Showing 21001 words to 24000 words out of 88290 words

Chapter 8 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

408

momy ”

yarinyar ta faɗa tana nufar elevator part ɗin mom.


girgiza kai kawai mahaifiyarta ta tayi tana faɗin “Allah ya shirya ki Enaaya”


A parlor ta samu mamy zaune saman sofa kayan ɗazu ne a jikinta,bakinta ɗauke da sallama ta ƙarasa ciki.


fuskar mamy da fara'a ta amsa mata sallamar tana sannu da zuwa,wuri ta samu saman sofa ta zauna.


“in wuni mamy, ya gida”
“lafiya lau NADIYA, ya gida?”
“lafiya lau”
“masha Allah,Ina uwayen sanabe ko ana islamiyya?”
murmushi nadiya ta saki tana faɗin“A'a ta shiga part ɗin mom ne” jinjina kai mamy tayi tana maimaita kalmar part ɗin mom.


“watau ni tafi ƙarfin ta zo ta gaishe ni,shine ta wuce wajen ƙanwar uwarta, tunda ban haifi mahaifinta ba ai ba tazo ta gaishe ni ba,zata zo ta sameni ne” murmushi kawai Aunty nadiya tayi dafa gaskiyar enaaya mamy ba dai faɗa ba.


“tana nan zata shigo,na san duk saurin ta haɗu da dady ne”
“A'a tayi zamanta kawai ba sai ta zo ba”
“kiyi haƙuri mamy idan ranki ya ɓaci”

uhmm kawai mamy tace mata ba tare da ta sake cewa komai ba.


sallama su ka ji daga bayan su ,Aunty nadiya ce kawai ta kai dubanta ga mai shigowa,riga da skirt na atamafa ne a jikinta ta yafa mayafi tun daga kanta fuskarta tasha make_up,manyan idanunta sun sha eyelashes na company, hand bag ɗinta ce riƙe a hannunta yayinda yaranta ke biye a bayanta mace da namiji ,namijin ya ɗau wankan jeans and t_shirt,hannuwan shi zube su ke cikin aljihun wandon shi kamar wani babban mutum, fuskar nan tashi a ɗaure take, ƴar macen ce ke sanye da Pakistan dress riga da wando ta yafa mayafin kayan saman kafaɗar ta, anyi mata parking gashinta a tsakiyar kai,light make_up ne a fuskarta,ƙafarta sanye take cikin wedge shoe masu kyan gaske, itama sunglasses ne a fuskarta mai butterfly kamar Enaaya.


da sauri Aunty nadiya ta miƙe fuskarta ɗauke da murmushi ta nufi matar dake shigowa, hugging ɗin juna su kayi,gaba ɗayan su suna sakin murmushi.



“sister NAFISAT shine baki faɗa man kuna tafe ba ai dana jira ku” Aunty nadiya ta faɗa yayinda su ke raba jikinsu daga na juna.


“uhmm ki bari kawai nima ban san da fitar ba, ina zaune ya NAEEM yace wai mu zo,Ni ban ma san mi ke faruwa ba” ta faɗa tana ɗan ya mutse fuska.

“tare ku ke dashi ne?”
“eh ajiye mu yayi yaje ya dawo”

zuba masu ido mamy dake zaune tayi tana kallon su,wurin mamy Aunty nafisat ta nufa, gaishe da ita tayi cikin girmamawa,mamy da fara'ar ta ta amsa mata,suma yaran gaishe da mamy da Aunty nadiya su kayi,taɓe baki mamy tayi

“miskili kafi mahaukaci ban haushi,yau kuma aljanun sun bari a zo a gaishe ni kenan?”


ɗan taɓe baki Aunty nafisat tayi tana dallama yaron harara da duk ya wani ɓata fuska shi dole an sa shi abunda baiyi niyya ba,da sauri ya kalli gefe ganin kallon da mahaifiyar tashi tayi mashi,tsaki taja.




“momy nadiya wai ina Enaaya ne?” ƴar macen ta faɗa
“tana part ɗin mom” ko gama faɗa nadiya ba tayi ba ta juya da sauri ta nufi ƙofar fita,bin bayanta namijin yayi, da sauri Aunty nafisat ta daka mashi tsawa


“ina za ka ,ko kaima Enaayar ƙawarka ce?”
“ai wajen Aunty Yumnah zan je” ya faɗa yana ficewa daga parlor ba tare da ya tsaya jin mi Aunty nafisat ɗin za tace,jinjina kai Aunty nafisat tayi.



“wai shi mi a kayi mashi yake wannan kumbura fuskar?” mamy ta tambaya


“saboda nace sai mun fara shigowa nan shi baiyi niyyaba shine yake wannan cin ɗacin”


“kaga ƴan bantan uban yara sun raina ni,sai kace wata uwar nake masu da ba sa son zuwa in da nake”


“iskanci ne kawai irin na su” a cewar Aunty nadiya

“zanyi maganin su ɗaya bayan ɗaya ne”mamy ta faɗa.
canza fira su kayi,su Aunty nafisat Nama mamy jajen abunda ya faru da mom,taɓe baki kawai mamy tayi ba tare da ta ce masu komai ba.




𝑸𝒖𝒆𝒆𝒏 𝑲𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒕💫



ƙarar takun takalminta ne ya cika masu kunne,da sauri su ka kai duban su gaba bakin ƙofa,mamaki ne gaba ɗaya ya cika su,dariya fa'iza ta saki tana faɗin


“ƙamshi duk ya cika mana hanci kace uwayen mata ne a hanya” tsayawa Enaaya tayi tana wani tsuke baki


“kar wanda yasa ran zanyi mashi oyoyo,saboda wannan kwalliyar ta dady ce” ta faɗa tana wani yi masu fari da ido ta cikin glass, murmushi su saki

“yanzu baby Enaaya ko ni baza kiyi ma oyoyo ba” Yumnah ta faɗa tana wani marairaice fuska.



“gaskiya yau sai dai kiyi haƙuri Aunty Yumnah kwalliyar nan ta dady ce,ki bari idan na dawo daga wurin shi nayi maki oyoyo”


tsuke fuska yumnah tayi tana riƙe ƙugu“ai kuwa bana so”
“shikenan tunda so ki ke su Aunty balqis suyi mana dariya” Enaaya ta faɗa tana nufar stairs case dake hannun daman parlor,tana tafiya tana wani jujjuya jiki.


murmushi kawai balqis tayi tana faɗin “manyan mata sun hallara kowa yayi ta kansa” dariya su ka kwashe gaba ɗayan su.




*KITCHEN*



Gaba ɗaya masu aikin gidan suna kitchen domin lokacin fara aikin dinner yayi,a hankali take tafiya dan karma taji ƙarar takalminta
alama tayi ma masu aikin dake ciki da kar suyi magana,da gudu ta nufi Eishrat dake tsaye gaban fridge tana jera drinks,kamar daga sama taji mutum ya faɗa saman bayanta, ƙara ta saki tana jefar da lemun dake hannunta,dariya ta fashe da ita.


“gaskiya chef Ishrat kin cika tsoro” ajiyar zuciya Ishrat ta sauke dan ba ƙaramin tsorata tayi ba saboda bata san da shigowar ta ba sai dai kawai tajita a jikinta.


tsuke fuska Eishrat tayi tana
“amma baby Aneesah kin raina ni da yawa” dariya Aneesah ta kwashe da ita
“ba wani kin dai cika tsoro ne”

“to naji,saukar yaushe?”

yamutse fuska Aneesah tayi “yanzu muka zo da momy fatan kin ajiye man Alƙawari na?”

yana yin fuskar Eishrat ne ya sauya “Ayyah! baby Aneesah ban san za kizo yau ba”

ɓata fuska Aneesah tayi “chef Eishrat na fa sanar dake jiya, ko kin manta na kiraki da landline ɗin kitchen?” Aneesah ta faɗa tana tsuke baki

“sorry baby Aneesah mantawa na yi,amma yanzu zan haɗa maki”

ɓata fuska Aneesah tayi “har dady ya fita baki kammala haɗa man ba”

murmushi Ishrat ta saki

“wasa nake maki baby, tunda ki ka sanar da ni zuwan ku na haɗa maki”


da sauri Aneesah ta dafe saitin zuciyarta tana wani lumshe ido

“wai Allah! har kin sa hankali na ya kwanta,da yau kin sa sister Enaaya tayi man dariya, duk wannan saurin da nake dan kar ta rigani ba dady wani abu”

“Ayyah sorry,na san ta rigaki dan tun ɗazu tana part ɗin shi”

yamutse fuska Aneesah tayi “ita komai nata cikin sauri take yin shi,ai na san duk abun da zata bashi bazai kai wanda zan kai mashi ba”

“nima ina fatan haka, bari na shirya maki komai” Ishrat ta faɗa.

ƙaton wooden tray Ishrat ta ɗauka, fridge ta buɗe fruit salad ta ɗauko a cikin bowl sannan ta ɗauko yogurt daga gani haɗin gida ne mara zaƙi da lemun wanda shima haɗashi tayi da kanta sai chocolate cake.

Murmushi Aneesah ta saki ganin abun da tafi buƙata,dish rag ta nufa cups ta ɗauko da fork guda biyu ta ɗaura saman tray,ficewa su kayi daga KITCHEN ɗin Aneesah na gaba yayin da Ishrat ɗin ke biye da ita.

bakin su ɗauke da sallama su ka shiga cikin parlor,su Yumnah na nan zaune kamar yanda Enaaya ta barsu,Jamal na kwance saman sofa yayi pillow da laps ɗin Yumnah.

murmushi su ka saki yayin da su ke amsa sallamar da su kayi,sama Aneesah ta nufa ba tare da tace ma kowa ƙala ba suma binta su kayi da ido dan sun san ba lallai ta tanka masu ba tana sauri taje wurin dady.

bin bayanta Ishrat tayi ,dariya fa'iza ta saki tana faɗin “yan bantan uban yara kowa zai haƙura ya barma wani dadyn a cikin su?”

“rabu da ƴan ƙwal uba sun gama iskancin su su barma su mom majin su,yara sai kilibibin masifa”
a cewar Balqis, murmushi laatifa ta saki

“kar kuga laifin su,kuma da kune a matsayin su na san sai kunyi abun da yafi nasu”

“haba Aunty laatifa mu mi yasa ba mu yima Abbah haka”

“babu face ne shiyyasa” murmushi kawai su kayi ba tare da sun ce komai ba.


A kishingiɗe yake saman rug carpet dake katafaren parlon shi, ya ɗaura kanshi saman tum tum yayin da Enaaya ke gefenshi ,cike da salo da kisisina take bashi labarin school ɗin su,ya ƙafeta da ido sai sakin murmushi yake.


sallamar Aneesah da Ishrat ce ta katse masu firar da su ke, waro ido waje Enaaya tayi yayinda take miƙewa tsaye
“wayyo Allah nah!, sister Aneesah dama za ki zo” Enaaya ta faɗa tana yarfe hannu

murmushi Aneesah ta saki tana ƙarasowa ciki, da sauri Enaaya ta nufeta, hugging ɗin juna su kayi sai sakin murmushi su ke,raba jikin su su kayi.

gaishe da junansu su ka shiga yi kamar wasu manyan mutane, Ishrat da dady ban da sakin murmushi babu abun da su ke.

cikin parlor Ishrat ta ƙarasa a gaban dady ta ajiye tray

“barka da hutawa dady” murmushi dadyn ya saki

“lafiya lau Ishrat,sannu da ƙoƙari” murmushi kawai Ishrat ɗin ta saki tana nufar ƙofar fita

“thank u” Aneesah ta faɗa, alamar jinjina Ishrat ɗin tayi mata tana ficewa daga parlorn.

wurin dady Aneesah ta ƙaraso tana sakar mashi murmushi haɗi da fari da idanu, murmushi kawai dadyn ya saki yana girgiza kai lamarin su Aneesah na matuƙar bashi mamaki.

a saman rug ɗin su ka zauna, gaishe da dady Aneesah tayi yayinda take zuba mashi lemu a cup,cikin kulawa dady ya amsa gaisuwar yayin da yake ƙarɓar cup ɗin lemun da take miƙa mashi.

a tare su ka shiga cin chocolate cake ɗin banda dady saboda ciwan sugar
fira su ka shiga zuba mashi yan sauraron su.


Aunty nafisat sun jima a part ɗin mamy kafin su ka shigo part ɗin mom lokacin har su mom Maryam sun tafi ya rage saura fa'iza da Yumnah kawai, nainarh har time ɗin tana kwance a bedroom ɗin Yumnah.

bedroom ɗin mom su ka shiga a zaune su ka sameta bakin bed ɗinta tunda su mom Maryam su ka tafi take a nan zaune.

cike da girmamawa su ka shiga gaishe da ita tana amsa masu cikin kulawa,sosai su ka nuna alhinin su kan abunda ya faru da ƙawar mom ɗin.

tambayar su Aneesah mom tayi dan tun ɗazu suna part ɗin dady ba su fito ba, murmushi kawai tayi ko da su ka sanar da ita suna can.


fira su ka shiga taɓawa sama sama har aka fara kiran sallar magrib, bedroom ɗin Yumnah su ka nufa domin yin sallah,sunyi mamakin ganin nainarh dan basu san da zamanta a gidan ba,kasa haƙuri Aunty nafisat tayi har sai da ta tambayi Yumnah wacece,faɗa mata ko wacece Yumnah tayi.


taɓe baki kawai Aunty nafisat ɗin tayi Aunty Nadiya kuwa ko kallon in da su ke ba tayi ba tana sallame sallah ta fice daga ɗakin zuwa na mom, anan ta samu Aneesah da Enaaya sai zubama mom fira su ke Jamal na gafen su zaune.

Aunty nafisat ma data gama sallah bedroom ɗin mom ta koma,ko da lokacin sallar isha yayi a nan su kayi ta,suna zaune saman carpet sallame sallar su kenan a kayi nocking ƙofar bedroom ɗin.


da sauri Enaaya taje ta buɗe, a tsaye suke su biyu ɗaya suit ne a jikinshi yayin da ɗayan ke sanye da Army trouser da white ɗin shirt.

Kamannin fuskar su ka ɗai zai tabbatar maka da su ɗin jinin dady da mom ne ba kamar mai Army trouser ɗin.


Da gudu Enaaya ta faɗa saman jikin mai Army trouser ɗin wando tana faɗin “oyoyo dady NAEEM ashe da rabon mu gana yau”

dariya su ka saki gaba ɗayan su

“ai kuwa da rabon mu gana, ya school?” ya faɗa yayinda yake raba jikinsu

“Alhmdllh dady NAEEM,wai ina ka shige kwana biyu bana ganin ka?”

“aiki ne ya yi man yawa baby Enaaya,kuma ma ai idan kina son gani na kin san in da zaki same ni”

ɗan zaro ido tayi tana kallon wanda ke kusa dashi “wannan maganar tafi karfina dady NAEEM,ga dady nah nan ka tambaye shi” ta faɗa tana komawa cikin ɗakin da gudu.


murmushi kawai su ka saki ya NAEEM na faɗin “kenan dai ADNAN kai ke hanata zuwa gida na?” ya faɗa yana ɗan tsuke fuska.

“haba SECOND FATHER sai ka ce baka san sharrin Enaaya ba,ni ƙarya take man”

cikin ɗakin su ka ƙarasa ya NAEEM na faɗin “yanzu dai maganar wa zan kama tsakanin ku?”

“tawa mana dady NAEEM” Enaaya ta faɗa tana wani marmar da ido.


da sauri ya NAEEM yasa hannu yana toshe bakin shi haɗi da ɗan zaro ido kamar yanda Enaaya tayi ɗazu, girgiza mashi kai ta shiga yi alamar kar ya faɗa tana zare ido.

dariya gaba ɗayan su suka sa dan sun san saboda mi ya NAEEM yayi mata haka watau dadyn ta ƙarya yake.

da gudu Aneesah ta faɗa jikin ya ADNAN tana mashi oyoyo, Jamal ma nufo su yayi,Barka da zuwa yayi masu yana koma bakin bed daya ta so.

gaishe da ya NAEEM Aunty Nadiya tayi tanama ya ADNAN sannu da dawowa,hakama Aunty nafisat gaishe da su tayi.


ta shi su kayi su ka fice daga ɗakin ya zama daga mom sai su ya NAEEM ɗin,a gabanta su ka zo su ka zauna ƙasa suna tanƙwashe gwiwowin su kamar masu neman gafara.

cikin girmamawa su ka shiga gaishe da ita tana amsa masu cike da kulawa.

“ya aiki” ta tambaye su da Alhmdllh su ka amsa mata haɗi da jajanta mata abun da ya faru.


“in sha Allah gaskiya za tayi halinta” ya Adnan ya faɗa, da Ameen su ka amsa.


sun ɗan jima suna fira kafin su ka tashi zuwa part ɗin dady dan su gaishe da shi,har sun kai bakin ƙofa mom tace ma ya NAEEM tana son magana dashi gobe idan ya dawo aiki ya zo ya sameta,da to ya amsa mata, ficewa su kayi zuwa part ɗin dady.

su Aunty Nadiya na zaune parlorn Ishrat ta shigo ta sanar da su an kammala dinner.


“sannunki da ƙoƙari Ishrat” fa'iza ta faɗa, murmushi Ishrat ɗin ta saki tana barin parlorn.


a dinning room su ka hallara saman makeken dinning table mai mazaunin mutum shabiyu, Aneesah da Enaaya sun sa dady a tsakiya, Nainarh ka ɗaice babu, itama ba bu yanda Yumnah ba tayi da ita ba a kan ta fito suyi dinner amma taƙi sai dai aka kai mata nata can,tsit ka ke ji sai ƙarar spoon da plate dake tashi kowa na ba ciki haƙƙin sa.


hakan ya ba dady damar kafe su da ido yana kallon su cike da Alfaharin yanzu duk shi ke da wannan danma wasu basa nan,yana yin fuskarshi ne ya canza da alama ya tuna da wani abun,hawaye ne su ka taru a idanuwan shi saurin goge su yayi yana kawar da tunanin a ranshi.

sai wurin ƙarfe goma na dare su ya NAEEM su ka bar gidan,har part ɗin mamy Aunty Nadiya da Aunty nafisat su ka shiga yi mata bankwana harda su ya NAEEM amma ban da su Enaaya dan cewa su kayi basa zuwa da iyayen su ka matsa masu sai ficewa su kayi daga gidan da gudu.

murmushi kawai fa'iza da Yumnah su ka saki suna bin bayan su Aneesarh.

cikin girmamawa su ya NAEEM su ka gaishe da ita amma sai ta amsa masu tana wani ya mutse fuska,hakan bai dame su ba idan da sabo ai sun saba.

ba su zauna ba su ka fice a parking space su ka samu su Enaaya tare da su fa'iza,sallama su kayi ma junan su su ka nufi motocin su yayin da fa'iza da yumnah su ka koma ciki, barin gidan su kayi zuwa na su gidajen dake cikin Estate ɗin...
_*Ep11_12*_


*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘


_____________________________



A main parlor fa'iza da Yumnah su kayi sallama fa'iza ta nufi part ɗin mamy yayin da Yumnah ta nufi na su part ɗin.


direct ɗakinta ta nufa, a hankali ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama, a tsaye ta hango Nainarh bakin sliding door ɗin dake cikin ɗakin ta zubama cikin estate ɗin da yake ƙwanyar da haske kamar rana ido, jefi jefi take hange motoci na kai kawo a cikin Estate ɗin.


A zahiri kallon cikin Estate ɗin take a ɓaɗi kuwa hankalinta na can prison wajen mahaifiyarta, ko a wane hali take, wasu irin zafafan hawayen su ka wanke fuskarta lokacin data tuna irin kisan wulaƙancin da a kayi ma mahaifinta.


Sosai take zubar da ƙwalla kwata kwata ko sallamar Yumnah ba taji ba, bakin door ɗin Yumnah ta ƙaraso, a hankali ta kira sunan Nainarh amma bata amsa mata ba saboda hankalinta da baya tare da ita, dafa kafaɗarta Yumnah tayi, da sauri ta kai dubanta ga Yumnah.


“nainarh dan Allah ki daina sa damuwa a ranki, komai zai wuce”


da sauri Nainarh ta faɗa jikin Yumnah tana sakin kuka mai sauti,jikin Yumnah ne yayi sanyi, wani irin tausayin Nainarh ne ya rufeta musamman yanda taji jikin Nainarh ya ɗauki zafi.


ɗan bubbuga bayanta ta shiga yi tana lallashin ta.

“nainarh dan Allah ki daina sa damuwa a ranki, komai zai wuce, ki daina kuka dan Allah,naji ma jikin naki ya ɗau zafi gashi ya Irfan ɗin baizo ba,amma bari naje medical room na samo maki maganin zazzaɓi kafin zuwa gobe”

Yumnah ta faɗa yayin da take raba jikin su,jan hannun Nainarh tayi zuwa ottoman chair dake bakin bed.


“ki zauna bari na kawo maki magani, naga ma ko dinner ɗinki ba ki ci ba” Yumnah ta faɗa tana kallon dinner ɗin da Ishrat ta kawo mata.


cikin dasashiyar muryarta tace
“bana jin yunwa ne”

girgiza kai Yumnah tayi “bazai yuwu ba, idan baki son wannan ne na kawo maki wani, amma zama da yunwa ba masalaha bace”


“na ƙoshi ne Yumnah, bazan iya cin komai ba”


“dole kisa wani abu a cikin ki” Yumnah ta faɗa tana kwashe kayan abincin da aka kawo mata tana nufar ƙofar fita ta fice daga ɗakin, kitchen ta fara nufa ta ajiye trayn kafin ta fice.

Ƙaton medical room ɗin su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login