Showing 42001 words to 45000 words out of 88290 words

Chapter 15 - Shiryayyar Kaddara Book 1 Hausa Novel Complete

06 Dec 2024

418

ribbon ta ɗauka ta ɗaure gashin kanta,mayafin rigar ta ɗauka tayi rolling, masha Allah kawai zamu ce Nainarh Allah yayi mata wani irin sanyi kyau,ba ƙaramin haska farar fatar ta rigar tayi ba,shagala tayi da kallon kanta a mirror.



“wayyo Allah na sister Nainarh ke ce haka?,kai masha Allah kinga yanda rigar nan tayi maki kyau kuwa?, wallahi kamar mutum ya saceki ya gudu,karfa ki rikita mana samarin family a kasa gane kan su”

dariya Nainarh ta fashe da ita jin irin sambatun da Yumnah ke mata,sosai Yumnah ta shiga zuzuta kyan da Nainarh tayi,ita kuwa ban da dariya babu abun da take.



“bari nayi sauri na shirya ko na samu nayi maki pics kar wannan wankan ya tafi haka nan” ta faɗa tana nufar dressing mirror.


shaf shaf tashiga shiryawa,itama simple makeup tayima fuskarta,rigarta ta ɗauka ta zura Nainarh na daga tsaye sai Binta da ido take harta kammala shiryawa,itama ba ƙaramin kyau tayi ba abunka ga farar fata sai rigar ta sake fito da haskenta.


jinjina kai Nainarh tayi tana faɗin
“masha Allah kema ba ƙaramin kyau ki ka yi ba”
“ban kai ki ba” Yumnah ta faɗa tana ɗaukar wayarta, hand bag ta ɗauko masu mai shegen kyau tare da sunglasses mai ɗaukar ido.

bedroom su ka nufa Nainarh ta ɗauki wayarta dake saman nightstand ajiye,ficewa su kayi daga ɗakin zuwa parlor,anan su ka ɓaje kolin ɗaukar photo, photo Yumnah ta shiga ɗaukar Nainarh ba ƙaƙƙautawa,bayan nan ta kira Ishrat tayi masu a tare.



A tare su ka shigo parlorn,a bakin ƙofar su kaci burki cikin shigar shadda gezna fara ƙal sai ɗaukar ido take,kan su a sanye yake da hula, kwantacciyar sumar kan su sai sheƙi take.


fuskar shi a tsuke take kamar ko da yaushe saɓanin ta ɗan uwan shi dake ɗauke da murmushi yana kallon Nainarh da Yumnah da su ka juya ma ƙofa baya, kallo ɗaya yayi masu ya ɗauke kai yana kai dubanshi ga Ishrat dake ɗaukar su photo,wani ɗan iskan kallo ya watsa mata wanda yayi sanadiyar hautsinawar ƴan hanjin cikinta.


saurin sauke wayar tayi ƙasa har tana sake ɗaukar su wani pic ɗin ba tare da saninta ba,da mamaki Yumnah ke kallonta “Ishrat wai lafiya ki ka tsaya sauri muke,ƙara mana ɗaya kafin mom ta fito” Yumnah ta faɗa tana kallonta

cikin rawar murya Ishrat ta furta
“barkan ku da zuwa ,ina wuni” ta furta


da sauri Yumnah takai dubanta ga...
_*Ep 19_20*_



*Bound by fate,freed by love, A romantic Odyssey*❤💘💘

______________________________




da sauri Yumnah takai dubanta ga Irfan da Waseef dake tsaye a bayan su, murmushi ta saki
“laa ya Irfan ya waseef ku ne?” yumnah ta faɗa cikin nuna jin daɗin ganin su, wani irin faɗuwa gaban nainarh yayi jin sunan da yumnah ta ambata, idan bata manta ba shine mutumin daya shigo ɗakin su ya sameta daga ita sai towel.


wani irin takaici da kunya ne su ke rufeta ji tayi ina ma ƙasa zata tsage ta shiga,ko ƙwaƙwaran motsi kasawa tayi.


da sauri yumnah ta nufe su
“kun zo a dai dai, Ishrat yi mana photo” nainarh ta faɗa tana shiga tsakiyar su, saurin kallon Irfan da yayi kicin kicin da fuska Ishrat tayi,kasa ɗaukar photon tayi saboda hararar daya watsa mata, ƙofar parlorn mom ya nufa ba tare da ya tsaya photon ba, da kallo kawai yumnah da Waseef su ka bishi, Nainarh kuwa tsananta faɗuwa gabanta yayi lokacin da taga giftawarshi ta idonta.


taɓe baki yumnah tayi tana kallon Waseef “ya Waseef wai mike damun ya Irfan ne?”
“ban sani ba yumnah, kin san halinshi sometimes ba iya mashi ake ba”
“Allah ya kyauta,Ishrat yi mana kinji” yumnah ta faɗa, saurin dakatar da Ishrat ɗin waseef yayi yana nuna Nainarh data juya masu baya.



“wacece wannan ita bazata zo muyi photon ba”
“laa sister Nainarh zo muyi photo tare da ya Waseef” yumnah ta faɗa tana nufar Nainarh ta kamo hannunta zuwa in da Waseef ɗin yake tsaye.


“sannu pretty, muyi photo ko?” Waseef ya faɗa yana sakar mata murmushi, murmushi itama ta sakar mashi tana gaishe da shi, cikin kulawa ya amsa mata, tsakiyar su ya shiga, photon Ishrat ta shiga ɗaukar su a nan Fa'iza ta same su itama ta ɗau wankan Abaya simple makeup ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba.


shiga itama tayi a kayi photon da ita,photona sosai su ka ɗauka Waseef sai da yasa Yumnah tayi masu su biyu shida Nainarh,Fa'iza ma sai da a kayi mata da Nainarh, sai da su kayi mai isar su tukun su ka bari a nan parlor su ka zauna suna kallon photunan.


mom ce ta fito Irfan na biye da ita, ta ɗau wankan Arabiyan Embellished open Abaya launin Royal blue tayi rolling da Veil ,babu makeup a fuskarta amma ba ƙaramin kyau tayi ba, cikin parlorn ta ƙaraso Irfan na riƙe da hand bag ɗinta.


“mom kinyi kyau sosai, dan Allah muyi photo dake kema” yumnah ta faɗa tana nufo mom ɗin
“lokaci ya ƙure Yumnah,na san mu kaɗai ne bamu je ba, ki bari sai wani lokaci” ɓata fuska yumnah tayi ba haka ta so ba.


ficewa su kayi daga parlorn gaba ɗayan su Ishrat na masu a dawo lafiya, parking space su ka nufa, motar Irfan mom da Waseef suka shiga yayin da Yumnah da Nainarh su ka shiga motar Fa'iza,key su kayi ma motocin su ka fice daga gidan zuwa gidan Abbah dake cikin Estate ɗin.



Tafiya su ka yi mai ɗan nisa kafin su ka iso gidan Abbah, katafaren luxury Villa ne na gani na faɗa,yaji kayan alatu kamar baza'a mutu ba,a katafaren parking space ɗin gidan su kayi parking Wanda yake cike da expensive rides masu matuƙar kyau.


fitowa su ka shiga yi ɗaya bayan ɗaya,a tare su ka nufi entrance ɗin shiga gidan mom da su Irfan na gaba yayin da Yumnah da su Nainarh ke bayan su, yanzu ma hand bag ɗin mom ce a hannun Irfan, bakin su ɗauke da sallama suka shiga katafaren parlorn gidan wanda aka ƙawatashi da manya manyan sofas masu matuƙar kyau da tsada.



matasan ƴan mata ne zaune saman sofa kowacen su ta ɗauka wanda Egyptian Abaya ɗaya tayi rolling da veil ɗin yayinda ɗaya kanta yake a buɗe,zallar gashin kanta ne kawai, gaba ɗaya wayoyinsu ne a hannunsu sun tasa gaba sai aikin latsawa su ke.


Kairiyyah da Noor kenan, Kairiyyah ta kasance ɗiya ga Aunty Adama Noor kuma ɗaya ce ga Uncle mutallaf.

sake ƙwaɗa sallama Yumnah tayi yayin da Irfan da Waseef su ka nufi glass elevator dake cikin parlorn.


saurin ɗago kai su kayi,riƙe ƙugu Yumnah tayi tana jijjiga jiki haɗi da kauda kai gefe,da sauri ƴan matan su ka nufo mom.


hugging ɗin ta su kayi cikin girmamawa wacce tayi rolling veil ta gaishe da mom, da fara'a mom ta amsa mata.

“lafiya lau Kairiyyah,ya school?”
“lafiya lau Alhmdllh mom”mom ta faɗa
“momy ina wuni” ɗayar ta gaishe da mom ɗin
“lafiya lau Alhmdllh,Noor zuwan yaushe?”



“jiya cikin dare mu ka zo”
“masha Allah harda dadyn ku kuka zo ne?”
Eh taba mom ɗin amsa, elevator mom ta nufa tana faɗin “bari na shiga wajen Abbah” da to su amsa mata, hugging ɗin Fa'iza su kayi cikin kulawa su ka gaishe da ita,kishi duk yabi ya cika Yumnah ganin sun ƙi kulata,kama hannun Nainarh tayi.


“mu tafi kinji sister”
da sauri Noor tabi bayan su, hugging ɗin Yumnah tayi ta baya “haba sister ba dai fushi ki ka yi damu ba?” fisgewa Yumnah tayi
“ni ki ƙyale ni”
“bazan ƙyale ki ba,sai kinyi haƙuri” murmushi Fa'iza tayi tana nufar su ita da Kairiyyah, Nainarh bin su kawai take da ido.


“sister sannu” Kairiyya ta faɗa tana kallon Nainarh, murmushi Nainarh ta sakar mata tana amsa mata sannu da tayi mata.


lallashin Yumnah Noor ta shiga yi da ƙyar su ka samu ta saki fuska,part ɗin Abbah su ka nufa gaba ɗayan su.


*MOM*💫


a second floor elevator ta sauketa, corridor da zai sadata da part ɗin Abbah ta nufa,tunda ta tunkaro ƙofar shiga part ɗin take jin muryoyin su suna fira cikin nishaɗin, a bakin ƙofar shiga ta tsaya,a hankali ta tura ƙofar ta shiga.


Masha Allah katafaren parlorn ne da yaji kayan more rayuwa, manya manyan sofas ne set uku masu matuƙar kyau da tsada ga taushi kamar audiga,haɗaɗiyar rug carpet ce shinfiɗe a ƙasa, kyakkyawan Dattijo ne mai cikar kamala cikin shigar farar Alkyabba a kishingiɗe saman rug carpet yayi matashi da tumtum yayin da ƴaƴan shi ke kewaye dashi sun saka shi tsakkiya,fira suke cike da nishaɗin.


su goma ne ƴaƴan Abbah dady shine babba daga shi sai uncle Ahmad daga su sai uncle Mustafa da uncle Ubaid daga su sai uncle mutallaf daga shi ne sai barrister Hashim da Aunty mariya daga su sai Aunty Safeenah da uncle Khamis daga su sai Aunty Adama ita ce Autar Abbah.


gaba ɗayan su ne a parlorn uncle Khamis ne kawai babu shima baya ƙasar ne tsawan shekara 19 kenan rabon shi da ƙasar,shi ka ɗai ne a cikin su baya da Aure.


Dady na daga hannun daman shi yayin da dady Ahmad ( mr president ) ke kusa da shi sai
Uncle Mustafa, Uncle ubaid da uncle Hashim, ɓangaren hagu kuma Aunty mariya,Aunty safeenah da Aunty Adama ne sai uncle mutallaf dake tsakiyar su,Irfan da Waseef na daga saitin kan Abbah zaune,gaba ɗaya hankali su na kan Abbah dake basu labarin yarintar su dady cike da nishaɗi.



sallamar mom ce ta katse masu firar da suke,gaba ɗayan su suka kai duban su gareta, murmushi ne ya bayyana akan fuskar Abbah da alama yaji daɗin zuwanta,kaf cikin surikan sa babu wacce yafi so sama da mom,tamkar ɗiya haka ya ɗauketa,idan ka cire barrister Hashim da Aunty Safeenah babu wanda baiyi farin ciki da zuwanta ba,da sauri Aunty Adama ta tashi fuskatar ɗauke da murmushi ta nufo mom.


hugging ɗin juna su kayi hakan ba ƙaramin ɓata ran Aunty Safeenah yayi ba,kauda kai tayi gefe tana jan tsaki, cike da kewar juna suka gaishe da juna,cikin parlorn su ka ƙarasa,wurin Abbah mom ta nufa fuskarta ɗauke da murmushi.


zama tayi kusa dashi “in wuni Abbah,mun sameku lafiya?”
“lafiya lau Alhmdllh,ya gidan ya kuma aiki”
“lafiya lau” Masha Allah Abbah ya furta,duban ta ta kai ga dady Ahmad cike da girmamawa ta gaishe da shi,cikin kulawa ya amsa mata yana tambayar Yumnah.


ɗaya bayan ɗayan tabisu tana gaishe da su,cike da kulawa su ke amasa mata in ka cire barrister da Aunty Safeenah da su kayi kamar ba su san da su take ba,hakan kwata kwata bai dameta ba dan idan da sabo ta saba da halin su,dady baiji daɗin hakan ba ya rasa miye matsalar ƴan uwanshi da matar shi.


“Ashe abun da ya faru da Asma'u kenan?, ubangiji Allah yayi mata mafita,Allah ya kuɓutar da ita,su kuma wanda su ka da baibaye ta da sharrin Allah yayi gaggawar tona masu Asiri” Abbah ya faɗa

da Ameen ya Allah Abbah su ka amsa banda uncle Hashim da yayi tsit kamar baya parlorn


“Allah ya kuɓutar da ita ya kyauta gaba” a cewar uncle Ahmad da Ameen su ka amsa suma,ɗaya bayan ɗaya su ka shiga yi mata jaje in ka cire Aunty Safeenah data miƙe ta nufi ƙofar fita, barrister Hashim kuwa lumshe idonshi yayi kamar mai bacci .


“saffenah!!” Abbah ya kira sunanta,dakatawa tayi da tafiya ta juyo tana fuskantar shi

“ina zaki kowa na nan?”
“zan shiga wajen mama ne,naga an gama firar zumunci tunda har bare sun fara zuwa shiy...”

bata ƙarasa ba sakamakon tsawar da dady ya daka mata
“Abbahn ki ke faɗama haka?,maza ki dawo ki zauna kafin ranki ya ɓaci” murmushi kawai mom tayi bata so dady yasa baki ba.

rai a ɓace ta nufi wajen zamanta zata zauna
“jeki kawai” Abban ya faɗa,babu ko kunya ta juya ta fice,kauda kai kawai dady yayi da alama baiji daɗi ba,kallonshi Abbah yayi yana sakin murmushi haɗi da girgiza kai.

A bakin ƙofa Aunty Safeenah taci karo da su Yumnah, fuskar su ɗauke da murmushi su ka gaishe ta,ta amsa ma kowa amma banda Yumnah da Nainarh da tabi da wani irin kallo mai wuyar fassarawa.


hankali Nainarh ba ƙaramin tashi yayi ba da irin kallon da Aunty Safeenah tayi mata,duk sai taji wani iri dama ba tayi niyyar zuwa ba Yumnah ta jawota tasan dama ba dole bane dangin Yumnah su sota ba.


ganin yanayin data shiga ne yasa Fa'iza kamo hannunta cikin nata,da murmushi akan fuskarta tace “muje ko”
tura ƙofar parlorn tayi su ka shiga bakin su ɗauke da sallama,gaba ɗaya parlorn su ka kai duban su gare su.


Amsa masu sallamar su kayi in ka cire uncle mutallaf daya kafe Nainarh da ido ko ƙyaftawa baya yi uncle Ahmad ma kallon sani yake mata,har suka ƙaraso cikin parlorn uncle mutallaf bai janye idanunshi daga kanta ba har sai da Abbah yayi mashi gyaran murya tukun yayi sauri kauda idoshi daga kanta ya kalli Abban,hararar wasa Abbah ya watsa mashi.


saurin duƙar da kai yayi duk sai yaji kunyar kamashin da Abbah yayi yana kallonta yasan Abbah zaiyi tunanin wani abu shi kuwa har ga Allah kama tayi mashi da wacce ya sani.


zama su kayi kan rug carpet ɗin cikin kulawa su ka gaishe da su suna amsa masu,nuna Nainarh Abbah yayi da hannu
“in ku ka samu wannan mai kama da mariyata?” gaba ɗayan su suka kai duban su ga Nainarh sai da Abbah ya faɗa su kaga kamaninta da Aunty mariya in ka cire mom da dady dan su sunfi ganin kamaninta da Carol ƙanwar mom,sai yanzu uncle mutallaf ya fahimci da wacce take mashi kama.


kallo ɗaya Irfan da barrister suka yi mata suka kauda kai
“ƴan mata yaya sunan ki?” Aunty mariya ta faɗa tana kallon Nainarh
“NAINARH” ta bata amsa,jinjina kai Aunty mariya tayi “masha Allah, Nainarh suna mai daɗi” Aunty mariya ta faɗa, murmushi Nainarh ta saki a hankali ta furta “nagode”



juyawa Aunty mariya tayi ta kalli mom,fahimtar abunda Aunty mariya ke nufi ne yasa mom faɗin “ɗiyar Asma'u ce”

“Allah sarki” Abbah ya faɗa cike da jin tausayin Nainarh,babu wanda baiji tausayinta ba jin itace ɗiyar Hajiya Asma'u, barrister Hashim kuwa ko a jikinshi.


“sannu kinji Nainarh Allah ya kuɓutar da mahaifiyar ki” a cewar Abbah ,gaba ɗaya parlorn su ka amsa da “Ameen ya Allah” fira suka shiga yi cikin kwanciyar hankali.


Noor tunda su ka shigo Irfan ke Binta da wani irin narkaken kallo,itama tunda ta zauna hankalin ta na kanshi,wasu alamomi yake mata da ido wanda daga ita sai shi su ka san ma'anar su,sosai su ka shagala da kallon juna ƙarshe da su ka gaji tashi Irfan ɗin yayi ya nufi ƙofar fita shida Waseef ,zambur ta miƙe tabi bayan su babu wanda ya lura da ita sai Yumnah da Kairiyyah dake kusa da ita.

A parlor Waseef ya tsaya Irfan kuma ya nufi back yard,wassef na zaune sai ga Noor,nufoshi tayi cikin takun sauri “ya Waseef yana ina?”


“back yard” ya bata amsa,da sauri ta nufi ƙofar da zata sadata da back yard ɗin gidan, gyara zaman shi yayi kan sofa yana ciro wayar shi daga Aljihu.



tun daga nesa ta hango shi ya jingina da wall gaba ɗaya hannuwanshi na cikin Aljihun wandon shaddarshi, idanunshi a lumshe suke kamar mai bacci,a hanzarce ta ƙarasa in da yake tun kafin tayi magana ƙamshin turarenta ya sanar da shi isowar ta,a hankali ya buɗe idanunshi a kanta.


wani irin kallo ya shiga binta da shi yayin da ita kuma ta marairaice mashi fuska kamar zata sa mashi kuka.



“shine daka shigo kayi kamar baka ganni ba ko?” ta faɗa a shagwaɓe,buɗe mata hannuwanshi yayi alamar ta zo gare shi, ba tayi musu ba ta nufe shi,faɗawa tayi jikin shi, hugging ɗin juna su kayi tightly kamar za su koma abu ɗaya.


matso da baƙin shi yayi saitin kunnenta,magana ya fara yi mata kamar mai raɗa
“duk laifinki ne miyasa kin san tare za ku zo da dady baki faɗa man ba,kin san yanda nayi kewarki kuwa?”

“ina so nayi surprising ɗin ka ne shiyyasa”ta faɗa a shagwaɓe
“kinyi missing ɗin na?”
“sosai ma,har gani nake kamar bama sauri da muna tafiya”

“amma shine baki nemi ni ba ki ka zo part ɗin Abbah?”
“saboda na san anan zan same ka”
“da ban zo ba fa?”
“nama san bazaka ƙi zuwa ba”


raba jikin su yayi yana jan hannunta su ka nufi wasu haɗaɗun chairs dake back yard ɗin,zama yayi saman ɗaya daga cikin kujerun yana nuna mata ta kusa da shi,maƙe mashi kafaɗa tayi alamar bazata zauna ba,hannunshi ya miƙa mata babu musu ta kama jawota yayi zuwa jikinshi yayi mata mazauni akan laps ɗin shi, murmushi ta saki tana lafewa a jikin shi.


shafa doguwar sumar kanta dake a buɗe ya shigayi yayin da ita kuma tayi lamo har wani lumshe ido take.



*😳 Irfan⁉️*



idan mu ka koma parlorn Abbah,sun jima suna fira sai da lokacin zuwa masallaci yayi tukun su ka tashi,ficewa mom tayi tare da su Aunty Mariya da su Yumnah, wani ɗan corridor dake kallon parlorn Abbah su ka nufa.


wani irin hamshaƙin parlorn ne su ka shigo,yaji kayan alatu kamar a gidan sarakai,ga wasu jigunannun sofas masu rai da lafiya har set biyu.


Aunty Safeenah ce zaune saman sofa mai mazaunin mutum uku yayin da mamy ke hakimce kusa da ita ta ɗau wankan less ɗinkin riga da zani kamar ko wane lokaci zaka samu fuskarta da makeup,sofa dake kusa da su Hajiya fatilah ce matar uncle mutallaf tare da Hajiya Halima matar Uncle Ubaid sun ɗau wankan tsadadden less mai shegen kyau,fuskarnan ta su tasha makeup hannuwan su a cike su ka da ƴan hannu da zobba na zallar zinari.


Mama Ameena ce hakimce saman sofa mai mazaunin mutum biyu dake kallon ƙofar shigowa parlorn,super atamface a jikinta anyi mata ɗinkin riga da zani kalar na su na tsaffi,ta dafka uban ɗaurin ɗankwalinta kamar koda yaushe.


cikin parlorn su mom su ka nufo bakin su ɗauke da sallama,tsuke fuska mama tayi lokacin da idanunta su ka sauka kan mom,taɓe baki mamy tayi tana kauda kai.


Amsa masu sallamar su kayi in ka cire mamy dake cin ɗaci sai wani buɗar hanci take,
har gaban sofar da mama take zaune mom ta ƙara so,cikin girmamawa ta gaishe da ita,cike da izza tana wani yamutse fuska ta amsa mata a taƙaice,lamarin yaba Nainarh mamaki ita da abun ya zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login