wacce ya tashi,murmushi ta saki tana shafa kanshi,zama tayi a tsakiyar su.
“ina kwana momy,kin tashi lafiya”
“lafiya lau Alhmdllh, kainart ya ƙarin ƙarfin jikin” da Alhmdllh ta amsa mata,da sauri sarah ta ƙaraso in da kainart ɗin take tayi serving ɗinta.
har time Zaabith na tsaye mamaki ne duk ya cika shi,kallon shi momy tayi “kai kuma lafiya kayi ma mutane tsaye a ka??”
“bakomai” shine kawai abun da yace ya koma mazaunin shi ya zauna.
“ashe baki jin daɗi Aunty kainart?” waseef ya faɗa yana kai duban shi gareta
“naji sauƙi waseef”
“Allah ya ƙara sauƙi,amma shine baki ce na zo na dubaki ba” Irfan ya faɗa yana wani ya mutse fuska.
ɗan zaro ido tayi “irfan nace ka dubani,rufa man asiri in ka ganni lahira kaini a kayi” dariya Irfan ɗin ya saki kamar ba shi ba
“nafa manta tsoron Allura ki ke”
dariya waseef ya kwashe da ita har da su Ammar
“gaskiya Aunty ya kamata ki rage wannan tsoron,akwai fa su Ammar a gabanki,amma kiyita abu sai kace farar kura” a cewar waseef.
jifar shi tayi da spoon ɗin dake hannunta saurin duƙewa waseef yayi,hakan da yayi ba ƙaramin dariya ya ba su,zuba masu ido kawai Zaabith yayi yana kallon su.
gyaran murya su kaji daga bakin ƙofar shigowa dinning ɗin saurin kai duban su ga magidancin dake tsaye cikin shigar Jogging suit launin blue black,a tsarin hallita dogo ne,launin fatar jikinshi fara ce ba irin sosai ɗin nan ba,sumar kanshi da gemun shi farare ne tas da alama rina launinsu yayi ba dan ya kai shekarun da za su koma haka ba,kunnen shi a manne yake da ear phone haka kyakkyawar fuskar shi a manne take baƙin glass.
Uncle Ahmad kenan, mahaifin Zaabith,Aunty Nadiya da Waseef,daga dady sai shi,shine President ɗin Nigeria na wannan lokaci.
da gudu Ammar da Aman su ka nufe shi saurin zame glass ɗin dake fuskar shi yayi ya tura shi a aljihun wando shi,faɗawa jikin shi su kayi suna mashi oyoyo, murmushi ya saki yana shafa sumar kansu,hannun su ya kama su ka ƙarasa cikin dinning room ɗin
“granfa shine yau ka fita ba tare da mu ba?” a cewar Aman
“bacci ku ke ne time ɗin,amma gobe idan zan fita tare da ku zan fita”
“gobe ai muna gidan big daddy tare da shi zamu fita”
“au haka ne?”
eh su ka bashi amsa,jinjina kai grandfa ɗin yayi
“shikenan idan kun dawo sai mu fita tare” ihun murna su ka saki suna koma mazaunin su.
gaishe dashi su Zaabith su ka shiga yi yana amsa masu cikin kulawa,sarah dake tsaye ma gaishe dashi tayi yayin da take matsowa domin tayi serving ɗin shi,da katar da ita hajiya salima tayi ,da kanta ta shiga serving ɗin shi.
“good morning” ta furta dai dai kunnen shi,kashe mata ido ɗaya yayi yana sakar mata murmushi, mazaunin ta dake kusa da nashi ta koma ta zauna tana sakin murmushi.
kallon Zaabith dady yayi
“zaabith ka kuwa haɗu da Muhsin??”
“A'a dady,ya dai kirani jiya yace yau su ke sa ran isowar su Mubarak”
“kai yaushe za ka tafi can kenan?”
“ƙarfe ɗaya su ke sa ran isowa,sai na tafi after Isha” wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar kainart jin yau zai koma
“good” kawai dadyn yace ba tare da ya sake cewa komai ba,kallon Zaabith momy tayi
“yau zaka koma ne?”
“A'a,sai next week” ya bata amsa, kainart ba hakan ta so ba ta so ace tafiya zaiyi ko ta samu ta huta da uƙubar shi.
Dady da Zaabith ɗin su ka fara tashi sai Irfan da Waseef,tashi kainart tayi itama ta fice aka bar momy da su Ammar.
*Big Daddy's house*
wajen awa biyu su ka ɓata wurin gyaran part ɗin, gyara su kayi mashi na musamman ko ina ka shiga sai tashin ƙamshi yake haɗe da sanyin AC.
“sannunku da ƙoƙari Ishrat,wannan idan dady ya gani dole ya baku tukwici” murmushi kawai Ishrat ɗin ta saki
“ai ina jin ku saki curtains ɗin kawai a kashe bulbs,tunda an kammal”
da to su ka amsa mata suna nufar bedrooms da falukan dan ciki umarninta,duk wani kayan wuta da su ka san sun kunna sai da su ka kashe shi hatta AC ba su bari a kunne ba,kayan da su kayi amfani da su suka kwashe,ficewa su kayi daga part ɗin bayan sun kammala.
ƙofofin bedrooms ɗin Yumnah ta rufe tukun suma su ka fice, direct part ɗin dady ta nufa Nainarh kuma ta nufi bedroom ɗin su,bata samu dady a part ɗin ba har ya fice,key's ɗin kawai ta ajiye ta fice.
A zaune ta samu Nainarh bakin bed,da kallon mamaki ta bita
“yanzu Nainarh maimakon ki shiga kiyi wanka sai ki zauna,ni ban san mi yasa ki ke haka ba komai sai nace kiyi sai kace wata ƙaramar yarinya?”
“ba haka bane,naga ke sauri ki ke saboda fitar da za kuyi ,shine na bari idan kin fito sai na shiga”
wani ɗan iskan kallo Yumnah ta watsa mata “mi ki ke nufi da fitar da za muyi,kina nufin ban da ke??”
“haɗuwa fa za kuyi da family ku ni miye nawa na zuwa”
“gaskiya Nainarh bana jin daɗin irin wanann abun,ni kawai ki tashi ki shiga wanka karma su mom su shirya su fara jiran mu”
“yumnah gaskiya ni bazan je ba,taro ne na familyn ku, taya za ayi naje”
“wallahi sai kin shirya mun tafi kin ma ji na rantse,kullum naita fama dake kamar wata yarinyar goye” Yumnah ta faɗa tana nufar dressing room ɗin ta.
tashi Nainarh tayi ta shiga wanka ta so Yumnah ta ƙyaleta dan bata san wane irin kallo family ɗin su za suyi mata ba ganin ta shigo cikin su,ba lallai suyi maraba da ita ba.
bata jima da shiga wanka ba Yumnah ta dawo bedroom ɗin jikinta ɗaure da towel,zama tayi gefen bed ɗin, Nainarh na fitowa ta tashi ta nufi toilet ɗin har ta kai bakin ƙofa ta tsaya “kayan da zamu sa na nan na fito mana da su”
gyaɗa mata kai Nainarh tayi
ƙofar bedroom ɗin ta buɗe ta shiga, dressing room Nainarh ta nufa, dressing mirror ta nufa,zama tayi saman stool, expensive body lotion ɗin dake jere saman dressing mirror ta ɗauka,shafama jikinta ta shiga yi, simple make up tayima fuskarta Masha Allah tayi kyau abunta.
tashi tayi ta nufi kayan da Yumnah ta ɗauko masu, expensive egyptian abayas ne Black color anyi masu ado da royal blue ɗin yadi a hannun,sunji adon stones a jikin su sai sheƙi suke.
ɗaya daga cikin rigunan ta ɗauka ta zura a jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba kamar wata balarabiya,kallon kanta tayi a gaban mirror ita kanta ta yaba da kyawun rigar a jikinta,baby