Showing 15001 words to 18000 words out of 88290 words
wuce masu matuƙar kyau wanda tsayawa fayyace su har littafin ya ƙare ba'a gama faɗar kyawu da haɗuwar su ba, tsayawa elevator yayi da alama sun kawo in da za su tsaya, ƙofar ce ta shiga zugewa,sai data gama zugewa tas tukun tasa kai ta fice ma'aikatan na biye da ita kamar wasu jela.
nan ma wani katafaren parlorn ne su ka shigo wanda yafi na farkon haɗuwa sai dai bai kaishi girma ba,ma'aikatan ne nan ma ke kai kawo, take su ka shiga zubewa ƙasa suna gaishe da ita, hannu kawai ta ɗaga masu yayin da take yin gaba, a bakin wata katafariyar ƙofa su ka dakata, ɗaya daga cikin matan ce tayi saurin miƙa mata wayarta dake hannunta, amsa tayi yayin da take ɗaura tafin hanunta saman na'urar dake jikin ƙofar, zanen hannunta ne ya fito a jikin na'urar ,scanning hannunta na'urar ta shigayi na tsawan secon biyar kafin na'urar ta fara magana kamar ta ƙofar da su ka fara shigowa yayin da ƙofar ke zugewa.
sai da ƙofar ta gama zugewa tas tukun ta kunna kai zuwa ciki yayin da matan guda biyu ke biye da ita sauran su ka kama gaban su, wacce ke ɗauke da backpack ce ta bi bayanta sai ɗaya wacce take riƙe da towel ɗin data goge mata jiki.
wani irin katafaren bedroom su ka shigo a ƙalla girman shi ya isa ayi ɗan ƙaramin plat house saboda girma da faɗin shi, bedroom ɗin yana ɗauke da king size bed light golding, gadon na shimfiɗe da tattausan bedsheet da ƙaton blanket mai azabebben taushi ga jerin pillows wanda su ka kusa cinye kwata gadon,
gefe da gefen gadon nightstand ne mai ɗauke bed sides lamps daga gaban gadon ottoman table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi daga saman shi anyi mashi kwalliya da wasu stones masu sheƙi an mamman a jikin shi.
daga ƙasan gadon wani haɗaɗɗe rug ne mai gashi gashi a jikin shi tsabar taushin shi har bacci mutum zai iya a kanshi ba tare da ya fahimci ba'a katifa yake ba,idan ka kalli saman ɗakin wani irin ƙaton chandeliers ne,daga hannun dama na ɗakin glass sliding door ce wanda nan ma wani bedroom ɗin ne sai dai komai na cikin shi white color ne, daga ɗayan ɓangaren kuma wani haɗaɗen stairs case ne can ma saman wani bedroom ɗin ne sai dai bai kai wannan dana kusa da shi girma ba, daga ɓangaren haggun ɗakin wasu ƙofofi ne guda uku a jere ɗaya bathroom sai spa and saloon wanda yake haɗe massege spa sai ɗaya ƙofar dressing room ne wanda idan ka shiga cikin shi zaka ɗauka boutique ne.
wacce ke goye da back pack ɗin ce ta nufi laundry room,ɗurƙusawa ɗayar tayi a gabanta takalamin ƙafarta ta shiga cire mata, zama tayi saman ɗan stool hakan ya bata dama wurin cire mata takalmin, bayan data gama cire takalmin,sama nailarh ta ɗaga hannunta hakan yaba matar damar cire mata rigar dake jikinta tayi ta barta daga ita sai bra ta ajiye gefe kafin ta koma kan wandon, wandon shima zame mata shi tayi shantala shantalan cinyoyinta ne su ka bayyana farare tas da su sai sheƙi su ke kai kace haske rana bai taɓa ratsasu ba,kwashe kayan matar tayi ta nufi laundry room da su,a tare su ka fito daga laundry room ɗin ita da wacce ta fara shiga sallama su kayi mata su ka fice daga ɗakin.
A kasalance ta shiga taka ƙafafunta tana nufar ƙofar toilet, tafiya take kamar bata son gaka ƙasa tana tafiya ko ina na jikinta na juyawa musamman ƙugunta da zanen rose flower na tattoo ya ƙarama fatar bayanta kyau,tun kafin ta ƙaraso bakin ƙofar ta shiga zugewa kutsa kai tayi ciki,wani irin bathroom mai girman gaske komai na cikin shi expensive ne,harda silver bed mai ɗauke da rober mattress mai haɗe da pillow sai daga jikin bangon toilet ɗin glass drawer ce mai girman gaske an rarrabata gida gida wanda bakomai ne a cikinta ba sai tarin shower gels,soaps,shampoos, towels, bathrobes,sponges da flip flops.
ƙofa biyu ce a toilet ɗin da wadda ta shigo sai wata dake can ɗayan ɓan garen , silver bed ɗin ta nufa kwanciya tayi rub da ciki tana sauke ajiyar zuciya,wasu irin abubuwa ne a jikin ɗayar ƙofar masu kama da bulbs haske su ka shiga kawowa suna fitar da wani irin sauti can kuma su ka daina suna sanar da isowar lolah da larah,a hankali ta furta open ba tare da ta ɗago ba, zugewa ƙofar ta shiga yi, wasu matan turawa ne su ka shigo manya da su kamar ƴan wrestling,baƙin mini skirt ne a jikin su tare da farar shirt ajikin rigunan su an rubata sunayen su da wani irin style, haka shigar ma'aikatan gidan take.
in da take su ka ƙaraso gaishe da ita su kayi suna ɗan rissinawa,bata amsa masu ba hakan bai dame su ba idan da sabo sun saba da halin uwar gidan ta su,lolah ce ta nufi glass drawer ɗin nan, buɗewa tayi ta ɗauko shower gel tare da soap da shampoo da sponge,a saman wani ɗan table mai ƙafafu ta ɗaura, maida ƙofar drawer tayi ta rufe turo table ɗin tayi zuwa gaban bed ɗin, ɗaukar shampoo larah tayi, buɗe marfin tayi ta shiga tsiyayama Nailarh shi a kai, bayan data gama ne tashiga cuɗa mata kan sai data tabbatar ya wanku tukun ta jawo hand shower ta shiga wanke mata kan, bayan data gama ne ta ɗauki shower gel ta shiga zubawa a ko ina na jikin Nailarh,sponge sock lolah ta saka a hannun ta larah na gama zuba shower gel ɗin ta shiga mulka mata mashi a ko ina na jikinta, ko motsi Nailarh ba tayi kamar matatta su ke juyata yanda su ke so dan su wanko ko ina na jikinta.
sangarta da gata ne yasa Nailarh ko wanka bata ma kanta ba wai dan bata iya ba isa ce kawai da lalacewa tasa bata iya yi da kanta musammusam ta ajiye lolah da larah dan su riƙa yi mata wanka wanda aikin su ke nan a gidan, daga wankan ta da yi mata massege sai gyaran jiki babu abun da su ke iya aikin su kenan.
ta ɗauki tsawan lokaci tana cuɗa mata jikinta sai data tabbatar ko ina na jikinta ya wanku tukun larah ta jawo hand shower ta shiga wanke mata jikin bayan data gama ne ta ɗauko hairdryer ta shiga busar mata da gashin kanta bayan data kammala busar mata da kan ta nufi glass drawer ɗin nan ta ɗauko bathrobe da flip flops ta dawo a bakin bed ɗin ta ajiye mata, a kasalance Nailarh ta sauko daga saman bed ɗin,flip flops ɗin ta zura a ƙafarta, miƙa mata bathrobe ɗin tayi , ƙarɓa tayi da kanta ta zura kafin ta cire hook ɗin bra ɗin dake jikinta ta ciro a ƙasa ta yarda ita kafin ta warware igiyar pant ɗin shima nan ƙasa ta sake shi, igiyar bathrobe ɗin ta ɗaure ƙofar fita ta nufa ba tare da ta ko kalli ɗaya daga cikin su ba.
bra da pant ɗin lolah ta kwashe ta nufi dustbin ta saka Nailarh tana da wata ɗabi'a ta rashin maimaita sutura idan har kaga ta maimaita sutura to ba ƙaramin sonta take ba bra da pant dama su daga idan ta cire su to sun zama wasted bata ƙara amfani da su,gyra toilet ɗin su kayi su ka maida komai mazaunin shi sannan su ka wanke toilet ɗin duk da ba datti yayi ba bayan da su ka gama ƙofar da su ka shigo su ka nufa tun kafin su isa ƙofar ta buɗe alamar an basu izinin fita, ficewa su kayi.
Nailarh tana fita daga toilet ɗin wannan sliding glass door ɗin ta nufa tana isowa ƙofar na buɗewa, ciki ta kutsa kai sai wani lumshe ido take, nan ma bedroom ne komai na cikin shi white color ne , babu wata hayaniya a cikin shi bed ne sai nightstand dake ɗauke da bedside lamps sai rug mai taushi dake shimfiɗe a ƙasa sai chaise lounge chair dake bakin wata ƙatuwar glass sliding door wacce da an buɗeta zata sadaka da ƙyataccen swimming pool wand kusan haɗe yake da ɗakin ƙofar ce kawai ta raba su sai ruwan da suke a kewaye daga bakin swimming pool ɗin lounger chairs ne guda biyu suna fuskantar juna sai daga can ɗan nesa da su ball chair ce daga gabanta ɗan madaidaicin glass table ne.
nightstand ɗin ta nufa ear phone ɗin dake ajiye ta ɗauka tare da eye mask,bed ɗin ta dawo a kune ta sa ear phone ɗin kafin ta rufe idonta da mask ɗin, faɗawa tayi saman bed ɗin ta ɗaura kanta saman pillow tana saka ɗaya tsakankanin cinyoyinta yayin da ta rungume ɗaya a haka bacci yayi awan gaba da ita yayin da waƙar data kunna a ear phone take ratsa ƙwaƙwalwarta, Al'adarta ce bacci tana sauraron sauti.
_*ABUJA . NIGERIA*_
_*G J I ESTATE*_
momy da laatifa ne zaune saman sofa da alama fita za su yi,momy ta ɗau wankan swiss lace maroon color ta yafa mayafi saman kanta, wayace kare a kunenta da alama waya take laatifa na daga gefenta zaune saman sofa mai mazaunin mutum ɗaya ta ɗau wankan black abaya tayi rolling da gyalenta simple make_up ne a fuskarta sai medical glass ɗinta dake ƙarama kyakyawar fuskarta kyau,wayar tace riƙe a hanunta tana aikin latsawa, janye wayar momy tayi daga kunenta tana ɗan jan tsaki
“du kace zaka fita tare da Balqis sai ta ɓata maka lokaci,gaskiya tafiya zanyi na barku ni driver ya kaini idan ta gama shiriritar kun ta ho”
momy ta faɗa tana miƙewa tsaye ta ɗauki hand bag ɗinta, tashi laatifa tayi itama tana ɗaukar hand bag ɗin ta “baza ki tafi ki barni ba momy, tare zamu tafi ita driver ya kaita
“gani nan bama sai an tafi an barni ba” Balqis ta faɗa yayin da take taka stairs case tana nufo parlorn, Abaya ce a jikinta tayi rolling gyalen kamar yanda laatifa tayi tana riƙe da hand bag a hannunta fuskarta tasha uban make_up ba ƙaramin kyau tayi ba.
harara momy ta watsa mata tana nufar ƙofar fita daga parlorn, murmushi Balqis ta saki yayin da ta ƙarasowa cikin parlorn, bin bayan momy su kayi,a parking space su ka sameta har ta buɗe back seat na wata ɓakar Acura ta shiga,ƙarasowa su kayi laatifa ta shiga driver seat yayin da Balqis ta buɗe front seat kusa da laatifa ta shiga, babu ɓata lokaci laatifa tayi ma motar key haɗi da reverse, cikin Estate ɗin su ka nufa tafiya su kayi mai ɗan nisa, parking space ɗin gidan dady su ka nufa, parking laatifa tayi haɗi da kashe motar, momy ta fara fitowa sannan sai Balqis, momy bata tsaya jiran su ba ta nufi main entrance ɗin villa ɗin,fitowa laatifa tayi a tare su ka jera zuwa entrance ɗin a lokacin da su ka ƙaraso har ƙofar ta buɗe alamar an basu izinin shiga.
a tare su ka kutsa kai, babu kowa a parlorn sai jefi jefin ma'aikata dake kai kawo, gaishe da su su ka shiga yi cikin kulawa momy da laatifa su ka shiga amasawa yayin da Balqis ko kallon banza ba su isheta ba, glass elevator dake parlorn ta ɓangaren mom su ka nufa,laatifa ta danna nombobin dake jikin elevator ɗin,zugewa ƙofar tayi, momy ta fara shiga kafin su ka bi bayanta rufewa ƙofar tayi elevator tayi sama da su.
ba su samu kowa a main parlorn mom ba hakan yasa su ka nufi ɗayan parlorn,yumnah da fa'iza su ka samu zaune a parlorn kowacce ta tasa waya a gaba sai aikin latsawa take ba su jima da dawowa daga prison ba duba jikin mahaifiyar nainarh, bakin su ɗauke da sallama su ka ƙarasa ciki, ɗagowa su kayi suna amsa masu sallamar da gudu yumnah ta taso ta nufi momy faɗawa tayi jikinta tana faɗin oyoyo, murmushi momy ta saki tana shafa bayanta.
“sannu da zuwa momy, ina wuni , yanzu mom ta shiga ciki”
“lafiya lau Alhmdllh ya hutu” da Alhmdllh yumnah ta amsa yayin da take raba jikin su gaishe da momy fa'iza tayi cikin kulawa momy ta amasa mata tana faɗin
“yan hutu, shine har yau banga ƙafarku ba ko” sunnar dai fa'iza tayi tana sakin murmushi
yumnah da sauri ta nufi laatifa buɗe mata hannuwa laatifa tayi tana sakar mata murmushi da sauri ta ƙarasa gabanta faɗawa tayi jikinta tana faɗin
“nayi missing ɗinki sosai Aunty laatifa” murmushi laatifa tayi tana shafa bayanta
“nima nayi missing ɗinki, ya hutu”
“hutu ya kusa ƙarewa” yumnah ta faɗa yayin da suke raba jikin su, taɓe fuska Balqis tayi tana nufar ƙofar bedroom ɗin mom yayin da take faɗin
“ni bari nayi ciki tunda babu wanda yayi missing ɗin na dama banyi na mutum ba” dariya gaba ɗayan su ka saki saboda sun san bakomai yasa Balqis faɗin haka sai tsabar kishi saboda babu wanda yayi mata oyoyo
“Aunty Balqis ai ni mun haɗu a court shiyyasa ban yi maki oyoyo ba” yumnah ta faɗa, murmushi fa'iza ta tayi tana faɗin “ke nan dai wannan faɗan dani ake, to Allah ya huci zuciyarki ƴar uwa nayi kewarki ya ki ke”
ya mutse fuska Balqis tayi tana faɗin “lafiya” dariya gaba ɗayan su suka saki ganin yanda ta amsa bayan abun da take so kenan, girgiza kai momy tayi tana nufar sofa ta zauna, ƙofar bedroom ɗin mom Balqis ta buɗe ta shiga,zama laatifa da Yumnah su kayi fa'iza itama zama tayi yayin da take gaishe da laatifa, cikin kulawa ta amsa mata, fira su ka shiga taɓawa.
Mom ce ta fito hannunta riƙe dana Balqis dake sakin murmushi, da sauri laatifa ta miƙe sakin hannun Balqis mom tayi tana buɗe ma laatifa hannuwanta alamar ta zo gareta, laatifa ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta ƙarasa ga mom ɗin, hugging ɗinta tayi fukarta ɗauke da murmushi
“mom ina wuni, mun same ku lafiya”
“lafiya lau agogo sarkin aiki” mom ta faɗa yayin da take raba jikin su, ɓata fuska laatifa tayi tana faɗin “mom kema haka za ki ce”
dariya Balqis tayi tana faɗin
“wallahi mom gaskiya ki ka faɗa Aunty laatifa bata saurarama aiki” momy na daga zaune,murmushi ta saki a ranta tana faɗin sarakai za ku fara
“ai ba sai kin faɗa ba Balqis na santa ne” mom ta faɗa
“shikenan mom tunda kema haka za kice” laatifa ta faɗa tana komawa mazauninta
“wasa nake maki laatifa ai aiki abu ne mai kyau” murmushi laatifa ta saki jin mom wasa take mata itafa babu abun da ta tsana sama da ace mata ta cika nacema aiki.
sofa da momy take zaune mom ta nufa, tashi momy tayi su kayi hugging ɗin juna kafin su ka raba jikin su fuskokin su ɗauke da murmushi, gaishe da juna su ka shiga yi cikin kulawa yayin da suke samun wurin zama su ka zauna,masu aiki fa'iza ta kira dan su kawo ma su momy abun sha ta hanyar landline ɗin kitchen.
fira sosai su ka shiga yi a tsakaninsu momy na jajanta ma mom abun da ya faru da aminiyarta hajiya Asma'u,tambayar mom momy tayi ina ɗiyar hajiya Asma'u take
“tunda mu ka dawo daga prison wajen mahaifiyarta ta shige ciki bata jin daɗi,yumnah je ki kira man ita” mom ta faɗa, har yumnah ta miƙe fa'iza tayi saurin tashin tana faɗin “bari na kira ta”ta faɗa tana nufar corridor da zai sada ka da bedroom ɗin yumnah, tura ƙofar bedroom ɗin tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
bedroom ɗin yana da girma sosai, king size bed ne a cikin shi mai matuƙar kyau gefe da gefen shi nightstand ne mai ɗauke da bedside lamps,daga saman headboard ɗin bed ɗin ƴar rumfa ce mai haɗe da sparkling bulbs,sai ƙaton dressing mirror an cika gaban shi da body lotion da perfume masu dadda ɗan ƙamshi da tsadar gaske, tsakar ɗakin shimfiɗe yake rug carpet.
daga bakin sliding door glass balls chairs ne guda biyu suna kallon juna, daga wajen door ɗin ƴar baranda ce mai ɗauke da chairs guda biyu tsakiyar su round table ne daga nan kana iya hangen cikin estate ɗin da swimming pool dake cikin garden ɗin gidan.
A kwance fa'iza ta hangota saman makeken gadon ta rufe jikinta da duvet, bakin bed ɗin fa'iza ta ƙarasa pillow da take kwance ta ɗan bubbuga tana kiran sunanta, a hankali ta shiga buɗe idanuwanta da su kayi mata ɗauyi ga wani irin azabebben ciwo da kanta yake yi mata
“ki tashi mom na parlor tana kiran ki”pro khaki eyes ɗinta ta sauke akan fuskar fa'iza da tayi maganar,eyes ɗin sun ɗanyi jajja jajja saboda baccin data fara ga ciwan kai.
A hankali ta tashi zaune hanunta dafe da kanta, matsawa fa'iza tayi tana bata hanya dan ta samu damar saukowa, a hankali ta zuro da fararen ƙafafunta ƙasa,rober gown ce a jikinta ,rigar ta kamata ta bayyanar da surar jikinta,kanta babu ɗan kwali, water wave hair ɗinta har gadon bayanta ya sauka, gashin duk ya ɗan yamutse saboda bai samu gyara kwana biyu ba,sannu fa'iza ta shiga yi ma mata yayin da take binta da kallon ba ƙaramin tafiya da ita kyan nainarh yayi ba yarinyar ce Allah ya zuba mata kyau ko mace ƴar uwarta ta kalleta sai ta sake kallon, hijab ɗin ta dake kan bed ɗin ta ɗauka ta zura a jikinta.
“muje”fa'iza ta faɗa, gaba nainarh tayi fa'iza na biye da ita, a hankali take taka ƙasa kamar zata faɗi saboda rashin ƙwarin jikinta,tunda su ka shigo parlor momy da laatifa ke bin nainarh da kallo har su ka ƙaraso ciki, wurin mom nainarh ta nufa tana faɗin mom gani, momy ta nuna mata tana faɗin “ga momyn su laatifa nan kun gaisa” sai a sannan nainarh ta kai dubanta ga momy.
gaishe da ita tayi cikin kulawa momy ta amsa mata tana faɗin“ ya jikin ki naji ance ba ki jin daɗi”
“da sauki