Showing 6001 words to 9000 words out of 88290 words
tura masu kuɗin su fara amfani dashi kafin zuwa ranar juma'ar na tafi, amma sai ta zaunar dani ta nuna man dacewar na tafi a goben shine na amince”
“da tace ki tafi a lokacin ba kiyi wani tunani ba ko akwai dalilin da yasa tace kije?”
Miƙewa brisster tayi tana ɗan dukan table ɗin dake gabanta “objection my lord”
“Overruled”Alƙali ya faɗa
komawa tayi ta zauna tana cizon yatsa na rashin bata dama da Alƙali yayi, side smile brisster hashim ya saki
amsar tambayar da brisster hashim yayi mata ta bashi
“banyi tunanin komai ba, saboda idan ahalina suna cikin matsala ta kan fini shiga damuwa akan halin da nake ciki,shiyyasa banyi zargin komai ba”
jinjina kai brisster yayi “mudi mai gadi ya sanar da koto cewa akwai wani matashin saurayi dake yawan zuwa wurin uwar ɗakin na ki, baki taɓa tunanin mike kawoshi wajenta ba , ko miye alaƙarta da shi ???"
“sunan sa Abid, ɗan ƙanwarta ne dake zaune a ƙasar waje, yana yawan zuwa wurinta duk lokacin da yazo suna samu saɓani da marigayi saboda kwata kwata jinin marigayi bai haɗu dana Abid ba, saboda Abid yaro ne mara tarbiya baya girmama na gaba da shi , gashi duk lokacin da yazo sai ya takura ma yarinyar su , hakan yasa marigayi baya son yana zuwa gidan, ita hajiya sai ta nuna ba taji daɗi ba kan nuna kyara da tsangwama da yake akan yaron, a ranar da mu kayi magana kan tafiyata ya zo gidan har saɓani ya shiga tsakanin shi da marigayi ya dake shi, abun yayi matuƙar ɓata ran hajiya har su ka samu saɓani da marigayi, bayan mungama magana da ita naje ɗakina na wanke kayan da zan tafi da su na zagaya baya zanyi shanya na hangesu ita da Abid suna tattauna wasu maganganu wanda ban san mi su ke tattaunawa ba, nayi ƙoƙarin naji abun da su ke faɗa amma abun ya gagara saboda tazara dake tsakanin mu,bayan na koma ɗakina cikin dare naji Abid ɗin yana waya a bayan ɗakina kamar yana faɗama wanda suke waya saɓanin da su ka samu da marigayi bana jin mi na ciki wayar ke faɗa masa na dai ji yana faɗin a cikin satinnan ya kamata suyi aiki a kanshi ko zai daina mashi shiga hanci da ƙudindine, na tsorata da jin abun daya faɗa har na kasa bacci , washe gari tunda safe na samu hajiya da maganar amma sai ta nuna kar na damu da abokan kasuwancin shi yake waya”
tunda Aisha ta fara jera wannan jawabin gaban hajiya Asma'u ke faɗuwa bata taɓa sanin komai dake faruwa a gidan Aisha na sane ba sai yanzu.
“abokan ka suwanci, ko kin san wane irin ka suwanci yake?, sannan wane saɓani ya shiga tsakanin shi da marigayi?”
“gaskiya ban san kasuwanci da yake ba, amma na taɓa jin labari a wurin mai gadi cewa yaron yana harkar kayan maye , kuma dukiyar da yake juyawa ta hajiya Asma'un ce ”
jinjina kai brisster yayi
“wane saɓani ne ya shiga tsakanin shi da marigayi?” ya sake maimaita mata tambayar
“gaskiya ban sani ba”
juyawa brisster hashim yayi ya kalli Alƙali “my lord , tun ranar da mai gadin gidan ya ba police duk wasu bayanai akan yaro suka tsaurara bincike sai dai kash bayan kwana biyu da fara binciken na su aka samu gawar shi yaron a cikin gidan shi anyi mashi kisa makamancin na marigayi,hakan na nufin hajiya Asma'u ta tura Aisha gida ne dan ta samu damar aiwatar da shirinta ba tare da wani ya ganota ba,sannan ta sallami ma'aikatan gidan dan kar su ga abunda zai faru,Abid ya ƙi bata haɗin kai ne shiyyasa ta tura makasan da su ka kashe cp su ka kashe shi dan kar ya zame mata matsala”
“Objection my lord”
jinjina mata kai Alƙali yayi alamar amincewa
“my lord lawyer masu ƙara na son tabbatar da laifi akan wacce nake karewa ba tare da ƙwararan hujjoji ba”
“brisster hashim ka kiyaye”
“tuba nake”
jinjina kai Alƙali yayi kafin ya ɗauki pen ɗin shi yayi ƴan rubuce rubuce
“lawyer masu ƙara ko kana da sauran wasu tambayoyi da za kayi ma malam Aisha”
“su kenan tambayoyin da nake son yi mata” brisster hashim ya faɗa, tsaki brisster taja a zuciyarta tana faɗin
“ko ina amfanin wannan tambayoyin”
“lauyan wanda ake ƙara ko kina da wasu tambayoyi da za kiyi ma malam Aisha?”
miƙewa brisster tayi “eh my lord” dama Alƙali ya bata, fitowa tayi brisster hashim kuma ya koma mazauninshi.
“malam Aisha a bayanan da hajiya Asma'u ta bada da kuma binciken da muka gudanar ya tabbatar mana da cewa kina a gidan a ranar da abun ya faru , hasalima kece ki ka fara sanar da su zuwa mugayen mutanen da su ka shigo gidan”
“wallahi brisster bana garin ita da kanta tace naje, munyi maganar da ita yau washe gari tunda safe na tafi”
murmushi gefen fuska brisster ta saki tana faɗin “ƴan uwan naki su su ka bada shedar cewa a ranar ba kije garin naku ba sai a washe garin ranar da abun ya faru”
shiru Aisha tayi ba tare da tace komai ba
“malama Aisha ke koto ke saurare?”
“ranar na tafi sai dai ban samu isa garin ba sai cikin dare,hakan yasa basu san da zuwa na ba sai washe gari”jinjina kai brisster tayi tana juyawa ta kalli Alƙali
“my lord malama Aisha ta sanar da koto cewa bata nan abun ya faru, a binciken dana gudanar ya tabbatar man da tana a cikin komai ya faru”
“binciken koto zai tabbatar da hakan, kina da sauran wasu tambayoyi da za kiyi mata”
“babu sauran wasu tambayoyi da zanyi mata”
“malam Aisha zaki iya komawa mazauninki kafin binciken koto ya kammala”
“godiya nake” ta faɗa tana ɗan rissinar da kai,barin witness stand ɗin tayi ta koma mazauninta ba tare da ta bari sun haɗa ido da brisster ba ko hajiya Asma'u.
brisster wurin zamanta ta koma itama,haka shari'ar ta cigaba da tafiya duk wasu jadawalin sunayen witness ( sheda) sai da Alƙali ya kira su gaban koto yana masu tambayoyi bayan ya kammala masu ya ba brisster's dama suma suyi masu nasu tambayoyi, ko wane sheda da kalar amsar da yake ba dawa a kan kisan marigayi CP,hajiya Asma'u tun tana sa ran kuɓuta har ta sadaƙata tasan bazata taɓa kuɓuta ba daga yanayin amsoshin da shedun ke ba court,brisster ma gwiwowinta sun sage bata taɓa shari'a irin wannan ba tana shari'a akan kisa amma kuma bata taɓa rashin nasara ba amma wannan shari'ar na neman tafi ƙarfinta , shedun da take taƙama dasu gaba ɗaya sun juya mata baya,duk wanda aka kira a cikin su abu ɗaya su ke faɗi hajiya Asma'u ta kashe mijinta kuma suna bada ƙwararan hujjoji wanda dole koto ta yarda .
brisster hashim kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha yasan zaiyi wuya yau bai yi nasara akan brisster zulaihat ba abun da ya daɗe yana jira kenan tsawan shekaru.
Magana Alƙali ya fara, tsit kotun tayi kowa na sauraron hukuncin da court zata yanke “binciken kotu ya tabbar da malam Aisha bata nan a ranar ashirin da ɗaya ga watan biyar”
Ajiyar zuciya Aisha ta sauke tana dafe saitin zuciyarta, brisster wani mugun faɗuwa gabanta yayi hajiya Asma'u kuwa tuni hawaye sun taru a cikin idanunta
“bayan kammala haɗa duk wasu hujjoji da binciken koto dana likitocin dake kula da gawar marigayi CP ya tabbatar da hajiya Asma'u itce ta kashe CP” tunda Alƙali ya fara magana brisster hashim ke sakin murmushi, brisster zulaihat kuwa banda faɗuwa babu abun da gabanta ke yi.
“kotu ta yanke ma hajiya Asma'u hukuncin kisa ta hanyar rataya tare da biyan tara ta naira milayan hamsin”
Wani irin murmushin farin ciki barisster Hashim ya saki yana kallon ƴan uwan shi wanda hukuncin yayi masu dai dai,a ɗayan ɓangaren kuwa barisster Zulaihart wani irin tashin hankali mara misaltuwa ta tsinci kanta, da dama mutanen dake Court ɗin abun yayi masu daɗi yayin da wasu ke tausaya ma Hajiya Asma'un.
ana cikin jimamin hukuncin da court ɗin ta yanke sai ga saƙo daga fadar shugaban ƙasa na nemama Hajiya Asma'u sassaucin kotu daga rataya zuwa ɗaurin rai da rai tare da biyan tara ta nera miliyan ɗari saɓanin hamshin.
Ran barisster hashim idan yayi dubu ya ɓaci ba haka yaso ba yaso hukuncin kisa aka yanke mata ta hanyar rataya bai so ɗaurin rai da rai ba amma idan ya tuna ba wai zata fito bane sai hankalishi ya kwanta, mom ta ɗan ji sassauci da ba kisa bane ɗaurin rai da rai ne sai dai idan ta tuna halin da hajiya Asma'u da nainarh za su shiga hankalinta na tashi.
wasu daga cikin mutane kwata kwata ba su so haka ba gani suke kamar wata maƙarƙashiya ce ake ƙullawa.
Miƙewa Alƙali yayi gaba ɗaya su ka miƙe,ƙofar office ɗin shi ya nufa kamar jira a ke Alƙali ya fita koto ta ɗauki haya niya kowa da abunda ke fitowa daga bakin shi,can compound ɗin curt ɗin kamar zai fashe saboda haya niyar mutane, mom tunda Alƙali ya fita ta kifa kanta saman desk ko motsin kirki ta kasa yi,matsowa wannan security guard ɗin tayi tana bata haƙuri, miƙewa brisster hashim yayi yana wani gyara zaman rigar shi fuskarshi ɗauke da murmushin mugunta, ɗaya bayan ɗaya mutane su ka fara fita daga cikin kotun suna tofa albarkacin su.
hanyar fita prison officers suka nufa da hajiya Asma'u, da ƙyar take taka ƙafafuwanta suna zuwa tsakiyar court ɗin ta yanke jiki ta faɗi a sume, salati mutanen da su ka rage a ciki su ka rabka da sauri mom ta miƙe kusan a tare su ka isa inda hajiya Asma'u ke yashe a ƙasa ita da wasu mata guda biyu, amma kafin su ƙaraso ma'aikatan gidan yarin sunyi mata rumfa mom ka ɗai su ka bari ta ƙarasa in da take, jijjigata ta shiga yi tana kiran sunanta amma ko gezau ba tayi ba, ɗaya daga cikin prison officers ne ya miƙoma mom ruwa,a hannu ta zuba ruwan ta shafa mata a fuska, tayi hakan kusan sau ba adadi amma bata farfaɗo ba mom bata san lokacin da ta fashe da wani matsanancin kuka ba,doctors ɗin gidan yari ɗaya daga cikin jami'an gidan yarin ya kira, ba'ayi five minutes ba sai gasu sun ƙaraso, nurses huɗu mata ne su ka kamata su ka ɗaura saman stretcher,ficewa su kayi da ita daga cikin court ɗin bayan su mom tabi tana goge hawayen dake zarya saman kumatunta, a hanzarce security guard ɗinta tabi bayan ta har zuwa in da su kayi parking Ambulance,ganin fitowar mom ne yasa sauran security guard ɗin nufota da sauri saboda mutane da ƴan jarida da suka fara jefa mata tambayoyi harda na hauka, wasu ma a fakaice magana su ke gaya mata,buɗe Ambulance ɗin ɗaya daga cikin officers ɗin yayi ciki su ka saka hajiya Asma'u,maganganu mutane ke jifa ma mom,tana jinsu amma tayi kamar bata jin mi suke cewa tana nan tsaye har sai da taga ficewar Ambulance ɗin daga cikin court ɗin tukun ta juya da nufin ta koma office ɗinta, juwar da za tayi taga brisster hashim tsaye ya harɗe hannuwa saman chest ɗin shi, wani ɗan iskan murmushi ya sakar mata yana tunkaro in da take tsaye, bashi hanya security guard ɗinta su kayi da alama dai shima ba ƙaramin mutum bane.
zuba mashi ido tayi har ya ƙaraso inda take, murmushi ya saki cikin wata irin murya kalar ta ƴan duniya yace
“ya dai lawyer Al'ummah?, yau ina goyan bayan Al'ummar taki yake?”
ɗauke kai mom tayi wani ƙululun baƙin ciki na tokare mata maƙoshi, dariya brisster hashim ya saki
“see u next time” ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya, barin wurin mom tayi securitys ɗinta su ka bi bayanta, da kallo brisster hashim ya bita har ta ƙarasa inda su kayi parking motocin su,duk Abun da ke faruwa balqis na tsaye tana kallo,hawaye ne su ka taru a idonta ta rasa dalili rashin jituwar brisster hashim da mom, juyawa tayi ta nufi motocinsu ta shiga barin court ɗin su kayi baki ɗaya.
wannan lawyer ce ta nufo brisster hashim dake tsaye
“brisster na lura so ka ke baƙin ciki ya kashe brisster zulaihat a yau ” ta faɗa tana sakin murmushi, martanin murmushi ya sakar mata yana
faɗin “yanzu ta fara gani in dai ni ne”
“Allah ya shirya ka, gaskiya baka kyautawa matar yayan ka ce fa”
“na tsaneta bana son ganinta” ya faɗa yana barin wajen, bin bayan shi lawyer tayi.
waya brisster ta ɗauka tayi dialing number yumnah bugu ɗaya tayi picking “ku fito ina parking space ku same ni” tana gama faɗa tayi rejecting ba tare da ta tsaya jin mi yumnah za tace.
miƙewa yumnah tayi tana kallon nainarh data zuba uban tagumi, girgiza kai tayi tana nufar ta, dafa kafaɗar tayi firgigit nainarh tayi ta miƙe a tsorace har sai da gaban yumnah ya faɗin
“yumnah an gama shari'ar ne?” nainarh tajefa mata tambaya
“ban sani ba, amma dai mom tace mu sameta waje ban sani ba ko an gam....” tun kafin ta ƙarasa nainarh ta nufi hanyar fita da sauri, bin bayanta yumnah tayi.
tana fitowa ƴan jarida su ka yo mata caaa, sai jefa mata tambayoyi su ke marasa kan gado, ruɗewa tayi ta rasa in da zata dosa hawaye har sun fara zuba daga idanuwanta,ganin halin da take ciki ne yasa securitys ɗin nufarta, zagayeta su kayi suna tutture ƴan jaridar, in da mom ke tsaye tana jiran su suka nufa,maganganun mutane ne su ka fara ɗaukar hankalinta da irin kallon da suke binta da shi
“itace ɗiyarta ko kunya ba tajiba ta kashe ma yarinya ubanta saboda neman duniya kawai”
“ai hukuncin da kotu ta yanke mata bashi ya kamata da ita ba hukuncin kisa ne dai dai da ita”
“saboda brisster zulaihat yasa ba'a yanke mata hukuncin kisa ba, kasan suke da ƙasar sai yanda su kayi da talaka” maganganun dake fitowa daga bakin mutane kenan, tunda ta fara sauraronsu gabanta ke faɗuwa.
bayan su yumnah ta biyo sai turo baki take kamar zata fashe da kuka,da sauri nainarh ta nufi mom hawaye na fita daga idanunta “mom ina ummah?” shine tambayar data jefa ma brisster, juyawa mom tayi ta shige motar ta ba tare da tace mata komai ba, motar da ke bayan wacce brisster ta shiga security guard ɗin ya buɗe ma nainarh da nufin ta shiga, a masifance ta maida marfin ƙofar ta rufe tana juyawa zata nufi cikin court ɗin, da sauri brisster ta fito tana faɗin “kar ku barta ta wuce”
umarnin mom su ka bi, duk yanda nainarh ta so shiga cikin court room ɗin hanata security su kayi ƙarshe data gaji zubewa tayi ƙasa tana fashewa da wani matsanancin kuka,kamata mom tayi ta miƙar da ita tana lallashinta su ka nufi mota, itama daurewa kawai take yumanh da yake saurin kuka ne gareta har ta fara matse ƙwalla abun tausayi, motar da su ka zo ita da nainarh ta shiga nainarh kuma a tare su ka shiga da brisster, kuka take kamar ranta zai fita tun brisster na daurewa har itama ta kaida zubar da ƙwalla, a tamanin security guard ɗin su ka shiga motocin su, da gudun gaske su ka fice daga court ɗin.
tun daga farkon shigowa anguwar zaka tabbatar da anguwa ce ta manyan mutane masu faɗa aji a cikin ƙasa,manyan gine gine ne ta ko ina,tun daga nesa ƙarar jiniyar motocin su ka cika anguwar,da wani irin matsiyacin gudu su ka shigo anguwar, miƙe titin su kayi shantal sai da su ka kusa kai ƙarshen shi tukun suka karya kwana,tun daga farkon street ɗin da su ka shigo check point ne na sojoji,kowanen su ƙatuwar bindigace a hannunshi yayin da wasu ke soke a ƙugunansu, tun kafin motocin su ƙaraso sojojin dake zaune bakin ɗan gate ɗin da su ke sawa su ka buɗe masu, suna isowa babu jira suka wuce,tafiyar kusan minti goma sha biyar su kayi a ƙalla sun wuce check point na sojoji da ƴan sanda kusan guda goma kafin su ka kawo bakin wani ƙatafaran gate,ba sojojin dake gadin gate ɗin ba shi kanshi gate ɗin abun kallo ne, wani irin zungureren gate ne ƙaton gaske.
ga wasu irin manya manyan sojoji dake gadin shi, kwata kwata babu ɗigon imani a fuskar su,sojojin dake zaune saman bench ne suka miƙe da sauri lokacin da motocin su ka ƙaraso bakin gate ɗin,wani mahaukacin horn akayi da motar dake gaba da sauri wani soja ya danna wani abu dake hannunshi mai kama da remote nan take gate ɗin ya shiga zugewa zuwa gefe ɗaya,da gudun gaske suka danna kan hancin motocin zuwa ciki, masha Allah na furta a yayin da nayi arɓa da ƙaton Castle ɗin da su ka shigo,gidajene a cikin shi na alfarma hagu da dama aƙalla za su kai kimanin guda hamsin kusan a jere suke sai dai akwai tazara mai ɗan yawa a tsakanin ko wane gida, security guard ne ke yawo a cikin Castle ɗin ta ko ina,babu abun da babu a ciki kama daga clinic ne sport center, garden babu abun da babu a ciki, duk wani abu na more rayuwa a kwaishi a cikin estate ɗin.
a ƙalla sunyi tafiyar kusan minti biyar kafin su ka kawo bakin wani ƙaton luxury Villa wanda yafi ko wane gida dake cikin estate ɗin girma haɗuwa da tsaruwa, yana yin shi ma da ban yake da gidajen dake ciki shi ba'a jere yake da sauran gidajen ba yana a tsakiyar su yana fuskantar gate ɗin estate ɗin, water falls ne masu matuƙar kyau da ban shawa'a a bakin villa ɗin da a ƙalla ya kai hawa biyar, parking motocin su kayi...
_*Episode 5_6*_
*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘
___________________________
A zaune take saman royal sofa mai mazaunin mutum uku dake a katafaren main parlorn dake villa ɗin,faɗa maku tsaruwa da haɗuwar parlorn ɓata lokaci ne,royal sofas ne a cikin shi kusan set shidda, komai na cikin parlorn white and golding color ne,wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke tashi a cikin parlorn haɗe da sanyi AC,parlorn iya haɗuwa ya haɗu.
duguwar rigar lace ce