Showing 75001 words to 78000 words out of 88290 words

Chapter 26 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

430

ke faɗa kuwa?”
“na san mi nake faɗa kuma ina cikin hankalina,wannan haɗin sam bazai yiwu ba ni ba hajiya halima bace ko salima da ku ka nunama fin ƙarfi akan ƴaƴan su,ku ka nuna basu da right ɗin zaɓarma ƴaƴan su abokan zama,ni sam bazan ƴarda da wannan ba,babu ƴaƴana babu ƴaƴan Zulaihart period”


kallonta kawai uncle mutallaf keyi cike da mamaki,ko a mafarki bai taɓa tunanin wannan amsar daga gareta ba,yayi matuƙar mamakin ta duk da ya san ba su jituwa da matar yayan nashi.

“wallahi babu ƴaƴana babu ƴaƴan Zulaihart,haka kawai kuyita kwasar mana ƴaƴa kuna ba ƴaƴan Zulaihart sai kace ita kaɗai ke da ƴaƴa, gaskiya ni ban amince ba”


“amma nayi mamakin jin haka daga gareki,banyi tunanin za ki yi haka ba,miye laifin Zulaihart ne da zaki ƙi son haɗa alaƙa da ita,ai ko dan ya Tahir da farin cikin ƴarki kin amince”

tashi tayi daga inda take zaune cikin ɗaga murya tace
“wallahi bazan amince ba,haɗa dangantaka da Zulaihart wallahi bazan yi ba,ai da Noor ke faɗa man na ɗauka shashancinta ne ai ban san abun da gaske bane da wallahi tuni nayi ma tufkar hanci,haka kawai kuyi ta haɗa mu da dangin yahudawa, wallahi tun wuri kace ma ƴan uwanka baka amince ba dan Noor bazata Auri Irfan ba” ta kai ƙarshen maganar tana huci


“kin gama” uncle Mutallaf ya faɗa yana tsareta da idanu
“ban gane na gama ba,haka kawai sai inƙi faɗin ra'ayina,kowace yarinya sai ku ɗauka kuba ƴaƴan Zulaihart haka akeyi,idan su hajiya halima sun amince saboda kwaɗayin abun duniya ni wallahi bazan amince ba”


“Fatilah ina so ki san wani abu Noor da Irfan are my kids, ke baki isa ki sa na fasa abunda nayi niyya ba,Aure tsakanin Noor da Irfan Kamar anyi an gama ne in dai ni ne ubanta ba wani daban ba” ya faɗa a kausashe


“lallai Dr zaka tafka babban kuskure in dai kace sai ta Auri Irfan”
“kwarai kuwa,kije kiyi duk abunda ki ke ganin zaki iya amma Aure tsakanin Noor da Irfan Kamar anyi shi angama,ke baki isa kisa na zuba ma ƴan uwana ƙasa a ido ba,yanda aka yi na Naeem da Adnan lafiya haka za'ayi na Noor da Irfan sai dai kiyi duk abunda za kiyi”


Kwashewa tayi da wata irin dariya“haka dai kace ko,za kuwa kaga abunda zan aikata” sosai saɓani ya shiga tsakaninsu akan wannan maganar.


Noor lokacin data nufi bedroom ɗin ta,wayarta ta ɗauka tayi dialing number Irfan,har Kiran ya katse baiyi picking ba, sake kira tayi sai a na biyun ne yayi picking
“hey beb, what's up?” ya faɗa daga cikin wayar

“am really happy dear,yau dai ka cika alƙawari, i really really love u irin billions ɗin nan,i wish kana kusa da na baka warm hug of happiness”ta faɗa tana sakin dariya

daga cikin wayar tana jin yanda ya sauke ajiyar zuciya “I would like that baby,but wait farin cikin mi kike?”
“ban gane farin cikin mi nake ba,kana nufin baka sani ba?”
“am serious dear ban sani ba” ɓata fuska tayi tana turo baki

“bana son wannan wasan yaya”
“am serious Qanwata ban sani ba”
“yaya yanzu maganar Auren namuce baka sani ba” ta faɗa tana wani murguɗa mashi baki kamar irin yana kusa da ita ɗin nan
“maganar Auren fa,a ina ki ka ji?”
“yanzu naji dady na waya da Uncle Ahmad yana sanar dashi” ajiyar zuciya taji ya sauke

“Alhmdllh, gaskiya naji daɗin jin haka,am really happy dear” dariya ta saki
“wai da gaske ba kai ka faɗa mashi ba”
“da gaske nake,i think Waseef ne ya sanar dashi”
“amma naji daɗi ya Waseef ya faranta man shima Allah ya faranta mashi”
“Ameen,yanzu shikenan beb mun kusa zama husband and wife”
“yeah very soon we became husband and wifeee” ta faɗa tana jan wife ɗin,dariya su ka yi gaba ɗayan su, faɗawa tayi saman bed ɗin ta
“gaskiya dole nayi ma ya Waseef kyauta yayi abunda ka kasa tsawan shekaru”


a shagwaɓe yace “beb Ni fa kyautar”
“taka special ce husband to be”
“beb,Ina so mu haɗu Please” ya faɗa yana wani shagwaɓe murya kamar ƙaramin yaro
“ka zo gida mana”
“No beby kunyar uncle nake ji,kina so yace daga faɗa mashi har na fara mashi Zarya a gida”
“kunya fa yaya,shi fa dady ba ruwanshi”
“ni dai bazan iya zuwa ba beb,kawai ki nema mana inda zamu haɗu”
“please Ni dai ka zo, ko a compound ne sai ka tsaya ba saika shigo ciki ba”
“ok let me see idan zan iya zuwa”
“zaka iya dear”


cike da farin ciki su ka cigaba da waya,daga yanayin yanda su ke wayar zaka tabbatar suna cikin farin ciki,hayaniyar da taji ne yasa tayi saurin ce mashi tana zuwa, rejecting call ɗin tayi,da sauri ta sauka daga saman bed ɗin ta nufi ƙofar fita zuwa parlor,anan ta samu dadynta da momynta suna saɓani saboda Auren su.


cikin parlorn ta ƙarasa,fashewa tayi da kuka “momy mi yasa za kice haka akan ya Irfan,gaskiya ki daina man wannan wasan”
“sai na mareki idan ba kiyi man shiru anan ba shashasha”turo baki Noor ɗin tayi hawaye na bin cheek ɗinta

“kowa na farin ciki sai ke ce zaki tsiro da haka,ni gaskiya ya Irfan nake so kuma shi zan Aura,haka kwai burinda na daɗe ina jira zaki wani ɓ...” bata ƙarasa ba saboda saukar marin da taji,da gudu ta nufi dadynta tana fashewa da kuka.


“shashashar banza wacce bata san inda ke mata ciwo ba,ai da duk a zatona kina da hankali ashe sakaryace ke ban sani ba”


“dady dan Allah karka bari ta rabani da ya Irfan” ta faɗa tana kuka
“yi shiru Noor,karki wani tashi hankalinki ni ne dai dadynki ba wani ba,babu wanda ya isa rabaki da Irfan sai Allah,Irfan shine zaɓi na” tsaki mom fatilah taja
“zaku sha mamakina daga kai har ita” tana faɗar haka ta nufi sama,hannu yasa ya shiga goge mata hawayen dake zuba.


“yi haƙuri kukan ya isa haka,where is my glasses?” bedroom ɗinta ta nufa da sauri, glass ɗin ta ɗauko mashi,amsa yayi yana ɗan shafa kanta
“karki damu kinji” gyaɗa mashi kai tayi,ficewa yayi daga parlorn ita kuma ta koma bedroom ɗinta ranta duk a jagule bata taɓa zaton haka daga momynta ba...


*Uhmmm mom fatilah yada haka*
*UNITED STATE❤*


_*Las Vegas (Nevada)*_



Suna isa hospital ɗin nurses na turo stretcher,tun a hanya Mrs malika ta sanar da zuwan su,da sauri Noah ya buɗe masu back seat ɗin,kama Nailarh su ka yi su ka ɗaura a gadon,a gaggauce su ka nufi cikin hospital ɗin da ita,bin bayan su su Mrs malika su ka yi.
Hospital ɗin yanda girma sosai,komai na cikin shi are expensive and extraordinary, parking lot ɗin su da reception ma kanshi abun kallo,sai ka kai wani kake iya jinya a hospital ɗin,manyan mutane ne ke Zarya a cikin shi.
suna shiga reception nurses ɗin dake wurin su ka shiga gaishe da Mrs malika,da yawansu sun santa wa su kuma Nailarh su ka sani,ko kallon inda su ke ba tayi ba,kwata kwata hankalinta baya jikinta,Aunty Sophia nose mask ta amsa ta sa,har bakin emergency ward su ka bi nurses ɗin amma basu basu damar shiga ba,suna kallo aka shiga da Nailarh.
doctors biyu ne su ka nufo Emegency ward ɗin,da sauri Mrs Malika ta nufe su,hannu kawai su ka ɗaga mata suna nufar Emegency ɗin a hanzarce.
mazauninta ta koma tana dafe kanta dake mata barazanar fashewa,Aunty Sophia tunda ta zauna motsi ma na kirki ta kasa,sai dai time to time take goge hawayen da su ka ƙi tsaya mata,itama Mrs malika hawayen ne ke zarya a fuskarta,su luna ma banda hawayen babu abunda su ke.
har 30 minutes su ka wuce babu wanda ya fito a cikin doctors ɗin sai ma wasu da suka sake shiga,hankalin Mrs malika da Aunty Sophia ba ƙaramin tashi yayi ba,after a hour su ka fito gaba ɗayan su,da sauri Mrs malika ta nufoso amma har sun bar wurin a hanzarce, ficewa su kayi zuwa compound ɗin asibitin,suna shiga compound wasu expensive rides guda uku na kunno kai cikin hospital ɗin.
da sauri su ka nufi ride ɗin dake tsakiyar su, parking motocin su ka yi,motar dake gaba aka fara buɗewa wasu irin securitys Army's ne jibga jibgan dasu su ka fito kowanen su da gun a hannunshi ga wasu a soke a ƙugunsu haka motar dake baya,motar dake tsakiya su suka nufa,ɗaya daga cikin securitys ɗin ne ya buɗe back seat ɗin motar,a hankali ya zuro ƙafarshi dake sanye cikin leather shoes masu shegen kyau kafin ya fito gaba ɗayan shi,sanye yake cikin suit one of the world most expensive suit brand black color,sosai suit ɗin yabi shape ɗin jikinshi,he has a gym product body, fuskarshi a sanye take da face mask,sumar kanshi har saman neack ɗin shi yayi parking ɗin ta da baby ribbon black color.
da sauri Drs ɗin su ka nufe shi,cike da girmamawa su ka shiga gaishe da shi,hannu kawai ya ɗaga masu yana nufar cikin hospital ɗin,da sauri nureses ɗin dake reception su ka miƙe,with full respect su ka shiga gaishe da su,babu wanda ya samu damar amsamawa sai dai ɗaga masu hannu da yayi,hannu ya sa ya shiga zame rigar suit ɗin dake jikinshi.
Amsar rigar Suit ɗin Dr Daniel yayi,naɗe hannun longsleev shirt ɗin dake jikinshi yayi,da sauri Mrs Malika ta miƙe lokacin da su ka ƙaraso,ciki ya nufa tare da drs guda biyu,Dr Daniel ya nufi Mrs Malika.
“Dr Daniel What's her condition now, has she recovered??” girgiza mata kai yayi
“please ma'am garin ya haka ta faru,you know her problem more than anyone,duk wani emergency treatment mun bata but her body fought to accept it,her heart became very weak she's stop beating, I don't know why you are so careless that her heart is weak like that,I don't want to use a defibrillator because of her myocardial, but it is necessary” wasu hawaye ne su ka zubo daga idanun Mrs malika jin abunda Dr yace.
“It's not my fault Dr,u know she's presenting a game at her Center,You know how she always wants to see her win in the game,here the problem happened,someone who we don't know where he is from, won her in the competition, shikenan ranta ya ɓaci har ya kaiga ta zamu Attack” ajiyar zuciya ya sauke
“I didn't think that what happened will throw her into such a problem like that, but don't worry our Dr has arrived,she will get better, don't worry Nailarh will recover soon”
da sauri Aunty Sophia ta miƙe tana nufar ƙofar Emergency ward ɗin,daga sama door ɗin ƴar madaidaiciyar glass window ce,tana iya hangen abunda ke ciki,sauke idanunta tayi akan Nailarh dake kwance saman Electrical bed,blue gown ce a jikinta sai ƴar cap dake saman kanta,hancinta a manne yake da oxygen.
da sauri takai dubanta kan Dr dake tsaye gaban Ventilator machine,Dr daya shigo yanzu ne har ya ɗaura gown akan kayan jikinshi hannunshi sanye da robber glove,inda Nailarh take ya nufo,oxgyen ɗin dake hancinta ya zare,defibrillator dake ajiye ya ɗauka,a saman ƙirjinta ya ɗaura,ɗaga defibrillator ɗin yayi gaba ɗaya Nailarh ta biyo abun,da sauri Aunty Sophia ta rintse idonta,sake ɗaura defibrillator yayi a ƙirjinta,gaba ɗaya bayanta ya rabu da bed ɗin,kasa jurar ganin halinda Nailarh take ciki tayi,da sauri tayi baya wata irin juwa ce ta kwasheta,daga haka bata sake sanin halin da take ciki ba sai farkawa tayi ta ganta a wani ward da drip a hannunta,kallon Nures ɗin dake zaune saman chair tayi,da sauri nurse ɗin ta nufota tana mata sannu,turo ƙofar ward ɗin akayi aka shigo,Dr Daniel ne da Mrs malika su ka shigo,da sauri Miss malika ta nufota.
“sophia how do u feel now” da kallo kawai Aunty Sophia ta bita without saying anything to her,wani irin tausayinta ne ya rufe Mrs Malika ta san ita kaɗai ta san yanda take ji a zuciyarta,tana matuƙar son Nailarh ko ita da take mahaifiyarta bata mata kalar son da Aunty Sophia take mata.
“sorry Sophia don't worry Nailarh will recover soon” kwantar mata da hankali Mrs malika ta shiga,amma um Aunty Sophia batace ba sai bin Mrs malika da take da ido,ita kanta malika daurewa take amma da tuni ta kai ƙasa itama.
Ficewa su ka yi daga ward ɗin, da kallo kawai Aunty sophia ta bisu kafin ta maida dubanta ga nurse ɗin dake kula da ita “Nailarh,where is she?” ta furta a hankali, murmushi nurse ɗin ta sakar mata “let the drip end and I will take you to her” hawaye ne su ka zubo daga idanunta
“please take me now, i need to see her”
“I'm sorry, let it end,our Dr is around and ya hana a shiga wajenta yanzu, but we'll go later, I'm sorry” kwantar mata da hankali nurse ɗin ta shiga yi harta samu ta haƙura.
Mrs Malika ce zaune a office ɗin Dr Daniel yana sanar da ita umarnin Dr da dalilin da yasa ya hana kowa ya shiga inda Nailarh take
“But Dr.how I will not be able to see her until the next two days”
“am sorry it's not my fault, it's our Dr's order”
“amma da ai ina shiga, ko last zuwanmu da tayi one week a ICU ai na shiga, Why are you stopping me now?”
“haka ne, time ɗin he's not around,but now babu tayanda zan kai ki wajenta,be patient
na san data farka ke zata fara nema”
“I'm really not happy. If you don't let me to see her, I'll take her to orphanage even if u don't discharge her.”
“I'm sorry ma'am, he did that because of her health”
“miye haɗinshi da ita da har zai hana mu relatives nata kula da ita”
“nothing, he's just so kind,as long as he is in the hospital duk wani patient dake buƙatar special care shike kula dashi ko nurses baya bari”
“wai miye alaƙarshi da Hospital ɗin ne ma” ɗan zaro ido dr daniel yayi yana kallonta “he's our CEO and he's the CMO of the entire USA,it's his hospital” jin jina kai kawai tayi tana lumshe ido without saying anything
“ma'am u need to have some rest, ki tafi gida zuwa anjima sai ki dawo ko gobe,na san zuwa lokacin ta farka”
“no bazan iya tafiya na bar Sophia ba, please ko ita ku bari taga Nailarh kunga halinda ta shiga saboda ita”
“i will do something, but kina buƙatar hutu, dan da yiwuwar saina auna BP ɗinki dan zaiyi wuya ace jininki bai hau ba”
“no need Dr,bari na koma wajen sophia” gyaɗa mata kai kawai yayi, ficewa tayi daga ɗakin zuwa ward ɗin da Aunty sophia take ciki, samunta tayi harta koma bacci, gefen bed ɗin ta nufa ta zauna,sannu Nurse ɗin dake wurin tayi mata, jinjina mata kai kawai tayi.
Su luna ne su ka shigo su biyu hannunsu ɗauke da madaidaitan basket, tunda aka fito da Nailarh daga Emergency ward su ka koma gida tunda an hana kowa shiga inda take, besket ɗin hannunsu su ka ajiye, sannu su ka yima Mrs Malika,jinjina masu kai kawai tayi, sofa dake cikin ɗakin su ka nufa su ka zauna, jugum su ka yi kamar masu zaman makoki.


*ABUJA NIGERIA*

Magana yake amma taƙi ɗaga ido ta kalleshi balle yasa ran zata tanka mashi akan maganar da yake, shiru yayi yana kallonta,mug ɗin tea data haɗa mashi ta miƙa mashi,ƙin amsar mug ɗin yayi yana bin fuskarta da ido,kallonshi tayi,ajiyar zuciya ya sauke yana amsar mug ɗin ya ajiyeshi saman Table ɗin dake kusa dashi, kamo hannunta yayi cikin nashi “mi yasa nake magana ki ka yi shiru?”
“mi ka ke so nace, hukunci ne da ku ka yanke kaida ƴan uwanka ni kuma miye nawa a ciki”
“akan Auren ɗannaki ki ke faɗin haka?”
“to ƴallaɓai mi zance, kun riga da kun gama yanke hukunci”
“sai kisa mashi albarka kamar yanda ki ka yima sauran ƴan uwanshi” ajiyar zuciya ta sauke tana kallonshi “I won't hide it from you but honestly speaking I am not happy with this relationship hasalima ɗiyata nake mashi sha'awar Aure ba Noor ba”
“nima nayi wannan tunanin barrister, amma da wanan maganar ta zo sai na barshi a haka Allah ya ƙaddara,haƙuri kawai za muyi”
“gaskiya banyi farin cikin da haɗin nan ba, da da yanda za ai a fasa shi gaskiya dana so” murza hannunta dake cikin nashi yayi
“mi yasa zaki ce haka barrister, ki sa mashi Albarka kamar yanda ki ka sa ma ƴan uawanshi, karki zamo uwa mai tauye farin cikin ƴaƴanta”
“bazaka gane bane yallaɓai, kasan cewa fatilah ba ƙaunata take ba, she hates me completely,a gaskiya a wannan yanayin banason abunda zai tada man hankali,ka fi kowa sanin yanda akayi bikin Naeem, wane irin tashin hanlali ne ban fuskanta ba daga wajen hajiya Halima?, har yau na kasa manta cin mutuncin da tayi man, kawai na amince da Auren ne saboda Abbah, dan Allah kafin maganar nan ta kai gareshi ku dakatar da ita” tuni hawaye sun cika idonta duk wani abu da zai haɗata da su mamy a yanzu ba ƙaunar shi take ba
“c'mom Zulaihart mi yasa za kiyi wannan tunanin, karki manta ba ita keda alhakin bada Auren Noor ba,ko ubanta bai isa ya hana wannan haɗin ba, Mustafa keda alhakin bada Aurenta kin kuwa san bazai taɓa hana Irfan ba” fashewa tayi da kuka “haba yallaɓai ka gane mana, mutanen nan fa ba sona su ke ba, miyasa kullum ku ke son haɗa alaƙa tsakanina da su” jawota yayi zuwa jikinshi, zaunar da ita yayi kan laps ɗin shi “ya isa haka miye na ku ka to,adu'a za kiyi mashi kisa mashi Albarka in sha Allah babu abunda zai faru sai Alkairi”
“haka kawai yara suyita ja man abun magana, dan mi zasu maƙale sai ƴaƴan su, su ka ɗai ne ƴaƴa da bazasu nemi wasu ba” hannu yasa ya shiga goge mata hawayen dake zuba
“ba nace ya isa haka ba, kiyi haƙuri in sha Allah babu abunda zai faru sai Alkairi, kuma yaran nan danƙon zumunci su ke ƙara mana,Don't forget that they are also my kids,my brothers kids, kuma idan dan saboda ƴarki ne bazaki amince ba karki manta ba shi kaɗai bane ɗanki, sai kiba yayansa” saurin kallonshi tayi “wa kenan ka ke nufi?”
“ɗana mana ko bazaki bashi ba?”
“tab ni gaskiya bazan ba SAM ba, yaronda ko mu ba mutuncin mu yake gani ba shi zanba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login