Showing 57001 words to 60000 words out of 88290 words

Chapter 20 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

427

irin haka ba sannan ki sani Zulaihart ta fiki haƙuri mabaruka”


wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare zuciyar mamy, idan da abunda ta tsana a rayuwa taji ana yabo mom musamman dady abun na ɓata mata rai, rai a ɓace ta fice daga part ɗin gaba ɗaya, da kallo kawai dady ya bita.



Su Yumnah suna fita daga part ɗin dady ficewa su kayi daga gidan baki ɗaya,suna fitowa motar ya Naeem na kunno kai cikin parking space ɗin, ɗan dakatawa su kayi, daidaita parking ya Naeem yayi, kusan a tare aka buɗe car doors ɗin su fito,ya Naeem ne ya fito daga driver seat yayinda ya Adanan ya fito daga front seat.


Uniform ne a jikin ya Naeem yayinda ya Adnan ke sanye da suit back color, da gudu su Ammar su ka nufe su, hugging ɗin ya Naeem su kayi ɓata fuska ya Adnan yayi kamar ƙaramin yaro yana faɗin
“abun ƴar haka ce ya Naeem kawai ku ka sani, shikenan nima ai ga Autar dady nan” ya faɗa yana buɗema Yumnah hannayen shi, da sauri ta nufeshi tana sakin dariya, faɗawa tayi jikinshi tana hugging ɗin shi.



murmushi Nainarh dake tsaye ta saki, yaran mom na matuƙar burgeta Irfan ne kawai take ganinshi daban a cikin su kamar ya banbanta da su.


“dady mun fara gaishe da second father ne fa”Aman ya faɗa yana turo baki
“ba wani nan, bana dai yi daku, da Autar dady nake yi”

“ku rabu dashi kishi ne kawai” ya Naeem ya faɗa yana basu hannunshi suka tafa
“sai ina haka?” Ya Adnan ya faɗa lokacin da yake raba jikinsu
“gidan uncle Mustafa” yumnah ta bashi amsa
“a dawo lafiya muna gaishe da mutanen gidan”
“za suji in sha Allah”


kama hannun ya Adnan ya Naeem yayi yana faɗin “sai kun dawo” da sauri Nainarh ta gaishe da su ganin za su bar wajen,duban suka kai gareta
Murmushi ya Naeem ya saki “lafiya lau Nainarh, ya gidan” da Alhmdllh ta amsa mashi, ya Adnan tunda ya kafeta da idanu ƙala baice ba, duk tsawan wannan lokacin da Nainarh ta ɗauka bai taɓa ganinta ba in fact ma baisan wacece ba, ɗan taɓoshi ya Naeem yayi


“baka ji ana gaishe ka” washe mata baki yayi yana faɗin “lafiya” murmushi ta sakar mashi
“muje ko, Yumnah sai kun dawo” ya Naeem ya faɗa yana nufar ƙofar shiga gidan, ya Adnan kasa ɗauke idonshi yayi a kan Nainarh har su ka nufi motar Yumnah su ka shiga, yumnah har ta buɗe driver seat zata shiga yayi saurin jawo Arm ɗinta, bayan motar yajata.



da tsantsar mamaki take binshi da kallo, hannu yasa ya kauda fuskarta gefe “kin wani tsare ni da ido, tambayarki zanyi wacece waccan?” ya faɗa yana nuna cikin motar

“wai Nainarh?”
“sunanta kenan?”
“eh sunanta kenan, ɗiyar fa mom Asma'u ce” ɗan zaro ido waje ya Adnan yayi “amma ya akayi ban santa ba?”
“may be baka zuwa gidan ne”
“eh gaskiya bana zuwa, wajen mom ta zo?”
“ai ka san abunda ya faru da mom Asma'u to shine mom ta dawo da ita nan gidan”


“ok na tuna”murmushi Yumnah ta saki tana kallon fuskarshi
“na tafi?”
“idan kin tsaya wani abun za kiyi man ne?”
“ok sai mun dawo” ta faɗa zata bar wajen,muryar Noor ce ta dakatar da ita, da sauri su ka kai duban su ga Noor dake fitowa daga cikin mota,palazzo trouser ne a jikinta haɗe da shirt open shoulder,daga sama rigar ta kama jikinta sosai kusan rabin brest ɗinta a waje,ga wasu irin high hills masu shegen tsini tasa, ɗan siririn mayafi ne a saman kanta.


fuskarta da fara'a ta nufo su, tana ƙarasowa tayi hugging ɗin ya Adnan, saurin tureta yayi daga jikinshi rai a ɓace yace“wai Noor har sau nawa zance maki kidaina hugging ɗina, wai ke baki san cewa ni ba muharraminki bane akwai fa Aure a tsakanin mu” ɓata fuska tayi kamar zata fashe da kuka
“ya Adnan daga kawai nayi murnar ganinka”harara ya watsa mata yana kallonta tundaga sama har ƙasa


“yanzu dan Allah miye amfanin wannan suturar dake jikinki, yanzu mom Fatilah na kallonki ki ka fito a haka?”

cike da shagwaɓa tace
“miye aibun kayan dake jikina ya Adnan?”
“ban sani ba” ya faɗa haɗi da jan tsaki, bari wurin yayi gaba ɗaya ya nufi cikin gidan.


taɓe baki tayi tana kallon Yumnah “ina zaki na zo wajen ki?”
“kindai zo wajen ya Irfan kuma duk yau baizo gidanan ba”
“kefa banza ce wa yace maki wajen shi nazo, na zo gaishe da Mom ne”
“a haka?” Yumnah ta faɗa tana kallon kayan jikinta, ɓata fuska Noor tayi “wai miye matsalar kayan jikina ne?”


“ok bama kiga matsalar su ba, na so ace second father ki kayi hugging ba ya Adnan ba,da kuwa kin san matsalar kayan jikin ki”
“shikenan ni dai naji, ina zaki?”
“gidan Uncle Mustafa”
“kai Yumnah yanzu sai ki tafi duk da na zo?”



“eh mana saboda na san ba wajena ki ka zo ba, idan kuma kina zuwa to?”
“kin san halin mom Maryam ina zuwa zata rufeni da mashifa ita komai nayi rashin kunya ne”
“da gaskiyarta Noor kuma tana yi maki haka ne dan ki gyaru, ki zo muje kawai”


gyaɗa kai Noor ɗin tayi, motar Yumnah su ka nufa, back seat ta buɗe kusa da su Ammar tashiga Yumnah kuma ta buɗe driver seat, key Yumnah tayi ma motar
“sorry kinjini shiru ko,ga sister Noor nan ku gaisa” ta faɗa tana kallon Nainarh.


Juyowa Nainarh tayi “sannu, ya gida” da lafiya lau Noor ta amsa mata, gaishe da Noor ɗin su Ammar su kayi da fara'arta ta amsa masu tana tambayar “wane ɗan kasadar ne ya baku wayarshi?” ta faɗa tana kallon wayar dake hannunsu suna buga game

Aman ne ya bata amsa da
“ta Aunty Nainarh ce” taɓe baki tayi tana kai dubanta ga Yumnah

“sister Yumnah wai da gaske ya Irfan baizo ba, daga Villa nake fa can ma baya nan kuma sai kiran wayarshi nake bana samu”
“ni dama na san ba wajen mom ki ka zo ba”
“ni dai naji, dan Allah yana ina?”


“wallahi rabona da ganin ya Irfan tun jiya da muka dawo daga gidan Abbah, amma yau da safe naji sunyi waya da mom, ki gwada kiran ya Waseef na san dole suna tare”


“kin kawo shawara” ta faɗa tana zaro wayarta daga cikin Aljihun wandonta, Number Waseef tayi dialing, bugu biyu ya ɗaga


“hello Noor, ya ki ke ya gida?”
“lafiya lau ya Waseef, wai ina ka kaiman ya Irfan ne tun jiya nake faman neman number shi baya picking??”
“amma kin raina man wayo Noor wato nima na kai Irfan ɗin wani waje ko”
“eh mana” ta faɗa a shagwaɓe.


shiru taji baice komai ba, jin Waseef yayi shirune yasata faɗin “dan Allah yana ina?” muryar Irfan taji daga cikin wayar
“hello beb”

“haba ya Irfan ka san kuwa halin daka jefani ciki kuwa, sai kiraka nake bana samu dama jiya ka bani haushi shine ma ka kashe wayarka ko nayi duk abunda zanyi?”


“sorry Noor ba haka bane, kina a raina wani uzuri ne ya sani kashe wayata amma kiyi haƙuri, kina ina ne yanzu?”
“gajiya nayi da nemanka na zo gidan big dady ko zan sameka”
“ok kina can yanzu?”
“A'a mun fita tare da su Yumnah zuwa gidan Uncle Mustafa”


“sorry gani nan zuwa kinji”
“zan jiraka fa karka shanya ni?”
“karki damu zan zo kinji”
“ok sai ka zo”
“ok bye” ya faɗa yana rejecting kiran, ajiyar zuciya ta sauke tana turu wayar cikin Aljihun wandonta.


murmushi yumnah ta saki “gaskiya na kusa tona maku asiri keda ya Irfan kowa ya san abun da ke tsakanin ku” saurin kallonta Noor tayi
“ban gane abunda ke tsakanin mu ba?”
“zan fallasaku kowa ya san soyayya ku ke” ajiyar zuciya Noor ta sauke tana dafe saitin zuciyarta da “da kuwa kin kyauta min Yumnah dan na gaji da hiding ɗin da ya Irfan ke yi”


dariya Yumnah tayi “da ɗina dake fa Noor rashin kunya, yanzu ya Irfan na hiding amma ke so ki ke a faɗa ko, idan basu amince ba fa??”
“wallahi har poising zan iya sha idan har su kace za su rabani dashi” da wani mugun sauri Nainarh ta juyo tana kallonta dan kalamanta sunyi matuƙar bata mamaki.


murmushi ta sakar mata tana kashe mata ido ɗaya, saurin juyawa Nainarh tayi tana girgiza kai.

murmushi Yumnah ta saki
“za ki iya fiye da haka,dan na lura baki da hankali a kan ya Irfan”

“duk ma wanda yace maki inda hankali akan ya Irfan yayi maki ƙarya”
“Allah ya shirye ki” shine kawai abunda Yumnah ta ce yayinda take shiga compound ɗin gidan Uncle Mustafa, parking tayi
“Ameen idan da gaske ki ke” Noor ta faɗa tana fitowa daga cikin motar, girgiza kai kawai Yumnah tayi.


A tare Yumnah su ka fito ita da Nainarh, back seat Yumnah ta nufa tana buɗema su Ammar.
sojoji ne ta ko ina a harbar gidan, da gudu su Ammar su ka nufi ƙofar shiga gidan.


mom maryam na zaune a katafaren mai parlorn gidan su ka shigo da gudu su ka faɗa samanta har sai da ta ɗan tsorata
“wane mai son gamawa da duniya lafiya ne ya kawo man ku?” dariya su kayi suna faɗin “su Aunty Yumnah ne” da sauri ta kai dubanta ga ƙofar shigowa saboda sallamar su Yumnah da taji.


zambur ta miƙe tsaye tana rabka salati “innalillahi wa Innah ilaihi raji'un” wani irin mummunan faɗuwa gaban su Nainarh yayi da sauri su ka juya...
______________________________



Da sauri su ka juya suna kallon bayan su dan duk a tunanin su wani abu ta gani a bayan su.


“amma Allah wadaran naka ya lalace, yanzu ke Noor fatilah na kallonki ki ka fito haka ƙirji a waje, ubanwa zaki nunama ƙirji da ki ka fito haka” gaba ɗayansu su ka sauke ajiyar zuciya dan ba ƙaramin tsoro ta basu ba.


turo baki Noor tayi gaba“ni dama shiyyasa bana son zuwa gidan nan idan muzo”
“dama yaushe zaki so zuwa gidanan tantiriyar banza, wallahi Noor kiyi ma kanki faɗa kwata kwata wannan ba ɗabi'a bace mai kyau, kina zubar ma kanki da mutunci ne”
“haba Momy yanzu dan Allah miye laifin kayan jikina?”


baki mom maryam ta saki “shaiɗaniyar banza tambayata ma kike, kin wuce kinje ɗakin Kainart kin nemi kaya na mutuncin kin sa ko kuwa”
baki Noor ta turo gaba“ni gaskiya bazan sa wasu k...” bata ƙarasa ba saboda yo kanta da mom maryam tayi,ai kuwa babu arziƙi ta kwasa da gudu zuwa cikin gidan.

“mara kunyar banza ai dakin tsaya” ta faɗa tana nufar sofa data tashi ta zauna,dariya Yumnah da Nainarh su kayi suma suna samun wajen zama su ka zauna, cike da girmamawa su ka gaishe da ita, da fara'arta ta amsa masu tana tambayar mutanen gidan.


“suna nan lafiya sun ma ce mu gaishe ku”
“muna amsawa,wallahi ku riƙa yima yarinyar can faɗa tunda uwarta ta kawo ido ta sa mata, kwata kwata shigar da take bata dace ba, da wanan shigar sai ta rasa mijin Aure dan duk wanda ya san kanshi baizai kwashi wannan tarkacen ba, dan ni wallahi AHMER ya kwaso man mace irin wannan da sunan zai Aure sai nace ubanshi daga shi har ita”


dariya Yumnah ta kwashe da ita“mom itafa Noor zaman waje ne ya maida haka”
“ke ni dallah rabani,ku da kuke da alaƙa ta jini da turawa mi yasa baki shiga irin haka ƙarshen dai rashin kunya kenan ko, mi yasa Zulaihart bata zuba maki ido kina shigar da ki kaga dama ba,saboda ta san ciwan kanta”

murmushi kawai Yumnah tayi ta san da ace mom maryam ta san Irfan ke son Noor da ya shiga uku dan saita rabasu may be shima dalilin da yasa kenan yaƙi bari kowa ya sani.


“ku riƙa yi mata nasiha”
“insha Allah mom zamu riƙa yi mata”

“hakan shi yafi”
“mom ina papah?” a cewar su Ammar
“papah na wajen aikin, sai anjima zai dawo”
“Allah ya dawo dashi lafiya” da Amee su duka su ka amsa.

Noor koda ta shiga bedroom ɗin kwanciyart tayi saman bed ɗin ɗakin, wayarta tashi latsawa.



*Uncle Hashim's House*



Zaune suke a parlorn Uncle hashim Laatifa ce kawai babu, mom maimunatu na daga zaune saman sofa mai mazaunin mutum uku Balqis na kwance tayi pillow da laps ɗinta yayinda Uncle Hashim ke zaune saman
rocking chair hannunshi riƙe da jarida yana dubawa.


juyowa Balqis tayi tana fuskantar shi da ƴar shagwaɓa tace “dady wai har yanzu shiru maganar fara aiki na?”

“ayyah sorry my daughter, shaf na manta na faɗa maki munyi magana da ya mutallaf harma na bashi takardunki”
“na gaji da zaman gida ne”
“karki damu zuwa next week za kuyi interview”
“thanks u dady, momy nima na kusa fara fita aiki kamar Aunty Laatifa”
murmushi mom maimunatu ta sakar mata tana shafa gefen fuskarta.


“amma dady a wane hospital ya samar man aiki?”
“muna da wani hospital ne bayan namu?” ya faɗa ba tare da ya kalleta ba
“eh mana dady akwai S J Hospital, ni nafi son can”
“wane hospital ne S J”
“SAM Internati...” kasa ƙarasawa tayi saboda wani kallo da barrister ya watsa mata, dan dole ta shanye sauran maganar,maida hankalinshi yayi kan jaridar da yake dubawa yana jan tsaki.


taɓe baki mom maimunatu tayi “ni da wannan sama mata aikin da miji kasa su ka fitar ita da ƴar uwarta kayi masu Aure in yaso sunyi Aikin a ɗakin mazajensu”


“idan kin tashi Aurar da ƴarki babu wanda zai hanaki amma ni ƴata ba yanzu za tayi Aure ba”

“ban gane idan na tashi Aurar da ƴata ba, wai kai barrister har yanzu bazaka sauko daga dokin zuciyar daka hau ba ka yafe ma ƴarka?”

“bayan Balqis bana da wata ƴa a duniya, karki sake dangantani da ƴarki dan ranki ne zai ɓaci” tashi yayi yana kwashe Jaridar shi, juyawar da zaiyi yaga laatifa a tsaye bakin ƙofa kaf maganganunsu a kunenta, ɗauke kai yayi kamar ma bai gantaba ya nufi bedroom ɗinshi.


juyawa tayi da nufin barin wajen, da sauri Balqis tace“laa Aunty Laatifa yaushe ki ka dawo?” juyowa mom maimunatu tayi tana kallonta

“dawowata kenan ƙanwata, ya kike ya gida?” ta faɗa tana nufo cikin parlorn
“lafiya lau Aunty Laatifa” murmushi kawai Laatifa tayi mata tana nufar mom
“momy barka da rana ya gida?”
“lafiya lau Laatifa, harkin dawo?”



“eh mom,bari na shiga ciki na watsa ruwa duk a gajiye nake” ta faɗa yayinda take juyawa ta nufi bedroom ɗinta, da kallo kawai mom maimunatu ta bita fatan dai Allah yasa ba taji abunda Dadynta yace ba, Laatifa na matuƙar bata tausayi ta rasa miye matsalar barrister da bazai yafe mata ba.


bin bayanta Balqis tayi, lokacin da ta shiga ɗakin Laatifa har ta shige toilet mayafinta da briefcase ɗinta kawai ta samu a kan bed, wuri ta samu saman bed ɗin ta zauna.


tana shiga toilet ɗin tap ta kunna ta barshi hakanan kawai yana zuba a ƙasa,bakin bathtub ta nufa ta zauna,fashewa tayi da wani kuka mai ban tausayi, ta rasa wace irin zuciya dadynta gareshi da bazai iya yafe mata tsawan shekaru, tunani ta fara yi anya mahaifinta ne dan ta san babu wani uba da zai ƙyamaci ƴarsa kan laifi da baya da tabbaci,tasan da ace shiɗin mahaifinta ne bazai ƙyamaceta ba ko da kuwa abunda yake zargi gaskiya ne,shawara ta yanke anya baza tayi nesa dashi ba ko hakan zai sa ya yafe mata, sosai tayi nisa a duniyar tunani.


maganar Balqis ce ta dawo da ita cikin hayyacinta “Aunty Laatifa lafiya dai, tun ɗazu nake jiranki fatan dai lafiya” da sauri tayi mata gyran murya, jinjina kai Balqis ɗin tayi tana komawa mazauninta ta zauna,shaf shaf Laatifa ta watsa ruwa ta fito ɗaure da towel, murmushi Balqis ɗin ta sakar mata “inata jiranki”
“gani ai na fito, akwai labari ne?” Laatifa ta faɗa tana nufar dressing mirrow.


yanyin fuskar Balqis ne ya canza zuwa damuwa “dady ne wai dole sai a G J I hospital zai sama man aiki ni kuma na fi son S J I”
“to ni yanzu mi ki ke so nace, kawai kiyi haƙuri da in da yake son kiyi”
“haba Aunty Laatifa nazo wajenki dan ki bani shawara amma shine za kice haka?”

“to Balqis ya ki ke so nace kin dai san yanda nake da dady bare naje na roƙar maki shi, kawai kiyi haƙuri kiyi mashi biyayya”
“na san da haka,amma ai sai ki bani shawara”
“to wace shawara zan baki bayan wacce na baki?” Laatifa ta faɗa lokacin da take neman wurin zama kusa da Balqis ɗin ta zauna harta shirya cikin doguwar riga mai hannun Armless.


gyara zama Balqis ɗin tayi “kina ganin idan na sanar da big dady bazai sa dady ya amince ba?”
“too! ki gwada ki gani wataƙil ya amince”
“ni bana so naga baki bani ƙwarin gwiwa, so nake naji kince zai amince”
“to shikenan zai amince”
dariya Balqis ɗin ta saki “yawwa haka nake son naji kince” murmushi Laatifa ta sakar mata.


“yawwa Aunty Laatifa dama ina ta so na...” ringing ɗin tab ɗin Laatifa ne ya dakatar da ita, da sauri ta buɗe briefcase ɗin Laatifa ta ta ciro tab ɗin, jiki na rawa ta miƙa mata, amsa Laatifa tayi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta lokacin da tayi arba da sunan mai kiran nata, da sauri Balqis ta matso tana leƙen wayar,da tsantsar mamaki ta kalli Laatifa, ɗan tahalikin da kullum sai tayi maganar shi, yanzu haka maganar shi take shirin yima Laatifa sai ga kiran shi.

Wani irin annurin farin ciki ne ya bayya akan fuskar Balqis yau dai ga abunda ta daɗe tana jira
picking call ɗin Laatifa tayi, sai da tayi picking call ɗin tukun ta fahimci video call ne, amma tayi mamakin ganin duhu babu haske,ƴan dube dube ta shiga yi a wayar tana faɗin “Balqis bani glass ɗina”


da sauri Balqis ta buɗe briefcase ɗin tana miƙo mata glass ɗin,gyaran murya a kayi mata daga cikin wayar, da sauri takai dubanta ga wayar still duhu ta gani,wata irin zazzaƙar muryar ce ta daki dodon kunan su, in low voice aka furta “LAATIFA”

da sauri Balqis ta leƙa wayar amma sai taga babu kowa, murmushi Laatifa ta saki
“yau kuma ni ka ke ɓoye ma fuskarka SAM”
“ya ki ke?”shine kawai abunda aka furta mata maimakon bata amsar tambayar da tayi

“ina lafiya SAM, kwana biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login