Showing 87001 words to 88290 words out of 88290 words
Chapter 30 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete
jikin ki” kauda Nailarh tayi yanayin fuskarta na canzawa zuwa tsantsar ɓacin rai “please baby ki amsa mana” Mrs Malika ta sake faɗa, ko kallon in da take Nailarh ba tayi ba,wayar tasa a speaker daga cikin wayar Muryar mutumin ta bayyana
“hello Nailarh” wani ɗan iskan kallo Nailarh ta watsama wayar without answering him
“baby are you hear me” ya sake faɗa,banza Nailarh tayi da shi,ajiyar zuciya ya sauke, a hankali yace “ya jikin naki,fatan da sauƙi,ina nan shigowa next week na dubaki” wani ɗan iskan tsaki taja tana ƙoƙarin sauka daga saman bed ɗin,saurin riƙeta Aunty Sophia tayi tana girgiza mata kai,ran Mrs Malika ba ƙaramin ɓaci yayi ba ta tsani wannan wulaƙancin da Nailarh ke mashi “baby are u Angry with your dady?” ya faɗa cikin kwantar da murya,hararar wayar tayi “who are you to said that,you will never be my father forever”
saurin cire wayar Mrs Malika tayi a speaker tana kara ta a kunenta “I'm sorry I will call u later” Bata jira jin mi zaice ba tayi rejecting call ɗin,rai a ɓaci ta kalli Nailarh
“baby mi yasa ki ke haka,ya damu da ya san halin da ki ke ciki shine zaki mashi haka??” ko kallonta Nailarh ba ta yi ba “mi yasa ko wane lokaci ki ke son wulaƙantashi,shifa Kamar mahifinki ne” sai a sannan Nailarh ta kalleta “he's not my father,I hate him”rai a ɓace Mrs Malika ta buɗe baki da nufin magana Nurse ɗin tayi saurin cewa “Be patient Ma'am, this may affect her health, I'm sorry” sai da nurse ɗin tayi magana tukun ta tuna da condition ɗin Nailarh,iska mai zafi ta furzar daga bakinta,har ta nufi sofa sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin rai a ɓace,ko kallonta Nailarh ba tayi ba,kwantar da kanta tayi jikin pillow haɗi da lumshe idanunta,Aunty Sophia just looked at her without saying anything,hannunta ta kama,note ɗin dake jikin hannunta Aunty Sophia ta zubama ido,buɗe ido Nailarh tayi tana kallonta,rufe mata hannun kawai Aunty tayi ba tare da tace mata komai ba itama Nailarh ɗauke idonta tayi, ficewa Nurse ɗin tayi,bayan kamar 2 minutes da fitarta wata Nurse ta shigo ɗauke da gown da body lotion cikin ɗakin ta nufo,gaishe da Aunty Sophia tayi kafin ta kalli Nailarh,ya jiki ta fara tambayarta kafin tace “It's time to take a bath ma'am” Nailarh looked at her before she looked away, da sauri Aunty Sophia tace “ok, bring the gown and I will help her to take a bath, thank you” ba tayi musu ba ta bata gown ɗin,zama tayi kan chair dake gaban bed ɗin, taimaka ma Nailarh Aunty Sophia tayi zuwa toilet,Sosai toilet ɗin ya haɗu kamar a gida,duk wani abu da za su buƙata akwai a ciki,ruwa Aunty Sophia ta haɗa mata,sanin halin Nailarh da koda tana lafiya ba wanka take da kanta bane yasa Aunty Sophia ta taimaka mata tayi,wani iri Aunty Sophia taji wannan shine the first time tayi ma Nailarh wanka bayan ta girma,hawaye ne su ka taru a idanunts lokacin da ta tuna yarintar Nailarh,da sauri tasa hannu ta goge kafin Nailarh ta gani,shaf shaf ta taimaka mata tayi wanka har ta canza mata rigar jikinta ta shafa mata lotion,ficewa su ka yi zuwa ɗakin,Nurse ɗin kaɗai su ka samu su luna sun fice da alama wajen Mrs Malika su ka nufa, taimaka mata tayi ta koma saman bed,kwanciya tayi,duvet Aunty Sophia ta ja mata ta rufe mata rabin jikinta,lumshe ido tayi kamar mai bacci,gown ɗin Nailarh ta cire Nurse ɗin ta kwashe ta fice.
*ABUJA NIGERIA*
gaba ɗayan su ne a bedroom ɗin mom ya Naeem,ya Adnan sai Irfan,mom na daga zaune gefen bed ɗin ta yayin da ya Adnan ke zaune saman stool a gaban mirror sai ya Naeem dake zaune kan sofa shida Irfan,tunda su ka fara magana kan Auren shi da Noor ƙala baice masu ba kanshi na ƙasa,ɗaya bayan ɗaya yake sauraren su
“idan har ba so ka ke kaga ɓacin raina ba,ka ƙyale masu ƴarsu kawai kaje ka nemi wata,Allah zai baka wacce ta fi ta” mom ta faɗa tana kallon Irfan ɗin
“akwai ƙanwar Usman abokin aikina yarinyar tana da hankali ga tarbiyya,Ni zan mashi magana sai kaje ka ganta idan tayi maka shikenan a gidan shi take zaune” ya Naeem ya faɗa yana kallon Irfan ɗin
“idan ba tai maka ba ma ga Kairiyyah nan ɗiyar Aunty Adama sai ka nemeta,tama fi Noor natsuwa da komai,kuma Mahaifinta bazai hanaka ba ko ita Aunty Adama” a cewar ya Adnan
“gaskiya bazan iya da tashi hankalin mama Ameenah ba,kawai ni nayi mashi alƙawarin ƴata indai har yana so,dama tuna farko ita nake da burin ya Aura ba Noor ba” sai a lokacin Irfan ɗin ya ɗago ido ya kalli mom,gaba ɗaya su ka zuba ma mom da tai magana ido,ya Adnan ne yace “dama kina da wata ƴar ne bayan Yumnah bamu sani ba?”
“NAINARH nayi mashi alƙawarin ta muddin yana so” tunda mom ta fara magana gaban Irfan ya faɗi,wani irin mugun ɓacin rai ne ya rufeshi, mom tama rasa wa za tace ya Aura sai wannan yarinyar,ya Adnan da ƙyar ya haɗiye wani abu daya tsaya mashi a maƙoshi,kwata kwata baiyi tunanin mom za tace haka ba,ajiyar zuciya ya Naeem ya sauke yana faɗin
“gaskiya tana da hankali da natsuwa uwa uba tarbiyya da Ilmi, gaskiya naji daɗin jin haka mom,wlh ni ban ma yi wannan tunanin ba saboda ganin halin da take ciki,kinga idan ya Aureta hakan zai rage mata raɗaɗin rashin iyayenta,amma mom dangin Mahaifinta kina ganin za su Amince?”
“wannan ba matsala bace Naeem,tunda mahaifinta ya rasu su ka datse duk wata alaƙa dake tsakanin su da ita”
“duk da haka mom,dole su sani”
“zan sanar da su amma sai in ya Amince itama ta aminta da shi tukun,idan duk sun amince sai na sanar da su yanda idan ba su amince ba ina da right ɗin da zan maka su a Court” kallon Irfan ɗin ya Naeem yayi “kaji abunda tace,minene ra'ayinka akan hakan,kana sonta ko dai mu bari kayi tunani”
“yaya mi yasa baza ku fahimce ni ba, ni gaskiya bazan iya son wata ba bayan Noor” da mugun sauri su ka shiga kallonshi, wato duk bayanin da suke da bashi haƙuri ba fahimtar su yake ba “dan mom fatilah Bata son Auren ai ba ita zata ban Aurenta ba kuma ba da ita zan zauna ba ni gaskiya Noor nake so,dukan ku ba wanda hakan bata faru ba lokacin Auren shi kuma ai kuna zaune lafiya,sai ni za a hana ni,ni gaski...” bai ƙarasa ba ta dalilin marin da ya Naeem ya ɗauke shi da shi,dafe cheek ɗin shi yayi yana kallon ya Naeem da kallo ɗaya zaka mashi ka hango tsantsar ɓacin da ranshi yayi,tashi Irfan ɗin yayi rai a ɓace ya nufi ƙofa,kuka mom ta fashe dashi,da sauri ya Adnan ya nufo inda take,hannunta ya kama cikin nashi “dan Allah mom Kar wannan abun da yayi ya ɓata ranki,wallahi ko yana so ko bai so bazai Aureta ba” tashi ya Naeem yayi ya nufi Irfan ɗin dake bakin ƙofa
“wannan yanayin ka ke son gani a tare da ita,to bari kaji na faɗa maka,to bari kaji kai baka isa ta dalilinka ka hana mata zaman lafiya ba,dan mun zauna muna baka haƙuri it doesn't mean cewa bazamu iya tursasamaka ba,wllh kaji na rantse baka ba wannan yarinyar”
“haba second father dukan ku kun Auri muradin ranaku sai ni ne zaku hana”
“ka dai ji abunda na faɗa maka,idan kuma ban isa ba to”yana faɗa hakan ya bar wurin ya nufi mom,ya Naeem yana da saurin fushi amma yana da saurin sauka,ficewa Irfan ɗin yayi rai a ɓace,karo su ka yi da juna,gaba ɗaya mug ɗin Coffeen dake hannunta ya zube mata a jiki,ƙara ta fasa saboda azabebben zafin daya ziyarci ganganr jikinta.