Showing 60001 words to 63000 words out of 88290 words
Chapter 21 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
bana jinka, har saƙo na tura maka namayi tunanin baka gani ba?”
“i saw it already,ayyuka ne su kayi man yawa” Balqis sai sakin murmushi take, tama rasa inda zata sa kanta dan daɗi.
“ayyah,ya aikin?”
“Alhmdllh” ya faɗa
“masha Allah,ya su Uncle da su ALYAR?”
“suna lafiya” shiru ne ya gitta tsakanin su, gyaran murya yayi mata “lafiya ki ke dai,yana yinki kamar baki cikin walwala” murmushi ta saki tana faɗin “lafiya lau nake”
“ban yarda ba Laatifa, yanayin fuskarki ya nuna kamar kina cikin damuwa, tell me who touch u?” ya faɗa cike da tsantsar kulawa, wani irin sanyi taji a ranta tana matuƙar son yanda SAM ke nuna mata kulawa duk da basa tare,Balqis wani daɗi ne ya rufeta duk da ba ita ya nunama kulawa ba tana dai fatan ta samu kulawarshi fiye da yayarta.
“kinyi shiru, mike damunki?” saurin sakar mashi murmushi tayi “babu komai SAM lafiya lau nake,ban jima da dawowa daga wurin aiki bane,duk a gajiye nake”
“ok, idan ma akwai abunda ke damunki kiyi gaggawar sanar dani”
“in sha Allah, nagode sosai da kulawarka a gare ni” shiru taji bai tanka mata ba dama ta san ba tanka mata zaiyi ba.
SAM na matuƙar kula da ita, a duniya babu wanda take samun kwanciyar hankali da natsuwa gareshi irin SAM,duk damuwar da take ciki data sanar dashi zaiyi mata maganinta,ko momy bata bata irin kulawar da SAM ke bata duk da suna jimawa ba suyi waya ba,amma kullum ne akwai masu sanar dashi halin da take ciki musamman yasa masu bibiyar mashi rayuwarta, akwai kyakyawar alƙa a tsakanin su, tun suna yara Allah ya haɗa jininsu kaf yaran family babu wacce yake kulawa kamar Laatifa in fact ma ita kaɗai yake kulawa tana da wani matsayi a zuciyar shi,wani ɓangare na zuciyarta tunzurata take akan ta sanar dashi abunda ke faruwa tsakaninta da dady ta san zai sama mata mafita.
ganin tayi shiru ne yasashi yi mata gyran murya, da sauri ta kalli wayar “lafiya?” ya faɗa
“lafiya lau” ta faɗa tana karkata wayar zuwa fuskar Balqis dake wani noƙewa a bayanta,fuskarta ɗauke da murmushi tace
“SAM ka gane wacece wannan?” saurin sadda kai ƙasa Balqis tayi, wata irin kunyarshi take ji duk da bawai ganinshi za tayi ba, a hankali ta gaishe shi
“who is she” shine kawai abuda yace,yanayin fuskar Balqis ne ya canza tuni hawaye sun cika idanunta, yanzu duk yanda take dakon sonshi amma tashi ɗaya yace bai ganeta ba.
“Balqis ce fa ƙanwata, kana nufin ka mantata?” Laatifa ta faɗa
“i don know her,bye take care” yana faɗa yayi rejecting kiran, da sauri Balqis ta kifa kanta saman mattress, murmushi Laatifa ta saki tana dafa bayanta, kamar jira take Laatifa ta taɓata ta fashe da kuka, hankali a tashe Laatifa ta ɗago da ita
“Balqis lafiya ki ke kuka?” kuka sosai take kamar ƙaramar yarinya, lallashinta Laatifa ta shiga yi harta samu tayi shiru
“haba Balqis miye abun kuka a nan?”
“dole nayi kuka Aunty Laatifa, yanzu duk tsawan shekarun dana ɗauka ina sonshi amma yace bai sanni ba, taya ma zaice bai sanni ba bayan ni shaidace akan ya sanni”ta faɗa cike da takaici
“kiyi haƙuri abun babu daɗi,amma ta yiwu ya mantaki ne shiyyasa ya faɗi haka”
“amma Aunty Laatifa ya tsaya kiyi mashi bayani mana, amma kawai yayi rejecting saboda ko kallona baya sonyi”
“ba haka bane Balqis, kiyi mashi uzuri tsawan shekara nawa baya ƙasar ya isa ya manta da kowa tunda ba waya yake da ku ba,dan yayi rejecting ba wai dan saboda ke bane haka yake baya da son yawan magana ne, ko ni idan muna waya ya gaji da magana rejecting yake,kiyi haƙuri kinji” lallashinta sosai Laatifa tayi har ta samu ta kwantar da hankalinta.
*Queen Kainart💫*
Noor tunda ta shige bedroom ɗin Kainart bata sake fitowa har yamma tayi gashi har lokacin Irfan bai zo ba baikuma kirata ba.
Su Yumnah na parlorn tare da mom maryam fira su ke hankali kwance, mom maryam ba ƙaramin nishaɗi tasa su ba.
Uncle Mustafa ne ya shigo,Army trouser ne a jikinshi tare da farar shirt, da gudu su Ammar su ka nufe shi, saurin buɗe masu hannayen shi yayi yana sakin murmushi, ai kuwa gaba ɗayan su suka faɗa jikinshi,hugging ɗin su yayi cike da farin cikin ganinsu.
raba jikinsu yayi yana faɗin “yaushe ku ka zo gidan?”
“tun ɗazu, har munata jiranka”
ɗan zaro ido yayi “amma shine ba'a faɗa man ba, da na san zaku zo ai da ban fita ba” ya faɗa yana jan hannusu zuwa cikin parlorn.
“sai da nace Aunty Yumnah ta kiraka amma taƙi”
“kai Jamal bana son sharri yaushe ku ka ce na kira maku shi iye??” da sauri jamal ya ɓoye bayan uncle Mustafa,dariya su ka saki gaba ɗaya parlorn ganin yanda Yumnah ta haƙiƙance da kuma Jamal ɗin daya ɓoye bayan Uncle Mustafa.
“Aunty Yumnah kinyi laifi kuma dole na hukuntaki”
“wallahi ƙarya yake man dady, ni baice na kira ka ba” ta faɗa kamar zata fashe da kuka,murmushi mom maryam tayi “rabu da su kinji kowa ya san ƙarya suke”
“sai na hukuntata dole” Uncle Mustafa ya faɗa,turo baki Yumnah tayi tana dallama su Ammar harara
“in wuni dady” Nainarh ta gaishe dashi cike da girmamawa
“lafiya lau, ya gida”
“Alhmdllh” gaishe dashi Yumnah tayi, cike da kulawa ya amsa mata.
up stairs ya nufa bin bayan shi mom maryam tayi,da gudu su Ammar su ka bi bayansu dan sun san sai Yumnah taci mutuncin su saboda sharrin da Jamal yayi mata.
sun jima zaune a parlorn su kaɗai, tunda su mom maryam suka nufi sama ba su sake saukowa ba,fara kiran sallar magrib da akayi ne ya sa su ka tashi su ka nufi bedroom ɗin Kainart, a kwance su ka samu Noor har bacci yayi awan gaba da ita.
tashinta Yumnah tayi akan tayi sallah amma fir taƙi tashi da Yumnah ta dameta ma rufeta tayi da masifa akan ta ƙyaleta ita ba yanzu za tayi ba
“ke ki ka sani sai kita kwanciya idan Alkairi ce”
bathroom ɗin ɗakin su ka shiga su kayi alwala,Yumnah ta ɗauko masu carpet haɗe da hijab cikin wardrobe.
shimfiɗa masu tayi su kayi sallah, basu tashi kan sallayar ba sai da su kayi harda isha tukun, har time ɗin Noor bata tashi ba, babu ma alamun zata tashin.
duka Yumnah ta kaimata a bayanta “yanzu ai sai ki tashi mu tafi gida, idan kuma anan zaki kwana naji, wallahi kin dai san halin Mom maryam” tashi tayi tana wani hararar Yumnah,murmushi Yumnah ta sakar mata
“ai da kin kwanta” tsaki taja tana nufar ƙofar fita
“uncle dai na nan idan kuma haka zaki fita tom” dawowa tayi ta buɗe wardrobe ɗin hijab ta ɗauka har ƙasa tukun su ka fice.
A parlor su ka samu Uncle Mustafa tareda su Aman sai zuba mashi surutu su ke,gaishe da shi Noor tayi da kulawa ya amsa mata, bedroom ɗin mom maryam su ka nufa zaune su ka sameta saman sallaya tana lazimi.
“ban gane ba, na ganku tsaye?”
“tafiya za muyi mom dare yayi”
“sai ku jira kuyi dinner tukun”
“A'a mom idan muje gida za muyi”
“ke zanci mutuncinki Yumnah, sai kace wasu baƙi, ku wuce gani nan zuwa” ba dan sun so ba suka koma parlorn.
sai bayanda su ka yi dinner tukun su kayi masu sallama, har parking space mom da Uncle Mustafa suka rakasu.
“yaushe ni zaku zo man weekend kenan” a cewar Uncle Mustafa, Aman ne ya bashi amsa da “sai next weekend”
“Allah ya kaimu, zan jiraci zuwanku kuwa” haɗa baki su kayi wajen furta sai munzo, murmushi su ka saki, ƴar madaidaiciyar jaka mom maryam ta miƙama Yumnah.
“sai da safenku, ku gaishe mana da mutanen gidan”
“za suji in sha Allah mom”
ba su koma ciki ba har saida su kaga tafiyar su tukun.
Yumnah harta kama hanyar gidan Uncle mutallaf Noor tayi saurin cemata gidan big dady zata kwana, hakan yasa Yumnah kama hanyar gidan su, tun a mota Noor ta kira momynta ta sanar da ita nan zata kwana, babu yanda mom fatilah ba tayi ba ta dawo gida amma taƙi bakomai yasa bata son Noor ta kwana gidan ba sai dan saboda ta san part ɗin Mom zata kwana gashi kwata kwata basu jituwa da Mom.
Motar Yumnah na shiga harabar gidan Motar fa'iz na shigowa, kusan a tare su kayi parking,yazdan ne ya fara fitowa sai Fa'iz, jeans da t_shirt ne a jikinsu, yau babu laifi anyi shigar kirki saidai a buge su ke kamar koda yaushe,har wani gaba suke suna baya kamar zasu kifa ƙasa.
tunda suka fito su ka kafe motar Yumnah da ido har suka fito, tsaki Yazdan yaja yana faɗin “ca nake baƙi akayi ashe wannan tsamayen ne”
harara Noor ta watsa masu haɗi da murguɗa masu baki
“kaiii ashe yau zan daka wata yarinya, ke dama kin rainani ko?” A cewar Yazdan yana yo kan Noor ɗin kamar zai faɗi dama sun saba kusan kullum ne sai mom Fatilah ta rabasu, muddin su ka zo ƙasar basu barinta sakat kamar mage da ɓera haka su ke, sauƙi ma ɗaya Yazdan baya binsu shi yana Nigeria.
riƙo hannunshi Fa'iz yayi “ kai dalla rabu da ita, daga ina kuke haka?” Yumnah ta bashi amsa da “daga gidan Uncle Mustafa”
“soja marmari daga nesa ba” Yazdan ya faɗa yana saluting Fa'iz,kwashewa su kayi da dariya kamar wasu taɓaɓɓu.
su Jamal tunda su ka fito daga mota su kaga su Fa'iz su kayi saurin ɓoyewa bayan Nainarh, bala'in tsoron Fa'iz da Yazdan su ke,Nainarh itama hankalinta a tashe yake dan bata san haka su ke ba ko jiya a gidan Abbah lafiya lau ta gansu.
“kaiii wa kuke ɓoyemawa” Yazdan ya faɗa yana leƙen su Ammar daketa faman zare ido, yana layi ya nufo inda Nainarh take, wani irin duka gaban Nainarh yayi su Jamal kuwa yana ƙarasowa su ka fashe da kuka suna barin bayan Nainarh su ka nufi main entrance ɗin shiga gidan da gudu.
“kaga ƴan iskan yara” Yazdan ya faɗa yana riƙe baki,da sauri Fa'iz ya nufo inda suke, wani ɗan iskan kallon ya shiga watsama Nainarh,kamar za su faɗo mata shida Yazdan aikuwa jikinta ya hau rawa ga hawaye da su ka cika idonta “mutum ko Aljana?” Fa'iz ya faɗa yana nunata da yatsa, Yumnah ce tayi saurin ce mashi “ƙawata fa ce ya Fa'iz”
“ƙawarki, ina ki ka samu wannan kayan??” rai a ɓace Noor tace “haba dan Allah ya Fa'iz, duk kunbi kun tsoratata,ƙawar Yumnah ce fa” ta faɗa tana jan hannun Nainarh “yi haƙuri kinj, muje ko” da sauri Yazdan yabi bayan su “ke kin raina mutane ko?” saurin riƙo hannunshi Fa'iz yayi, tsaki taja tana jan hannun Nainarh suka shige gidan.
jakar da Mom maryam ta basu Yumnah ta ɗauka, bayan su tabi, part ɗin dady ta fara shiga ta sanar dashi sun dawo tukun ta fice, a bedroom ɗin mom ta samu su Noor su Jamal sun lafe a jikin mom,jakar dake hannunta ta ajiye haɗe da mayafinta.
“mom maryam na gaishe da ke”
“ina amsawa, kun barosu lafiya?”
“lafiya lau” Yumnah ta faɗa tana buɗe jakar data shigo da ita, chocolate ne kala kala haɗe da wasu expensive perfume masu daɗin ƙamshi, da sauri su Aman su ka nufota, saurin rufe jakar tayi.
“kun tsaya na baku ko” turo baki su kayi “to ba namu bane?”
“ko naku ne kunsan dai bazan tasa maku su gaba ba ku shanye su yanzu” ɓata fuska su kayi kamar za suyi kuka.
ɗiba tayi ta basu sannan ta rufe jakar “wannan sai gobe” ta faɗa tana ɗaukar mayafinta da jakar “kuzo muje ayi shirin bacci, mom sai da safe”
“a tashi lafiya” mom ta faɗa, ficewa su kayi daga ɗakin su duka, bedroom ɗin da suka koma tunda su Ammar su ka zo su ka nufa Noor kuma ta nufi na Yumnah.
tana shiga bedroom ɗin kayan jikinta ta rage ta faɗa toilet,bayan kamar 10 minute ta fito ɗaure da towel, dressing room ɗin Yumnah ta nufa, body lotion ta shafama jikinta haɗe da perfume, wardrobe ta nufa, ɓangaren PJ ɗinta ta buɗe,ƴar baby doll ta ɗauka sabuwa pink color mai haɗe da top.
rigar ta zura haɗe da top ɗin sai dai bata ɗaure igiyoyin ba, gaban rigar net ne sharara ana hangen jikinta,ribbon tasa ta ɗaure gashinta perfume ta sake fesama jikinta kafin ta fice, bedroom ɗin ta koma, kwanciyarta tayi ba tare da ta kashe bulbs ɗin ɗakin ba.
Parking Motar su suka yi a parking space ɗin gidan big dady, Waseef ne ya fito sanye da cargo pant haɗe da shirt yasa p_cap haɗe shade, Irfan ne ya fito daga driver seat,suit ne a jikinshi black color idanunshi a manne da baƙin shade.
ciki gidan su ka nufa, part ɗin dady su ka nufa, a bedroom ɗin shi suka sameshi har yayi shirin kwanciya mamy na daga gefen bed ɗinshi zaune har ta gama fushin, PJ ne a jikinta riga da wando,cikin girmamawa su ka gaishe da su, da kulawa su ka amsa masu har mamy na tambayar ya mutanen gidan, da lafiya lau su ka amsa mata.
“daga ina kuke a cikin daren nan” dady ya faɗa, Waseef ne ya bashi amsa da
“dinner bikin abokin mu”
“dinner yanzu?”
“eh dady”
“shikenan sai kun dawo, amma dan Allah ku kula kundaiga yanzu yanda zamani ya canza da mata da samari sun haɗu sai shashanci, dan Allah ku kula”
“In sha Allah dady, sai da safe”
“dare naƙarayi ku dawo, dan ma kun shirya ne yasa zan barku ku tafi”
“in sha Allah dady bazamu jimaba”
“shikenan sai kun dawo” sallama su ka yi mashi su ka fice.
bedroom ɗin mom su ka nufa harta kwanta,faɗa sosai tayi masu kamar wasu ƙananun yara kan mi za su fita yanzu cikin dare, haƙuri kawai su ka bata su ka fice,a bakin ƙofar bedroom ɗinta su ka rabu Irfan ya nufi ɗakin Yumnah saboda Noor tace mashi tana nan,parking space Waseef ya koma “kayi sauri fa kaga dare nayi” ok kawai Irfan ɗin yace mashi.
bakin ƙofar bedroom ɗin ya tsaya yana nocking amma shiru ba'a amsa mashi ba, gajiya yayi da nocking ɗin ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, a kwance ya hangota saman bed ɗin idanunta a rufe tana jan numfashi a hankali alamar bacci.
ƙarasawa yayi bakin bed ɗin,kallon fuskarta yayi, baccinta take hankali kwance, murmushi ya saki yana shafa gefen fuskarta, motsi tayi kamar zata farka hankan da tayi ba ƙaramin tafiya yayi dashi ba, ya san da idonta biyu daya bani da ƙorafi.
a hankali ya duƙa yayi kissing forehead ɗinta ai kuwa ta buɗe ido dama idonta biyu kawai tayi kamar tana bacci ne ko nocking ɗin da yayi tana ji, sauri tashi yayi tsaye “dama ba bacci ki ke ba?”
“eh, ya Irfan wai mi nayi maka ka ke gudu na wannan time ɗin, ko dai bakayi farincikin zuwana bane??” ta faɗa a shagwaɓe
“nayi farincikin zuwanki mana”
“to mi yasa kake guduna” ta faɗa tana sauka daga saman bed ɗin ta nufo in da yake,faɗawa tayi jikinshi tayi hugging ɗin shi
“ko nayi maka wani laifi ne?” shafa bayanta ya shiga yi a hankali
“ba kiyi man laifin komai ba Noor, kawai wani uzuri ne ya riƙe ni”
“amma ai ba haka kake man ba duk muka zo, kofa zaman one hour ba muyi ba, a da da kake ɓata kowane lokacinka a tare da ni” tana a kwance saman ƙirjinshi take faɗar haka,cike da salon bariki take manna mashi ƙirjinta a nashi,hakan da take mashi ba ƙaramin jefashi a yanyi take ba,ɗago da kanta yayi yana kallon kyakyawar fuskarta,turo baki tayi kamar zata fashe mashi da kuka.
“kasan yanda nake ji kuwa saboda guduna da kake?” bai bata amsar tambayar da tayi mashi ba sai manne bakinsu da yayi waje ɗaya, ai kuwa da sauri ta kama tongue ɗinsa tana kissing dama abunda take so kenan,wasu irin hot kisses su ka shiga bama juna kamar za su haɗiye juna, cikin ƙanƙanin lokaci suka fita a hayycin su suna a wannan yanayin ne Nainarh ta faɗo ɗakin, Yumnah tace ta zo nan su kwanta kar a bar Noor ita ka ɗai.
wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi da sauri ta juya masu baya gabanta na wani irin duka kamar zai faɗo ƙasa, da sauri Noor ta tureshi tana faɗin Nainarh! , saurin kai duban shi yayi gareta,da gudu ta fice daga ɗakin...
______________________________
wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi da sauri ta juya masu baya gabanta na wani irin duka kamar zai faɗo ƙasa, da sauri Noor ta tureshi tana faɗin Nainarh! , saurin kai duban shi yayi gareta,da gudu ta fice daga ɗakin.
A jiyar zuciya suka shiga saukewa kamar wanda su kayi tseren gudu
“amma ba kince man ke kaɗai bace?” Irfan ya faɗa
“eh, ban san ya a kayi ta zo ba”
juyawa yayi ya nufi ƙofar fita,saurin kamo Arm ɗinshi tayi
“when zaka dawo,saboda kaifa zan kwana?”
“zuwa safe” ya bata amsa yana wani lumshe ido,gaba ɗaya jinshi yake a wani irin yanayi na daban ƙafarshi ma da ƙyar yake ɗagata
“shikenan saika dawo ka kula man da kanka” jinjina mata kai yayi ya fice daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kama igiyoyin rigarta ta ɗaure,switch ɗin ɗakin ta nufa ta kashe bulbs ɗin bedside lamps su ka kawo, kwanciya tayi saman bed ɗin,lumshe idanunta tayi tana jan iska haɗe da fesarwa,wani irin yanayi take ji a jikinta, kwata kwata ba taji kunyar ganinsu da Nainarh tayi ba sai ma haushin katse masu jindaɗi da tayi, tsaki taja tana gyara kwanciyarta.
Nainarh tana fita daga ɗakin da gudu parlor ta nufa tasan muddin ta koma bedroom ɗin da Yumnah take dole taji ba'asin abunda ya dawo da ita koma ta nufi ɗakin dan ganema idonta, a jikin pillar ta samu ta ɓuya, ajiyar zuciya ta sauke tunda take a rayuwarta bata taɓa jin haushin wani ɗan Adam ba kamar yanda take jin haushin Irfan da Noor a yanzu, ko wace irin taɓewace ta samesu haka,idan sun san suna son junansu danmi bazasu sanar da iyayen su suyi masu Aure ba amma